Sashe 110
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fudail sai dariya yakeyi yana kallon su, Domin Mummy taki yarda shi kuma sai ƙoƙarin saka mata cokalin a baki yakeyi, ana haka colonel ya fito yana duba agogon hannun shi "kuyi sauri kuzo muje kada muyi lattin ɗauko su kun.......
Kafin ya ƙarasa Magana sukaji ana knocking ɗin kofa, Daddy colonel ne ya ƙarasa bakin Kofar ya buɗe....
Sakin baki yayi yana kallon su, Aayaan ya gani riƙe da Nawaz wadda daƙyar take tafiya saboda tirtsetsen cikinta.
"Son yanzu fa nakeso muzo mu ɗauko ku, how manage kuka rigamu isowa?"
Murmushi Aayaan yayi yana cewa "ashe flight ɗin 7:30am ne nace maka 8:00am"
Okay to sannun ku da zuwa, mummy ce tayi saurin ƙarasawa ta riƙe Nawaz Daddy kuma sai Sannu yake jera mata, Naufal ma kamar ya fashe da kuka sanda yaga Nawaz ɗin.
"Anya yaya Captain ba ƴan-biyu bane a cikin Aunty kuwa?" Fudail yace cikin jin tausayin halin da yaga Nawaz ɗin a ciki.
Lallabawa Mummy tayi ta zaunar da Nawaz ɗin a saman kujera sannan ta waigo gurin Aayaan wanda idonsa yana kan Nawaz ɗin.
"Sannu da ƙoƙari Aayaan! Yanzu dama haka daughter take fama Amma shine kaki Kawo mini ita Saida nayita fama da kai? To yanzu yaushe ne EDD ɗin ta?"
"Kiyi haƙuri mum! Nifa naso ne ace sai dai ku gammu da jinjiri, ko yanzu ma Kawai don kin matsa ne"
Sakin baki mummy tayi tana kallonshi, su kuma su Daddy me zasuyi idan ba dariya ba.
"Ƙaniyarka Aayaan! Cemaka nayi yaushe ne EDD ɗinta? Ba surkulle nace kayi min ba"
"Ai EDD ɗinta ya wuce tun shekaran jiya ne!"
" Wai me ke damun kane Aayaan......
Bata ƙarasa zancenba tayi kan Nawaz da sauri tana rike ta ganin yadda ta fara murkususu alamun naƙuda.......
*Pls kuyi haƙuri, naso ace wannan ne last page Amma naga yaƙi ƙarewa, don haka in'sha Allah sai zuwa gobe zamu yi last page ɗin*
Matar Rasheed ❤️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*92*
*LAST PAGE* 😭😭😭
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Shima Aayaan a rikice ya ƙarasa gurin Nawaz ɗin yana cewa "me ya faru?"
"Naƙuda ce! kama ta mu tafi asibiti" cewar mummy tana riƙe hannun Nawaz cikin nata, Alamun bata kwarin gwuiwa.
"Hankalin Daddy Sosai ya tashi shima ganin cikin ƙankanin lokaci Nawaz ta fita daga hayyacinta, tunawa yayi da maman su Naufal, duk sai yaji zuciyar shi babu daɗi, suma twins wato Naufal da fudail sai sukayi ɗaki suna sharar ƙwalla.
Shikanshi goga Aayaan ɗin sai ya rasa duk wani kwarin gwuiwar shi, gani yake kamar mutuwa zatayi, "Son be strong! Ɗauketa muje mota, kaida ita sai ku zauna a baya Ni sai nayi driving ɗin."
Ciccibarta yayi zuwa motar ita kuma Mummy ta shiga ɗaki Don kwaso siyayyar da tayi ta haihuwar duk da bata san me Nawaz ɗin zata haifa ba.
Driving yakeyi yana addu'ar Allah ya sauketa lafiya, domin ya gama lura da Yadda Aayaan ya sallamawa Nawaz ɗin duka rayuwarshi, yasan idan ta mutu to Aayaan ɗin shima sai dai ya zama kawar gwawa ce ke rayuwa cikin Duniya.
Mummy ma sai addu'a takeyi, bini bini take waigowa tana duba Nawaz ɗin, shikuwa me gayya Aayaan duk yabi ya rungumeta sai sannu yake jera mata.
Nawaz dama tun suna jirgi take fama, daure wa kawai takeyi, saida suka isa gidan ne abin yaci ƙarfinta, addu'oi takeyi a cikin ranta iri iri, idan ta kama wannan saita saki wannan.
Ɗan sauki taji sanda ta fara karanta *"Allahummah la sahla illah ma ja'altahu sahla, wa'anta taj'alal huzna iza shi'ita sahla, Allahu, Allahu, rabbi, la ushrika bihi shai'a"* sosai take ta maimaita ta a cikin zuciyarta ta har Saida ta fito fili, duk ta jiƙe da zufa tsabar azaba, Ayanda take ji daba don Mummy da Daddy suna kusa ba tanaga kila saita zabgawa Aayaan mari, ya wani kanainayeta bayan ita kadai tasan irin azabar da takesha.
Da gudu nurses suka fito da gadon da za'a ɗora Nawaz akai domin takai gejin da bazata iya takawa da kafar taɓa. ɗora ta Aayaan yayi yana binsu cikin hanzari, mummy kuwa tsabar damuwa rungume colonel tayi ta saka kanta a cikin ƙirjinshi ko zata samu sauƙi.
Sanda za'a shiga labour room dinne wata daga cikin nurses ɗin tace wa Aayaan "yallabai iya nan zaka tsaya domin maza basa shiga"
Kofar da take ƙoƙarin rufewa yasa hannu ya riƙe tare da cewa "Matsa ki bani guri Kafin nayi ball dake! Halan kece kika yi mata Cikin!"
Yadda taga idon Aayaan ɗin yayi jajir ga jijiyoyin kanshi duka sunyi ruɗu-ruɗu yasa ta kauce ta bashi guri, fita tayi don taje ta faɗawa Babban doctor.
Shi ko Aayaan be jira komai ba ya gyara mata kwanciya a saman gadon tare da janyo table ɗin da ake ɗora duka abubuwan buƙata, Ruwan naƙuda yasa mata sannan ya ɗura allurar oxytocin a ciki.
Sauran nurses ɗin tsaye sukayi suna mamakin wannan lamari.
Damƙe hannuwanshi Nawaz tayi tana cewa "yaya pls idan na mutu ka yafe min"
Ƙara rike hannunta Aayaan yayi tare da cewa "pls kidena cewa haka, lafiya kalau zaki haihu in'sha Allah"
"Yaya azabar tayi yawa, bansan yadda Zan kwatanta maka yadda nakeji ba"
"I'm sorry, pls be strong! I need you, mum need you, dad need you, ummi need you, Abba need you, Aseey need You, and last of all babyn da zaki haifa shima yana buƙatar ki fiye da kowa, pls ki taimaka mana"
Dai dai nan Dr Uthman ya shigo ɗakin don ganin waye wannan me ƙarfin halin, shiru yayi yana kallon Aayaan Sannan yace "buddy ashe kaine, yanzu wata nurse ta kawo min ƙara wai wani ya shiga ɗakin amsar haihuwa kuma wai har yana ce mata zaiyi kwallo da ita"
"Dr nine, saukar mu kenan daga England madam ta fara naƙuda, shine mukayo Nan, ita kuma ta tsaya tana min zance"
"Ayyah! Allah ya raba lafiya, ka duba komai babu wata matsala Koh?"
"Eh babu, riga kawai za'a bani na chanza mata, sannan duka nurses ɗin nan zasu iya tafiya, idan ina buƙatar wani abu zan danna mic"
"Okay to babu komai, ke mariya ɗauko mishi rigar naƙuda, ku kuma ku biyoni " Abinda Dr Uthman yace kenan tare da fita daga ɗakin
Itama mariya tana bashi rigar ta fita daga ɗakin. Doguwar rigar jikinta ya zame mata cike da kulawa sannan yasa mata rigar.
Ko minti ɗaya beyi da gama sa mata rigar ba ruwan faya ya fashe, matso da plate ɗin almakashi yayi Sannan yasa hand gloves, bazai iya kallon jikanta ba sai kawai yace ta riƙe duka hannuwanshi tayi pushing.
A haka dai sukaita gwagwagwa har Allah yasa tayi wani yunƙuri me ƙarfi saiga baby ta fito, rasa me Aayaan zaiyi yayi don farin ciki, hannu yasa ya ɗauki baby ɗin tare da daidaita cibin yana yanke wa, gefen hannun daman Nawaz ya ajiye ta tare da yiwa Allah tasbihi a cikin zuciyarshi yana ayyana ya mummy zataji idan tasan mace Nawaz ta haifa? "Ga Mumtaz (Biyunin mummy,wato maman Sarfraz) kiyi mata addua, Domin ke kadai kikasan irin azabar da kika sha."
"Nagode, Nagode, Nagode sosai sweetheart, bansan dame zan iya biyan kiba san...... "Yaya cikina" Abinda Nawaz ta iya cewa kenan cikin murya mai nuna zallar jigatuwar da mai ita yayi.
Da sauri yasa hannun shi a Kasan rigar donjin ko mahaifa ce ta tawo, ga mamakinshi sai yaji kan wani jinjirin ne ke ƙoƙarin fitowa, jikinshi har rawa yakeyi tsabar farinciki, taimaka mata ya riƙa yi tana pushing a hankali, cikin ikon Allah kuwa taji wani karfi yazo mata ta turo shi duka zuwa mararta, ai kuwa sai wani uban ihun jinjira ya cika ɗakin, tare suka fito ita da mahaifar lokaci ɗaya, bata jira komai ba tun kafin Aayaan yakai ga yanke mata cibi ta turmuka hannunta a baki ta fara tsotsa.
Duk Aayaan ya rasa yadda zai yi, farincikin yayi mishi yawa shi kaɗai, yanaso ya samu wanda zai taya shi.
Mumtaz tana gefen Nawaz ɗin inda ya ajiye ta tun dazu, dama ita tunda aka haife ta batayi kuka ba, ta biyun ce akoke kuma acici, gaba ɗaya ta tsotse ruwan haihuwar Sannan taci gaba da yanyara ihu.
Zanin gadon dake saman ɗaya gadon ya janyo ya saka su duka a ciki ya nannaɗe Sannan ya maida su saman ɗaya gadon. Yanzu gaba ɗaya ta Nawaz yakeyi, she look so pale, gaba ɗaya idonta ya rufta fuskarta tayi pink bakinta kuwa yayi jajir dashi.
Dagota yayi ya tallabe kanta yana sakin mata murmushi "dear har two kid's? I Don't know what to do, me zanyi miki ne?"
"Son da kakeyi min nakeso Kaci gaba dayimin har zuwa ƙarshen rayuwata" Abinda Nawaz tace kenan cikin dasashshiyar murya
"Har dai wannan ne to kisa a ranki ƙaunar da nakeyi miki zanma ƙara ninninkata ne har zuwa sau babu adadi, Nagode sosai dear"
Maida ta yayi ya kwantar tare dace mata "bari na nemo Doctor mace ta gyara miki jiki, bazan iya kallon yadda honey pot ɗina yasha wahala ba, i love You"
Fita yayi yana waiyayensu kamar zai cinye su duka, a bakin ƙofa yaga Mummy da Daddy sai zarya sukeyi suna tsumayen jin ance ta sauka, mummy ce tayo gunshi da sauri "Son ta sauka kuwa?"
Ƙarasa cire hand gloves ɗin hannunshi yayi yana cewa "mum and dad ta haifi twins, all girls"
Rukunkume dady mum tayi tana jin kamar tashiga ɗakin ta kwaso yaran, amma babu hali.
Office ɗin Dr Uthman ya ƙarasa inda yace pls a bashi mace doctor wadda ta haura shekara arba'in yanaso zata gyara Nawaz ɗin, wai beson yara saboda sun cika rashin kunya, tare da ita suka tawo, a bakin kofar ya amshi kayan jinjirayen dake hannun mummy Sannan suka shiga ciki shida doctor munira, Allah Sarki Nawaz har barci ya ɗauketa.
Cikin ƙankanin lokaci aka shirya twins tsaff dasu, itama Nawaz lokacin ta tashi, kwashe mata jinin doctor tayi sannan tayi mata allurorin da zata ɗan ji kwarin jikinta, shiko Aayaan yana zaune ya riƙe hannuwanta sai godiya yake yi mata, saida aka gama shirya su tsaff Sannan Doctor munira tace taza tafi, hannu Aayaan yasa a aljihu ya ciro kudi masu kauri ya miƙa mata tare dayi mata godiya
"Pls idan kika fita kice su mummy su shigo"