Sashe 21
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida ya bashi da ɗan yawa sannan ya ajiye ragowar a gefe, abinda keba bandi mamaki shine jikin SARFRAZ ya saki gaba ɗaya babu alamar yanada rai amma kuma zuciyarshi na bugawa kuma idonshi a bude yake.
Damuwa ce me karfi ta kamashi ya kalli hassu yace "hassu kinga duka jikinta baya motsi amma kuma bata mutu ba.
"Nima tun dazu nake kallonta, abin ya mini kama da abinda ya samu babansu jauro fa.
"Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, kana nufin kace mutuwar jiki ce ta sameta?
"Eh " cewar hassu tana mai tabbatar mishi da abinda take nufi
Zama sukayi kusa da SARFRAZ sunanta kallonshi ga wani tausayinshi daya kama su,
Babu abinda SARFRAZ ke iya yi illah dai idonshi a buɗe yake kuma yana ƙiftawa.
Hassu ce tace "gashi su Dada ba yanzu zasu dawoba, yanzu ya za muyi da ita?
"Nima ban saniba, Amma muci gaba da kula da ita koh?
" Eh" tace haɗe da yin tagumi.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Tunawa tayi da wukar da ilu ya bata, sai kuma zuciyarta tace "anya Nawaz zaki iya kashe mutum?
Tunani ta fara yi "ba kashe shi zanyi ba kwatar kaina zanyi, da inbar mugu, azzalumi irin wannan ya kwanta dani Gara na mutu kawai.
Kuma Alamu ya nuna ya saba da zina ma, ƙilama har ciwo gareshi, kuma inje tsautsayi yasa in samu ciki, subhanallah, ji tayi zuciyar ta kara karfi akan ta ciro wukar kawai koma me zai faru ya faru.
Kafarta ta ɗaga sama sannan a hankali ta zame takalmin kafarta, ta ciro wukar.
Yunkurin mayar da ita kasanshi ya fara yi don yakai gejin da bazai iya resisting ba. Aikuwa cikin azama Nawaz ta Chaka mishi wukar a saitin marar shi inda dayan hannunta yake.
Wani irin ihu me karaji ya saki tsabar azabar data ratsa mishi ƙwaƙwalwa, hankaɗe Nawaz yayi gefe yana neman ta yanda zai cire wuƙar.
Hannu yasa ya taɓa wukar da niyar cirewa take wata azabar ta kara ratsa mishi cikin ƙwaƙwalwa..
Ihu ya ƙara saki ya fara laluben inda ya ajiye bindigar shi, don bazai barta ta gudu ba sai dai ayi mutuwar kasko.
Ita kuwa Nawaz sai lalube take ko zata samu abinda zata rufe jikinta.
Ji tayi ta taɓa zanin gado, ai da sauri ta janyeshi ta ƙudundune jikinta dashi.
A hankali take tafiya tana laluben hanyar kofa cikin Sa'a kuwa taji ta taɓa kofar, cikin azama ta bude kofar tayi waje da gudu duk da bata ganin koda gabanta tsabar duhu.
Shi kuwa yana cikin bukkar ya fadi kasa yanata birgima tsabar azaba...
Sassarfa kawai takeyi hannuwanta a gaba kamar makauniya.
Babu abinda jikinta keyi sai rawa, zuciyarta kuma kamar zata fashe.
Gani takeyi kamar ta aikata wani babban lefi, anya Allah zai yafe mata kuwa, to idan ya mutu fa?
Haka take tafe tana saƙe-saƙe a zuciyarta.
Tayi tafiya mai nisa sosai amma tsabar tashin hankalin datake ciki besa ta saniba.
Haske ta fara hangowa a ɗan gaba da ita kaɗan, nan take zuciyarta ta bada dummmm gani takeyi ta kuma haduwa da wasu mugayen ne.
Rasa inda zatabi tayi, ga shi ko hasken farin wata babu, ji tayi kamar ta koma baya, to amma a bayan ma me zata tarar?
Gefen damanta tabi taci gaba da lalube, aikuwa sai ji tayi ta bugu da bishiya, take ta saki yar ƙara.
Haske ta akayi da torch light, Bata ganin komai illa hasken da aka dallare mata ido dashi.
Yanda fargaba ta kamata ji tayi kamar ta saki fitsari a wando, Jin taku tayi an ƙaraso kusa da ita, sannan aka ɗauke hasken daga idonta
Soldier ta gani tsaye yana kare mata kallo "ke kuma wacece, from where?
"Don Allah kayi hakuri" cewar Nawaz a daburce
"Babu abinda kika min meyasa kike bani hakuri?
"Babu komai?
" Ke wacece kuma daga ina kike?
Hakanan taji zuciyar ta ta yarda da shi "sunana Nawaz ina daya daga cikin wadanda yan garkuwa da mutane suka kama.
Kwalalo ido waje yayi "what? Wai kina nufin kin gudo ne?
"Eh wani ne a cikinsu ya taimakeni.
Bai kuma cewa komai ba sai Ciccibarta da yayi ya ruga da gudu, gurin hasken da Nawaz ta gani dazu nan ya karasa , yana zuwa ya sauketa a kofar wani ⛺ tent, ashe tantinane dayawa a gurin, duk sojojine wadanda gwamnati ta turo dajin bayan video ɗin da ƴan ta'addan suka tura dazu.
"Stand here, and don't move an inch.
Wani tent ya shiga da sauri, yana shiga ya ƙame sannan ya sara wa wanda yake zaune a ciki.
"Aayann any spot?
"Daɗa Sara mishi Aayann yayi sannan yace "sir yes a good one, na shiga cikin dajin ina ɗan dube dube sai nahango wani abu kamar mutum yana zuwa, sai kuma naga ya chanza hanya.
Saina bi abin a hankali Nasha gabanshi, ashe wata yarinya ce.
To dana tambaye ta dai tace wai tana daga cikin wadanda akayi garkuwa dasu.
Da sauri ogan ya mike "were is she?
"Tana waje sir"
Waje suka fita tare, a inda ya barta nan ya ganta tsaye.
"Stupid! mace ka bari tsaye a haka?
Come-on ka bata kaya tasa tukuna sai mu yi abinda ya dace.
Tent ⛺ dinshi ya buɗe ya shiga , be daɗe ba ya fito riƙe da wandon sojoji da t-shirt ɗin sojoji cotton,
Miƙa mata yayi sannan yace "kishiga ciki kisa.
Amsa tayi ta shiga ciki, cikin yan mintoci ta fito, kayan sunyi mata kyau sosai.
Kallonta Aayann yayi sannan ya kauda kai.
A gaba ya tasa ta har dakin ogan nasu , itadai Nawaz sai kakkare jikinta takeyi saboda kayan sun kama jikinta.
Guri ya nuna mata ta zauna sannan ya Sara wa ogan shima ya samu Guri ya zauna,
Cikin kulawa colonel ɗin yace "ƴata ya sunanki?
Ahankali tace "sunana Nawaz Muhammad "
zaki iya faɗa mana Abinda ya faru tun daga farko sanda suka zo suka tafi daku har zuwa sanda kika gudo daga wurinsu.
"Eh zan iya"
"To muna sauraren ki, Kuma ƴata inason ki nutsu kinji..
"To "tace sannan ta fara basu labarin abinda ya faru tiryan tiryan, babu abinda ta ɓoye Musu illa ɗan fashin data gamu dashi wanda Yaso ya kwanta da ita ta Chaka mishi wuka.
Ajiyar zuciya colonel ɗin yayi " to Aayann kaji abinda tace koh?
Gaskiya fitarka tayi kyau, yanzu zan yi waya can barrack a turo mana da 🚁 helicopter da karin colliques saboda da asuba nakeso mu farmakesu.
"And kuma ka tafi da daughter na ka samar mata wani abu taci, kuma ka kular min da ita zuwa safiya sai asan yadda za'a yi.
"Yes sir" sannan ya mike yayi waje.
"Daughter ki bishi he will take good care of you nasan Aayann sosai...
Mikewa tayi itama ta bishi, a waje ta ganshi tsaye yana ganinta yayi hanyar tent ⛺ dinshi...
Ta daɗe tsaye a bakin kofar tana wasi wasi, anya in shiga kuwa, kada a maimaita abinda ya faru dazu domin ita yanzu maza ma tsoro suke bata.
Kamar daga sama ta jiyo Muryar shi "ki shigo mana"
Zirif ta shige saboda iya yan mintocin data haɗu dashi tsoronshi takeji sosai..
Irin katifar da ake pumping dinta da iska ya nuna mata, "ki zauna anan, and kuma me zakici in kawo Miki?
"Banajin yunwa"
Be kula taba ya tashi ya haɗa mata Black tea ya dauko cake a cikin bag pack dinshi ya kawo gabanta ya ajiye.
Can nesa da ita ya zauna, "eat, i want to ask you some questions.
Kamshin da tea ɗin yakeyi yasa ta dauka ta kai bakinta tayi sipping a hankali.
Ta ɗan sha da yawa sannan taji yace " wanda kikace kun tawo tare dashi sun harbeshi a kafaɗa mijin kine?
A hankali tace "a'a yayana ne"
"And kuma meyasa dazu kika rufe jikinki da bedsheet, ina kayan ki?
Jikintane ya hau rawa, tana tunanin yanda za'a yi ta faɗa mishi abinda ya faru.
"Calm down Nawaz, kada kiji tsoro faɗa min koma menene?
Yanda yayi maganar sai taji ta samu kwarin gwuiwa, a hankali tace " bayan na gudu daga can shine na haɗu da wasu a hanya, kuma ogansu yaso yayi raping ɗina amma shine na gudu.
"Good girl, yanzu ki kwanta kinji, zuwa gobe zamuje mu kama su duka mu tafi dasu duk zasu gane kuransu.
Sai sannan Nawaz ta kalli fuskar Aayann.
Ganinshi tayi mekyau kamar ba soldier ba harda gyaran fuska da gashi, gashi kyakkyawane sosai
Ita tasha iya tsawo gareshi sai yanzu taga ashe me faɗi ne jikinshi a murde yake alamar training.
Daga mata gira ɗaya yayi "ya akayi"
Da sauri ta juya baya ta kwanta ta ƙudundune jikinta da bedsheet ɗin...
Murmushi yayi "good night"
Ba barci takeyiba amma sai tayi luf harda numfashin ƙarya .
Shi kuma Aayaan mikewa yayi ya dauko laptop 💻 a cikin jakarshi ya kunna yanata dube dube
To Nawaz da Aayaan asuba ta gari.....
*_MATAR RASHEED_*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*EPISODE 25*
*NA HAFSAT ALIYU SHUAIBU CHIKAJI*✍️
Hasken Rana ne ya haska cikin tent ɗin da Nawaz ke kwance, kasan cewar tent ɗin light blue ne kuma yana fuskantar gabas,
Hakan sai yasa cikin tent ɗin yayi wani irin hasken kamar wutar nepa,
Tashi zaune Nawaz tayi tana mutstsike ido alamun farkawa daga barci, waige waige ta fara yi domin ta manta a inda take,
Shiru tayi sanda komai ya dawo mata, babu kowa a cikin ɗakin sai dai tana jiyo hayaniya a waje sosai..
Mikewa tayi a hankali ta ɗan bude labulen tent ɗin ta leka waje, daarararammmm gaban Nawaz ya faɗi, dalilin ganin sojojin da tayi bila adad kowa na sharafin gabansa.
Ai da sauri ta saki labulen ta koma ta zauna, tunani ta fara "wai haka rayuwa take dama, duniya juyin juyi, yau ta kaika nan gobe ta kaika chan, Allah Sarki ko ina sarfraz? Yana raye koya mutu, kuma nasan duk inda mummy take tananan hankalinta a tashe, ummi nama nasan tana cikin damuwa..
Oooh nama manta da akwai waya a duniya, ƙilama suna ta kiram mu...