← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 112

Sashe 64

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aayaann ya fara basu labarin tun randa haidar yazo ya kaishi kauyen su hassu har zuwa kaisu England dayiwa Sarfraz aiki da kuma dawowarsu..

Daddyn sarfraz ne ya numfasa Sannan yace "Lallai Aayaan kai kyauta ce daga Ubangiji Allah, waye zai iya irin wannan sadaukarwar? Irin wannan kashe kuɗi Haka, lallai kai ɗin na daban ne, kuma in'sha Allah zaka gama da duniya lafiya. Godiya sosai da addu'oi Daddy yayita yi mishi.

Shikam SARFRAZ jingim yayi yana ganin shikuwa mezaiyiwa Aayaan ya biya shi Irin wannan sadaukarwar da yayi mishi, kuma gaba ɗaya ya shiga rudani akan Aayann ɗin wanene a gurinshi.

Kamar Daddy yasan me sarfraz yake tunani, kallon sarfraz yayi yace "kasan wadannan su waye a wajen ka?

Girgiza kai sarfraz yayi tare da cewa "daddy ban saniba Amma dai yaya Aayaan yace shi yayana ne!

"Tabbas shi yayan kane kuma me kaunarka ta haƙiƙa, domin halin daka shiga ba ƙaramin tashin hankali zamu fuskanta ba da munganka a lokacin, amma saboda hankali da tunani irin na Aayaan ya gwammace ya ɗauki komai nadaga tashin hankali da damuwa har zuwa kisan maƙudan kudade shi kadai, tabbas bakada kamarshi....

Labari Daddy yakeba sarfraz na aurenshi shida muntaz har zuwa sanda ta haifi sarfraz ɗin da kuma mutuwarta, gaba ɗaya falourn yayi shiru bakajin komai face saukar zuciya a hankali, duka kuwa idonsu cike yake da ƙwalla, barin mummyn sarfraz da Mummyn Aayaan.

Cigaba Daddy yayi har zuwansu mummy da bayyanar ita ɗin tagwayen muntaz ce, zuwa lokacin SARFRAZ yayi kuka har ya gaji, gaba ɗaya ji yayi Duniyar tayi mishi zafi ta ina zai soma rayuwa da sanin cewa ba Mummy bace Asalin wadda ta haife shi ba, ga wani irin girmanta daya ƙara cika mishi zuciya, lallai ita ɗin ta kwarai ce, don be taɓa fuskantar wani abu daga garetaba wanda zai nuna cewa ba ita ta haife shi ba....

Yanzu baida wani hope a rayuwarshi, ji yake komai nashi ya rushe, da sauri ya miƙe tare da cewa "ina Nawaz? Yaya Aayaann yace min anganta, don Allah Kada kucemin ba'a gantaba!

Murmushi Daddy yayi "ka kwantar da hankalinka anga Nawaz yanzu haka tana cikin ɗaki tana barci, bata jin dadin jikinta ne.

Aida sauri SARFRAZ yace daddy don Allah ka aura mini ita nan da sati daya, wallahi ina sonta, kuma bazan iya rayuwaba idan babu ita. Sannan yayi Hanyar ɗakin cikin hanzari don yaje ya ganta..

Daga Aayaan har hassu babu wanda zuciyarshi bata buga ba, Aayaan kam har wani tuƙuƙin wuta ne yaji ya maƙale mishi a wuya.

Mummy kam harta fara hasashen yadda zatasa Aayaan ya saki Nawaz ɗin don SARFRAZ ya aureta jin yace bazai iya rayuwaba idan babu ita.

Da sauri daddy ya dakatar da Sarfraz kafin ya ƙarasa ɗakin "SARFRAZ sai dai kayi hakuri domin Yanzu Nawaz matar aurece!

Cikin wani irin vibration safraz ya waigo Tare Da cewa wane ɗan kutumarrrrr uba ne ya auremin mata? To wallahi koda shine sarkin duniya saiya saketa, na rantse da Allah be isa yayi min wannan yankan kaunar ba, Nawaz ɗin tawa?

Wallahi banida lafiya ne, ina buƙatar addu'oin ku masoya

Sannan ina jiran comments da sharhi, yadda banida lafiyan nan na daure nayi muku typing kuma ku daure kuyi comment da sharhi.

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*57*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

"Ƙaniyarka Sarfraz! Nace ƙaniyarka!!, Kanada hankali Kuwa? Kallon Aayaan dady yayi sannan yace "Wai Aayaan nikam kodai yaron nan ya samu wata matsalar ne a kwakwalwa dadilin ciwon da yayi?

Kasancewar Aayaan ɗin nada shekaru kuma ya karanci rayuwa sai ya zamana koda ka kalleshi bazaka taɓa gane yana cikin tashin hankali ba, amma a baɗini kuwa shikadai yasan Yadda zuciyarshi ke tafarfasa.
"Daddy Allah duk gwaje gwajen da za'ayi anyi kuma an tabbatar kwakwalwar shi ta koma normal babu wata matsala.

"Eh Lallai! kenan iskancine yasa yake ƙunduma min ashariya a cikin gida, to Wallahi Sarfraz ka kiyayeni! saboda kai ɗan Gwal ne shiyasa mijinta zai saketa kai ka aureta, kuma naga ai Allah dakanshi yace saki halal ne amma bayasonshi.

Wato saboda wani shirmen banzan ka sai ayi abinda Allah bayaso Koh?

Aseey kam haushin sarfraz ne ya kamata, "wato a saketa! to sannu ɗan lu'ulu'u, idan ba lu'ulu'u ba taya Muna murnar munsamu gwarzuwa kazo zaka ja mana jarfa" abinda Aseey ke tunani a zuciyarta kenan, daga karshe ma tace "ka mutu mana! Ka daɗe baka mutunba, ya gama wahala dakai shine zakazo kuma kana ƙunduma mishi ashariya, don kaga yarinya gwanin kyau, ga komai da komai shine kake ganin da kai ta dace".

Mummyn sarfraz ce tace "haba fabulous meye kuma na zagi bayan kana kallon manya a gabanka, ai Nasha kai me hana wani ne idan kaji yanayi".

Ita kuwa hassu ji tajeyi kamar ta zunduma ihu, yanzu Sarfraz wata zai aura ya manta da ita kenan, shidai bandi zaune yake yana kallon ikon Allah.

Mummyn Aayaan kam tayi nisa cikin tunanin yadda zatasa Aayaan ya saki Nawaz ɗin salin alin, domin ita kallon sarfraz takeyi a matsayin mumtaz ɗinta, kuma duk duniya babu Abinda take ganin bazata iya yiwa mumtaz ba.

Ɗan ɗaga murya Aayaan yayi "sweet bro dawo, zo gurina, ka manta alƙawarin da mukayi nida kai? To yau zan fara amfani dashi.

Takowa Sarfraz yayi ya dawo gaban Aayaan ya tsaya.
"Ka tabbatar kana ƙaunar Nawaz? kuma zaka iya zama da ita har ƙarshen rayuwarka? Aayaann ke tambayar Sarfraz yana kallon Cikin idonshi.

"Eh yaya, wallahi ina matuƙar ƙaunarta! Sarfraz yace shima yana kallon Aayaan ɗin.

Miƙewa Aayaan yayi Tare Da cewa "Aunty Aseey zo muje, kaima Sarfraz tawo."

Mummyn Sarfraz ce tayi sauri ta miƙe Tare da cewa "kul Aayaan! Kul nace! Kada ka sake kayi abinda bashi bane, kadaiji na gaya maka.

Shima daddy cewa yayi "laillai Aayaan! Ina kallonka a matsayin me hankali, taya zakayi abinda Allah ma zaiyi fushi damu?

Kwantar da kai Aayaann yayi Tare Da cewa "Dad and mum pls trust me! I will never do something that all of us will regret, but I'm just trying to do something that will be a way to both of us.

Shiru kawai duka sukayi basuce komai ba, amma zuciyarsu na ɗan bugawa kada fa Aayaann ya saki Nawaz, ita kuma Mummy addu'a takeyi akan Allah ma yasa Aayaan ɗin ya haƙura da Nawaz ɗin ne.

Fita harabar gidan Aayaan yayi, Aseey da sarfraz suna biye dashi a baya har zuwa wani gefe inda aka Wadata da hasken lantarki duba da Lokacin dare yayi sosai "SARFRAZ inaso ka saurareni dakyau, yanzu zansa Aseey taje ta tawo da Nawaz nan gurin, Ni zan matsa inda bazata ganni ba.
Inaso ka tambayeta shin zata iya aurenka ta zauna dakai a matsayin miji? Ni kuma wallahi nayi maka alƙawarin har dai tace eh to Wallahi saika aureta duk wuya duk rintsi.

Murmushi SARFRAZ yayi "to yaya Nagode sosai, zan tambayeta.

Aseey kuwa baƙin cikin daya cika mata zuciya ji takeyi kamar ta kama SARFRAZ da duka, amma in'sha Allah tasan babu yanda za'ayi Nawaz ta yarda da wani SARFRAZ bayan tasan Aayaan mijin tane.

Tun kafin Aayaan ɗin ma yace taje ta kira Nawaz ta juya don kiranta, da sauri sauri ta isa falourn zata buɗe kofar dakin da Nawaz ke barci a ciki, dad ne ya kirata "zo nan Asiyah!"
Gaban dad Aseey ta ƙarasa tare da cewa "daddy gani"

"Asiyah ke babba ce, ko babu komai kin girmi Aayaan kuma kinyi aure har kin haihu, nasan ko iya nan aka tsaya za'a saki a jerin waɗanda suke da cikakken hankali kuma suka san babin rayuwa, don haka nake roƙo a gareki don girman Allah kada ki bari Aayaan ya saki Nawaz, idan kuma har ya saketa to bazan bashi laifin shi kaɗai ba, Wallahi har dake zan kalla da abin kuma bazan taɓa bari SARFRAZ ya auretaba har abada Kinga kenan kinjawa yarinya bata jiba bata ganiba.

Sosai Aseey taji maganar tayi mata nauyi kamar an ɗaura mata wani dutse ne akanta ga kuma wani irin bugawa da zuciyarta Keyi, "to Daddy in'sha Allah hakan bazai faruba.

"To Asiyah Nagode, Allah yayi miki albarka!.

"Ameen dady Nagode" Aseey tace tana kai dubanta gefen dasu Mummy suke zaune, gaba dayansu sunyi tagumi hannu bibbiyu, kana kallonsu zaka gane suna cikin tashin hankali mai girman gaske. Ita Mummyn SARFRAZ tana addu'a Allah yasa kada Aayann ya saki ƴar mutane saboda Sarfraz, ita kuma Mummyn Aayaan tana tararrabin ya za'a ƙare da Sarfraz idan Aayaan yaƙi sakin Nawaz?

Wucewa tayi zuwa Dakin, gaba ɗaya sai take jinta babu nauyi, ga duka gwuiwowinta sun sage, a zaune ta Tarar da Nawaz ɗin alamun yanzun ta tashi daga barcin, domin idonta ma be gama washewa daga barcin ba.

"Sister kin tashi?" Aseey tace tana ƙarasawa gefen Nawaz tare da zaunawa.

Murmushi Nawaz tayi "Eh Aunty na tashi, ina muhsin?

"Muhsien yayi barci, ya jikin naki?.

"Da sauƙi aunty, Nagode da nuna kulawa.

Kada ki damu ai kedin yar uwata tace, burina kullum na ganki cikin farin ciki da walwala. Gyaran murya Aseey tayi sannan taci gaba da cewa "Nawaz! Ina ƙaunarki, mummy tana ƙaunarki, ƙanina AAYAANN yana ƙaunarki kuma muhsien ma yana ƙaunarki, Don Allah Nawaz muma ki ƙaunacemu koda na second ɗaya ne!
Ayanzu Aayaan bashida sauran farincikin daya Wuce ke, tunda nake ban taɓa ganin Aayaan yaso wata ba, kuma ban taɓa jiba face a kanki, Nawaz don Allah ki zama ƴar halal ki maida Alkhairi ga wanda yayi miki Alkhairi.

Gaba ɗaya Nawaz ta shiga rudani, ta rasa meyasa Aseey keyi mata wadannan maganganun, numfasawa tayi sannan tace "Aunty nayi miki alkwari bazaki taɓa yin kuka daniba, Sannan nima ina ƙaunar ku kamar Yadda kuke ƙaunata, kuma a yanzu banida wani family da nake kusa dashi kuma suke nunamin ƙauna kamar naku familyn, And Game da yaya Aayaann ko naƙi Allah bazan taɓa watsa mishi ƙasa a ido ba, domin shidin ɗan halal ne kuma ya nunamin halalci.

Farinciki ne ya mamaye Aseey jin abinda Nawaz tace, tasan in'sha Allah Yanzu batada wata Matsala tanada tabbacin Nawaz bazata yarda ta amshi Sarfraz a matsayin masoyi ba.
Chapter 64 · 0% Book details