← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 112

Sashe 45

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa yayi ya danne ta "Okay bari nayi me gaba ɗaya Kinga sai Allah yafi sakawa shi mijin naki dakyau, kuma itama Mummy kyafi jin daɗin faɗa mata!

Hannu yasa da nufin ya zuge zip ɗin dake gaban rigar ta, aikuwa da sauri Nawaz ta ƙanƙame zip ɗin tana cewa "Don darajar Annabi kada ka buɗe Min riga, Wallahi na fasa faɗa, kuma ko dama bazan iya faɗa ba nadai ce ne saboda ka rabu Dani.

"Nop! Nikuma bazan iya haƙura ba" hannu yasa ya ɗage rigarta ta ƙasa.
Nawaz bata ankaraba sai jin _bare hand_ ɗinshi tayi a saman cinyarta, ai take wani irin shock ya ziyarci kwakwalwar ta.
Shima ta ɓangaren Aayaann Hakan ne ya faru, domin wani abu yaji tun daga yatsun kafarshi har cikin kwakwalwar shi, a Tare suka sauke nunfashi mai ɗumi.

Idon Nawaz duk ya cika da hawaye "yaya Aayaann kaga kai yayanane kuma wallahi ina girmama ka har cikin zuciyata, kuma na baka babban matsayi saboda ta sanadinka nake Raye har zuwa yanzu, don Allah kada ka yarda ruɗin zuciya yasa mu tafka abin kunyar dazai yita bibiyarmu har kabarinmu....

"Sosai Aayaann yaji daɗin maganganun Nawaz, kuma Hakan ya daɗa tabbatar mishi da hankalinta, sannan yasan cewa tana Ganin girmanshi sosai...

Cikin raunanniyar murya yace "Nagode sosai, kuma insha Allah zan kiyaye gaba, amma zaki bani abincin?

"Eh" Nawaz tace domin ta ƙosa ya ɗaga ta...
Aikuwa yana dagata har wani irin ajiyar zuciya tayi tana sauke nunfashi a hankali...

Warmers ɗin ya janyo gabanta da plate Sannan ya buɗe, kallonta yayi yace "All this for me? Naji Aseey tace ke kikayi mini, is she telling the truth?

"Eh Nina Yi" Nawaz tace cikin ƙosawa, gaba ɗaya ta ƙosa tabar ɗakin ga Wani nauyinshi da takeji bata soma yana kallonta, cewa yayi "Madam pls ayi feeding ɗina mana!

"Haba Don Allah, yanzu dambun naman ko meat pie 🥧 ɗin ne zan baka? Bayan kasan cewa basa ciyuwa da cokali Saida hannu!
Murmushi yayi "ai dama da hannun nakeso ki bani, amma pls a fara bani smoothie ɗin nasa saboda kamshin shi ya cika min hanci..

Banza tayi dashi ta dauki tumbler ta tsiyaya takai center bakinshi ba tare data ce komai ba. Shima yasan ya matsa mata shiyasa ya kafa bakinshi ba tare da yayi korafi ba, Saida yasha da yawa sannan ta cire yashaƙi iska sannan ta kara mayarwa, bayan ya shanyene ta matso da bowl ɗin wanke hannu ta wanke hannunta a ciki Sannan ta ɗibi dambun naman takai bakinshi, buɗe wa yayi ya amsa amma saiya riƙe hannunta a cikin bakin.

Kallonshi tayi "kaga ka sakin mini hannu"
"Bakiga na kasa Magana bane, smoothie ɗin ne yayi daɗi da yawa, saikuma da kika ƙara min da dambun naman nan naga bazan iya resisting ba, Gaskiya you are a good cook!

Zare hannunta tayi taci gaba da bashi, data lura ya ɗan ci da yawa sai ta dauko meat pie 🥧 guda ɗaya shima ta riƙa bashi a hankali harya cinye..

Bottle water ta buɗe ta kafa mishi a baki, nanma Saida yasha da yawa ta cire mishi ta ajiye sannan ta wanke hannunta.
Cewa tayi "iya abinda zan iya baka kenan, amma idan baka ƙoshiba zaka iya ƙarawa..

Janyo hannunta yayi da nufin ta faɗo jikinshi amma saita choge "ya mukayi dakai?
"Au na manta I'm sorry, Amma ya akayi kikasan gejin cikina?

Sham mur tayi Sannan tace "kintace kawai nayi"

"Masha Allah, shiyasa nake ƙara sonki saboda akwai ki da zurfin tunani.

Taɓe baki Nawaz tayi "Nidai kaga ɗaki zani"
Kallonta Aayaan yayi yana murmushi ƙasa ƙasa don ya gane kunyarsa takeji saboda Sam taƙi Bari su haɗa ido "Nan titi ne kenan?
Ɗago ido Nawaz tayi ai kuwa suka haɗa Ido, ɗaga mata gira yayi haɗe da kashe ido ɗaya "yadai?
Da sauri ta ɗauke kanta bata kuma Cewa komaiba don ita so take yi su rabu lafiya, amma taga take taken Aayaan bazai barta ba...

"Madam i love You! Please Don Allah ko 1% kisoni a cikin 100% danake Miki.
Banza tayi dashi, ai kuwa ya miƙe ya koma kusa da ita, riƙe mata hannu yayi "sweet heart Ina magana kinyi shiru meyasa?

"Shagwaɓe fuska tayi "Ni nace maka ɗaki zani! Pls ka barni na tafi.
"Okay to tashi muje na rakaki" da sauri Nawaz ta miƙe tana jin daɗi cikin ranta, don zata rabu da wahalar Aayaan.

Ai kuwa bata ankara ba taji Aayaan yayi wuff ya dauketa, yana dariya.

Yaya Aayaann pls ka saukeni don Allah, "bazan sauke kiba saina kaiki falour saboda nina daukoki daga can"
Sanin cewa ko me zatayi bazai sauketaba yasa tayi shiru don kada tace Wani abu ya fasa kaita...

Buɗe Kofar yayi ya nufi cikin falour yana cewa "I Love You... Pls kema kice You Love Me!

A tsakiyar faloun ya sauketa inda Mummyn SARFRAZ Da Mummyn Aayaan ne zaune suna hira, sai Aseey a gefe alamu ya nuna waya takeyi, MUHSIEN kuma yana barci a Saman two sitters couch...

Kunya da tashin hankalin da tunda take bata taɓa jin irinshi bane ya kamata, da ace ƙasa zata tsage ta faɗa ciki da hakan yafi mata daɗi fiye da komai.

Shikuwa ko a jikinshi sai murmushi yakeyi Sannan yace "sannunku mummies, Sanda na dawo Aunty Aseey tace kuna part ɗin daddy shiyasa ban muku sannu da gida ba...

Ita kuma Nawaz yana sakin Mata hannu ta kwasa a guje tayi ɗaki tana haki Kamar wadda ta yini gudu..

Kowa Saida yayi Daria, shikuma Aayaan yaɗan sauke kai yana murmushi, shidai kunyar Nawaz tana bashi sha'awa matuka... Yasan kuma Yanzu Kafin ta bari aganta sai an sha fama..

Balla mishi harara Mummy tayi "wai Aayaann yaushe ka zama mara Kunya kuma mara jin magana ne? Nace maka Babu ruwanka da yarinyar nan har sai randa nida kaina naji na gamsu, amma shine ka cicciɓeta ta karfi da yaji ka tafi da ita, saboda kai ga ILIYA ƊAN MAI ƘARFI ko?

Mummyn SARFRAZ ce tace "Don Allah ki rabu dashi mana, wai Duk dokar ta meye haka, Mutum da matarshi, kuma dai yanason kayarshi to meye na sa Miki wasu tsauraran sharuddan da Allah ma besa mishiba? Gaskiya nidai kirabu dashi..

Simi Simi Aayaan ya wuce ya tafi ɗaki, Aseey kam sai dariya takeyi tana toshe baki....
Balla mata harara Mum tayi sannan tace ai Nasan harda haɗin bakin ki, kuma kici gaba tunda duka kun maidani sa'ar ku.

Tunda Aayaan ya koma ɗaki yake murmushi, ya kasa yin komai dai ya juya nan ya juya chan akan makeken gadon SARFRAZ...
Wayar shi dake cikin aljihun wandon shi ce ta hau ƙara, cirowa yayi don yaga waye...
Murmushi yayi ganin Babban abokinshi kuma school, class, and course mate dinshi Wato Farouk , "Assalamu alaikum bross yadai?
Ta chan ɓangaren Farouk yace "soja mazan fama! Soja marmari daga nesa...... Ina fatan ba'a Filin yaƙi kake ba dai Koh?

"Oh Zaka Fara kenan Koh Farouk? Aayaann yace yana shafa ƙasumbarshi...

Da gaske nake akwai Magana ne Wallahi! Farouk yace cikin serious tone.....

"Okay to inaji! Ya akayi?

Gyaran murya Farouk yayi Sannan yace "dama Akwai wani patient ne da wasu Fulani suka kawo min shi, to lalularshi tayi kama data Shaheed wanda aka Kawo min chase ɗinshi last year.
To kuma kaga an kashe maƙudan kudade Kafin ya samu lafiya, kuma su waɗannan da alamun ko kobo basuda ita, shine nace musu zanyi maka magana idan da hali zan kirasu saboda na amshi lambar babansu....

"Ohhhh ayyyah ALLAH Sarki amma dai abin da sauƙi Koh? Eh da sauƙi saboda shi ba hauka yakeyiba sai dai abin nashi yayi kamar wanda yayi loosing ɗin memorinshi ne...

"Okay to inaga zuwa next week zamu Shigo garin, zanzo asibitin ayi duk Abinda ya dace sai a shirya fita waje dashi.

"Okay to, the billionaire Allah yaja kwana, ALLAH ya jikan baba...

AMEEN Aayaan yace Sannan suka ci gaba da hirar su ta matasa.....

°°°°°°°°

NAWAZ kam tunda ta shiga ɗaki ta kasa zaune ta kasa tsaye, gaba ɗaya zuface take karyo mata duk da sanyin gari da kuma sanyin A.c ɗin dake zagaye dakin..

Shawarar data yanke guda ɗaya itace zata gudu da asuba, domin wannan gagarumin abin Kunyar da Aayaan yasa suka aikata bazai barta ta iya kallon su mummy ba.

To masu karatu kunjifa, shin Nawaz zata samu damar guduwa kuwa, sannan Aayaan zai haɗu da SARFRAZ ko kuwa saɓani zasu kuma yi????

Ku biyoni shafi ba gaba don jin Yadda zata kaya....

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 45*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

Haka Nawaz ta yini a ɗaki ko abinci bata ciba, tana tsoron fita falourn saboda kada ta haɗu dasu mumy.

Sai da Aseey taga abin dagaske ne sannan ta samu ta dafa mata Noodles ta kawo mata, da kyar Nawaz ta tashi ta amsa, Saboda kwanciya tayi ta rufe da duvet.

Aayaan kam yana chan yana fama da muhsien, wai dole sai sunje yawo gashi kuma shi sam bayason fita yau, yanaso yaɗan huta kafin al'asar...

Hakanan dai daƙyar ya samu yayi mishi wayau akan zai kaishi gobe, sannan ya zuge back pack dinshi ya kwaso chocolate ya haɗa shi dasu.

A Ranar kam kowa Saida jikinshi ya gaya mishi da yunwa, kasancewar dama Nawaz ce keyin girkin sai kowa ya sakankance.
Sai wajen ƙarfe biyu da hantsi ya dubi ludayi shine Aseey ta leƙa kitchen ɗin ta dafa Noodles da kwai, haka kowa yaci don sun san mai dafawar bazata fitoba balle su sa ran samun abincinta.

Ko bayan da Aseey ta dame ta akan ta tashi taci abincin hakanan ta ɗaure fuska "Aunty a Gaskiya Abinda kikayi baki kyautaba, kinsan dai babu kyau namijin daba muharraminka ba ya riƙa taɓa maka jiki amma kina kallo ya Aayaan yana daukaka kuma a matsayinki na Babba baki tsawatar mishi ba...

"I am sorry dear! Bazaki gane komaiba har sai an sanar dake, amma bani keda wannan damar ba sai dai idan zaki tambayi Mummy ita zata feɗe Miki biri har wutsiya.
Chapter 45 · 0% Book details