← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 112

Sashe 73

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannu kawai Nawaz ke jera mata fuskarta ɗauke da alhini.

Ayanda hassun ke cije baki Nawaz tasan hakuri kawai takeyi don babu yanda zatayi ne. Duk jikinta yayi jajir alamun tasha damƙa, haka fuskarta da hancinta duk sunyi Pink tsabar wahala, bakinta kuwa yayi jajir kamar jini zai fito.

Saida ta daɗe sosai a Ruwan Sannan Nawaz tace "bari a chanza miki wani Koh?

Marairaice fuska hassu tayi "Aunty Don Allah kiyi hakuri ki bari Sai anjima sai a kuma yi"

Murmushi Nawaz tayi Domin tasan hassu ɗin ma tayi ƙokari, "to Bari na chanza miki wanda zakiyi wankan tsarki yanzu"
Tana tsaye harta gama wankan, babu laifi ta iya sosai sai dai abinda ba'a rasa ba, wani ruwan ta chanza mata tace tayi wankan sabulu ta Daura alwala Idan ta gama saita kirata ta ɗauke ta.

Dakin ta koma ta chanza zanin gado sannan ta gyara guraren da ba'a rasa ba sannan ta shiga kitchen. Ruwan lipton ta ɗora haɗe da Kayan kamshi kala kala Saboda tasan bakin hassu ɗin babu daɗi, harzata fita daga kitchen ɗin ta hango ledar kajin da SARFRAZ ya siyo jiya, tsayawa tayi ta gyarasu ta zuba a oven ta saita time sannan ta koma ɗakin Don ganin ko hassu ta gama wankan.

Tana shiga taji hassu na cewa "Aunty na gama" ai da sauri ta ƙarasa bayin tare da chukuikuyeta a cikin towel ta daukota ta direta akan gado.

Sosai ta taimaka mata ta gyara jikinta, riga da skirt ɗin wani jan material tasa, ɗinkin das ya zauna ajikinta kamar anan aka dinkasu Sannan tadanyi mata light make-up daga powder sai dan lip stick kaɗan da kwalli, ruwan zafin ta Kawo mata tace tasha saboda cikinta ya warware kuma bakinta yaɗan yi mata daɗi, nan ma saida akayita gwagwagwa sannan tasha kaɗan.
Naman kazar nema tadanci da yawa sannan tace ya isheta, gyara zama hassu tayi Domin ta gaji da zaman ma gaba ɗaya "Aunty jikina duka ciwo yake yimin Wallahi barinma gurin fits...... Toshe mata baki Nawaz tayi Kafin ta ƙarasa faɗar Abinda tayi niyyar faɗa.

"Sannu kinji Zai dena gaba ɗaya, Yanzu Bari na kirasu a waya in faɗa Musu su tawo miki da magunguna.
Tsalle hassu tayi ta dire akan itafa bazata jira su dawo ba, domin ita gidansu zata tafi.
Mamaki ya hana Nawaz motsi domin itafa hassu bilhaƙƙi take nufin gida zata, "hassu wai idan kinje gidan me zakiyi? Ko kuma ma ince me zakice musu yasa kin dawo" Nawaz ta faɗa tana tsare hassun da ido domin taga iya gudun ruwanta.

"Faɗa musu abinda ya faru zanyi kawai, Kinga sai a ɗauki mataki, idan zai dena sai in dawo muci gaba da zama, idan kuma bazai dena ba sai kowa ya kama gabansa.

"Yanzu hassu duk soyayyar da kikewa Sarfraz ɗin dama ta ƙarya ce? Kuma naga har dai don wannan ne basai anje gidaba za'a iya yin sulhu, kuma nasan zai dena tunda yana sonki, kuma ko wannan ma nasan akasi aka samu"

"Wallahi Aunty ba akasi bane yana sane Domin babu Irin duka da cizon da banyi mishi ba amma yayi banza dani, nasan idan aka barni dashi wata rana kasheni zaiyi.

Sosai Nawaz ke ganin tsantsar wauta da yarintar hassu a fili, ita tama rasa me zatace mata Yanzu.

Miƙewa tayi zataje kitchen sai kuma ta waigo "hassu ina jakar da kika riƙe ranar biki?"

"Tana cikin drawer menene?

"Dama akwai ragowar Diclofenac ɗin da Aunty Aseey tasha saboda aciki ta saka, Kinga kema zaiyi miki amfani yanzu, wace drawer ce in ɗakko?

Nuna mata hassu tayi da hannu, ita kuma Nawaz ta ciro maganin tare da buɗe fridge tana ɗauko ruwa mara sanyi,

Guda biyu ta ciran mata tare da buɗe ruwan tana miƙa mata...

Nawaz takai awa kusan uku da zuwa amma har yanzu shiru su SARFRAZ basu dawoba, su Hassu Diclofenac ya Fara aiki domin harta saki tana ɗan wasanta sai dai tafiyar ce har yanzu Saida dabara.

Jollof rice Nawaz ta dafa musu domin ta gaji da zama babu abinda takeyi, sun gama ci kenan saiga su SARFRAZ sun dawo.
Ba hassu Wadda abin ya faru da ita ba hatta Nawaz saida taji zuciyarta ta bada dararam dam dam, don ita Yanzu tamafi hassu ɗin jin tsoro.
Saida ta daburce da Aayaan ya ƙaraso kusa da ita, kallonshi takeyi tana kallon SARFRAZ, babu ta inda be fishi girma da murdewar jiki ba, wani irin tsinkakken miyau ne taji yana ƙokarin Wuce mata ta ƙaramin makoshi, ai kam babu shiri ta haɗiye shi.

Itakam duk randa Aayaan ya damƙeta ya zatayi kenan? Ji tayi tsoron da takeji na Aayann data samu ya gushe mata na ƴan kwanaki ya dawo mata sabo fill, take zuciyarta ta fara bugawa da sauri da sauri.

"Sweetheart yanaga Kamar bakida lafiya? Meya faru?" Aayaann yace idonshi nakan Nawaz yana nazarin ta.

"Babu komai kawai dai ji nayi bana jin daɗi" Nawaz tace muryarta na ɗan rawa

"Malam ka matsa kusa dani Wallahi, tunda kai mugune kuma azzalumi mara tausayi"

A tare Nawaz da Aayaan suka waiga inda suka jiyo muryar hassu na shatatawa Sarfraz rashin kunya.

Marairaice murya Sarfraz yayi "haba Ikraam bana baki hakuri ba! Kuma kinga nace bazan kuma ba ai.

"Nawaz kuwa ji tayi Kamar ta zunduma da gudu tabar ɗakin saboda Yadda hassu da SARFRAZ suke taɓara, tasan ko makawo ya shafa dole zai gane abinda ya faru.

Ɗage gira Aayaan yayi "yadai Madam C.A Maigoro? Naga kina zufa?

Shiru dai Nawaz tayi tabishi da Ido tana kallon shi don batasan me zatace ba.

"Wallahi Ni kada ka daukeni, kabarni zan iya"

"No Ikraam bazaki iya ba, kin manta akwai ciwo a jikinki sosai, kumafa kalli yadda kike tafiya daƙyar "

Maganar Nawaz Kwarewa tayi, take tari ya turnuke ta, aikuwa da gudu tayi kitchen tana haki, shikuma Aayaan Mai zaiyi inba dariya ba, Duk ya gama lura da yanayinta gaba ɗaya, kuma ya gane tsoro ne tsantsa ke cinta da fargaba, kamar ya miƙe ya bita sai kuma ya fasa domin ya gane tarinma ƙakaloshi tayi Kawai donta gudu daga falourn.

Magungunan da suka siyo Sarfraz ya ciccirarwa hassu tare da bata tasha, sai wani nan nan yakeyi da ita, "anjima Doctor tace zatazo ta Duba jikinki, saboda Kada taje ko kinji ciwo da yawa.

Shidai Aayaan har mamakin Sarfraz yakeyi, ya lura sam bayajin Kunyar shi ko kaɗan, Kodayake gani yakeyi shima ya rigada yasan komai And kuma dama Aayaan ɗinne ya Fara nuna mishi cewar sun zama ɗaya.

Kamar me sanɗa haka Nawaz ta fito daga kitchen ɗin riƙe da babbar warmer da plate guda biyu da cokali.
A tsakiyar center table ta ajiye Sannan ta zuba, kitchen ta koma ta fito riƙe da ruwa da kwalin five alive a saman tray da tumbler guda biyu.

"Ga abinci Bismillah nasan har yanzu da kyar in kun karya"

"Wallahi Aunty kamar kinsan wata uwar yunwa ce ke damuna yadda kikasan ban taba cin abinci ba" cewar sarfraz yana miƙewa kusa da hassu Don karasowa kusa da abincin.

Guri Nawaz ta samu ta zauna kamar gunki, ko ƙwaƙwaran motsi ta kasa yi, duk fargaba ke cinta a Cikin zuciyarta.

"Aunty zoki mikar dani muje bayi ki kuma gasa min jikin, don naji kamar ya fara min tsami"

"Wai meke damun hassu da SARFRAZ ne? Wallahi da nasan abinda zanzo suyi ta mini kenan da ban zoba, Sai neman kiramin ruwa sukeyi.

Miƙewa tayi ba tare data ce Komai ba ta kama hannun Hassu ta miƙar da ita tare da ciccibarta suna shiga cikin bedroom ɗin.

Sai bayan kamar minti talatin suka fito hassu ta chanza kaya, "inaso na tafi gida" nawaz tace batare data kalli inda Aayaan ɗin yakeba, domin wata irin kunyarshi takeji sosai.

"Okay to bari nazo na kaiki" Aayaan yace yana ƙoƙarin sai sun haɗa ido.

Knocking sukaji anayi a kofar falourn, koda Nawaz ta duba sai taga ashe doctor ce harta ƙaraso.

Bata guri tayi ta shigo tana gaisheta, "wacece majinyaciyar? Hassu Nawaz ta nuna da hannu.
"Ayyah Sannu ƴata! Ya jikin naki?

"Da sauki" hassu tace.
" Ku muje ciki inaso na dubata dakyau"

Bedroom ɗin suka shiga inda Doctor ɗin tasa hassu ta cire short ɗinta ta duba jikinta, "dole Sai anyi ɗinki gaskiya saboda kinji ciwo kuma yayi zurfi da yawa ba Lallai ya haɗe da kanshi ba..

Jikin Nawaz ne ya ɗauki rawa, take ta ƙara tausayawa kanta tana jin kamar itama tace ta fasa Auren.

Duk tananan tsare doctor tayiwa hassu allurar Barci har zuwa inda ta gama mata ɗinkin, "Yanzu ƙoƙarin da za'a yi shine ta riƙa shiga Ruwan dumi, kuma a ɗan riƙa zuba gishiri kaɗan a ciki, and bayan kwana shida zan dawo in kwance ɗinkin, kuma Don Allah kada a tasheta Daga barci nan, abari saita tashi da kanta Domin anason jikinta yayi relaxing sosai domin da gani tasha wuya.

Jinjina kai kawai Nawaz ke iyayi.

Har gate Nawaz ta rakata dayake tun a Asibitin Aayaan ya gama biyan charges ɗin harda na Doctor ɗin.

"Sarfraz tace wai Don Allah kada a tasheta a bari ta tashi da kanta saboda wai tana buƙatar hutu.

"To Aunty In'sha Allah bazan tashetaba"

"Yaya Aayaann zo ka kaini gida pls banaso Aunty Aseey ta tafi batare da munyi sallama ba.

Miƙewa Aayaan yayi tare da cewa SARFRAZ "sai munyi waya Bro, Allah ya bata lafia"

Har bakin mota sarfraz ya rakosu yana ta yiwa Nawaz godiya, Domin yasan ba ƙaramin taimaka mishi tayiba, Don shi rasa me zai wa hassu ɗin yayi.

Koda suka ɗauki hanya sai Aayaan ya rage speed ɗin motar tare da kallon Nawaz yana murmushi "sweetheart ni yaushe za'a bani Irin wannan damar da Hassu taba Sarfraz? Ko bakyason mu cikawa mummy burinta na samun yara da yawa daga gurin mu?

"Kunya gaba ɗaya ta dabaibaye Nawaz tama rasa me zatace.
Sosai Aayaann ya lura da halin data shiga amma be nuna mata ba, to ko mu wuce hotel ko guest inn kawai Yanzu? Kinga sai kuyi jinyarku tare da hassu ko?
Chapter 73 · 0% Book details