Sashe 51
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan karan kam saida Nawaz taga kamar magungunan sunyi yawa, amma sanin cewa inna bazata cutar da ita ba yasa ta kawar da zancen daga zuciyarta.
Da yamma bata bari inna ta kuma yin komai ba, ita ta daɗa share gidan tayi wanke wanke ta ɗora wani sabon abincin wanda zasuci da dare...
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Washegari.....
Zaune Aayaan yake a stool yana taje kanshi alamun yanzu ya gama shiryawa, wayarshi ya ɗauko yana duba sakon daya Turawa Nawaz kota gani, aikuwa baiyi delivered ba "it means bata ganiba kenan" yace yana yana dafe kanshi.
Dai dai nan kuma wayarshi tahau ƙara, koda ya Kalli screen ɗin saiyaga Farouk ke kiranshi, Aikuwa yaji daɗin kiran saboda dama kiranshi yakeso yayi yanzu, "yooo ya dai"
"Alhamdulillah" Aayaann yace yana miƙewa...
"Ganifa a compound, nakai minti goma Acikin gidan nan, "meyasa baka shigo ciki ba?"
"Hakanan wajen ne naji yamini daɗi yau Wallahi.
"Okay to bari na fito!" Sannan ya nufi kofa ya buɗe zuwa falour, a dining ya tarar da Aseey tanaba muhsien abinci ita kuma Mummy tana zaune riƙeda hisnul Muslim tana karantawa, tsaff take kamar ba ita bace jiya take cikin tashin hankakiba, "mum zan fita, Farouk yana waje yana jirana!"
"Allah Sarki Farouk meyasa be Shigo ba, kace ina gaishe shi, saika dawo.
" Bro a dawo lafiya" Aseey tace tana ɗaga mishi hannu.
Murmushi yayi "Insha'Allah dear, muhsien babu magana? Sannan ya juya ya fita zuwa harabar gidan...
Zaune ya tarar da Farouk a saman mota, ganin Aayaann ɗin ya fito yasa Farouk ɗin ya diro daga motar tare da nufar shi cikin sauri, rungumeta juna sukayi sannan sukayi musabaha.
Sosai suka gaisa inda Farouk yayi mishi ban gajiya, cikin mota suka shiga suka zauna, Farouk a driver seat Aayaan kuma a gefen mai zaman banza....
Farouk ne yace dama nazo na ɗaukeka ne muje kauyen fulanin nan, kasan bayan munyi waya naje har gida na dubashi.
"Gaskiya ka kyauta, Toya jikin nashi?
"To da sauƙi zance dai, amma dai jiya iyau, don koda naje tarar wa nayi yanata ihu waishi sai ansiyo mishi ice cream, gashi namijin bayanan sai macen, infada maka haka na kwaso su muka fito gari na siyar mishi sannan na maida su.... Ai ranar naga rukici....
Murmushi Aayaan yayi "to muje but Farouk wallahi ina cikin wani hali! Amma it's a long story....
Shiru Farouk yayi Sannan yace "koda na ganka na lura Akwai Abinda ke damunka, but saina zata ƙila daga barci ka tashi, Amma hope it's not serious...
Fita da motar Farouk yayi daga gidan suka dau hanyar, sannan ne Aayaan ya Fara bashi labari tun randa suka haɗu da Nawaz a daji har zuwa bikinsu da guduwarta.
Farouk kam jin abin ya rikayi Kamar mafarki, "Aayaan Are You alright? Wai kana nufin wannan abun a gaske ya faru? Kodai Wani littafin ka karanta kake bani labari...
" Farouk zaka soma Koh! Nifa dama shiyasa wani zubin banason Neman Shawara a gurinka saboda saika gama yiwa Mutum shakiyanci tukuna....
"Afwan! Kaina bisa wuya abokina" farouk yace yana gyara fuskar shi Irin da gaske ɗin Nan yake..
Dai dai Nan ya iso bakin bukkar su hassu, parking yayi suka shiga harabar gidan suna sallama, ai kuwa Muryar Aayaan ce ta maƙale a wuya, Domin wani yagani sak Kamar yanda yaga SARFRAZ a photo, tabbas wannan SARFRAZ ne Duk da ban ganshi a fili ba amma wallahi shine....
Da gudu ya ƙarasa kusa dashi Yana cewa "SARFRAZ, kaine?
Bandi dake gefe yana fama da SARFRAZ akan yaje hassu tayi mishi wanka ne yace"kai waye???
"Ni yayan shine " Aayaan yace babu ko ɗar a zuciyarshi, Hassu Dake gefe riƙe da kwandon wanka tace "wallahi ko kai waye baka isa ka rabamu ba, Sannan ta kalli likitan tace " kai likita haka mukayi dakai? Bacewa kayi zaka memo mana taimako akaishi ayimishi maganiba, to meyasa ka nemo ƴan uwanshi???
Ɗago Kai Aayaan yayi Yana kallon hassu wadda tayi kicin kicin da rai
Ina jiran sharhi, yaudai SARFRAZ ya dawo💃💃💃💃💃
*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*
*Episode 49*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*
Sai wani mazurai takeyi, ita ala dole babu mai rabata da sarfraz.
"Sarfraz zo nan!" cewar hassu tana daɗa cin magani, Ai kuwa da sauri sarfraz ya miƙe ya karasa kusa da hassu, shima sai kallon Aayaan ɗin yakeyi.
Farouk ne yace "hassu ki barshi yazo gurin yayan shi mana, bakiga sunyi kama da juna ba? *_(Shi ɗin ma bawai yasan shi bane illah dai yagane SARFRAZ ɗin da Aayaan ya gama bashi labarine, duba da Yadda kamanninsu ya nuna a fili)_*
Chuno baki Hassu tayi sannan tace "bazai zoba" Tare Da rungume sarfraz ɗin. Shima SARFRAZ saiya ƙara rungume hassu sannan shima yace "bazai zoba".
Aayaann kam sai abin ya bashi dariya yadda SARFRAZ da Hassu suka rungume juna kamar zasu haɗe, ga mazuran da hassu takeyi, bandi ya kalla Sannan yace "wai yaushe suka saba ne haka? Bayan naga ko cikakkiyar wata biyu ba'a yiba".
"Hmmm ai waɗan nan ka kalle su Kawai, don nima Babu Yadda banyiba amma ganin abun yafi ƙarfina shiyasa na zubawa sarautar Allah ido, itafa keyi mishi wanka, ita keyi mishi komaima, to ƙarshe ma bari kaji gado ɗaya suke kwana rungume da juna...
😳zaro ido Aayaan yayi "Lallai, ikon Allah, kace abin Babba ne! Shikam Farouk dariya yakeyi Tare Da nuna Hassu yana cewa "Ashe ɗa kika tsinta, to aini danasan da labarin nan da tun tuni Maman SARFRAZ nake ce Miki..
Ɗan murguɗa baki Hassu tayi " ina ruwanka? Ai kai wallahi bakada amana, daga cewa ka taimaka shine zaka wani nemo yan uwan shi, to basai muga wanda zai raba muba.
Shima dai sarfraz saiya murguɗa baki sannan yace "ina ruwanka? Ai kai wallahi bakada amana, daga cewa ka taimaka shine zaka wani nemo yan uwan shi, to basai muga wanda zai raba muba.
Me Aayaann zaiyi inba dariya ba "aaah Lallai Ashe Hassu tazama role model ɗinshi, wato duk abinda tayi shima sai yayi.....
Shi dama Farouk tun tuni dariyar yakeyi, abin kamar a Film..
Guri Aayaan ya samu ya zauna sosai sannan yace "hassun SARFRAZ yanzu ya kikeso ayi to?
Ɗan kallonshi hassu tayi Sannan ta wani basar irin ita isasshiyar nan, saida ta ɗauki Kusan minti Uku Sannan tace "kawai mu Yanzu Bama buƙatar taimakon ku, kawai ku tafi ku barmu, inyaso Ni sai in siyar da su gwalbo mukai kuɗin chan Asibitin da za'a yi mishi maganin.
Tuntsirewa da dariya Farouk ya kuma yi "wai ke in banda abunki meye Abinda ya shafe ki dashi? Naga ga dan uwanshi ko, to kibari su tafi mana! Ke meye naki?
Daɗa ƙanƙame sarfraz hassu tayi "wallahi baku isa ku rabamuba, ina ruwanku damu, kunsan kuna sonshi kuka bari ya ɓace?
Shifa Aayaan Abin harya fara sashi tunani, Wato haɗuwar jini ma wata abace kenan, yadda yaga hassu ta dage yasan idan aka rabasu zata iya shiga Wani hali, duba da Yadda shima yaketa fama da damuwar rashin Nawaz
Kwantar da murya Aayaan yayi "haba ƴar ƙanwata! Ai ki kwantar da hankalinki domin ƙafarki ƙafar sarfraz, babu Wanda Zai rabaku ko don wahalar da kikasha dashi. Yanzu abinda nakeso shine ki haɗo kayan ki kizo mu tafi tare.
Cewa tayi harda bandi amma Koh?
"In banda abinki dama ya za'a yi a tafi ba tare da yaya bandi ba?
Mota suka shiga Dukansu suka tafi gidan baffa malam, anan Aayaan ya shaida mishi cewa zasu tafi da sarfraz tare da su hassu amma insha Allah ba za'a daɗe ba zasu dawo, domin idan Allah yasa anyi aikin a Sa'a ba za'a wuce wata Uku ba Komai zai daidaita...
Da dai baffa malam Yaso ya hana, amma yadda ya gansu duka babu alamun cutarwa sai ya amince amma duk da haka saida yace amanar hassu ya basu, don Allah su kula da ita.
Bukkarsu suka koma sannan suka haɗa abubuwan da zasu nema duk da dai Aayaan jira yakeyi su kwasa in anje ya zubar ya sai musu wasu...
A mota ne Farouk da Aayaan suka chanza harshe zuwa Turanci, anan Aayaann ya ƙarasa ba Farouk labarin abubuwan da suka faru, da kuma ta inda sarfraz ya zama ƙaninshi...
"Lallai wannan Nawaz ɗin Alkhairi ce a gareka, duk dalilinta abubuwa masu kyau sunata faruwa, Allah dai ya daidaita kanku, shi kuma safraz Allah ya bashi lafiya.
" Ameen Aayaan yace Tare Da cewa yanzu ya kake gani, in tafi dasu duka gida ne, ko Akwai wata shawarar da kake ganin zatafi?
Farouk ne ya kalle shi sannan yace "A nawa tunanin kada ma ka faɗawa kowa ka ganshi, yanzu haka kada kaje dasu gida, mu wuce gidana kawai, ko mummyn ka please kada ka faɗa mata.
"Haba Farouk! Meyasa zakace haka? Bayan kasan kowa burinshi yaga sarfraz, kuma kowa damuwarsa a yanzu ita ce a ina za'a ganshi?
"Na fahimceka yoo, amma abinda nakeso ka sani shine, a yanzu kowa ya fara cire rai dashi, kuma zuciyar kowa ta ɗan ragu da raɗaɗin rashin shi, to yanzu idan ka kaishi a hakan kasan Dole hankalin kowa zai tashi dalilin ganin halin da yake ciki, kuma ba Lallai idan anyi musu bayani su yarda ba, sannan hakan zai iya kawo delay a tafiyarsu chan England ɗin, gashi irin wannan amfiso ayi surgery ɗin da wuri.
Shiru Aayaan yayi "to Shikenan, Allah yasa haka shi yafi Alkhairi, pls zanbar komai a hannunka na arrangements ɗin, ka shirya komai daga kan yin visa har ticket, And kuma ka kira haidar ɗin ka sanar dashi Kafin su isa, wai Farouk Dukansu zasu tafi ko kuwa?
Kyalkyalewa Farouk yayi da dariya Sannan yace "ai kai Alhaji ne basuda matsala.
"Niba wannan nake nufi ba, shin zasu yarda su hau jirgin sama ma kuwa?
Kamanta ko wane masoyi kanyi komai a kan masoyinshi? To naga ai suma masoyane😉!
Haka dai sukayi parking a harabar gidan Farouk, ciki Farouk ya kaisu hassu gurin mai dakinshi (Safna), Sannan ya dawo gurin Aayaan dayake yayi-yayi dashi ya shiga ciki, shikuma yace ba zai shiga ba.