Sashe 41
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kama mata hannu Nawaz tayi "I'm sorry sis insha'Allah Nima zan tayaki da addu'a, kuma kisa a ranki kamar ya samu mace ta gari ya gama, Aayaan mutumin kirki ne Nima na shaida hakan saboda bai Sanni ba kuma bai taba ganina ba amma ya zage damtse Saida ya taimakamin iya karfinshi. .
Murmushi Aseey tayi sannan ta raya a zuciyarta " hmm Nawaz manya ai Aayaan ya riga da ya samu mace ta gari tunda ya rigada ya sameki a Matsayin matar Aure, domin na lura ke din mutumce mai halayen kwarai.
Amma a fili sai tace "Ameen sis Nagode sosai sosai da nuna damuwarki a kaina..
"Babu komai, what are friends for? And what are sisters for? Cewar Nawaz tana murmushi
"Sis Nawaz kinsan waye asalin Aayaan kuwa? Labarinshi ba kamar na kowa bane, Ni kaina danake yayarshi labarinshi yana bani mamaki.
Girgiza kai Nawaz tayi sannan tace "A'a sis bansan labarinshiba....
Gyaran murya Aseey tayi sannan ta fara magana "Aayaan ya kasance yaro mai ƙarfi da kuma hazaka kuma ya kasance duk abinda yasa a gaba saiya iyashi koda kuwa zaisha wahalar da bai taɓa shan irin taba, Sannan gashi wani irin muskilin mutum ne, domin idan aka cire mum da Ni babu mai ganin dariyar shi.
Tun yana ƙaramin yaro yake haɗa abubuwan ban mamaki, wani zubin muna barci da dare Ashe shi yanachan yana haɗa mota da kwali kuma yayi mata wiring kuma kiga tana tafiya idan akasa battery, haka wani lokaci har jirgi ya taɓa haɗawa kuma wallahi ya tashi sama ...
Ɗaga Kai Nawaz tayi alamun ban mamaki.
Sannan Aseey taci gaba "ke in takaice Miki magana har Aayaan ya gama makaranta be taɓa daukar position din daya wuce na ɗaya kona biyuba daga islamiyya har boko.
Inda akaso asamu Matsala shine sanda muka gama SSCE Daddynmu yace zaikai Aayaan soja, jin hakan ba ƙaramin tashin hankali bane a gurin Aayaan sakamakon shi anashi yanasone ya zama Medical doctor, wai yanaso ya riƙa taimakawa mutane sosai, wai zai buɗe asibitin kanshi kuma free duk wanda yazo aka dubashi kada a amshi kuɗi...
Har ciwo Saida Aayaan yayi, to dayake sunada goodtime da Daddy sai Daddy ya hakura ya samar mishi Oxford University England inda anan yayi 8years yana karantar health issues.
To bayan ya dawo ne bada jimawaba Allah yayiwa daddynmu rasuwa...
Aayann yayi kuka yayi kuka, yadda kikasan zai haukace, Anan nema ya riƙa nadamar cewa meyasa be yarda yayi soldier ba kodon ya cikawa daddy burinshi...
To fa Anan ne zance ya sauya, Aayaan da kanshi ya shirya yaje ya samu aminin dadynmu wato colonel yayi mishi bayanin cewa yanaso ya zama cikakken soldier wanda duniya zata amfana dashi bawai iya Nigeria kaɗai ba..
Colonel yaji daɗi ainun, domin sunada buƙatar sojoji irin Aayaan duba da ƙirar da Allah ya mishi ta jarumtaka da gwarzontaka ga zuciyarshi babu tsoro a cikinta sam.
To anan ne colonel ya daukeshi ya kaishi tent ɗin da ake yiwa soldiers training na ƙasa da ƙasa wato international soldiers training forum...
Saida mukayi shekara uku bamusa Aayaan a idon muba, mummy har kuka takeyi, nice dai nake karfafa ta Wani zubin dukda cewa Nima tawa zuciyar a karye take ..
Bamu tashi Ganin Aayaan ba sai a BBC ana hira tare dashi da Colonel, cewa wai Aayaan yazama cikakke kuma babban sojan ƙasa da ƙasa, kuma ba a iya nan ba, air force da navy duka zai iya shiga cikinsu ayi yaƙi dashi idan hakan ta taso...
Yanzu dai in takaice Miki magana babu sojan da gaba ɗaya duniya take so kuma take alfahari dashiba kamar ƙanina AAYAANN, Ni kaina idan na tuna cewa Aayaan ƙanina ne har wani daɗi ne yake ziyartan zuciyata....
Kuma abinda zai baki mamaki game da Aayaan shine muskilancin shi bai taɓa bari yayi budurwaba, duk da kullum yanmata tururuwar zuwa mishi da tasu soyayyar suke
Amma akwai wata yarinya sanda muna Oxford taso ta samu cikin bala'in rayuwa....
Domin zuwa tayi ta haɗa baki da likitan Aayaan akan yayi mishi allurar desire inda dole ya kwanta da ita, wai ita kawai so take Taga ta haifi yaro me kama da Aayaan...
To Allah shi kadai ya iya kare bawanshi, domin Saida likitan yayi mishi allurar, ita kuma yarinyar Saida ta tabbatar allurar ta fara aiki a jikinshi sannan taje dakinshi ba tare da ko ɗan kamfai ba amma Aayaan ko kallon yarinyarnan beyiba, inda daga karshema dukan tsiya yayi mata ya jefota waje, kuma ta cikin jikinshi shi kadai yasan azabar da yake sha.
"Nawaz Ya kamata na barki haka ki kwanta, zuwa wani lokaci zancigaba da baki labarin ahalinmu insha Allah...
Murmushi Nawaz tayi, Sannan ta mike ta shiga bayi ta ɗauro Alwala tazo ta kwanta bayan tayi addu'ar kwanciya barci kamar yadda Annabinmu ya umarce mu dayi....
Sai dai sam barci yaƙi zuwa idon ta, illa zuciyarta da take ta nanata mata Tarihin Rayuwar Aayaan, tana mamakin wane irin mutum ne shi.
Sai da dare ya tsala sosai Allah ya taimaketa barawon ruhin kowa ya lallaɓo ya saceta yayi gaba da ita.
Rashin barcin da basuyi da wuriba yasa basu tashi da wuriba...
Tun da asubar fari Aayaan ya fito Cikin shirin kayan sojoji rataye da luggage ɗin shi wadda ita ma da yadin sojoji aka ɗinka ta.
Gurin su Mummy ya karasa ya gaida su Sannan yayi musu bankwana, kuma ya shaida musu cewa bazashi da Nawaz ba Saboda tace batason zuwa, sai dai idan yaje yasan bayanin dazaiyi musu game da Rashin zuwan nata....
Mummy taji daɗin hakan sosai barin dama suma sun riga da sun yanke cewa baza'a je da itaba tunda yanzu tayi aure...
Sun gama komai amma Aayaan ya kasa tafiya, yanaso koda bazata Kula shiba ya ganta.
Tsaff Mummy ta gane me Aayaan yake nufi amma sai tayi banza dashi, mummyn Sarfraz ce tace kaje ɗaki kuyi sallama yau basu tashi da wuri ba.
Da sauri Aayaan ya mike yana murmushi sannan ya wuce dakin su Aseey, Dukansu barci sukeyi hani'an, tsayawa yayi ya kare mata kallo tanata barci peacefully baby face ɗinta tayi lufluf da kwabtaccen gashi.
Kasa tashinta yayi saboda bayason ya katse mata barcinta, kuma yasan ma ba Lallai ta kulashiba duba da yadda suka rabu jiya.
Har yakai bakin kofa ya dawo ya sumbaci goshinta sannan ya fito da wayarshi ya dauke ta photo ya maida ita aljihu..
Koda ya fita harabar gidan anan ya tarar duka bodyguards dinshi sun shirya shi kadai suke jira,.
To Aayann Allah ya tsare hanya ..
*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*
*Episode 42*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*
Be jima da fitaba Nawaz ta tashi, lokacin har gari ya fara haske, da sauri ta tashi Aseey Sannan ta shige bayi don yin Alwala.
Bayan tayi sallar ne tayi azkhar ɗin data sabayi bayan kowace sallar asuba sannan ta miƙe ta nufi kitchen don ɗora breakfast domin ta lura Aseey mayyar barcin safe ce saboda tana idar da Sallah ta koma ta kwanta
Ita kuma anata gurin tana ganin abin kunya ne ace akwaisu agidan sannan ace wai sai mummy ta shiga kitchen.
Ba wani abu tayi mai wahala ba, illa dai tayi French toast sai ruwan tea data dafa me haɗe da Na'a na'a da citta da kanumfari da dai sauran kayan kamshi masu kara lafiya da kuzari da kuma ɗanɗano a baki.
Koda ta gama sai ta shirya a dining Sannan ta koma ɗaki tayi wanka ta shirya, ɗan kishingiɗa tayi da nufin taɗan huta kafin muhsien ya tashi tayi mishi wanka, aikuwa ba ita ta tashi ba sai wajen ƙarfe sha-ɗaya da wasu mintina.
Sosai tayi mamakin wane irin Barci tayi haka? Kallon Aseey wacce ke gefe tanayi mata dariya tayi "sis meyasa baki tasheniba?
Dariya Aseey tayi "haba ke kuwa! Nifa na hanaki barci jiya da dare, idan ban bari kin ramaba zunubi kikeso na dauka?
"Haba sister wane zunubi kuma? Kin manta ke yayatace?
Dariya Aseey tayi"to shikenan yanzu dai ki tashi kije kiyi break fast, kowa ya karya amma keda kika dafa baki karyaba.
Miƙewa Nawaz tayi tana murmushi sannan ta fita falour, a nan ta tarar dasu Mummyn SARFRAZ Da Mummyn Aayaan suna zaune suna hira.
Har ƙasa ta tsuguna ta gaishesu Sannan ta miƙe cike da kunya tayi dinning area ɗin. Tana wucewa Mummyn SARFRAZ tace "Wallahi Nawaz tana burgeni matuƙa, yarinyar Akwai hankali ga sanin ya kamata, sannan ga kunya Wallahi sosai da mutunta na gaba da ita, gaskiya kinyi dacen surukar da ake burin samun irinta koda da kuɗi ne.
Ajiyar zuciya Mummyn Aayaan tayi "gaskiya yarinyar Akwai tarbiyya sosai a tare da ita, kuma addini ya kama jikinta sosai...
Nan dai sukayi ta tattaunawa gameda Nawaz ɗin har ta gama karyawa, gabansu ta karasa ta duƙa har kasa Sannan tace " Mummy yau me za'a dafa naga Rana ta fara yi.
Murmushi Mummyn sarfraz tayi "A'a daughter yau ki huta gaskiya, tunda kikazo fa kike hidimar yi mana girki.
"A'a mum babu wata hidima Wallahi, ai girki ba komai bane a gurin mace, Ni daɗi ma nakeji idan inayin girki saboda banaso na zauna tunani ya dameni..
Ƙin yarda mummy tayi Saida Nawaz ta dage tukuna suka haƙura suka barta.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sosai Aayaann yake jin kewa ta kamashi domin tunda ya fito ya barta tana barci fuskarta keyi mishi gizo, ya rasa wace irin soyayyah ce ta kamashi Lokaci guda, duk sai yake jinshi a takure, tafiyar ma ta fitar mishi a rai ba kamar sanda yake ɗokin zuwaba da Farko.
Tsaki yayi Sannan yasa hannunshi a aljihu ya ciro wayarshi don ya ɗan daddanna koya rage lokaci, yana danna wa sleeping face ɗin Nawaz tayi mishi welcome, shiru yayi sosai ya maida hankalinshi wajen kallon photon, photon yayi kyau sosai Domin fuskarta very calm tana barcinta peacefully.
Samun kanshi yayi da yin murmushi Sannan ya furta "Sleeping beauty!!!
Hannu yasa ya shafi pink lips dinta sai kuma ya kashe hasken wayar ya jingina da jikin kujera yana fatan ta soshi kamar yadda yakesonta koma rabin haka, domin yanasone suyi tsabtatacciyar soyayya wadda babu ɓoye ɓoye a cikinta, shidai a nashi ɓangaren baya tunanin Akwai Abinda Zai iya ɓoyewa Nawaz kuma haka yake fatan itama ta daukeshi nan bada daɗewa ba..