Sashe 28
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To mummy kiyi hakuri ba laifina bane, munje wani mall ne siyayyah to wayan na hannun muhsien shine ya manta da ita a cikin folder chocolate a cikin mall ɗin...
Babu irin nemanta da banyi ba, sai jiya ina cikin shiri naji doorbell koda na duba ashe keeper din mall ɗinne wai sunje zasu ƙara abubuwa a cikin store ɗin shine suka ganta, to da suka duba emergency information din wayar shine suka ga address ɗinmu..
Hamdala mummy tayi jin kowa na cikin ƙoshin lafiya, sai sannan suka gaisa da tambayan juna bayan rabuwa....
"Mummy wai ko ina sturbborn brother ɗina yake? Dan Allah kada kice min baya gida.....
"Hmm Aayaan ɗan rikici, yananan munyi tafiya ne bamu ɗade da dawowa ba shine yake barcin huce gajiya. Cewar mummy tana kallon Aseey cike da ƙauna.
Sai kuma tace Aseey ina muhsien ɗin?
Murmushi Aseey tayi "Au na manta yana falour gurin Wata beautiful lady,
Sai kuma ta rike baki "mummy kada dai kice min bro Aayaan ne yayi aure!
"Da dai bakizoba da anyi"
"Eye mummy da raina da lafiya ta ina cikin duniyar nan ban mutuba ace ƙanina ɗaya tilo zaiyi aure amma ban saniba... Aseey ta faɗa cikin tashin hankali
"Calm down Aseey, ba haka bane nadai yi Miki ne.
Sai sannan Aseey ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya....
Mikewa tayi "bari naje gurinshi in bashi surprise"
Murmushi Mummy tayi mata "Adawo lafia, Ni dama bana shiga abinku saboda yanzu zakuyi faɗa Yanzu kuma zaku shirya, idan mutum ya shiga ma kunya Zai sha...
Tana fita ta nufi ɗakin Aayaan da gudu ko knocking batayiba tasa security kofar ta buɗe, dai dai ya fito wanka sanye da Blue Black ɗin bathrobe fuskarshi duk alamun ruwa sai gashin dake kwance luff a faffaɗan kirjinshi sai ƙyalli yakeyi.
Tsayawa kawai yayi yana kallonta, mamaki ne da farin ciki suka kamashi lokaci ɗaya, da gudu Aseey ta ƙarasa ta rungume Aayaan, saboda girman jikinshi sai ta zama ƴar ƙarama a gaban shi dukda ita ce yaya
"My One And only bro nayi kewarki sosai Wallahi, hannu tasa ta ɗan jamishi kumatu, naga ka ƙara kyau ne "hope mummy tana kula dakai yadda ya kamata?
Cikin idonshi ta kalla tana jiran amsar da zai bata, shikuwa Aayaan gira ɗaya ya ɗaga mata bece komaiba...
Dukan wasa Takai mishi "Lallai ne Aayaan wato har yanzu wannan ɗabi'ar taka ta ɗagawa mutane gira tananan, Wallahi bakasan yanda kakeyi bane shiyasa kakeyi...
Wallahi idan kayi komawa kakeyi sak kamar kwarto, kwarton ma irin wanda ya saba da kwartanci, sannan ta ruga da gudu
Binta yayi da gudu shima yana cewa "gaskiya sister kin cuceni wallahi, nifa na rigada na saba bawai inayi da wata manufa bane, kuma Wallahi inaso na Dena Amma na kasa.
Hakuri ta bashi sannan ya hakura ya tsaya, "ina Sweet boy ɗina?
"Au yana gurin bakuwar mummy, tunda muka shigo ya tafi gurinta.
"Au Nawaz?
"Ban san sunan taba, wata dai mai kyau sosai.
"Eh itace" cewar Aayaan yana basarwa
Kallonshi Aseey tayi "bro wace ita?
"Sis bari na shirya its a long story.
Guri ta samu ta zauna, shikuma ya shiga ciki don shirya wa,
Ba'a daɗe ba ya fito sanye da baƙar T-shirt da Blue Black ɗin cinox trouser, gashin kanshi sai ƙyalli yakeyi saboda gyaran daya sha.
Ga wani fitinannan kamshi da yakeyi,
Ɗago dakai Aseey tayi "hey bro wannan adon yayi yawa kaida ba mata garekaba sai kayita wahalar da kanka, dama ace Kanada matane to saika riƙa samun lada.
Murmushi yayi ''Sis yanzu maganar da kikayi kinyi adalci kenan, ache saboda banida mata kada nayi wanka da kwalliya?
"To ai kaine Aayaan munjira munjira amma shiru, mummy ma tayi Maganar, tayi maganar!! Har ta gaji ta dena, yanda bamuda Yawan nan kamata yayi ka duba ka samo mana mai hankali a haɗu a rufawa juna asiri.
"Sis bawai Auren bane banaso Wallahi yanda mata suka zamane yanzu abin yake bani tsoro.
"Kada ka damu muna tayaka da addu'a insha'Allah Allah zai baka mata ta gari fiyeda wacce kake tunani.
"Ameen Nagode sosai sis, kitashi muje naƙosa naga muhsien wallahi.
Miƙewa sukayi Aseey na murmushi "to mayen yara, Allah dai ya nuna mana naka......
Koda suka fito falour basuga su Nawaz ba, "may be suna ɗaki, muje mu duba" cewar Aayaan yana nufar ɗakin Nawaz....
General password yasa a kofar ta buɗe, tare suka shiga, babu su a falourn sai kawai Aseey ta wuce cikin ɗakin.
Kwance ta gansu sai sharar barci sukeyi Nawaz ta rungume muhsien gam....
Murmushi Aseey tayi "wow ko yaushe har suka saba haka?
Bin Nawaz tayi da kallo tana mamakin irin farinta (milky white) duk da ita ma fara ce amma ita Golden white ne kalar skin Ɗin su ita da Aayaan...
Ga kuma yanayin gashinta, kuma da alamu ba relaxer tasa ba, cewa tayi "ko a ina suka sami wannan yayinyar?
"A daji na samota" Abinda Aseey taji muryar Aayaan tace kenan daga bayanta..
Da sauri ta waiga "A daji kuma?
Gira ɗaya ya ɗaga mata sannan yace "Eh"
"Fita muje, ka wani shigo ɗakin mata, kasan dai ita ba muharramar ka bace koh?
Muje main falour ka bani labarin achan...
Gaba ya shiga tana binshi a baya.
Da ƙarfi tace "tsaya Aayaan"
Waigowa Aayaan yayi da sauri jin yanda tayi maganar.
Da sauri ta karasa gabanshi ta riƙe hannun shi tana dubawa "bro yaushe kaji Wannan ciwon?
Baya son yayi mata ƙarya sannan kuma bayaso yace Dalilin Nawaz aka harbeshi..
"Harboni akayi shine na kare da hannuna"
"Subhanallah, Allah Nagode maka! Wallahi don babu yanda zanyi ne amma Sam banason Wannan aikin sojan da kakeyi.
Haɓarta ya tallabo "sis calm down, kawai kici gaba da yimin addu'a insha Allah nothing will happen.
Riƙe mata hannu yayi zuwa main falour, a kujera ya zaunar da ita sannan ya fara bata labarin yanda suka haɗu da Nawaz.....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sarfraz bawan Allah, yananan kwance kamar kullum, babu um babu um'um.
Yauma hassu ce zaune a gefenshi ta zabga uban tagumi kamar yadda takeyi koyaushe.
Tunani takeyi anya lafiya kuwa! Tunda suka tsinci sarfraz be taɓayin bayan gida ba ko sau daya.
Sanin batada amsa yasa ta hakura sai bandi ya dawo ta faɗa mishi..
A zahirin gaskiya bata taɓa tunanin zata haɗu da wani wanda bata saniba taji tausayinshi haɗe da kaunar shi kaman yanda takeji game da sarfraz ba.
Batada sukuni kullum illa tayita Sallah tana yi mishi addu'a akan Allah ya bashi lafiya duk da sallar ma rabi da rabi ce....
Tashi tayi zuwa gabanshi, kanshi ta ɗaga ta sa mishi pillow sannan ta maida kan a hankali, haka take yini tanayi, idan tasa mishi bayan wani lokaci saita cire wai kada ya gaji idan aka kuma daɗewa sai ta kuma maida mishi.....
~To sai dai muce sannu hassu Allah ya bada lada~
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Rufe baki Aseey tayi jin abinda ya faru "tabɗijan wai! Ashe abinda ya faru kenan? Hu um cewa zakayi tsawoncin kwana gareta amma Aida sun ganta sanda ta gudu da harbeta zasuyi...
"Wallahi sis Nima Saida naji fargaba sanda na ganta, Wallahi daurewa nayi amma na zata aljana ce saboda bazan taɓa tunanin mutum sai fito daga cikin wannan uban dajin ba....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Mummyn sarfraz dai a fili ta hakura amma a baɗini kullum idan ta keɓe ita kadai ta rinƙa kuka kenan har sai kanta yayi mata kamar zai rabe biyu,
Kullum gidan nasu a cike yake da mutane, ana addu'a akan Allah ya bayyana shi idan kuma ya mutu Allah ya jikanshi kuma yayi mishi Rahma.....
Yan islamiyyar su SARFRAZ su Abdul duk sunzo amma da kuka suka fita jin abinda ya faru,
Kowa yana tuna yanda suke abubuwan su a makaranta, ga sarfraz dama akwai farin jini da shiga rai, ko Malam Abdullahi shugaban makarantar da yazo Saida yayi kuka...
Haka dai kullum gidan yake wasu na fita wasu na shiga.....
Daddy kam ya hakura ya fawwalawa Allah komai Nashi, ya amshi kaddara kuma ya ajiye cewa haka Allah ya tsara mishi, haka masoyiyarshi abar kaunar shi ta rasu sanda zata haifi sarfraz sai kuma yanzu shima SARFRAZ ɗin babu, Fatan shi yanda Allah ya musanya mishi da mummy to Allah ya musanya mishi yanzuma da abinda yafi Alkhairi.....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Nawaz ce ta fito daga ɗaki riƙe da hannun muhsien, sanye take da normal riga da zani, kayan sunyi mata das ajikin ta kamar an gwada ta,
Shiko muhsien sanye yake da pant suna tafe yana mata rikici waishi zaici chips, "my friend kayi shiru yanzu zan haɗa maka kaji?
"Cewa yayi to Aunty muje kitchen ɗin, sam bataga su Aayaann ba saboda hankalinta nakan muhsien gaba ɗaya.
Su kuwa tunda ta fito suke kallon dramar da muhsien yakeyi.
Ciccibar muhsien tayi suka shiga kitchen...
Aseey ce tace "bro kallon ya isa haka.
Aayann wanda gaba daya tunanin shi da ruhinshi sun tafi gun Nawaz ne yayi ajiyar zuciya "nifa muhsien nake kallo ba itaba, naga ya wani ƙara girma da wayau, ga wani kyau da yayi.
Tsaff Aseey ta gane Nawaz yake kallo kawai dai ya waske ne...
Tun bayan fitowar Nawaz Aseey ta gane hankalin Aayaan sam baya gurinta, binibini sai yayi tsaki sai kuma ya kalli ƙofar kitchen ɗin.
Ta ɓangaren Aayaan kuma ji yayi yanaso ya ƙara ganin Nawaz gashi Aseey ta Kafa ta tsare kuma shi beso tayi mishi wata fassarar ta daban.
Daurewa yayi yace "sis bari nazo, mikewa yayi ya nufi hanyar kitchen ɗin Ya shiga, dai dai ta gama kwashe chips ɗin kenan Aayaan ya shigo..
Kirjinta ne ya fara heaving yana sama yana ƙasa saura ƙiris chips ɗin ya zube Aayaan yayi saurin riƙe plate ɗin.
"Meya faru?" Aayann Yace yana karantar Yadda jikinta yake rawa...
Idonshi ne ya faɗa kan zoben da sarfraz ya bata, da sauri ya riko yatsan yana kallon zoben..
Ƙiris ya rage ta zabga ihu amma saita tsaya ganin beyi mata komaiba...
"Wa ya baki zoben nan" Aayaan yace yana ƙoƙarin cire zoben daga yatsanta.....
Sorry for the late update, WALLAHI na ɗan samu matsala ne ....
*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*Episode 31*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️
Muryar ta na rawa tace "don Allah kada ka cire.
"To ki faɗa min waya baki?