Sashe 106
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk maganar nan da sukeyi Mummy na bakin kofa tana jinsu saboda ta dawo ta ɗauki muhsien da yayi barci a kujera,
Jinjina kai mummy tayi "lallai kuwa dole nabar gidan nan tun kafin a kira mini ruwa *Ni ko matar Rasheed nace ai an riga da an kira miki ruwan*
Kamar ta koma ɗaki sai kawai tayi shahada ta shiga da sallama, duk sai suka bita da Kallo suna nazarin maganar da goggo ta gama yi Yanzu, shi kuma colonel ji yake kamar ya ɗauketa su tafi inda babu kowa su zauna, amma ina babu hali.
Wani irin kyau ta ƙara mishi sosai, babu wanda zai kalleta yace ita ta haifi Aayaan balle kuma Aseey, irin madaidaicin jiki gareta me kyau kuma ya haɗu da tana kula dashi, koda yaushe zaka sameta da jan lalle kuma fatar nan tata kullum a gyare..
Ko yanzu ma haka take kamar amaryar Maiduguri, domin ta nannaɗe jikinta cikin jan lafaya dukda ba kwalliya tayi ba saboda a gidan rasuwa take kuma mutuwar ta taɓa ta sosai, amma a haka idan ka ganta zaka zata kwalliya tayi sai dai idan ka lura da kyau zakaga damuwa kwance saman fuskarta.
A tare suka amsa mata sallamar kamar haɗin baki, duk saita ji ta wani iri, har takejin dama komawa tayi bata shigo ɗakin ba.
"Sannunku goggo! Na dawo na ɗauki muhsien ne"
"Allah Sarki! Ki bari ɗan lele yakai miki shi naga kamar ba daɗin jikinki kike ji ba?"
Da sauri Colonel ya miƙe ya sunkuci muhsien tun Kafin yaji amsar da zata ba goggo.
Itafa Abin nan ya fara isarta, wai ya za'ayi gotai gotai da ita har da jikoki a riƙa ƙoƙarin yi mata auren dole?
Sai kawai ta juya ta fita ba tare data ce komai ba, da sauri colonel yabi bayanta shima.
A dai dai corner ɗin kitchen sukaci karo da Aseey riƙe da manyan warmers guda biyu, shiru tayi tana kallonsu, domin ganin colonel tayi ya juye kamar daddyn ta sak, ji tayi dama Kawai su zama ma'aurata kila ma Mummyn nata ta samu sauƙin ƙuncin da take ciki na wasu abubuwa da yawa.
Colonel ne yace "daughter me aka samar mana ne haka?"
Murmushi tayi "Daddy cous cous na dafawa sis Nawaz nasan zataji daɗin shi, shine na tuna da kai nace bari kaima na dafa maka na neman Albarka, kuma ko Daddy the funny facts shine nayi amfani da method ɗin mummy ne yadda takeyi mana tace a Sudan haka sukeyi"
"Wow wow!!! masha Allah kice daɗin shi ma na musamman ne, bari na raka mummy na dawo sai nazo muci"
"Mummy kuwa data zama kamar gunki a tsaye ji tayi kamar ta rufe Aseey ta duka, meyasa taza sakata a cikin abinsu bayan ita ba tankasu tayi ba.
Fuu haka ta wuce su tabar gun, ba tare data kuma ko kallon inda suke ba..
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sai bayan kamar awa uku Abban Nawaz ya buɗe Kofar ya fito, ɗaga labulen ɗakin umma yayi tare da cewa "kizo ki wuce ki fitar min daga gida, kuma ki tabbatar kin ɗauki jamila kun tafi tare, sannan koda wasa kada ki sake na kuma ganinki ko a Kofar gidan nan ne.
fadin irin tashin hankalin da suka shiga duka ma kamar ɓata baki ne, kada ma jamila taji labari, nan take ta fara murkususu tana cije baki, kafin wasu mintoci jini ya fara malama daga gurin da take zaune yana gangarawa, ita kuwa fauziyya neman numfashin ta tayi ta rasa, ai kuwa da gudu inna talatu tayi kan jamila ita kuma Ummi tayi gun fauziyyah...
*NOVEL YAZO GANGANGARA, 08093215055 GA NUMBER TA GA MAI BUKATAR ZUMUNCI, GYARA KO SHAWARA (WHATSAPP KAWAI) NAGODE*
*Matar Rasheed ❤️**🎀 🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*89*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Sakin labulen ɗakin Abban Nawaz yayi ba tare da ya damu da halin da yaga su Jamila ba, Domin yanzu duk wani abu da ya shafi Umma baƙinshi yake gani.
Cikin ikon Allah ummin Nawaz ta samu fauziyyah ta farfaɗo dakyar, Ruwa ta bata tasha sannan ta koma gurin jamila inda inna talatu ke tunanin sai anje asibiti Domin dukkan alamu sun nuna naƙuda takeyi kuma gashi cikin be isa haihuwa ba.
"Inaga fa sai anje an taro adaidaita mu kaita asibiti kada wani abun ya faru, saboda jinin da yawa yake zuba gashi ta fara fita daga hayyacinta"
"To bari na samo" cewar ummin Nawaz tare da hanzarin fita daga ɗakin
"Kada ki sake ki fita daga cikin gidan nan" Suka jiyo muryar Abban Nawaz a kausashe.
A zuwa wannan lokacin zuciyar umma ta gama bushewa gaba ɗaya, jira kawai take taji ance mata Jamila ta mutu, tana inda take a zaune domin babu ƙafa kuma koda da kafar bata tunanin zata iya tashi saboda tashin hankalin da take ciki, hannuwanta kawai tasa ta rufe fuskarta tana jero istigfari a cikin zuciyarta.
Tsaye ummin Nawaz tayi tana ta'ajibin wai ya akayi Muhammad ɗinta ya zama haka ne? shirin bashi haƙuri takeyi saboda kada wani abu ya sameta. "Abban Nawaz don Allah kayi haƙ....."
"Sanda tayi cikin tayi shawara dake ne da yanzu kike nemar mata mafita?"
Maganar data ƙara dukan Jamila kenan jikin nata ya ƙara rikicewa..
Itama Inna talatu sai ta fito da nufin su haɗu su ƙara bashi haƙuri kila ya sauya ra'ayinsa, kafin ta ƙarasa gurin da suke tsaye ma ya shige ɗaki ya turo ƙofa.
Cirko cirko sukayi a bakin kofar suna tunanin mafita, "Rahma kinada garin kanumfari da garin Cinnamon" Inna talatu ta tambayi ummin Nawaz
"Eh inada su" ummin Nawaz tace tare da nufar falonta don daukowa
"Ki haɗo da sabuwar reza nasan bakya rabo da ajiyewa" inna talatu tace da ƙarfi yadda ummin zata jiyota
Da sauri ta fito riƙe dasu har tana neman yin tuntuɓe tsabar tashin hankali.
A inda suka barta Anan suka sameta, gaba ɗaya jikinta yayi laushi, "Umma inaga fa sai dai muyi mata dabaru irin namu na gargajiya don inba haka ba zamu iya rasa ta" inna talatu tace tana ayiye hijabinta a gefe
"Kuyi mana, Allah ya taimaka" Abinda umma ta iya cewa kenan ta maida hannunta ta rufe fuskarta.
Kofi ummi ta dauko ta ɗebo ruwan dumi ta kawowa Inna talatu, amsa tayi ta juye Garin kanumfarin da na Cinnamon ɗin ta jujjuya saboda ya jiƙu da wuri.
Fita ummi tayi ta ɗauko muciya a kitchen saboda itama zasu bukace ta, dago kan jamila tayi ta kafa mata kofin a baki tare da cewa sha.
Tsabar azabar da jamilan take ciki yasa bata ji daci da yajin kanumfarin ba ta riƙa kwankwanɗa har Saida ta shanye shi tass, jira sukayi na Tsawon minti goma amma shiru babu wani yunkurin tawowar ɗa daga cikin.
Ummi ce ta mikawa Inna talatu muchiyar tace "inaga fa sai anyi amfani da muciya kada karfinta ya gama ƙarewa, buɗe bakin jamilan ummin Nawaz tayi ita kuma Inna talatu ta tura mata muciyar chan cikin makogoronta, cikin ikon Allah kakarin da tayi sai ta fara yunkuri, bata cire muciyar ba saima ta ƙara turawa ciki yadda za'a samu tayi yunkurin mai karfi.
Allah ya taimaka har jinjirin ya fara tawowa, gyara kafafuwanta ummi tayi don ta duba taga ko jikin nata ya buɗe, amma cikin rashin Sa'a ɗan ya sako kai har ana ganin gashin kanshi amma jikin a tsuke yaƙi buɗewa.
Da sauri ummi ta fita zuwa dakinta ta ɗauko man zaitun da man kwakwa, sosai take zubawa tare dasa hannunta tana bude cikin jikin jamilan ko Allah yasa yaji santsin man ya buɗe, amma ko gezau yaƙi buɗewa, babu yadda basuyiba amma abu yaci tura.
"Ina rezar nan take" inna talatu ta tambayi ummin Nawaz
Miƙa mata rezar ummin Nawaz tayi tana jin zuciyarta na karyewa saboda tasan yanka ta talatu zatayi tunda ta kasa haihuwar da kanta,
Aikuwa dai abu babu daɗi saida ta ƙara ta har guri biyu sannan aka samu kan ɗan ya fito, cikin dabara suka taimaka jinjirin ya gama fitowa..
Saida ya gama fitowa suka lura baya numfashi, gashi dama ɗan karami ne sosai, jijjigashi suka riƙa yi ko suma yayi amma daga baya sai suka gane ya mutu ne, wato wahalar da yasha a ciki yasa ya mutu kafin a haifeshi.
Inna talatu ce taciro mahaifa tare da kwashe mata jinin cikin marar ta sannan tasa wani zani ta tare jikin jamilan dashi, ko motsi kwakkwara ta kasa illa idonta da yake abude ne kawai zai shaida maka tana raye bata mutu ba.
Shirun fauziyyah ne suka ga yayi yawa, koda ummi ta ƙarasa kusa da Ita ta duba sai taga ashe ta kuma sumewa ne, cikin tashin hankali ta fita ta ɗebo ruwa ta fara yayyaafa mata....
*(Jama'a kun dai ga Yadda jamila tasha wuya, yau da ace Aure tayi ta samu cikin, ana farin ciki za'a kaita asibiti kuma ayita nan nan da ita, kowa yana cikin tashin hankali har saita haihu, ballantana ma mijinta, idan yanada hali ma har kyauta zaiyi mata bayan ƙaunarta da zai kara, ga abinci me kyau da gina jiki da za'a tanadar mata tun sanda ta samu cikin ta yadda idan tazo haihuwar Allah zai taimaka naƙudar tazo mata da sauƙi)*
*ALLAH KASA MUFI ƘARFIN ZUCIYAR MU, KUMA ALLAH KA ƘARA NESANTAMU DAGA KAIDIN SHAIDAN DA SHARRINSA (AMEEN)*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Bin bayanta colonel yayi, koda ya shiga ɗakin be ganta ba sai kawai ya kwantar da muhsin ɗin yaja musu Kofar ya fito ya koma falon.
Anan ya samu Aseey zaune a dining tana jiranshi, ta fara serving dinshi kenan saiga su Naufal sun fito kowa da rabin ƙatuwar kaza a hannunsa yana yaga "ina kuka samo kaza ƴan-biyu" goggo ta tambayesu miyaun ta yana tsinkewa
"Yaya Captain ne ya bamu" Naufal yace yana ƙarasawa dining din shima.
Kafin yace wani abuu tuni muryar Fudail ta karaɗe ɗakin "Aunty pls Nima a zuba kin better ɗin da aka haɗawa Daddy"
"Kaji ɗan baƙin ciki" abinda Naufal yace kenan yana balla mishi harara "wato saboda kaga na riga ka shine zaka yimin katsalandan Koh"
Daddy ne yace "kuci gaba kunsan sauran ai, tunda ku ako ina kuma a gaban kowa ma saikun raba hali"
Shiru duka sukayi ba tare dasun shirya ba