← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 112

Sashe 52

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

ATM 🏧 card Aayaan ya mikawa Farouk "gashi duk Abinda ya kamata kayi, pls ka taimaka gobe su samu Flight saboda na ƙosa naga ɗan uwana ya koma dai-dai, pls ko ta online kayi musu bulking da daren nan, yadda zasu samu morning Flight.

"To Insha'Allah yoo, komai zaiyi neat kamar kananan, sallama sukayi Sannan Aayaan ya tuƙa motar ya fice daga harabar gidan.
Ahankali yake tuki yana tunanin Nawaz. "meyasa zata yanke wannan hukuncin, Ni dai Nasan tsakani da Allah nake ƙaunar ta, ko kaɗan banaso na ganta Cikin damuwa.

Haka dai ya Isa gida jikinshi tiɓus, ga farincikin ganin SARFRAZ amma babu halin faɗa, a falour ya tarar da Aseey tana taje gashin kanta.

"Bro sannu da dawowa! Ya hanya?
Murmushi yayi"hanya Alhamdulillah, ina mum?
"Baffa ne ya kirata kuma naga alamun ta shiga damuwa, shine ta shiga ciki ta kwanta....

Babu shiri Aayaan ya nufi ɗakin mumy, domin a nashi gurin gani yakeyi ƙilan Wani abu ne ya faru da Nawaz ɗin shi.

Yana shiga yace "mum faɗamin Meya faru? Aunty Aseey tace wai baffa ya kiraki!

Ɗago kai mumy tayi "ya kirani son, amma Alamu ya nuna Nawaz bata chan, Domin baffa ma Cewa yayi wai akwai wata goggonta da ta haihu wai in faɗa mata ta kira tayi Mata Barka....
Saboda wai umminta tace wayarta bata shiga kwana biyu....

Wata zufa ce ta karyowa Aayaan, Yanzu yazaiyi, mai ze cewa baffa da ummin Nawaz Idan suka titsiyeshi?

"Mummy meye mafita, ko a faɗa Musu ne?

"Kul Aayaan, kada ka soma! Ya za'a yi muje gidan Mutane mu ɗauko musu ƴa cikin mutunci Sannan Yanzu kuma mu kirasu muce ta ɓace bamu gantaba? Ai abinma babu hankali a ciki.

"Shikenan mum, bari zanyi tunani naga meye mafita, Allah dai ya bayyana ta ...

"Ameen dear, kaje kaci abinci, nasan ba Lallai Kaci wani Abu ba.

Falour Aayaan ya dawo yanajin zuciyar shi a karye, "shi yanzu ya zaiyi? Ta ina zai Fara Neman Nawaz? Ga rashinta ya fara yi mishi illah, kwata-kwata baya samun isasshen Barci da dare, gashi yayi ta mafarkinta.

Zama yayi a kujerar Dake kallon ta Aseey "sis bata gida, meyasa Nawaz zatamin haka? Wallahi sis jinake Kamar zuciya ta zata fashe.

Hakuri Aseey taketa bashi, a haka dai ta kwantar mishi da hankali.

Miƙewa Aayaan yayi da nufin ya ƙarasa dining ɗon yaci abinci ko babu yawa, ɗon yanzu ba wani iya cin abincin yakeyiba, duk ya faɗa gashi kuma bakinshi yafison taste ɗin abincin Nawaz yanzu.

Ƙarar buɗe ƙofar da akayi ne yasa Aayaan waigowa, ai kuwa take ya shamur kamar wanda be taɓa dariya ba, Ashley ya hango _*(yarinyar ƙanin babansu ce, bata jin magana sam, babu kamun kai, Sannan ta likewa Aayaan akan wai ya taimaka ya aure ta)*_

Ko dinning area ɗin be jeba ya buɗe daki ya shige Tare Da Sawa kofar key, don beson Ashley tazo ta dameshi hakakurum ita gata kamar horo, jiki kamar ansawa muciya doguwar riga, sai uban salo da kisisina.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Sati daya kenan da tafiyar su hassu London, inda har anyiwa SARFRAZ surgery ɗin, sai dai har yanzu yana process ɗin magunguna, don a ka'ida bazai farfaɗo ba sai nan da 30days, saboda haka tsarin aikin yake, ita kuwa hassu an haɗa ta da matar haidar sai gyara ta takeyi tana koya mata abubuwa, Gashi an samar musu lesson teachers ita da bandi, wannan na tafiya wani zaizo,

Kuma babu laifi domin suna gane abubuwan da ake koyar dasu, don Allah ya albarkacesu da budaddiya kwakwalwa, Hassu harta fara sajewa da ƴan kasar, domin madam haidar ta kaita body steaming da Mani cure, harta gashin kanta saiya koma kamar samatashi akayi, domin har wani ƙyalli da sheki yakeyi, kuma dama gashi baƙi.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Zaune Nawaz take a saman dressing mirror, abin duniya Ya isheta, duk rigunan ta sunyi mata kaɗan, Domin idan tasa sai taji ƙirjinta kamar Zai fashe. Kuma Alhali da sunyi mata yawa, siket siket ɗinta ma data sa sai zip ya dare, gashi ita kanta takaanji nauyin jikinta Yanzu ba Kamar da data ke jin kwanta a Iska ba..

Gaban standing mirror ɗin dake Hanyar bayi taje ta tsaya tana ƙare wa kanta kallo, ganin ƙirji ta tayi yayi full Kamar zai fashe, ga hips ɗinta ya daɗa buɗewa sai taga Kamar ba ita ba, domin full figure 8 haka ta koma, ɗan tafiya tayi a gaban mirror ɗin, Aikuwa taga hips ɗinta na sukutur-sukutur.
Zare ido tayi 😳😳😳 "nashiga uku! Yaushe na zama haka? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, a'a, to wannan kibar ta meye?
Shiru tayi tana tunani, iya tunanin da tayi babu abinda zatace dalilinshi tayi ƙiba, Abu ɗaya take zargi yanzu :- ~magungunan da inna ke ɗura mata,~ tabbas Akwai alamun tambaya, sosai inna take dagewa akan saitasha magungunan gashi yanzu harda su nonon raƙumi da garin Riɗi take dama mata a Madara tace ta shanye, Tsumi kuwa ba'a magana ga Gumba, anya kuwa? Ni kam kodai Akwai abinda inna takeyi ne? Ga subulan Dilka kala-kala suma....

Hannunta ta kalla taga yayi wani fau, ga taushi da yayi tubus sai ƙyalli yakeyi, har wani damshi-damshi yakeyi alamun cikar Ni'ima a Tare Da ita...
Shiru tayi ta zubawa hannun ido "anya kuwa! Allah kasa ba gaskiya bane? (A shirmen Nawaz tunawa tayi sanda Aayaan yacewa Nafisa tanada ciki?
Idan kuwa ciki gareni na shiga uku, to yaushe akayi min cikin, to ko Aayaan ya bani Wani Abun da yasa nafita hayyacina ne? To yaushe? Haka ta zama kamar zararriya, daga ta saƙa wannan ta warware saita kuma tufke wancan.

Doguwar riga ta samu tasa sannan ta fito falour gurin inna, "Inna wallahi Ni Sai Yanzu na lura da jikina sai naga nayi ƙiba.

"Ooh Nawaz wace ƙiba kikayi? Nifa Ban ganiba! Jikinki dai ya murje..

"Inna don Allah ki barni naje gidan Nafisa ƙawata, kinga tunda nazo ban taɓa zuwa ko ina ba, kuma yau kusan kwana na ishirin.

Fir inna taƙi amincewa, amma daga baya sai ta yarda ganin yadda Nawaz ɗin ta shiga damuwa, "amma karki daɗe, kuma karki kula Kowa, kuma ki kula da kanki..

Dubu ɗaya Inna ta miƙa mata "gashi kiyi transport da ita.
"Inna kibarshi Akwai sauran kuɗi a hannu na, hararar da inna ta zabga Mata ce ta sata amsar kuɗin babu shiri tare da yi Mata godia, ɗaki ta koma ta shirya cikin Wasu riga da skirt, suma daƙyar suka shigeta Sannan ta samu dogon hijab har ƙasa tasa, "inna saina dawo!

"Yauwa Nawaz ki gaisheta, Allah ya tsare Adawo lafia. "Ameen" Nawaz tace Tare Da fita daga gidan....

Kasan cewar iska akeyi yasa hijab ɗin duk ya maƙale mata a jiki, sai gyarawa takeyi amma yaƙi yi, gashi taƙi samun abin hawa, duk inna tabi sai maza sun bita da ido, waɗanda suke machine har waige sukeyi.

Wani me napep ne nazo wucewa ta gefenta, Aida sauri ta daga hannu tana tsaidashi, ciki ta shiga tana cewa "gaskiya layout zaka kaini.

"Okay to Hajiya, amma in zaki bani dama danayi Miki wata tambaya.
"Menene fadi tambayarka mana! Ɗan murmushi me napep ɗin yayi "kusan sati Uku da suka wuce na dauko wata daga gaskiya na kawota unguwar nan, kuma wallahi kunyi kama, saidai ita bata kaiki cika ba da haske. Amma kunyi kama matuƙa, shine nace koku Yan biyu ne?

"Tab ashe bani kadai naga cikar danayi ba, harda ƴan duniya" Nawaz ta raya a zuciyarya,

"Nice mana, unguwar daka daukoni Nan zaka maidani amma ba gidan ba"

"Anya zan iya yarda cewa kece ta rannan! Hu'um inkuwa kece ina zargin ke amaryace amma? Murmushi nawaz tayi "Allah Nice kuma single nake banida aure!

"Shiru yayi badon ya yarda ba, amma fa abun ya bashi tsoro kwana nawane da zata Zama haka inhar da gaske itace?

Har Kofar gidan Nafisa ta nuna mishi Sannan yayi Parking, bayan ta sallame shi ne yace ƙarfe nawa zaki koma in dawo in ɗaukeki?
Murmushi Nawaz tayi "inaga wajen ƙarfe Uku yayi, nagode sosai kuwa, saika dawo..

Cikin gidan Nawaz ta shiga da sallamar ta.
Galala Nafisa ta tsaya tana ƙarewa Nawaz kallo, "i lallai gaskiya mijinki ya iya kiwo, ji yanda yayi miki ɗure, Kinga yadda kika cika tako ina, ga wani sheƙi da kikeyi, shikuwa meyasa ya fito dake, ai sai ayimai kwace, Kinga yadda kika zama wata ɗanya ɗanya ne, sai kace amaryar da mijinta baya wasa.

Ballamata harara NAWAZ tayi "Ni dai kibar wannan soki burutsin naki kizo muje kiji abinda ya kawo Ni.
Daki suka shiga tare, ko zama Nawaz batayiba ta cire hijabi "Nafisa nashiga uku, ji Yadda na zama!
"Wane shiga Uku? Ai sha'awa ma kika bani, das dake, gaskiya mijinki na kwasar ganima, ko ince kuna kwasa tunda shima da gani jarumi ne.
" Dalla! Ni kidena min wannan zancen banzan ki faɗa min mekesa mace ta zama haka Cikin ƙaramin lokaci?

Dariya Nafisa tayi Sannan tace "A iya sanina nidai nasan amare ne ke zama haka, saboda sinadarin namiji da yake zuba Musu ance yana yi musu amfani, sai kuma mace mai danyen ciki daga sati biyu zuwa wata uku, to zakiga itama kirjinta ya cika hip ɗinta duk sun buɗe...

Toke meye na tambayar bayan kinsan Dalilin da yasa kika zama haka, cikin naki zai kai wata nawa?

Miƙewa Nawaz tayi"Allah Nafisa idan kikace zaki ɓatamin rai wallahi zanyi tafiya ta.
Da sauri Nafisa ta miƙe "yi hakuri na Dena, ina ogan, naga baki shigo da muhsien ba.

"Ni kadai nazo" cewar Nawaz tana kishin giɗa a kujera.
"Shikuwa ya barki kika fito a haka, bayan a Yanzu duk namijin dazai ganki a haka saiya haɗiye miyau, balle kuma Yanzu ga ƴan lesbian cike da gari, suna ganin ki ai Shikenan kin shiga uku.

Duk idon Nawaz yayi ja, ita yanzuma ta dena zargin inna, ganin takeyi dole Akwai abinda Aayaan yayi mata, Sannan ya ɗirka mata ciki bata saniba, ita Yanzu ya zatayi! Me zatace wa umminta idan ta tuhumeta?

"Nafisa don Allah babu wani abu dakesa mace da zama haka bayan abubuwan nan da kika lissafa min?

"Gaskiya ban san waniba, iya abinda na sani kenan...
Chapter 52 · 0% Book details