← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 112

Sashe 26

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maganar mum ce ta dawo da ita daga duniyar tunani "daughter bakice komai ba?
"Ehm mummy au ehm dama babu komai.

Aayann dake gefe ne yace "taɓ ai wannan uwar in'inan da kikayi da ace a barrack ne sai kin gane kuranki wallahi..

"Dakata malam! Idan bazaka iya kalloba to kabamu guri, naka ido kada ka kuma sa mana baki a cikin maganar mu.

Chuno baki yayi "Allah Sarki Aayaan, Allah ya ƙara baka hakuri, tunda yinka da Allah yayi a jinsin maza ya ja maka baƙin jini ya zakayi, sai hakuri.

Buɗe baki mummy tayi tana kallonshi " lallai Aayaan wuyanka ya isa yanka Ni kake kallo kake fadawa maganar da kaga dama ko? To ai idan ka isa ba hakuri zakayiba kamata yayi kawai inga ka zama mace....

Dariya ya kyalkyale da ita "mum idan na zama mace ai abin bazaiyi kyan ganiba wallahi, sunan wani abu wai shi kwaftari..

Dariya Nawaz ta kyalkyale Da ita "mummy ai idan yaya Aayaann ya zama mace wallahi babu namijin dazai aureshi.

"Saboda me" mummy tace cikin jin dadin ganin yadda Nawaz ɗin take dariya.

" Ai wallahi da wannan jikin nashi mai kama da dutse idan mijin yayi mishi laifi zaneshi zaiyi tsaf, rannan fa ya daukeni amma gudu yakeyi.

Buɗe baki Aayaan yayi yana kallonta "kaf dama tana surutu haka? Wow shifa dama yana son macen da zata riƙa yi mishi hira ba wadda zata zauna tayi maka dunkum ba.. ji yayi ta ƙara burgeshi balle da take zance a kanshi tana murmushi...

Mummy ma dariya ta kyalkyale da ita " gaskiyar kine Nawaz dama gashi da ƙosawa..

Murmushi Nawaz ta kuma yi "ai mummy Gara kawai yayi zamanshi a namijin shi, zaima fi kyau kuma kinga shi zai bada doka ba bashi za'a yiba...

Duk Wannan hirar da akeyi mummy tana binsu ne amma akwai abinda take karanta a bangaren Aayann.

Aayaan da baisa bakiba sai lokacin yace " sister ashe kina hira dama?
Kunyace ta kama Nawaz sai lokacin abubuwan da ta faɗa suka dawo cikin kwakwalwar ta, ai ji tayi kamar ta fasa ihu....

Mikewa tayi "Amma ina zuwa , bata jira amsar taba tayi hanyar dakin da akace natane da gudu..

Dariya mummyn da Aayaan suke mata..
Mum taji daɗi sosai ganin yanda kowa ke farin ciki "Aayaan nace maka daughter Alkhairi ce a cikin rayuwarmu kaga yanda kowa ke farin ciki dalilin zuwan ta, amma kai sai kai tayin wani kishin banza....

Murmushi yayi "mum ai kece kin Dena kulani sam tunda tazo, ko ɗan abincin da kike bani a baki ma kin Dena.

"Oh to Wayace kada kayi aure, da kayi aure matar kace zata rika baka cikin so da kauna...

"Mum zaki fara kenan koh?
"To nayi shiru, kirata mu tafi tunda naga ga dukkan alamu ka samu sauki..

Mikewa yayi yaje daidai mic ɗin kofar dakin yasa bakinshi a jiki "ki fito mu tafi ko a fasa.

Nawaz na zaune taji muryar Aayaan kamar daga sama, ai zunbur ta mike ta gyara rolling ɗin kanta tayi hanyar kofa,
Tana budewa sukayi ido huɗu Brown Hazel eye's dinsa ne suka yi mata wani irin kwarjini har saida gabanta ya faɗi da sauri ta kauda kanta gefe, shima abin a bazata yazo mai.
Duk mummy na kallon abinda sukeyi "muje" mum tace tanayin hanyar waje.

Da sauri Nawaz tace "ya ciwonka? I'm sorry please dalilina kaji, pls kayafemin!

Wani daɗi yaji a ranshi" oh wai dama idan aka nuna an damu da kai daɗi kakeji, lallai mu sojoji muna ruwa, sai ka rasa hannu ka rasa kafa amma babu me jajanta maka.

Murmushi yayi mata me kyau "kada ki damu da sauki baya min ciwo...

Gaba yayi tabi bayan shi cikin sauri...

Wata kofa daban taga sunbi bata farkon ba, sai sannan taga ashe wannan itace asalin main door ɗin, wato dazu ta back yard door Suka biyo...

Sojoji ta gani duk a ƙame riƙe da bindiga kamar basuda rai.
Wata baƙar land cruiser Prado latest series Taga wani soja yayi sauri ya bude gaba da bayanta,
Wani ne shima yayi hanyar driver seat zai shiga, Aayaan ne yayi saurin dakatar dashi
"No I am going to drive my self.
"Yes sir " cewar mutumin yana Sara wa Aayaan

Ita dai Nawaz sai ido, da sauri mum ta shiga baya ta kishingiɗa, yunƙurin shiga Nawaz tayi "daughter kije gaba zan ɗan mike kafa ta anan kada jini ya tarun mini.

To Nawaz tace sannan tayi side ɗin me zaman banza,
Kusan tare suka zauna da Aayaan, sai kuma ƙofofin suka rufe kansu da kansu, take wani sanyi da kamshi me daɗi ya garwaye cikin motar.

Key yayi mata ya nufi gate ɗin da dama an wangaleshi tun tuni, sun ɗanyi nisa ta mirror ya hango kamar motoci na binsu , birki ya danna sannan ya buga stiyarin da ƙarfi "mummy kinga guards ɗin can sun biyomu koh?

"Ninace su biyomu tunda garin babu kyau, ko kanaso wani abu ya faru damu ne?

"Nidai mumy Wallahi nagaji da binbinin nan ace duk inda zaka ana binka ana gadi kamar wani ƙaramin yaro... Amma tunda kince kece shikenan..

Kunna motar yayi suka ci gaba da tafiya...
Saida suka dauki kusan awa ɗaya a hanya sannan Nawaz tace "can layin zaka shiga gida na hudu..

Layin Aayaan ya shiga sannan ya duba gida na hudu yayi Parking..

Da sauri sojojin suka zo suka buɗe musu kofofin sannan sukaja gefe suka tsaya

Nan yara suka fara taruwa ganin motar sojoji har guda uku, manya kuma so suke suga su waye zasu fito daga motar...

Mummy ce tace "daughter ki shiga kiyi mana iso ko!

"Ai saimun fara shiga faɗa tukuna kafin mu shiga cikin gidan kinsan shine hakimin garin nan.

" Okay to muje" gaba Nawaz ta shiga har gaban fadar, ciki ta shiga ta samu Guri ta zauna, suma su mummy guri suka samu suka zauna.

Aayann ne yace "dan Allah ayi mana iso gurin hakimi.

Wani bafade ne yace to sannan ya shiga cikin gidan ya isar da cewa baffa yayi baƙi..

Shiru baffa yayi kamar yace ace bazai samu damar zuwaba sai kuma yace " kace ina zuwa"

Tafiya bafaden yayi don isar da sakon baffan.

Bafffa ne ya miƙe bari naje naji meyasa ake nemana?
"Allah yasa Alkhairi ne cewar amma (kakar Nawaz).

"Ameen yace kawai ya fita daga ɗakin,
Ai be karasa zamaba Nawaz ta mike tayi gurinshi ta rungume shi da karfi tana dariya.

"Muryar wa nakeji haka kamar ta Nawwarah?

Cikin zumuɗi Nawaz tace "wallahi baffa nice.

Sakin shi tayi tace kagani, nice
Bai shirya zama ba yaji shi zaune a kan kujerar shi, Alhamdulillah yaketa maimaita wa a cikin zuciyarshi.

Sai sannan kuma Nawaz tayi cikin gidan da gudu.....

Gaisheshi mummy tayi Sannan shima ya gaisheshi...

Da sauri baffa yace "wa nake gani ne sak kamar ɗana Muhammad?

Mummy ce ta kalli Aayaan, shima ita ya kalla.

A tare suka ce ...........

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 29*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

A tare sukace "Baba wane Muhammad ɗin?

"A.V.M Muhammad mai goro, nida babanshi malam Aliyu me goro aminaine irin amincin da ake zama kamar ƴan uwa... Ba irin na yanzu ba

Yanzu hakama bamufi awa ɗaya da gama waya dashiba.
Amma dai Allah yayiwa Muhammadun da na sani rasuwa, yaron Arziki...
Allah dai yayi mishi Rahma, sau biyu yana kaini Saudiyyah.

Wani daɗi ne ya ziyarci mummy jin yanda ake yabon mijinta marigayi...

Cewa tayi "Ni matar shice wannan kuma ɗan shine sunan shi Aayaan,

Da sauri baffa ya miƙo hannu "zo zo zo nan jikana Ayatullah, Allah sarki ashe dai inada wasu ahalin ban saniba.
Miƙewa Aayaan yayi yaje gaban baffa yana sussunne kai
Akan cinya baffa ya ɗora shi, ai da sauri Aayaan ya miƙe yana murmushi..

"Baffa ai sai in karya maka kafa" Aayaan yace yana murmushi...

" Aikuwadai, baba Wannan gabjejen zaka ɗora a cinya? Cewar mummy tanajin farinciki a zuciyarta

fadawa dai sai murmushi sukeyi saboda sun daɗe basu ga hakimi yana farin ciki hakaba....

NAWAZ
Koda ta shiga cikin gidan da gudu ta faɗa jikin umminta tana farin ciki, Allah na gode maka da kasa na ƙara ganin ummina..

Sakin baki kowa yayi ganin Nawaz tsaf cikin kwanciyar hankali.
Nura ne yace "Nawwarah daga ina?
Hmmm kawu ai abin akwai tsawo, bari na gama ganin ummina zan baku labari, ina Amma?

Ta shiga bayi cewar Nura, wanda a kallo ɗaya zaka fahimci irin farin cikin da yake ciki.

Ummi kuwa tama kasa magana domin ganin abin takeyi kamar a mafarki, sai hamdala taketa yi a zuciyarta tana godewa Allah subhanahu wata'ala daya dawo mata da ƴarta sanda ta cire rai da kuma ganinta.

Itama Amma da gudunta ta fito daga bayi, Nan ta zauna gefen Nawaz tana jin wani irin farin ciki a zuciyarta, domin bata taɓa zaton zata kuma ganin Nawaz ba.

Bayan an kimtsa ne Nawaz ta fara basu labarin abinda ya faru da ita....

Su kuwa acan fada hirace ta ɓarke tsakanin baffa da Aayaan, saboda baffa nata bashi labarin yarintar mahaifinshi...

Sai daga baya baffa yace, au farinciki ma yasa na manta komai..
Ga dukkan alamu kune kuka tawo da Nawwarah koh?
"Baba Nawaz kake nufi? Cewar mummy

"Eh ita nake nufi ƴata,

Aayann Mummy ta kalla "son kabashi labarin abinda ya faru.

Nan ya sanar da baffa duk abinda ya faru, tundaga farko babu abinda ya ɓoye mishi...

Baffa ne keta yi mushi godiya, yana sawa Aayaan albarka, sannan ya ƙara da cewa wannan wahalar da kasha bazata tashi a banza ba, zanyi maka kyauta mai girman gaske, saboda ka dawo mana da farin cikinmu har gida, don haka kyautar guda ɗaya ce tamkar da dubu kuma zata ƙara mana danƙon zumunci..

Mummy ta fahimci abinda baffan yake nufi amma Aayaan ko a takalmin shi, domin shi bema gane me baffa yake nufi ba, shidai abinma dariya ya bashi, wai shi za'a yi wa kyauta.

°
A cikin gida kuma Nawaz ta gama basu labarin abinda ya faru da yanda Allah ya kuɓutar da ita...

Sunyi farinciki sosai da fatan Allah ya daɗa kiyaye gaba, sannan suka taso don zuwa fada su yiwa su Aayaann godia...
Chapter 26 · 0% Book details