Sashe 112
Safraz Complete Hausa Novel · about 6 min read
Aikuwa ranar idon Nawaz ya raina fata, domin ta gurzu a hannun Aayaan ba kaɗan ba, duka bashin wata biyun da beyi ba saida ya sauke mata su, koda tazo miƙewa kasawa tayi, sai ta koma ta zauna tare da fashe mishi da kuka, haka ranar tayita yi mishi raki shi kuma yana ta jinya....
Wata sabuwar shafin soyayya da kulawa Aayaan ya buɗewa Nawaz, har dai akace abu na Nawaz ne to baya wasa dashi sam.
Itama bayan su maman Sudeis da fatima an kawo sababbin zuwa Makarantar su, Wadda yanzu suna zuwan tane kawai don buɗe ido bawai don koyan wani abu ba, saboda suma sun rigada sun zama yan gari. Anan Nawaz taga yadda ake kula da lamuran miji, ake girmama duk wani abu daya shafi miji....
A groups groups na manyan mata suka sata a Whatsapp, hakan saiya daɗa wayar da Nawaz ɗin sosai, ita da bata damu da waya ba sai gashi yanzu tana dubawa sosai.
Irin sabbin salon kular da Nawaz takeba Aayaan saiya sa ya ƙara sakar mata duka ragamar komai nashi.....
Sanda Yan biyu sukayi wata shida ne suka koma Nigeria.
Anan Aayaan ya biya wa Abban Nawaz da ummin ta Hajji da Umrah, umma kuma ya biya mata kuɗi aka fita da ita zuwa Egypt don ayiwa kafarta aiki tunda har zuwa Lokacin bata warke ba.
Bayan sun tafi ne kuma yasa aka rushe gidan duka sannan aka chanza mishi fasali, Sosai ya kashewa gidan kuɗi don Kawai ya farantawa Nawaz rai.
Kusan duka manyan ahalin Saida ya biya musu umrah daga ciki kuwa harda inna talatu, matasa kuma ya basu jari, waɗanda kuma suka gama makaranta ya samar musu akin yi.
Anan ne wani daga cikin securities din Aayaan ya nuna yana son Jamila,
Ba'a tsaya boye boye ba aka ce mishi bazawara ce harma ta haihu amma ɗan ya rasu, a haka yace yaji ya gani.
Nanma dai duka Aayaan ne ya dauki nauyin komai aka yi bikin taro ya tashi Lafiya, itama Fauziyya ya bata jari me kauri.
Umma kuma sanda aka dawo da ita, kafarta ta warke tsaf tana takawa saidai babu yatsu guda biyu. Haka ta riƙa kuka tana shiwa Nawaz Albarka, Ashe ita ɗin data tsana wata rana itace zata zame musu garkuwa, kuma bango majingina.
Ita kanta Nawaz idan ta kalli kanta ta kuma tuna cewa itace ke koyarwa a HAYATUL ISLAM don a bata dubu Goma saboda su sai abinci, Lokacin da umma ta rufe store, sai taga kamar mafarki....
Komai yazo mata a bazata, itama bata tsaya iya nanba saida tabi duka kawayanta tayi musu sha tara na arziƙi.
Kullum Cikin ƙara godewa Allah takeyi, ta kama mijinta da yaranta ta riƙe kam, haka ma Yan uwan ta dana mijinta, duk shekara idan akayi lissafin riba a Companyn ta da AAYAAN ya bata, bata cire komai a ciki, duka take rabawa yan uwa da abokan arziƙi.
Haka idan suna england duk bayan sati biyu sai ta ziyarci su haidar da Aunty Aseey, sosai muhsien ya saba dasu mamaa, har cewa yakeyi shima mumynshi ta haifi irinsu.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Ita kadai ce take saukowa Daga cikin jirgin babu komai a hannun ta sai karamar 👛 purse, sanye take cikin farar abaya Wadda akayiwa kwalliya da Golden yellow, sosai rigar ta amsheta, domin ta haska ɗanyar farar fatarta.
Idan ka kalleta zaka zata irin larabawan misra ɗin nan ce, kuma ba Lallai ka yarda tayi Aure Bama balle a kai ga haihuwa.
Wai a hakan ma tana cikin tashin hankali ne.
Cab ta tara ta kaita har Kofar gida, tana shiga ta rushe da kuka tun a bakin falour.
Hankalin kowa tashi yayi ganinta ita kaɗai gashi kuma tana rusa kuka.
Da sauri mummy ta tareta tana cewa "daughter ina Aayaan ɗin, ina su mamaa?"
Suma dai su Colonel miƙewa sukayi saboda fargaba.
Cikin muryar kuka Nawaz tace "duka suna england"
"Meya faru kika tawo ke kaɗai?" Mummyn ta kuma cewa zuciyarta na bugun uku uku.
"Mummy ashe tun wata huɗu da suka wuce yaya Aayaan ya lura inada ciki, saboda kada na gane sai ya siyo mini wani magani yace kullum nasha Guda daya, wai yana hana ɗaukar ciki kuma wai idan ina shan shi bazan kuma haihuwa ba sai bayan shekaru da yawa kum......
"Su Naufal dake gefe ne suka kwashe da dariya "
"Au dama akwai sa'an ku Anan kenan, kun wuce ko kuma saina ci muku " Daddy colonel yace cikin faɗa, ai kuwa da gudu suka shige ɗaki suna dariyar dramar Nawaz da Aayaan Wadda bata ƙare wa.
"Daughter go on muna jinki" mummy tace tana kallon Nawaz ɗin cikin fargaban me zata ce a gaba.
To cikin kwanakin nan sai naketa fama da tashin zuciya da amai ga kwaɗayi, kuma inajin kamar ana motsi a ciki na, shine naje asibiti, da ya hana amma daga baya ya yarda naje."
Ƙara fashewa tayi da kuka Sannan taci gaba
"Shinefa a asibitin akace ciki gareni kuma har yafi wata huɗu, kuma da akayi scanning akace wai har yan biyu fa, kuma duka maza"
Da gudu su Naufal dake labe suka fito suna murna, "wayyooooo daɗi, munata ƙara yawa"
Duk yadda Mummy taso ta kanne Amma saida dariya ta kwace mata, shima Daddy Saida yayi murmushin manya ...
"Lallai ne abinda son yayi kenan? To ai kuwa zamu haɗu, Naufal kira yayan ku kace daughter nanan kuma maza maza ya biyo flight ɗin yamma yazo ya sameni shida su mamaa"
Zukar majina Nawaz tayi Sannan tace "mummy kumafa yanzu watansu mamaa takwas fa"
"Kada ki damu ki barni dashi, ai zaizo ya sameni ne"
Haka dai aka lallaba Nawaz aka samu ta hakura, koda Aseey taji labari kamar ta zuba Ruwa a kasa tasha don farin ciki, itama daman tanata fama da laulayin ƙaramin ciki.
Kafin wani lokaci labari ya bazu a cikin dangi, inda itama hassu tana nan tana fama da nata ƙaramin Cikin, koda Sarfraz yaji labari sai cewa yayi Allah yasa itama hassu ta haifi ƴan biyu.
Koda Aayaan ya iso cikin dare baice komai ba sai aikin lallashin Nawaz da yayi ta fama, haka dai aka haɗu aka bata baki ta haƙura akan zata bishi su koma sai dai fir mummy taƙi basu su mamaa, tace dama nata ne jira kawai take yi a yayesu, yanzu kuma tunda an yayesu ta dauki abin ta.
Koda suka koma england ɗin sai Aayaan ya zama kamar wani sabon ango kullum yana nakiƙe da ita barin babu kowa daga ita sai shi.......
*Tammat bi hamdulllah*
*Komai farrare ne kuma kararre, amma banda ikon Allah*
*Yau dai Allah cikin ikon sa yasa na gama wannan littafin na SARFRAZ lafiya, Alkhairin dake ciki Allah ya bamu ladansa, kurakuran dake ciki kuma Allah ya yafe mana.....*
*Ina miƙa godiya ta ga duka members na*
*MATAR RASHEED NOVELS*
*AK SARAKI PALACE*
*AK SARAKI NOVELIST GROUP*
*INUWAR SHARRI FANS GROUP*
*SANADIN HIJIRA FANS GROUP*
*SIRRIN RUHI*
*ASLI SMASHER FANS GROUP*
*RUƊANI FANS GROUP*
*FADAR AUTAR MANYA*
*M&Z NOVELS*
*WOMEN 24 TV NOVELS*
*VIP 24 TV NOVELS*
*HAUSA NOVELS 2K2*
*ƘASAITACCIYAR MACE GROUP*
*DAUDAR GORA FANS GROUP*
*ROYAL STAR WRITERS*
*Da dai sauransu, ina fatan zamu haɗu a littafina na gaba mai suna IZAYAR RAYUWA......*
*08093215055 Number ta gamai buƙatar zumunci, gyara ko shawara, Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji tana ƙaunarku duka.*
*29/5/2023 Monday*
*9/11/1444 Monday*
*Nagodeeee da ɓata lokacinku mai ɗunbin daraja da kukayi kuka bibiyeni har zuwa ƙarshen littafin.........*
*Matar Rasheed ❤️*