← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 112

Sashe 58

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Aayaann yake yi mata addu'a tare da shafa Mata Ruwan zam'zam ɗin a fuska, wanda Mummy ta tsiyaya a kofi ya amsa ya karanta fatiha ƙafa bakwai Sannan ya barbaɗa garin ganyen magarya a ciki Tare Da Kafa Mata kofin a bakinta,

Saida ya tabbatar ya zuba a bakinta sannan ya cire kofin, aukuwa nan ta fara atishawa, sai kuma a hankali ta riƙa ajiyar zuciya...

A tare sukace Sannu Nawaz!

Buɗe ido tayi ta kallesu sai kuma ta maida ta rufe da sauri, don wani nauyin Mummy taji ya kamata... Har dai da gaske ita matar Aayaan ce yazatayi da wannan Abin Kunyar data tafka? To yaushe ne ma ta zama matar Aayaan ɗin?

Fara Maganar da Mummy tayine yasa Nawaz ta tsaida tunanin da takeyi tayi shiru tana saurarenta.

Tsaff mummy ta zayyanewa Nawaz komai tundaga sanda sukayi magana da baffa har zuwa randa aka daura aure babu abinda ta ɓoye mata...

Mummy batayi shiru iya namba har Saida ta kara da cewa "Nawaz ina sonki da yawa! Yaro Nama yana sonki sosai, kaunar da muke Miki ce tasa muka nemi alfarmar haɗa zuri'a dake, Sannan ƙin sanar dake da akayi dukni naja, saboda nina roƙi hakan saboda a tunanina idan aka faɗa Miki a lokacin zakiga kamar anyi Miki karfa karfa ne, amma ina Neman afuwarki, Don Allah ki yafe min, Kuma ko yanzu kikace bakyason Aayaaaann Wallahi take zansa ya rubuta Miki takarda...

Shiru Nawaz tayi tanajin abin kamar almara "wai itace matar Aayaan!

Tsugunawa Mummy tayi tare da cewa "Nawaz kiyi magana, kuma wallahi Duk Abinda kikace shi za'ayi.

Da sauri Nawaz ta miƙe tare da kama hannun mummy tana mikar da ita "mummy kefa mahaifiya tace a gurina kuma duk Abinda kika umarceni dayi zanyi, Don Allah ki Dena Duka min..

Aayaann yana gefe yana murmushi, sosai Mummy ta rumgume Nawaz, shima Aayaan Sai ya haɗa su ya rungume..

Nawaz kam nauyinshi ne ya saukar mata a kirji kamar an ɗora Mata gungumen ice... Sifsif ta juya ta fita bayan Aayaan ya sakesu, dakin da aka bata ta shiga tare da zama a gefen gado, Azahiri ita bataji farin ciki ba kuma bataji baƙin ciki ba, saidai Wani Abu dayayi mata nauyi a zuciya..

So take ta fadawa Wani ko zata samu sauƙi a zuciyarta, kuma tana mamakin meyasa umminta bata fada mataba!

Tunanin kiran Nafisa tayi, sai kuma ta tuna Cewa Nafisa garmaho ce ba lallai ta fahimcetaba..

Cikin aljihun doguwar rigar jikinta tasa hannu ta ciro wayarta,
Tabbas Khadija ya kamata ta kira, sosai taji daɗi Kasancewar ta haddace Number KHADIJAT tun tuni, domin zan iya cewa ma batada kawar data fita, sauran duk bogi ne.

Number ta loda tayi dialing, aikuwa ƙara Uku ta ɗaga Tare dayin sallama.

Nawaz na amsawa khadija tace "nayi fushi dake besty, gaskia baki kyautaminba, nazo gidanku yafi so goma amma bakyanan kuma kinsan bana shiri da umma balle in tambayeta.

"Kiyi hakuri deejert, wallahi Yanzu haka ina cikin damuwa, jin rayuwata nakeyi kamar ba tawa ba..

Ƙasa da murya khadija tayi "kawalli meke damunki?

Gyaran murya Nawaz tayi Sannan ta Fara ba Khadija labari, tundaga sanda suka haɗu da Sarfraz har zuwa yanzu da Mummy ta gama fada mata cewa Aayaan mijin tane.

Kasa magana Khadija tayi sai salati takeyi da sallallami, daga baya kuma tace Lallai umma, abin nata har yakai ta Turo amiki fyade, ke duniya.

Amma Nawaz naji daɗi da Allah ya kuɓutar dake daga hannun ƴan ta'addan nan, kuma kika tsira daga gurin wanda yaso yayi Miki fyade.

And Ina tayaki murna da Allah ya baki gwarzon miji me kaunarki tsakani da Allah. Naji daɗi sosai da Hakan ta faru kema sai kiyi ta yiwa Allah godia. Dama kullum idan nayi Sallah saina saki a addu'a, saboda duk set ɗinmu kinfi kowa kokari daga islamiyya har boko gakida kyau, to amma sai Allah yayi jinkiri kawo miki miji, Ashe tanadi yakeyi Miki.

"Khadijah nifa abinda yake dan tayar Min da hankali shine gani nakeyi Aayaan Kamar ba sona yakeyiba sha'awata yakeyi, saboda bini bini yayi ta taɓa min jiki..

"Kai Nawaz! Wai yaushe zaki Dena wannan shirmen nakine? Kefa yanzufa kika gama faɗamin cewa shi jinin Asia ne, saboda Maman shi Yar Pakistan ce kuma a Sudan ra girma, to kuwa kinga dabi'un mu ba ɗaya bane, su sun maida runguma da sunbata ta zame musu al'ada, hakan da yake yi wallahi kauna ce, domin da wani ne ya samu damar da Aayaan ya samu a kanki da tuni ya buga kwallo cikin raga, amma shi ya tsaya yana ta lallaba ki.

Ke in faɗa miki iya damar daya samu jiya a gidan inna ta isa yayi abinda zaiyi ya gama.

To amma saboda kaunarki da yake yi ita ta hanashi bawai don kinfi karfin Shiba.

"To khadija ya zanyi da sarfraz?

"Hmm Nawaz kenan, bazanyi mamaki ba tunda ke Yar farice, me zakiyi da ɗan karamin yaro, so kikeyi ki aureshi nan gaba kuma yace kinyi mishi tsufa? To ki kwatanta ni babu ruwana, da kike zancen sarfraz yanzu, zakisa Aayaan ɗin ya sake kine?
Abinda nakeso ki lura dashi shine Sarfraz harda kuruciya, kuma shi kyau kawai kikeyi masa bawai Wani abuba, kuma Yanzu abinda zakifi focusing akai shine idan yana raye Allah ya bayyana shi, Ni kaina naji tausayinshi sosai domin jarumi ne kuma ya taimake ki matuka, Allah ya bayyana shi..

"Ameen Nawaz tace tare da cewa Nagode sosai khadija zanyi tunani akai, Yanzu sai munyi waya, sallama sukayi Sannan ta kashe wayar tana juya maganar khadija a zuciyarta...

Ji tayi an turo ƙofa, tana Daga kai taga Aayaan ne tsaye har yayi wanka ya shirya..

Kusa da ita ya karaso ya tsuguna tare da kama hannuwanta, "sweet heart pls kiyi min addu'a zanje wani aiki but In'sha Allah bazan wuce 3weeks ba zan dawo.

Mamaki ne sosai ya kama Aayaan jin da yayi nawaz tace "Allah ya tsare, kuma Allah ya dawo dakai lafiya cikin aminci.

Mikewa yayi Tare Da rungume yana jin wani farin ciki da be taɓa jin irinshiba... Sunbatar ta yayi sannan ya fita daga Dakin yana haɗa hannun wuri ɗaya alamar love🫶🫶🫶🫶.

Yana fita kafin ya shiga Mota kiran haidar ya shigo wayarshi sakamakon ya kunna wayoyin bayan sun dawo, dama abinda yasa ya kashe wayar saboda wannan lokacin ya wareshine ga Nawaz..

Yana ɗagawa haidar yahau faɗa yana cewa " wai me yasa ka kashe wayane tun jiya, sai kiranka nakeyi taƙi shiga.

"Meyafaru basai kaji me nakeyi ba ai!

Sarfraz ya farfaɗo, kuma anytime daga Yanzu zai iya tashi.

Ai Saida ayann yayi wata kabbara, sannan yace haidar ganinan, yanzu zan zo In'sha Allah, dama zamuje Eritrea ne nida Colonel amma yanzu zan nemi alfarmar kwana ɗaya saboda nazo na ganshi, komai dare ka jirani haidar i am on my way...

Kiran colonel yayi akan cewa su su tafi zuwa gobe zai riskesu achan Eritrea ɗin.

Allah ya taimake shi koda yaje airport akwai night flight Kuma saura Mutum biyu, ba'a ɗauki lokaciba jirgin ya tashi..

Misali karfe takwas da rabi jirginsu Aayaann ya sauka a England, Kiran haidar yayi yazo ya daukeshi, suna isa asibitin suka tarar sarfraz ya tashi yanata daru wai ina Nawaz da mummyn shi da Daddy...

Hassu kam tana gefe Kamar wata yar tsakuwa, ganin bema nuna yasanta ba.

Aayaann ne ya ƙarasa ya riƙe shi tare da kwantar mishi da hankali, sosai sarfraz ya nutsu yana sauraron shi...

"Ina Nawaz" abinda SARFRAZ taketa mai mai tawa kenan.

"Tana gida, tana gaisheka ma".
"Babu abinda ya sameta Koh?

"Eh babu" cewar Aayaan tare da rike sarfraz yana mikar dashi don su tafi zuwa gidan haidar.

Koda suna hanya babu abinda sarfraz yakeyi sai raba idanu, da dai yaga abin yafi karfinshi sai cewa yayi, wai nan inane?

Bandi ne tace "England ne?

Wani ihu SARFRAZ ya saki tare da cewa wai dagaske nine a England? My best country....

Aayaann kam sai murmushi yakeyi ganin SARFRAZ cikin farin ciki.

Koda aka isa gidan haidar namna dai hassu tsumu tayi tana kallon shi,

Kallonta SARFRAZ yayi yace "wancan me kama da alia bhat dinfa wacece?

Haidar ne yace mamar kace, saboda sanda bakada lafiya ita takeyi maka komai, Kama daga wanka, wanke poo dadai sauransu.....

Zaro ido sarfraz yayi "haba don Allah Nidai ku dena irin wannan abin kada ta rainani....

Haidar bece komai ba face wayarshi daya ciro a aljihu yana danne danne sannan ya miƙawa sarfraz ɗin,

Zaro ido SARFRAZ yayi yana kallon video ɗin, shine daga shi sai gajeren wando yana rikici wai shi hassu ce zata yi mai wanka ga haidar a gefe yana Cewa kabari inyi maka, amma sam yace shi na Hassu yakeso..

Wani miyau ya haɗiye "yanzu wannan yarinyar tasan komai game da shi kenan? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, duk sai yaji kunya ta kamashi..

Wayancewa yayi yace to saime ma, ai ƙawata ce, ko alia bhat?

Murmushi tayi tare da daga kai...

Haka dai aka kwana yin raha, Aayaan ya faɗa mishi cewa shi yayan shine amma sauran karin bayanin saisun koma gida.

Koda safiya tayi da Aayaan Zai tafi Eritrea sai yaba sarfraz daya daga cikin ATM 🏧 CARD Dinshi, akan duk abinda yake bukata ya siya.

Ai kuwa Aayaan yana tafiya bayan haidarr ya tafi asibiti SARFRAZ ya dauki motar haidar, ba Tare dayasan ko inaba yace su Hassu da bandi su hau, map ya saita saboda kada su kasa dawowa..

Kasancewar titunan waje básuda cinkosi yasa SARFRAZ ya riƙa falfala gudu, wani guri da ake Saida waya ya tsaya ya siya aka haɗa mishi komai, dama shifa, sunan daya gani a jikin Kayan Aayaan yakeso ya duba Google yaga matsayinshi...

Ai kuwa yana gama dubawa yace hooooniii ashe babban soja ne, wallahi zanyi bura uba ashe..

Tun daga ranar SARFRAZ ya ishi kowa, daga yaje bishiyar kofar gidan wancan ya ciri guava, sai yaje waccan ya ciri lemun, kuma haka duka zai bata maka kofar gida da ganye, in kayi magana yace shi ƙanin Captain Aayaan ne..

Gaba ɗaya ya ishi haidar, kuma ga gudun bala'i a titi idan ya ɗauki mota..

Yauma zuwa yayi ya siyo (racer) keken nan irin ta yan tsere .
Chapter 58 · 0% Book details