← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 112

Sashe 68

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan gicciyawa umma tayi domin gaba ɗaya ta gaji da zama guri ɗaya, gashi kuma ba iya tashi zatayi ba domin ko motsa ƙafar tayi wata irin azaba ce ke ziyartar ƙwaƙwalwarta, a zuciyarta sai tsinewa bokan takeyi.

"Fauziyya yaushe zakije Makarantar su Jamila ki dubo min wane hali take ciki?"
"Umma gaskiya a halin da kike ciki bazan iya tafiya wani guri na bar ki ke kaɗai ba"

"Fauziyya don Allah badon niba ki taimaka kije ki gano min meke faruwa wallahi tun shekaranjiya take fado min a zuciya, kuma kinsan ko dama Jamila ba Wani jin magana takeyiba"

"To umma zanje! Amma saina samo wanda zai kula dake kafin na dawo"

"To fauziyya Nagode"

Duk sai fauziyya taji tausayin umma ya kamata sosai, duk jikinta yayi sanyi tama rasa me zatayi, yanzu haka tana nadamar abubuwan da suka aikata akan Nawaz.
"To yanzu haka ma ina Nawaz ɗin take? Ina ummi? A Wane hali sukema? Fauziyya ke zancen zuci (Nikam matar Rasheed nace suna hali me kyau domin hassada game rabo taki ce)

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Da kyar Nawaz ta kwaci kanta a gurin Aayaan shima don hassu ta shigo dakin ne, koda ya fita dakin SARFRAZ ya koma Tare da kiran securities ɗinshi a waya yana shaida musu Cewa su shirya gobe da sassafe zasu tafi Maiduguri, Sannan ya tashi ya shiga bathroom don tsaftace jikinshi.

Sarfraz da bandi kuwa mota suka ɗauka suka nausa cikin gari don zagayawa wajen abokan Sarfraz ɗin, domin susan ya dawo, har HAYATUL ISLAM sukeda niyar zuwa.

Nawaz na kwance ne amma tunani ya cika mata zuciya, tsoron yadda zata ƙare da Aayaan takeyi duk randa hakurinshi ya kare, domin ta lura hakurinshi Ya kusa karewa daurewa kawai yakeyi, kuma a jarabar mazan yanzu ma Aishi sai dai a bashi girma don kuwa ya nuna shi mai dattako ne.
Abu ɗaya ne yaƙe sanyaya mata zuciya shine gobe zataje taga umminta, ta kwanta a jikinta taji duminta kuma su tattauna abubuwa da dama wanda da bata samu damar faɗa mata ba.

Hassu kam murna takeyi bilhaƙƙi saboda zata auri SARFRAZ, bini bini sai tayi murmushi har ɗan tsalle takeyi, ita dai Nawaz sai dai ta kalleta ta kauda kai, domin tasan kuruciya ke damun ta, domin data San me zata tarar bazatayi wannan murnar ba, kuma ta lura shima SARFRAZ ɗin ba baya bane wajen jaraba domin ba zai ɗaga mata kafa Kamar Yadda Aayaan yayi ba.

°°°°°°

Washe gari Misalin ƙarfe Bakwai na safe su mummy da mumyn Aayaan da dai sauran duka Yan gidan harda Daddy aka ɗauki hanyar Maiduguri.

Tsaf Aayaan ya cire kunya yace shi mota ɗaya yakeso Shida matarshi, Mummy da mummyn sarfraz da Aseey da muhsien suma mota ɗaya, hassu da sarfraz da bandi da Daddy suma mota ɗaya.

Nawaz kam ba haka tasoba taso a basu ɗaya ne ita da Aseey da hassu amma Aayaann yayi ruwa yayi tsaki ya shafe idonshi da toka yace basan zancen ba.

Tunda suka shiga motar yake lalubeta, daga ya taɓa nan saiya taɓa chan, tayi tayi ya bari amma kamar ma ƙara zugashi takeyi, daga ƙarshe ma banza tayi dashi sai dai intaga zai wuce gona da iri tace "bafa mu kaɗai bane akwai driver" shine zai ɗan sassauta mata.

A azare suka tsaya sukayi Sallah sannan suka kuma ɗaukar hanya, sosai tafiyar tasu take sauri domin a jere suke tafiya kuma hanyar babu cunkoso, sanda suka iso dai dai gurin da Yan ta'adda suka tsaresu saida Nawaz taji firgici ya kamata amma ganin an wuce salin alin yasa taji zuciyarta tayi sanyi.
Duk abinda take yi Aayaann na lura da ita, barcine fal idonta amma taki yarda tayi saboda kada Aayann ya rungume ta, amma saida yaci karfinta tayishi bata shiryaba.

Sai yammah lis suka isa maiduguri, domin har an fara kiraye kiyaren magrib.
A gidan su Aayaann aka yada Zango domin kowa ya huta gajiya.

Oga Aayaann kuma sai haɗa Target yake na yadda Nawaz zata kwana a dakinshi....

Ina yiwa kofa fatan Alkhairi, *SISTER NAJIDAT BICHI WANNAN SHAFIN NAKINE*

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*60*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Wannan shafin nakine *KHADIJAT SUNUSI LAWAL (SEEMAH)* Kiyi yadda kikaga dama dashi domin nakike halak malak "Aayaan yace a baki shi kyauta"

Haƙarshi bata cimma ruwaba domin tunda ta shiga ɗaki taƙi fitowa, Sannan kuma daya dameta da kira a waya ta kashe wayar.

Duk Aseey na ankare da abinda ke faruwa sai dai tayi murmushi tace "kaɗan ka gani, har dai aka cemaka mace ai an gama komai."

Washegari gidansu ummin Nawaz aka fara zuwa, kowa sai mamakin Yadda Nawaz ta cika yake, wasuma gani sukeyi kila ciki gareta.
Baffa ma ba ƙaramin daɗi yajiba yadda yaga Nawaz ɗin yasan In'sha Allah sun rigada sun haɗa kansu ba sai ya tsaya dogon jawabi ba.

Ummi kuwa kamar ta cinye Nawaz ɗin tsabar murna, tama rasa inda zatasa ta.
Su mummyn Aayaan da Mummyn SARFRAZ sun samu tarba me kyau sosai, haka ma dady shima sai mamakin irin karamcin su yakeyi, don tunda suka sauka a gidan kowa sai haba-haba yakeyi dasu, cikin ƙanƙanin lokaci aka dama musu fura taji mai da kwakwa, ga farfesun zabi da burabusko sai kamshi yakeyi.

SARFRAZ da bandi cikin gari suka bazama don ba idanuwansu abinci, shi kuma Aayaan yana fada shida baffa domin yayi duk yadda zaiyi yaga Nawaz Amma abu yaci tura, Mummyn SARFRAZ da Mummyn Aayaan kuma kwantawa sukayi don su miƙe jiki su samu relief ɗin zaman da sukayi na mota.

Aseey da Nawaz da hassu kuma suna ɗakin kaka sunata hira dasu ummi, muhsien na fara rigima ummi ta ɗauke shi ta goya, Aseey sai dariya takeyi tana cewa "mama don Allah ki sauke wannan gardin kada ya gajiyar dake"

Ummi kam tace ta kyalesu babu ruwanta, haka dai aka yini kowa cikin farinciki da walwala.
Kwana ɗaya sukayi suka ɗauki hanyar rigar su bandi Domin aje gurin malam aji yadda za'a nemi auren hassu, sanda zasu tafi saida kowa yaji babu daɗi a gidan kakannin Nawaz. hakanan dai aka rabu badon zuciya nasoba.

Cikin ikon Allah koda suka isa rugar sai suka tarar iyayensu hassu ɗin sun dawo daga yawon kiwon jiya, malam ma yana gidan domin yazo yayi musu bayanin abubuwan da suka faru bayan basa nan.

Murna gurin Bandi ba'a magana domin da gudu yaje ya dire a jikin ummansu, itama hassu haka domin mancewa dasu Sarfraz tayi ta fara taɓararta son rai.

Bayan komai ya lafa ne Daddy yayi bayanin Abinda ya kawo su, wato sunaso abasu auren hassu inda hali, kuma sunaso ne ayi bikin cikin ƙanƙanin Lokaci.

Basu wani nuna wata damuwa ba, domin mutanene masu karamci da girmama baƙi, dukda dai daka kallesu zakasan fulanin daji ne amma sunada faran faran da mutane, farinciki a gurin malam ba'a magana tunda ya gama jin abinda ya kawosu dady yaketa kabbara "Allahu Akbar, Ashe hassu mijine ya biyota har gida, Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi"

"Ameen" kowa yace

Daddy ne ya Nemi alfarmar cewa don Allah su dena tafiya kiwon da suke zuwa, su zauna a gida za'a samu wanda za'a ba ya riƙa zuwan musu kiwon, sannan za'a chanza musu gida a fitar dasu cikin gari dasu da baffa malam.

Ansha gwagwarmaya kafin su yarda amma daga baya sukace sun amince.
Gyaran murya Aayaan yayi Sannan yace "Daddy idan babu matsala inason na ɗauki nauyin gidajen da zasu zauna, yanzu zanyi waya nasa a nemar musu masu kyau a cikin gari.

"Aayaann baka gajiya da hidima, babu Komai Allah ya bada lada kuma yasa ka gama da duniya lafiya, yabaka masu yi maka fin wanda kayi wa jama'a.

Kowa saida ya amsa da "Ameen"

Wata alfarmar suka kuma nema "sunaso su koma da hassu da bandi, domin za'a fara shirye shiryen bikin, kuma bandi anason a nemi makaranta mekyau asashi yaci gaba, Aayaan ne ya bada sadakin hassu dubu ɗari biyu cif. Sannan sukayi haramar tafiya da Alkawarin idan bikin yakusa da kwana uku zasu aiko da mota ta kwashesu duka zuwa Zaria ɗin, don sun nemi alfarmar ayi duka taron bikin achan.
Daganan gidansu daddyn Aayaan aka wuce dayake Babu nisa sosai tsakani.

Sosai sukayi farinciki suma, kuma dama duk sun ƙagu suga amaryar Aayaan ɗin, sai Sannan ma mummy ta tuna da Ashley dataga kannenta, zancen zuci ta fara "to ina Ashley ɗin take? Bata gida dai sanda muka sauka, Sannan namma da alamun batanan, kawar da zancen kawai tayi daga zuciyarta don bata son damuwa.

Gabatar musu da Sarfraz tayi tareda Daddy da mummy, sosai sukayi mata barka domin suma sunsan labarin biyuninta mumtaz.

Flat guda aka basu akace su zauna, kowa sai nan nan yakeyi da Nawaz. Domin sun lura akwaita da kunya ga hankali.

Kwana biyu sukayi anan saboda akwai gidajen da aka ɗan zazzaga na dangi.

Kakan Aayaan shima yaji daɗin Kasancewar Nawaz a matsayin matar jikanshi, dayake duk baffa "(kakan Nawaz na Wajen uwa) yayi mishi bayani tun tuni, kuma ƙarin farincikin shi shine itadin jinin amininsa ce.

Daga nan gidan kakannin nawaz na ɓangaren babanta suka wuce, basuso su kwana ba amma fir suka dage akan sai sun kwana, kundai san Mutanen da akwai son baƙi.

Cikin dare kakar Nawaz wadda akasa mata sunanta (Nawwarah) ta tashi Nawaz tare da bata Wani rubutu data zuba zuma da garin kanumfari aciki tace ta shanye, da sassafe ma suna tashi ta bata wani tace ta shanye..

Sosai kaka malam yaketa nan nan da sarfraz da Aayaan, domin lokaci ɗaya yaji sun shigar mishi zuciya
Ko Bayan sun gama shiryawa da nufin tafiya Saida kaka taja Nawaz gefe ta ƙara bata wani haɗin tace ta shanye.

A gajiye suka koma gida, don haka babu wanda yabi takan abinci, kowa makwanci ya nema ya miƙe jikinshi tunda dama basu baro chan gidanba saida sukayi dam.

Koda gari ya waye babu wanda ya fito falour domin kowa yananan kwance sai juyi yakeyi, shikuma dady tun bayan asuba yacewa mummyn zai fita Saboda yanason yaje Wajen abokanshi nanan Maidugurin.
Chapter 68 · 0% Book details