Sashe 75
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daka tsalle yayi ya dire "mummy wato nine bakyaso da kika barni nake zuwa kenan?"
"Ni ina ruwana a wannan? Ra'ayin kane kaga babu abinda ya shafe ni, kuma bazan yarda insa Rayuwar ƴar mutane da aka bamu ita cikin mutunci ba a hatsari"
"Mummy wallahi dakanta tace zata bini fa, kuma bari kiji.
Kunna wayarshi yayi saiga muryarshi yana cewa "sweetheart inaso Nima naje England fa nanda Three days, kuma Gaskiya zan daɗe acan, Don a ƙallah zan iya kaiwa Three months"
"Ya dai Madam what happened?
Kasa kunne mummy tayi har zuwa inda Nawaz ɗin tace "eh Allah zani"
Murmushi mum tayi domin tasamu abinda takeso, tasan yanzu Nawaz ta yarda cewa ita matar Aayaan ce, and ga Dukkan Alamu zasuba juna kulawar data dace, "to wa ya sani ma ko honey moon zasuje suke Min noƙe noƙe? Mum ta ayyana a zuciyarta.
"Mummy bakice komaiba pls"
"Aayann me zance illa ka ɗauke matarka ka tafi!"
Ɗaga ta sama yayi tare da jujjuyata yana cewa "U Are the Best mum ever! I Love You so much, Naji daɗi da Allah yasa kece mamana.
Murmushi mummy takeyi tare da cewa "saukeni Aayann kada surikata tazo ta ganni a haka inji kunya.
Shima dariya yayi tare da sauketa yana cewa bari naje na shirya Don Flight ɗin safe nakeso mubi In'sha Allah, don so nakeyi gobe war haka muna chan.
Nawaz Dake laɓe a gefe Duk tanajin yadda sukayi da mummyn sai taji duk kunya ta kamata, ta rasa yadda zatayi ta fito.
*DON ALLAH A ƘARA MIN AFUWA NA RASHIN GANIN POSTING ƊINA DA KUKEYI AKAI AKAI, WALLAHI UZURURRUKA NE SUKAMIN YAWA, DON ALLAH ASANI A ADDU'A 🤲🤲🤲🤲🤲🤲 NAGODE"*
*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*65*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Saida ta tabbatar mummy da Aayaan sun bar wajen sannan ta fito ta shige ɗakin da umminta suke zaune.
Tana shiga ta faɗa jikin ummi tana haki "lallai Madina, daga zuwa saiki faɗa jikinta Kamar kin faɗa saman gado?" Cewar Ammah tana hararar Nawaz.
"Ai Wallahi Ammah Bansan sanda Nawwarah zata dena yarinta tasan ta girma ba"
Ammah ce tayi dariya tare da cewa "hmmm ai Madinatul munawwarah bazata dena yarintaba sai taga wani ɗan Ko ƴar a hannunki, inaga shine Kawai Abinda zaisa ta haƙura.
Kunya ummin Nawaz taji, amma a cikin zuciyarta cewa tayi "Allah ka bayyanah Min mijina kila nima ina da rabon kuma ganin Wani ɗan nawa"
Ita dai Nawaz duk Maganar da akeyi bata ɗaga ummin tata ba, saima daɗa lanjarewa da tayi a saman cinyarta.
"Gobe War haka in'sha Allah muna gida abin mu" cewar Ammah tana samun gefen gado tana zama
"Nifa Ammah nasan tsohon mijinki Kawai kika ƙosa kije ki gani" cewar Nawaz tana kanne ido ɗaya.
"Eh ɗin ja'ira!! Mijin nawa nakeso naje na gani, ance muku mu irin kune da basu ɗauki miji a komai ba, saikiga mace tayi tafiya tabar miji a wata ƙasa kusan wata ɗaya wasuma har biyu...
Aimu Tunda Allah yace Aljannar mu tana kasan kafarsu muka saduda muke musu biyayya, idan kema zaki yiwa kanki faɗa to gwara kiyi duk da dai Bansan Yadda kamun ludayin naku zai kasance ba.
Duk sai Nawaz taji ta zargi kanta, sai take ganin kamar Ammah tasan tsakaninta da Aayaan ne shiyasa take faɗa mata wadannan maganganun.
"To Ammah da kike faɗan wadannan maganganun cemiki yayi bana yi mishi abinda yakeso?
"Banga alamun anayiba koda shi be faɗa minba, domin alamar ƙarfi ai tana ga mai ƙiba "
Balla mata harara Nawaz tayi tareda cewa "wani mai kibar Koh? Don wani siririn yafi kwarin ƙashi"
"Au Madina Rashin kunya zakiyimin saboda ina baki Shawara akan ki kula da mijinki domin ki samu Aljannah ranar gobe kiyama"
Miƙewa Nawaz tayi tana karkaɗe hijabinta tare da cewa "ba'a son shawarar taki, ƴar sa eyes a abinda be shafeta ba kawai"
"Yanzu Madina nice ƴar sa ayiss ɗin" kallon ummin Nawaz tayi tace "ke Rahmatu meye ayiss ɗin?
Dariya ummi tayi Sannan tace "eyes yana nufin ido da Hausa".
"Uwariyonki nace Madina, wato nice ƴar sa ido Koh?"
Ficewa Nawaz tayi daga ɗakin gaba ɗaya tunda dama a miƙe take ...
"Ƴar ƙaniya! Allah ya raka taki gona, kuma kada ki sake ki dawo ɗakin nan tunda fitsara zaki riƙa yimin"
Ɗaga murya Nawaz tayi "zan gani idan ɗakin nakine da zakice kada na dawo''
Tana fita sukayi kicibis da Aayaan shima ya tawo da nufin shiga ɗakin, gani tayi ya daɗa yi mata kyau fuskarshi cike da farin ciki, idonshi har wani kyalli yakeyi, ga gashin kanshi yasha gyara haɗe da sajenshi.
Murmushi yayi mata me kyau "sweetheart keda waye nake jiyoku tun ina corridor?
Shagwaɓe fuska tayi "ba Ammah bace ta dameni ba"
Shagwaɓar da tayi sai yaji Kamar an tsikare shi, murmushi yayi aranshi yace "mun kusa shiga duniyar da shagwaɓar zatayi Amfani" amma a fili sai yace tafiyarki zanji da ita nasan kishi ne ke damunta, kinsan tunda taga kinfita Komai shine kullum take tononki da faɗa.
Dariya Nawaz tayi ta Wuce abinta tare da mamakin Kasancewar Aayaaaann soja babu abinda ya hanashi, idan yana wani abun ma bazaka taɓa cewa shi soja bane illa jikinshi da zai tona shi saboda murɗewar tayi yawa dole sai dai sojan.
Shiga yayi suka cigaba da sabga dukda yana ɗan jin nauyin ummin Nawaz, "ummi Nawaz tayi muku Sallama kuwa?
"Au wai dama Sallama Madina ta shigo tayi mana shine ta ɓige da yimin tijarah?" Cewar Ammah tare da kama haɓa.
Murmushi Aayaan yayi "to ai Shikenan tunda bata samu tayi muku ba, nina wakilceta, dama yanzu zamu wuce Abuja ne saboda gobe zamu tafi England In'sha Allah.
"Eye ɗan nan Ingila fa kace? Kai da Madina ɗinne zaku tafi Ingila?
"Eh tare zamu tafi In'sha Allah"
"Hmm ashe Dole tamini tijara tasan abinda ta taka, ashe tsallake Najeriya zatayi ta tafi ƙasar masu jajayen kunnuwa?
Dariya Aayaan yayi " Ammah ai addu'a zakiyi mana Koh bakyaso muje ne?
" Ni na isa! Allah ya kaiku Lafiya ya dawo daku lafiya, kuma Allah ya tsare ku ga dukkan sharri, yanzu zaku tafi habuja kace Koh?
"Eh Ammah In'sha Allah, saboda inaso gobe mu sauka da wuri ne a England ɗin domin Akwai abubuwan da nakeso nayi, da goben zamu tafi gaba ɗaya amma sainaga bazai yiwuba"
"To Shikenan Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, kuma dai abinda zan ƙara faɗa maka shine ayita haƙuri, kasan mata akwai su da rauni, don Allah idan kaga tayi ba dai-dai ba a riƙa tsawatar mata.
Sosai suka ɗan taɓa hira Sannan ya fita daga ɗakin zuwa gurin su mummy don ya faɗa mata yau yakeso su sauka a Abuja ɗin.
Ita kuwa Mummy tana tare da Mummyn SARFRAZ inda suka chanza Shawara akan kada a Kawo hassu gidan, tunda har yanzu akwai sauran baƙi, abin zai iya zama na Magana, tunda dama mutane Abinda sukeso kenan.
Wata innar mummy aka sa driver yakai gidan saboda ta kula da hassu ɗin.
Sai bayan sun isa ta kira a waya ta tabbatarwa da Mummyn SARFRAZ ɗin cewa jikin hassu ɗin da sauƙi Sannan ne hankalin ta ya kwanta ta samu nutsuwa.
Knocking ɗin Kofar Aayaan yayi, muryar Mummyn SARFRAZ ce tace "Shigo ciki"
Koda Aayann ya tura ƙofar ya shiga sai mummyn tace "Au ashe ma kaine, shigo ka zauna mana"
Zama yayi yana murmushi, "ya akayi ka wani zauna kana washe mana baki?
"Mummy damafa nazo nace miki yanzu fa zamu Wuce abuja saboda gobe Flight ɗin safe zamubi "
"Toni ina ruwana! Kawai ka ɗauki matarka ku tafi duk inda kake so kuje, na gaji da wannan zargadilar dakake yimin sai kace wani mai bikon matar datayi yaji"
"Haba ke kuwa? Ya za'ayi kice haka? Aayaann kayi haƙuri kaji, Allah ya kaiku lafiya yasa aje a Sa'a, kuma ayita haƙuri da kauda kai don Allah.
Murmushi Aayaan yayi domin yaji daɗin addu'ar da Mummyn sarfraz tayi mishi.
Ita ma Mummyn nashi sai taji bata kyauta ba, ai ko babu komai Aayaan ɗin ya nuna kawaici da dattako tunda wata nawa amma har yanzu ya zuba ido, jifa Sarfraz jiya fa aka kai mishi yarinya amma ya kasa haƙuri.
"To Aayaan Allah ya kaiku Lafiya ya dawo daku lafiya, ya bada Sa'a a Abinda zakuje yi, kuma nima dai abinda zan ƙara faɗa maka shine kada ka ɗauki Yar Mutane ka rabata da ƙasar ta ka kaita wani guri kuma kaje kana ƙuntata mata kayi tunanin Allah zai kyaleka, to wallahi kada naji kada na gani, kuma wallahi har dai ka wulakanta musu ƴa ban yafe maka ba, ina fatan dai kaji abinda nace?
"Naji Mummy, kuma in'sha Allah babu abinda zai faru, zanyi iya kokarina wajen sauke nauyin ta da Allah ya ɗora Min.
"To naji daɗi sosai, Allah yayi muku albarka ya baku zuri'a ɗayyiba.
"Ameen mummy, mungode Allah ya saka da Alkhairi, bari naje nace ta fito sai muyi muku sallamar gaba ɗaya"
Murmushi mummyn sarfraz taketayi tanajin dama Sarfraz ne haka, Amma shi ji yadda yaja mata tashin hankali daga ɗaura Aure jiya.
Yana fita ya Wuce ɗakin Nawaz, be ganta ba amma yaji alamun saukar ruwa a bathroom, yasan wanka takeyi, sai kawai ya samu guri a saman side drawer ya zauna yana jiran ta fito tare da tunanin Anya ma zata yarda ta bishi yau kuwa?
Befi minti biyar da zama ba sai gata ta fito ɗaure da towel pink wanda da kyar ya rufe mata mazaunai, sai wani ƙarami a hannunta tana tsane kanta dashi.
Bata tsaya ako inaba sai a gaban dressing mirror, jan Kujerar tayi ta Zauna tare da ajiye towel ɗin tana ɗaukar hand dryer zata jona a socket donta busar da gashinta.
Shi dai Aayaan sakin baki yayi yana Binta da kallo, be taɓa zaton kyawunta yakai haka ba, cinyoyinta da suka haɗu da hips ɗin ta suka cika towel ɗin da kirjinta daya yi bisa cikin towel ɗin yake kallo, sai fuskarta da tayi lufluf da gashi haɗe da ruwa tayi wani fresh da ita.
"Hmmm lallai Allah yana sona da banyi gigin yin Aure da wuri ba, nasan da yanzu na rasa wannan.