Sashe 74
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina yiwa kowa fatan ALKHAIRI, naga wannan kaunar, shin batayi min yawa ba kuwa??? Naga texts, na amsa kira naga online message ɗin da bansan adadinsu ba, Nagode Nagode sosai sosai Allah ya bar ƙauna da zumunci.
Kwana biyune abubuwa suka cikurkuɗemin wallahi, amma In'sha Allah komai yazo ƙarshe.
*MATAR RASHEED* ✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*64*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Shiru Nawaz tayi tana kallon shi da gefen ido, addu'a takeyi azuciyar ta "Allah dai yasa bada gaske yakeba, Duk saitaji zaman motar ma ya isheta.
"Madam bakice komai ba?"
Namma dai tsit tayi batare da tace komai ɗin ba illa wasa da taketayi da yatsun hannunta.
Ganin halin data shiga yasa Aayaan ɗin yin shiru ya kyaleta, amma a zuciyarshi yana cewa "sarfraz ya kuma maida min da hannun agogo baya, da harta fara sakin jiki dani sosai amma yanzu tsoro ya dawo sabo fill"
Ita kuma Nawaz babu abinda keyi mata yawo a zuciya illah yadda taje ta tarar da hassu da farko hajaran majaran kamar gawa "yanzu ace ƙaramin yaro kamar SARFRAZ ne yayi wannan aika aikar to babba kamar Aayaan ya zaiyi kenan?" Cewa tayi "wayyo nashiga uku na wallahi"
Ashe a fili tace bata saniba, jan birki Aayaan yayi tare da cewa "sweetheart shiga uku kuma? Meya faru?
rimi-rimi da ido tayi don tama rasa wace ƙarya zata rantaɓa mishi Sai kawai tace "Ni ummina nakeso nagani"
"Is that the only problem? Aayaan yace yana son gane gaskiyar abinda take nufi
Gyada kai Nawaz tayi alamun "eh"
"Okay to kibari muje gida yanzu zaki ganta, ai sai gobe zasu tafi Koh?
"Eh da yau zasu tafi amma mummy tace su bari gobe akaisu "
"Okay hmmm ai Mummy akwai son baƙi, don ma tasan idan tace ta zauna ba zama zatayiba to Wallahi da cewa zatayi su zauna tare"
Murmushi Nawaz ɗin tayi sannan tace "ai hakan yanada kyau sosai, kuma Ni Wallahi duka dabi'un Mummy suna burgeni, akwaita da son jama'a da mutuntasu
Daɗi sosai Aayaann yaji a ranshi ganin Nawaz ta ɗan saki har suna hira.
Cigaba da tuƙin shi yayi yana sako mata zance jefi jefi.
Koda suka isa gida be bari ta fita daga motar Ba saida ya ɗan jata da hira yanata tsokanarta "wai yaushe ne matar nan tawa zata yarda da cewa ita ɗin mata tace?
"Nayarda mana" Nawaz tace tana murmushi
"Anya kuwa sweetheart maganar nan har zuci take kuwa?"
Murmushi ta kumayi batace Komai ba.
Sai Sannan ya buɗe mata motar suka fita a tare, a bakin kofar falour suka ci karo da kakar Nawaz "A'a megida daga ina kuke ne, tun ɗazu sai cigiyarku akeyi amma babu ku babu alamun ku, nifa nafara ganin alamun rashin adalci a wannan tafiyar, ka ɗauke Amarya kun fice kabar uwargida ko kuɗin karin kumallo baka bar mata ba.
Murmushi Aayaan yayi tare da saka hannu a aljihu yana ciro kuɗaɗe, a cikin hannun ta ya zuba kuɗin Sannan ya haɗe hannunshi guri ɗaya yana cewa "uwargida Sarautar mata don Allah ayimin afuwa, na tuba nabi Allah na biki"
Kyalkyalewa da dariya Ammah tayi tana cewa "Ato Shikenan an yafe maka ka fanshi kanka, aini nazata har za'a juyamin baya ne.
"Wane Ni? Ai ban isa ba, kin manta kece nishaɗi na!
Ita dai Nawaz raɓewa tayi ta barsu nan ta shige ciki don taga abin nasu bame ƙarewa bane.
Tana shiga ta tarar da Aseey ta janyo trolly fuskar nan a kumbure kamar an watsawa flour yeast.
"Aunty kardai kice min har kin shirya?
"Hmm sis wallahi baban muhsien yaso ya ƙure nine, nayi nayi dashi ko kwana ɗaya ya ƙaramin don naje gida na kwaso ragowar kayana amma ya baɗe idonshi da toka yace shi sam besan zancen ba, wai kafata ƙafarshi.
"To Aunty ai yayi ƙokari wallahi, kin fa daɗe da zuwa, Allah da wanine bazai yarda ba.
"Hmm amma wanin ba irin mijinkiba Koh? Don naga alamun kece ma mijin don sam bayason ɓacin ranki, yayarda shi ya cutu da ranki ya ɓaci.
"Kai Aunty! Allah ba haka bane, kawai dai shi yanada tausayine sosai"
"Hmmm mu namu mazajen basada tausayin kenan Koh?
Zaro ido Nawaz tayi "Allah Aunty ba haka nake nufi ba Wallahi..
Bata ƙarasa faɗan Abinda zata faɗa ba saiga Mummy ta shigo riƙe da ƙaramar jakar hannu tana miƙawa Aseey, kallon Nawaz tayi "daughter Kawai sai mu nemeki mu rasa da sassafe, ina kukaje ne?
"Ina kwance da safe yaya Aayaann ya kirani a waya wai inzo muje Gidan Sarfraz wai bashida lafiya, saida mukaje naga ashe hassu cema.
Saida ta faɗi hakan kuma kunya ta rufeta ta fara sunne kai.
Basarwa Mummy tayi "ayyah ai gajiyar biki ce nasani, amma ai jikin da sauƙi yanzu ko?
"Eh taji sauƙi sosai don ko yanzu da muka tawo tana barci.
Juyawa Mummy tayi ta fita da sauri don tanaso ne taje ta faɗawa Mummyn SARFRAZ cewa SARFRAZ yayi aika aika ya kamata aje a duba yarinyar mutane, kuma kada abari kowa yaje balle azo ana yada ƙananun maganganu.
Bayan mummyn Aayaan ta gama faɗawa Mummy jikinta har rawa yake yi wajen dialling ɗin number Sarfraz.
Cikin Sa'a kuwa kiran na shiga ya ɗaga "hello mummy"
"SARFRAZ ina hassu ɗin take? Ina fatan dai tana lafiya?
"Eh da sauki, barci ma takeyi"
"Kenan batada lafiya Koh?
"Eh mum! amma Aunty Nawaz da yaya Aayaan sunzo, ta kula da ita sosai, shikuma mukaje asibiti muka tawo da Doctor ta duba ta"
"Amma dai jikin da sauƙi sosai Koh?"
"Eh mum amma dai wai har ɗinki Doctor ɗin tayi mata"
"Subhanallah!!! nashiga uku! Sarfraz dama bakada hankali? Kayi irin wannan aika aikar sannan ka iya faɗa Min Babu ko jin kunya balle nauyi..
"Mum kefa kika tambayeni, kuma Bansan me zance Miki ba, kumani banaso nayi miki karya"
"Okay to Yanzu tana tashi daga barcin ka kawo min ita"
"To mum In'sha Allah zan kawo ta" Sannan ya kashe wayar
Juɓur mum ta Zauna a kujera tare da haɗa tagumi hannu biyu "gaskiya Sarfraz akwai sauranshi, shiyasa fa na dage akan Abar min yarinyar nan a gidan nan amma dadynshi ya ɗaure mishi gindi wai abashi matarshi su tafi.
Murmushi Mummyn Aayaan tayi tare da cewa "to ai Yanzu aikin gama ya gama, sai dai akawota a kula da ita kada ya tasata agaba, don nasan idan aka barsu guri ɗaya ba lallai abar ɗinkin ma ya warke ba.
Girgiza kai Mummyn SARFRAZ tayi "hmmm ni kadai nasan halin danake ciki wallahi, amma gaba ɗaya tunda naji maganar nan zuciyata ta tsinke, yanzu babu Ni babu samun sukuni sai naga yarinyarnan a gaban idona.
"Yaran namune na yanzu sai hakuri wallahi" cewar Mummyn Aayaan.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Zaune Nawaz suke a mota ita da Aayaan bayan sun kai Aunty Aseey gidan yayar baban muhsien, don acan yace taje ta sameshi daganan saisu wuce Abuja, washegari kuma saisu ɗaga zuwa England.
"Sweetheart inaso nima naje England fa nanda Three days, kuma Gaskiya zan daɗe acan, Don a ƙallah zan iya kaiwa Three months"
Duk sai Nawaz ɗin taji babu daɗi saboda tasan Yanzu idan Aayaan ya tafi haka zatayi ta zama kamar mayyah, tunda Aunty Aseey ta tafi gashi Maiduguri zasu koma balle ta riƙa zuwa koda gidansu SARFRAZ ne.
"Yadai Madam! What happened?" Aayaann yace yana kallonta sosai
A sanyaye Nawaz ɗin tace "Babu komai, kawai dai Naji Babu daɗi ne da kace zaka tafi wata ƙasa kuma har wata Uku fah? Yanzu Ni kadai Zan ta zama a gida Kamar mayyah, Babu Aunty Aseey, Babu Sarfraz balle hassu"
"Ko zaki bini?
"Eh Allah zani"
Ware ido Aayaan yayi cikin mamaki Domin abin yazo mishi a bazata, be taɓa tunanin zatace "eh" ba koda wasa.
"Da gaske zaki bini?"
Rufe fuska tayi tana murmushi tare da ɗaga Kanta alamun eh.
"Okay naji daɗi sosai, har dai zaki je ma to gobe kawai zamu tafi tunda kinga kowa yananan be koma ba sai muyi musu Sallama kawai.
Ita dai Nawaz sai bayan tace zataje ta tuna aika aikar da SARFRAZ yayi "to Yanzu idan Aayaan ya chafketa a inda babu kowa ya zatayi kenan? Duk saitaji kamar tace ta fasa binshi ma.
Farin ciki a gurin Aayaan ba'a Magana, jiyakeyi Kamar ya dena tuƙin ya miƙe yayi ta rawa...
Suna Isa gida bayan ya buɗe mata kofa ya nufi falour da gudu yana kwala wa mummy kira "mummy! Mummy!! Mummy!!!, Mummy kina ina?
Mum ta fito daga ɗakin da su ummin Nawaz suka sauka taji Aayaan na ƙwala mata kiran mafarauta, tsaye tayi kawai tana kallonshi.
"Mummy inata miki magana amma kikayi shuru, Koh So kike zuciyata ta buga?
Balla mishi harara Mummyn tayi "hmmm Aayaan manya, nidai wannan washe bakin da zargadilar da kakeyi nasan ba banza ba, dole akwai wani abu, faɗamin meya faru?
Kama hannunta yayi "zo muje kiji"
Binshi takeyi tana mita "oh Aayaan wai kai har gobe bakasan ka girma bane? Ji yadda kake jana!
"Mummy kiyi hakuri, banason kowa yaji abinda zamuce ne, saboda sirri ne.
"To ai nan yayi tunda kaga mun bar inda mutane suke, yanzu faɗa min menene?
"Dama Colonel ne yace gobe in shirya inje in sameshi a Abuja wai zamu wuce England akwai wani aikin ujula daya taso mana.
Kanne ido Mummy tayi domin hakanan taji maganar bata gamshe taba "to Allah ya kiyaye hanya ya tsare ya kaiku lafiya yasa aje a Sa'a kuma a dawo a Sa'a" sam bata bashi damar da zaice mata zashi da Nawaz ba.
Botsare fuska Aayann yayi "mummy meyasa zakice haka?
"Kajimin ɗa to addu'ar danayi maka ce bakaso ko kuma wani abun nayi daban? Ni a nawa ma da zakaji shawarata kawai ka shirya kayanka yanzu kabi Aseey kaga tafiyar ma zatafi yi muku daɗi.
Tsalle Aayaan yayi irin wanda yara sukeyi idan sunajin yin rigima, Wato duka plan da karyar da ya haɗa sun tashi a banza kenan! "Nifa mummy tare da sis Nawaz zamu tafi "
Zaro Ido mummy tayi "lallai Aayaan akwai sauranka matar taka zaka ɗauka ka kaita filin yaƙi?
"Mummy bafa yaƙi za'ayi ba, semina ce fa kawai"
"Hmm to bari na faɗa maka kome za'a yi bazan baka ƴar mutane ka tafi da ita ba"