Sashe 37
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zubura Nawaz tayi zata shiga ɗakin don bata san Aayaann yana gurin ba, daƙyar Aseey ta riƙe ta "tsaya Nawaz kidena biye mishi so yake ya rainaki.
Marairaice fuska tayi "Aunty Don Allah ki bari na shiga ciki sai muyi maganar anjima, matsa mata Aseey tayi tana mamakin wai meyasa Nawaz takejin tsoron Aayaan ne haka..
Shikuma yana tsaye yana murmushi, shidai kome zatayi burgeshi takeyi, musamman idan tana abun yarinta...
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Ta chan bangaren baffa (kakan Nawaz) yaje ya samu mahaifin baban Nawaz ya faɗa mishi cewa akwai wani jikanshi dayake neman Nawaz ɗin da aure kuma ya shirya,
Hamdala sosai baba'Ango yayi domin ya daɗe yanaso ayi auren Nawaz ɗin tun kafin a nemi mahaifinta a rasa.
Cewa baffan yayi "Aminina ai nabar maka Komai a hannun ka, kuma a matsayina na mahaifin Abban Nawaz na baka walicinta duk sanda yaron ya buƙata kawai a daura auren ko ta waya saika sanarmin tunda kace yaron na gida ne,
Anan kuma saina sanar musu suje chan wajen ka ayi taron bikin ko?
"Alhamdulillah Nagode sosai Aminina da wannan damar daka bani, kuma INSHA Allah Alkhairi zai zame mana sosai.....
Dariya baba'Ango yayi "ai ko baka faɗa ba Nasan insha Allah bazanji kunya ba tunda yau sama da shekara hamsin munatare amma alkhairi ne ke zuwar mana ta dalilin juna.
Bayan sun gama tattaunawa baffa yayi mishi sallama ya tafi zuciyarshi fal farin ciki, yana duba cewa ƙudirin daya dauka zai yiwu bada jimawaba.
Waya ya dauka yasa Nura ya kira mishi Mummyn Aayaan domin su tattauna yadda abin zai wakana.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Kwana biyu bamu leƙa wajen umma ba👀👀
A Cikin daki na hangi umma tana Safa da marwa, da alamu tana jiran wani abu ne.
Fauziyya ce ta fito daga bayi ta shiga ɗakin,
"Yauwa fauziyya kin haƙa ramin kin binne? Umma tace jikinta na rawa.
Eh na binne umma, "yauwa ai insha Allah Rahmatu bazata dawo gidan nan ba, kuma ita Nawaz ɗin databa wani dama har yana dukana to wallahi ta daki aurenta sai dai idan anayi a kabari tayi .
Nifa sam na rasa meyasa na tsani Nawaz da mamarta?
" Kinjiki da wata magana umma saboda ta aure Miki miji mana..
Fauziyya tace tana kashe ido daya
Tafawa sukayi suna dariya kamar sa'annin juna....
*Kai umma Ni na rasa meyasa wasu suke ɗaukar kishi da zafi ne*
_Kuma yauma idan kun karanta saura Kada kuyi comment👀, zakuji wayam ne gobe don hutun wata ɗaya zan ɗauka_🤗🤗
*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ🎀🎀*
*Episode 38*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️
Shiga dakin da Nawaz tayi yayi dai dai da gama wayar mummyn Aayaan ita da baffa, Yadda mummy taga Nawaz ɗin a hargitse yasa tace "matso nan daughter na! meya faru dake?
"Murmushi Nawaz ɗin ta ƙaƙalo Wanda be wuce iya leɓe ba tace "mummy babu komai"
Daidai Aseey ta dawo cikin ɗakin tace "mummy Allah da Komai Aayaan ne yake takura mata wallahi, yanzu fa daga kitchen nake naje na tarar abincin harya fara ƙonewa.
Daram gaban mummy ya faɗi saboda ita tafison su fahimci juna, domin idan basu fahimci junaba taya zaman aure zai yiwu "me Aayaan ɗin yake mata?
"Ban saniba gaskiya saidai wannan kusan shine karo na uku dana kamashi yana firgita ta"
Nawaz tace " A'a mum bawai wani abu daban yakeyi mini ba, wani zubin idan ina aikine kawai sai inga inuwar mutum to Ni kuma sai in firgita....
Sosai mummy taji daɗin kare Aayaan da Nawaz tayi, hakan yana nuna zata zama macen kwarai mai ɓoye sirrin mijinta ga dukkan alamu..
"Nawaz na fahimceki kema sak Aayaan ɗin ce, kuyita fama da abu a zuciya bazaku faɗa ko kwa samu sauƙi ba.
Ita kanta Aseey taji daɗi domin tana yiwa Aayaan fatan ya samu Nawaz a matsayin mata.
Muhsien ne ya Turo ƙofar ya shigo yana tangaɗi alamun barci bai isheshiba, gefen da Nawaz ke zaune ya zauna yana mutstsike ido "Aunty kimin wanka please, Uncle ne yace wai zaki rakamu muga gari...
"Zanyi maka wanka, amma yawo saikun dawo don banida lafiya.
Shiru muhsien yayi tunda ta yarda zatayi wankan, koma meye ayi daga baya...
"To isasshe! Wato kana kallon kowa amma babu Wanda ka iya cewa sannu sai faman bada doka da order, bazatayi wankan ba!
Kyaɓe fuska yayi "to ina kwana mummy?
Harara ta zabga mishi "Ni zaka fara gaisarwa?
"Au mummy babba ina kwana?
Murmushi mummyn Aayaan tayi "lafiya lau megida fatan ka tashi Lafiya!
Murmushi yayi shima daga bisani ya gaida mummyn shi sannan ya gaida Nawaz ..
Kama hannun muhsien Nawaz tayi ta shiga dashi bathroom ɗin Cikin Dakin..
Mummy kuma ta ciro wayarta ta ɗanyi danne danne sannan ta kara a kunne " wa'alaikumus salaam baba, okay to Babu komai dama nacene kawai a daura yau ɗin Allah ya tabbatar mana da Alkhairi....
Kashe wayar tayi cikin farin ciki, kana kallon fuskarta zaka gane kwanciyar hankali taysamu matsuguni a cikinta, domin sai murmushi takeyi ..
"Mummy me za'a daura? Nifa ban gane wayar da kika gama yiba" Aseey tace tana kallon Mummy don jin ƙarin bayani..
"Ikon Allah!! Sai kuma akace komaine saikun gane Koh? Tunda mutum ya haifeku shikenan shi bashida sirrin kanshi Koh?
"A'a Mummy kiyi hakuri ba haka nake nufiba wallahi, kawai dai maganar ce naji tamini wani iri.
"To tashi ki bani guri tunda kin Zama Yar jarida, mummy tace tana miƙewa.
Falour mummy ta fito tanaso suyi magana da Mummyn sarfraz amma har yanzu bata fito daga sashen daddyn sarfraz ba .
Ta ɓangaren Aayaan kuma wanka yasha da wata irin bugaggiyar shadda saƙar Australia asalin waterproof getzner wadda ya haɗo a cikin kayan shi daga gida, gaba ɗaya kwarjinin shi da zallar kirarshi ta mazantaka saida ta bayyana duba da faffaɗan kirjinshi da cikakken damtsen shi, das kayan suka zauna mishi kamar a jikinshi aka tsara su, fuskarshi dake dauke da dara daran idanu da dogon hanci har zuwa bakinshi mai tudu wanda ya ɗan yi faɗi daga kasa, sai lips dinshi waɗanda suke pink amma sun sirka da ruwan ƙasa ƙasa, saje da ƙasumbarsa kuwa dama a gyare suke sai ƙyallin gyara sukeyi, shikaɗai yau yake jinshi cikin wani irin sihirtaccen farinciki
Daka kalleshi kaga chocolate skin Pakistani.... Turarukanshi waɗanda suka zame mishi jiki suya kwaso ya fara fesawa tundaga kan body spray har zuwa cloth fragrance......
Shi kadai yake sakin murmushi don jinshi yakeyi sakayau, falour ya fito be tarar da kowa ba kai tsaye kawai sai ya wuce dakin dasu mummy suka sauka....
A hankali ya tura kofar ya shiga, babu kowa a ɗakin illa Nawaz wadda ta juya baya tana shafawa muhsien mai..
Bata damu data juyo ba domin a tunaninta Aseey ce ta dawo daga kitchen Kasancewar mummy tashiga yin wanka itama....
Tsaye yayi a bayanta yana kare mata kallo "Lallai Allah yayi baiwar halitta anan gurin, mamakin yanayinta yake yi yau sosai domin ko farkon ganinta da yayi be lura da Irin halittar jikintaba Kasancewar ana cikin tashin hakali. Amma yau tsaff ya ƙare mata kallo iya iyawarsa yana fatan Allah yasa ta Zamo mishi mahaɗin ruhi..
Nawaz dakeji kamar ido nabinta a jikinta sai ta ce "Aunty halan kin fasa cin abincin ne?
"Nine ba Aunty bace" Aayaan yace with full confidence, da wani irin razani Nawaz ta waigo kirjinta na bugawa kamar zuciyarta zatayo waje
Baya tayi tana tunanin yadda zata kaucewa kallon dayake yi mata, kunyar kanta ne ya kamata kasancewar rigar jikinta robace kuma tsaff tabi duk wani lungu da saƙo na jikinta ta lafe.
Rurrufe kirjinta ta fara yi cikin dabara "nifa Malam kaga ka fita gaskiya, "idan naƙi fa?
Aayann yace yana daɗa nufota haɗe da ƙara ƙare mata kallo.....
Baya tayi tana nuna shi da yatsa "Malam ka fita nace inba haka ba Allah zanyi maka ihu.
Daɗa matsota yakeyi yana cewa to saimene idan kinyi ihun? Aini dama nafison kowa yazo ya gammu a haka.
Sosai ya hadeta da bangon wardrobe yana nufar cute pink lips ɗinta da nashi lips ɗin, ita kam Nawaz jitake inama ta mutu ta huta! Wai meye Aayaan yakeyi mata haka ne, shin wai besan yadda turarenshi ke hanata sukuni bane, kashe mata jiki yakeyi ya hanata sakat....
Ganin kuma kamar yanaso ya sunbace yasa tace "wayyo mummy" iya karfinta.
Ai kuwa da gudu mummyn ta fito daga bayi dama dai dai ta gama wankan kenan,
Ganin yadda Aayaann yayi mata rumfa yasa Mummy tace "ƙaniyarka Aayaan! Banason wulaƙanci fa, Wayace ma kashigo ɗakin? Me zakayi mata? Nifa banason fitina..
Ɗan daburcewa Aayaan yayi Kasancewar be zaci mummy tana dakinba sai kuma yace "mummy dama nazone nace ta shirya zata rakamu masallacin juma'a tunda Kinga bamusaniba, ita kuma yar garin ce.
"Ohooo wato a yanda na ganka tare da ita shine kake tambayar ta, Aayaan ka kiyayeni ya mukayi dakai?
"Sorry Mummy bazan sakeba INSHA ALLAH "
"Wallahi kama sake" mummy tace tana balla mishi harara, sai Sannan ya buɗe ƙofar ya fita daga ɗakin..
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Nawaz ta sauke tare da fezar da iska mai dumi daga bakinta...
Mummy ce ta nuna mata kusa da ita " xoki zauna anan daughter!
Salalaf ta kama hannun muhsien ta tawo ta zauna kusa da mummyn, tare dajin nauyinta cikin zuciyarta.
"Nawaz don Allah ki Dena jin tsoron Aayaan, daɗi fa yakeji idan yaga kinajin tsoronshi shiyasa yake daɗa shiga harkar ki, amma idan kika share kika nuna mishi Bakya wani jin tsoron shi duk zai dena takuramiki kinji my daughter?
"To Mummy! Amma mummy nifa tun farkon dana fara ganinshi nakejin tsoronshi,
"Af nace Miki dole ma ki marzaye, inba haka ba kisha wuya ....
"To mummy" Nawaz tace tana nufar bayi itama don watsa ruwa
Bayan ta shigane aseey ta shigo tana murmushi "Mummy Kinga Aayaan kuwa yau? Yadda kikasan wanda ake daurawa aure yau, wallahi kamar ango fuskarshi har wani ƙyallin kyau takeyi...
Balla mata harara mummy tayi don tsaff ta gane nufin Aseey ɗin, so take dole saitaji menene wayar da Mummyn tayi dazu... "Come on wuce ki bani guri, maza ki shirya muhsien
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°