← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 112

Sashe 25

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai Nawaz tana bayi tana wanka, koda ta fito tsayawa tayi gaban dressing mirror, lotion ta shafa sai light blonde powder data shafa kaɗan a fuskarta, tadansa wet lips me kyalli da bakin kwalli a idonta.
Ita kanta Sai taga tayi wa kanta kyau... Ga idonta yayi wani haske madaidaicin lebenta yayi kyau kamar tasa light pink ɗin lipstick me ƙyalli.
Ta daɗe a gaban closet ɗin, shahada tayi ya buɗe.
Wow abin gwanin ban sha'awa, gefen komai daban, laces, Atampa, Materials, Shadda, Hijabs, wandina da tops masu kyau, Abaya, lafaya, Shoes, komai dai gasuna .

Idonta ne ya faɗa kan wata abaya ja anyi mata aiki a hannu da kirji da bayanta, Sannan anbi jikin aikin da Stones...

Cireta tayi a jikin hanger ɗin tana addu'ar Allah yasa tayi mata dai dai.
Pant ta zaba da bra masu kyau tasa sannan ta saka abayar, Saida tayi tsallen murna ganin rigar tayi mata daidai kamar an gwadata...

Gaban mirror ta koma tana kallon kanta tana murmushi, sai sannan taga dan ƙaramin akwatin dan kunnaye, budewa tayi suma da yawa, nan dai ta zabi wani fashion Golden colour me baza.

Taje kanta tayi ta maida ribbon dinta...
Sannan tayi rolling din gyalen, kasan cewar yadin rigar irin mirror ɗin nanne sai tabi jikinta ta fidda shape dinta mekyau musamman kirjinta sai kuma wajen hips dinta da ya buɗe kamar faranti.

Har zata fita sai ta tuna ya kamata tasa takalmi, closet din ta buɗe, da kyar ta samu wani flat Golden colour me stones tasa sannan tayi hanyar fita.

Dai dai nan Aayaan ya gama cin abincin shi ya mike, mum bari na shiga na kwanta,
"Stop Aayaan kada ka kwanta Please inaso akai Nawaz gida yanzu saboda hankalin ta ya kwanta suma ƴan gidan nasu ya kwanta susan tana raye.
Inyaso sai mu rokesu mu dawo da ita sai ku tafi Abujan koh?

"To" kawai yace ya shige daki domin shi yanzu mum ma mamaki take bashi...

Yana shiga Nawaz na fitowa, tsaye mummy tayi tana kare mata kallon "tabarakallahu ahsanal kaliƙin, ashe kwatakwata da bataga kamaiba a kyaun Nawaz.
Lallai kam bazata bari Wannan kyakkyawar hajar ta wuce ɗanta ba, duk da ta lura shi ɗin ɗan tijarane...

Tarbo ta tayi "Masha Allah, Masha Allah, yarinyata kinga kyaun da kikayi kuwa, gaskiya kinyi kyau...

Ki zauna kici abinci kafin Aayaan yayi wanka saimu tafi koh?

Murmushi Nawaz tayi "To Amma Nagode Allah ya saka da Alkhairi...

"No no my dear kidena gode min, kefa ƴa tace ko Bakya sona a matsayin mama?

"Ina so sosai, Nawaz tace cikin jin kunya.

Yauwa kokefa yanzu muje kici abinci n, mikewa sukayi suka ƙarasa dinning, da kanta tayi serving din Nawaz ,
taɗan ci da yawa sannan tasha green tea ɗin da Amma ta miƙo mata....

Falour suka koma suka zauna, waya mummy ta miƙa mata "gashi kiyi game kafin na fito saboda kada ki gaji da jira, zanje na shirya.

"To Nagode" Nawaz sai jinjina irin kulawar amma takeyi, sai kuma ta tuna da mummyn sarfraz, Allah sarki ko tana wane hali oho?
Buɗe wayar tayi tana ɗan dubawa, cikin Sa'a kuwa taga make up game , ai take ta shafa ta fara yi tanata murmushi...

Fitowar Aayaan kenan daga ɗaki zai fara ƙorafi, kawai ya hango ta,
Tsaya wa yayi sosai yana so ya gane wacece, a iya tunaninshi ya kasa tuna inda ya santa gashi fuskarta is familiar to amma bari mum ta fito ...

Gaban fridge ya karasa ya dau ruwa yana sipping a hankali.. sai kallonta yake yanaso ya tuna inda ya santa, yama manta da batun wata Nawaz .

Mum ce ta fito sanye da baƙin lafaya me ratsin ja,
"Au ashema ka fito inata sauri inzo in kiraki?

Murmushi yayi "na fito mum, amma mum baƙuwa mukayi ne?

Kallon mamaki mum tayi mishi kana nufin baka gane daughter na ba, Aayaan banason wulaƙanci fa?

Ruwan dayake shirin haɗiyewa ne yabi ta ƙaramin maƙoshi, ai take ya kware ya fara tari
Nawaz da hankalinta nakan game dinta, sai jin tari tayi, ai da gudu ta mike tare suka ƙarasa gabanshi ita da mummy,
Sannu kawai suke mishi, ganin yanda suka ruɗe sai ya ƙara tarin yana dafe kirji.

Mum ce tace Nawaz ɗauko min wayana in kira doctor...

Da gudu ta koma falour ta dauko wayar, sai sannan Aayaan ya ɗan rage tarin da yake yi yana nishi kaɗan kaɗan
Fasa kiran likitan mun tayi tana mishi sannu, itama Nawaz duk hankalinta ya tashi..

Shi ko Aayaan sai dariyar zuci yakeyi, domin ba kwarewa yayiba shifa kunyace ta kamashi gashi bayaso a cigaba da maganar shine yayi musu acting..

Ruwan mummy yia bashi a hankali tana mishi sannu, shikuma sai lumshe ido yakeyi.

A hakan ya karewa Nawaz kallo duk basu luraba,
"Oh ita kuma haka take ta riga canzawa kamar hawainiya?
Dazu fa ba haka take ba, Aayaan ke zancen zuci...

Mummy ce tace pls kije kitchen ki samomin green tea kinji,
A hankali ta miƙe ta nufi hanyar da mummy ta nuna mata,
Lumshe ido yayi yana kallonta ta ƙasan ido, mamakin yanda hips dinta suke juya wa yakeyi..

Sai yakejin kamar kar ta shiga kitchen ɗin yayi ta kallon tafiyar,

Mummyn ce tace Aayaan kaji tsoron Allah ka dena irin wannan,

Ji yayi zuciyarshi ta bada daraammm to ko mummy taga kallon da yakeyiwa Nawaz ne..

Daure wa yayi " mummy me nayi?

"Wai kai kanaso ka ɓatawa yar mutane rai sai kuma Allah ya shake wuyan da zakayi wulakancin dashi.

Wani sanyi yaji a ranshi da mummy bata ganeba...

Mikewa yayi "mum nifa naji sauƙi kuzo muje?

Aayann bana wasa dakai nasanka da ɓoye ciwo, baza mu fitaba sai nan da minti talatin lokacin jikinka yayi relaxing kada fa ka manta akwai wani ciwon a hannunka.

Ba yanda ya iya, haka ya koma ya zauna a one sitter sofa.

Fitowa Nawaz tayi rike da mug, gabanshi ta karasa ta ɗan risina ta miƙa mishi,
Ganin yanda sukayi matching take amma taketa addu'ar Allah ya amsa mata kudirin ta....

~*_MATAR RASHEED_*~✍️*🎀🎀 SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 28*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️

Ko kyakkyawan parking mummy bata bari drivern yayi ba ta buɗe ƙofar motar ta fita, cikin asibitin ta shiga tana bi gado gado tana dubawa.

Da sauri daddyn sarfraz ya bita, sunata dubawa tare.

Har gadon karshe amma babu sarfraz, wani irin kuka mai cin rai ne ya kufcewa mummy "shikenan ta faru ta ƙare"

Shima daddy gaba ɗaya gwuiwar shi ta sare, ji yayi kafar shima bazata iya daukarshiba, guri ya samu ya zauna a kasa dirshan.
Mummy kuwa sai kuka takeyi duk idon mutane ya dawo kanta...

Wani dattijo ne ɗan kimanin shekara sittin ya karasa gurin ta "ƴata kiyi hakuri, kuma kiyi tawakkali sannan ki dauki kaddara....

Allah yana son masu hakuri da karɓar kaddara mai kyau ko mara kyau.

Kin manta da kissar matarda ɗanta ya rasu taje har makabarta ta duƙa gaban kabarin tanata rusa ihu, wani mutumi yazo wucewa yace kiyi hakuri idan kikayi hakuri kika dauki ƙaddara sai Allah ya jikansa kuma kema ki samu Rahma.

Amma matarnan sai ta ƙiyin hakuri ta cigaba da ihu tana dukan kanta...

Sai daga baya ta gane ashe mutumin nan dayace mata tayi hakuri Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne,
Take ta tafi gabanshi ta faɗi tana cewa nayi hakuri ya nabiyy.
Murmushi Annabi yayi yace, sanda nace kiyi hakuri dakinyi to shine kikayi hakuri don Allah, amma yanzu darajata ne yasa kikace kin hakura, kuma alokacin danace kiyi hakuri da kinyi to da danki Allah ya saka shi a aljanna kuma kema haka...

To ƴata abinda nakeso ki fahimta shine Allah ne ya baki kuma ya amsa to saikiyi mishi hamdala kuma ki dangana tunda wanima ko haihuwar be taɓa yiba, dalilin hakan sai kiga Allah ya Miki wata baiwar ta daban.

Wani irin imanine ya shiga daddy da mummy da duk ma mutanen dake gurin, goge hawayen ta tayi tace "baba Nagode Allah ya saka da Alkhairi...

Shima daddy godiya yayi mishi sosai sannan suka nufi mutuary don ɗakko gawar sarfraz...

Nan ma duka babu gawar da ba'a ɓude musuba amma babu sarfraz babu alamar shi..

Kuka mummy zatayi Daddy yace "kada ki manta da nasihar da aka gama yi mana yanzu, Allah ne kaɗai yasan me hakan take nufi...

Shiru mummy tayi sai kuma ta kalli dadyn tace " amma kasan wani abu? Idona ya rufe akan sarfraz sam banma tuna da Nawaz ba, kuma gashi itama babu ita,
Dole akwai wani abu..

Daddy yace"to abinda nakeso dake shine kiyi hakuri mu mikawa Allah komai, muriƙa addu'a..

Fita daga asibitin sukayi mummy tanata goge hawaye, cikin motar suka shiga don komawa gida....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Hassu na nan zaune batada abinyi sai kallon sarfraz, ko fitsari bata iya zuwa tayi saiya matseta saboda kada ta tafi wani abu ya samu Sarfraz.

Ta ɗura mishi nono yafi sau bakwai wai kada yaji yunwa..

Anan ta lura wandonshi ya jike, kuka ta fashe dashi "don Allah kiyi hakuri wallahi bansan kinajin fitsari ba dana ɗagaki kinyi...

Ruwa ta ɗebo da yawa ta zuba a gurin sannan ta samu zaninta ta ɗora a saman wandon sarfraz sai kuma ta zare wandon ta ƙasa....

Shidai sarfraz babu um babu um'um ko ƙifta idoma bayayi..

Haka ta koma ta zauna tanata kallonshi ''wannan daga ganinta irin ƴan birnin nan ne masu kyau da kwalliya, jifa kayanta har yanzu kamshi sukeyi ..

Nonon ita ma ta kamfato a ƙoƙo ta fara sha, don bazata iya barin sarfraz shi kadai ba ta tafi dafa abinci ba, kuma gashi ta fara jin yunwa...

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sai da ya kalleta ya ɗaga mata gira ɗaya yace "Nagode" sannan ya amsa tea'n
Ɗaya daga cikin kujerun Nawaz ta zauna tayi tagumi...

Mummy ce ta kalleta "daughter what is wrong?

Murmushin iya baki Nawaz ta ƙaƙalo "babu komai Amma, i am okay..

"Ban yarda ba, wato kema halinki daya da Aayann koh? Kuyi ta ɓoye abu har sai yayi muku illa tukuna za'a sani..

Atare suka kalli junansu, daga mata gira Aayaan yayi tayi saurin kauda kanta...

"Waishi wannan Aayaan ɗin saikace tsohon kwarto bini bini ya riƙa daga wa mutum gira.. Nawaz ke zancen zuci
Chapter 25 · 0% Book details