← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 112

Sashe 98

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon duka Mutanen dake zaune a Babban falourn yayi yace "zamuje asibiti zanyi mata hoto inga cikin yana nan ko ya zube"

Kowa kallon wannan ƙarfin halin yakeyi, mutumin da Yan awannin baya yake kwance be iya motsa koda yatsanshi ne yanzu yake tsaye dauke da mutum, lallai Allah shine mai iko akan komai da kowa,

Mummy ce tace "haba Aayaan! Dukanku fa ba lafiya ce daku ba, don Allah kabar yarinyarnan ta huta gobe sai kuje"

Ganin Idan ya tsaya sanya mummy zata hanashi sai kawai yace "mummy Don Allah Don darajar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam kibarmu muje"

Baffa ne yace"kibarshi yaje amma ɗan uwanshi Sarfraz ya kaisu a mota"

Ummin Nawaz kam kunya ta isheta, wannan abu nasu Nawaz yana bata mamaki, wai har yaushe suka shaƙu da juna haka?

Yankewa tayi gobe in'sha Allah zata tafi gida tunda dai Allah yasa be mutu ba, da ace ya mutu ne to dole ko kwana bakwai tayi zuwa a share makoki.

Fita SARFRAZ yayi da sauri don yayi warming ɗin motar kafin Aayaan ya ƙaraso, dayake dole sai anbi ta usulin main falour za'a fita daga gidan yasa mutane suka riƙa tsaida Aayaan, jaje kowa keyi mishi inda wasu kuma suke tambayar meya faru da Nawaz ɗin..

Sarfraz ne ya koma cikin gidan Don ganin me ya tsayar da Aayaan ɗin ya hanashi fitowa har zuwa lokacin, a main falour sukayi kicibis da Aayaan ɗin wanda ke tsaye rungume da Nawaz a hannunshi.

Ran Sarfraz a bace ya hau cewa "Don Allah ku bari mu dawo saiku yi mishi duka tambayoyin da kukeso kuyi mai, yanzu sauri mukeyi zamu kai mara lafiya asibiti kuma dare yayi"
"Muje yaya" cewar sarfraz yana dafa kafaɗar Aayaan ɗin

Koda suka shiga motar Aayaan be sauke Nawaz ba illa gyara mata zama da yayi a Saman cinyarshi, "wai yaya meyasa kacika sanyi ne? Kasan abinda ya fito damu amma ka tsaya biyewa mata suna Daɗa ɓata maka lokaci.

"Bro banason Mutum yaga kamar na wulakanta shi ne, sam banjin daɗi naga wani ya shiga cikin damuwa komi kankantarta balle kuma ace nine sila.

Haka dai suka isa cikin harabar Asibitin, Parking Sarfraz yayi sannan ya fito ya buɗewa Aayaan ƙofar motar, yana kallo Aayaan ya shiga cikin hanyar da zata sada ka da ko wane ward kakeson zuwa, tsalle yayi ya zauna a saman motar yana kalon cikin Asibitin.

Da kalle kallen ya ishe shi sai ya ciro wayarshi ya bude wajen video, mutanene maƙil tsaye a ƙofar gidansu Aayaan, wasu ma kuka sukeyi wasu kuma idonsu yayi jajir alamun sunma gaji da kukan, "wai me yaya Aayaann yake yiwa Allah ne da ya zama mai wannan uban farin jinin? Mtsewwwss! Kodai kulawar da taimakon da yakeyiwa al'ummar Annabi ne? Girgiza kai yayi sannan yace "tabbas hakane, domin daba don shiba da yanzu Allah ne kadai yasan yadda rayuwata zata kasance, ko na haukace ko kuma ina cikin dajin su hassu inata shirme, murmushi ne ya kufce mishi daya tuna da hassu, sam ya manta da babinta tunda suka iso garin, sai yanzu da zance yazo kanta.

Aayaan yana shiga be tsaya a ko'ina ba sai a ultrasound Room, a mutunce cikin girmama wa docton dake ciki ya gaida Aayaan Sannan ya tashi daga seat ɗin dayake zaune, saida ya kwantar da Nawaz a saman gadon scanning ɗin Sannan ya zauna a seat ɗin tare da cewa likitan wanda ke tsaye yana jiran umarni "you can go" juyawa yayi ya fita daga ɗakin.

Saida ya saita komai Sannan ya ɗaga rigar Nawaz saboda shafa mata ultrasound gel, cikinta wanda ke shafe ya kalla yanajin wata yar fargaba na kamashi.

Saida aƙalla yakai kusan awa ɗaya yana abu ɗaya, idonshi duk yayi ja ga wata zufa data ke tsatstsafo mishi a goshi.

Kuka yakeson yayi ko kila ya samu sauƙi daga Abinda yakeji, amma kuma zuciyarshi ta ƙi bashi haɗin Kai, buga tebur yayi yana cewa "wane mara hankalin likita suka kira wanda ya riƙa dirkawa matata allurar barci kamar wata mara galihu? Gashi yanzu ya jamin asara mafi girma a duniya" cije lebenshi yayi yai ƙwafa sannan yace "gaskiya saina ɗauki tsatsauran mataki akan koma wane likita ne, fisbilillah yanzu da hantarta ko ƙodarta ta samu matsala fa?"

A hankali Nawaz ta sauko daga saman gadon, takowa tayi har zuwa gabanshi, zama tayi saman cinyarshi tare da rungumeshi sosai.

"My Reality ban sanka da saurin fushi ba, kuma ban sanka da rashin haƙuri ba, Ni nasanka da yarda da ƙaddara, da hakuri da kawaici!!! Don Allah kada ka sauya daga yadda na sanka wato kyakkyawa kuma mai kyakkyawar zuciya.

Idanma Allah yasa cikin ya zube to please inaso ka ɗauka jarrabaka Allah yakeso yayi, to kayi hakuri ka ɗauki kaddara sai Allah ya chanza maka da mafi alkhairi a garemu baki ɗaya, kuma banso ka manta cewa da ba don ƙudirar Allah ba da yanzuma ka manta da wata rayuwa wai ita *Rayuwar Duniya*, to da me kenan yanzu?
Kuma idan yara kakeso Ni nayi maka alƙawarin zanta haifa maka su har saika ce nabarshi haka"

Kallonta kawai Aayaan yakeyi yana mamakin Irin basirar maganar da Allah ya bata, Lallai shiyasa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace "Duniya wajen ɗan jin daɗi ce amma mafi alkhairin jin daɗin duniya shine mace tagari" Lallai yau yagani da idonshi, Domin Kafin ta iso gareshi ji yake Kamar zuciyarshi zata fashe amma zuwan ta da kalamanta masu sanyi sunsa yaji komai ya goge daga cikin zuciyarshi.

Fuskarta ya ɗago yana kallonta "kince kinyi alkawarin haifa min yara da yawa, to da wannan tsoron naki zaki haihu ɗin?"

"I promise!! Kuma ka bari jinin ya dena zuba zakasha mamaki"

"Wai meya chanza Nawaz haka lokaci ɗaya? Shifa abin har tsoro yake bashi, zallar kaunarshi yake gani a cikin kwayar idonta kuma sam yanzu babu wannan kunyar dake Kawo mishi cikas"

Shima daɗa rungumeta yayi sosai yana ajiyar zuciya a hankali, "dear mutafi pharmacy in sai miki magunguna sai mu wuce gida Koh? But me zaki ci?"

Shagwaɓe fuska Nawaz tayi sannan cikin yanga da jan aji me cike da salo tace "kaza da madara da ice cream"

Dariya ce ta kwacewa Aayaan "Allah Sarki little Aayaan, yazo ya koya miki kwadayi shi kuma ya tafi, aini ko duka kajin duniya kikeso ki cinye in'sha Allah sai an nemo Miki su"

Murmushi Nawaz tayi sannan cikin salo da salsala tace "godiya nake yi ranka ya daɗe, Allah ya ja kwana yasa sai kaga jikokin yaranka ma, kuma bi'iznillah tsufa me cike da lafiya zakayi"

"A'a wai me ya kawo wannan chanjin ne lokaci ɗaya" Abinda Aayaann ya tambayi zuciyar shi kenan cikin ƴan sakwanni.

"Wallahi da ace ka mutu da gaske ko! To wallahi haukacewa zanyi babu ko tantama, nifa a Lokacin gani nakeyi kamar ni kadai ce a cikin Duniyar nan, Don Allah habibi kada ka kuma zuwa yaƙi"

Nawaz fa Neman rikita Aayaan takeyi, ba lafiya gareshi ba amma duk ta dagula mishi lissafi, "wai Nawaz dai daya sani ce wannan?"

Ita kanta Nawaz bawai da gangan take yi mishi abubuwan da take yi ba, ita kanta Batasan ma tanayi ba, tsabar tsagwaron kaunarshi ce kawai take fito da kanka da kanta, tunda dama ai bahaushe yace *SO BAYA ƁUYA* .

"My soulmate bakace komai ba!" Nawaz ta faɗa kamar zata zunduma ihu.

"I'm sorry sweetheart, bazan kuma zuwa ba"

Kanta ta ƙara cusawa cikin ƙirjinshi tana sauke ajiyar zuciya a Hankali "Yaya na rasa wane irin so nakeyi maka, yanzu haka ji nakeyi kamar in shige jikinka mu haɗe mu zama ɗaya"

Lallai akace mahakurci mawadaci, kuma lallai addu'a bata taɓa faɗuwa a ƙasa, wai yau shi Aayaan Nawaz ke faɗawa duka wadannan maganganun, shikam ina zaisa kanshi don farinciki, dama ace yau ƙalau take da saiya nuna mata irin tashi tsantsar ƙaunar da yake yi mata. But never the less yasan kwana nawa ne jinin ze dauke"

"MADINATUL MUNAWWARAH! Na ƙaunace ki a cikin rayuwata, na soki son da ban taɓa zaton zan iya yiwa kowa ba, bani da burin daya wuce naganki kina cikin farin ciki, kyau kikeyi sosai idan kina cikin farin ciki da murna, bazan miki ƙarya ba amma wallahi ko sanda naji numfashina yana ɗaukewa babu wanda ya fara faɗo min a cikin zuciyata face ke"

"Ina ƙaunarki, ƙaunar da bansan irin taba, Don Allah kada ki gujeni koda wasa, plssss sweetheart mu rayu cikin so, kauna da aminta da juna, pls ko laifi nayi Miki ki faɗa min wallahi zan baki hakuri, amma kada kice zaki hukunta Ni da fushinki. Nan suka taɓarɓaren, kowa yana faɗawa ɗan uwanshi irin kaunar da yake yi mishi..

Ganin sha ɗaya tana nema wucewa yasa Aayaan kashe duka na'urar scanning din, ɗaukar Nawaz yayi ya tallabeta tare da miƙewa Sannan suka fita zuwa doguwar hanyar dake ɗauke da kowane daki a cikin asibitin, tsirarun mutanen da suke waje ne sukayi ta gaishe shi tare da natsuwa kada suyi wani laifin, wasu kuma mamaki neman kashe su yayi saboda sunji labarin ance ya mutu.

Koda ya ƙarasa gaban motar, cewa SARFRAZ yayi "Don Allah bro I'm sorry, na barka kai kadai ko?"

Murmushi SARFRAZ yayi "wallahi a'a Ni naga ma saurin fitowar ka, zaune nake inata amsa waya anata tambayata wai baka mutu ba ko?"

"Oh wai haka abin yabi duniya" Aayaan yace yana shiga cikin motar.

"Wallahi yaya, ai farin jini gareka na fitar hankali, kaga yadda mutane suka taru kuwa? Wasu kuka kawai sukeyi kamar suma zasu mutu.

Murmushi Nawaz tayi tana ƙara lafewa a cikin jikinshi, ji take yi kamar ta dauwama a haka.

Koda suka fita daga Asibitin a wani babban pharmacy suka tsaya Aayaan ya amsar mata magunguna sannan suka biya ta Almas ya amsar mata duka Abinda tace tanaso harda ƙarin wadanda ma bata ce ba.

SARFRAZ dai kasa shiru yayi "wai yaya naga baka fito da kuɗi ba amma duk inda kaje sai inga sun baka abu cikin rawar jiki da girmama wa"

Murmushi Aayaan yayi yace "talk active"

"Yaya don Allah ka faɗa min meye sirrin" cewar sarfraz yana kama hannun Aayann.

"Okay to ɗan jarida, duk inda kaga munje yanzu mallakina ne?"
Chapter 98 · 0% Book details