← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 112

Sashe 18

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

tun tuni sai kashe kudi nake a banza, aiki bayayi, yanzuma ji rashin mutuncin da aka mini kuma ta sanadinta... Amma ko abin ya dameki ki tashi tsaye.

fauziyya tace "umma kiyi hakuri don Allah, kuma kibani kwana biyar saina nemo mana hatsabibin boka aduk inda yake......

umma tace na baki amma ki tabbatar aikinshi Kamar yankan wuka yake....

to umma zan ƙoƙarta cewar fauziyya tana Mikewa "bari naje gida mamarshi zatazo yau, kada tazo bananan kinsanta da gulma donma a tsaye nake.. ..

to ki tafi Amma idan ta tafi ki dawo......

*SARFRAZ*

ya shirya Tsaf ya fito amma daka ganshi zaka gane akwai damuwa a tare dashi, fitowa gurin mummy yayi.
"mummy na shirya, gashi kuma kaina ciwo yake dakyar in zan iya yin tu'kinma,...

dariya mummy tayi "SARFRAZ kenan, ai Bakada matsalar tuki, domin y'ar uwar ka ta nemar maka sau'ki, tace driver ya kaiku jigawa inyaso sai Kai ka karasa daku Maidugurin,

Murmushi yayi "Allah sarki malama Inaga ta gane banajin dadine,
Murmushin mummy takuma yi "uhm kundaifi kusa.....

cikin y'an minute har an had'a komai, Suma sun shiga motar.

mummy ce tsaye a gaban motar tana yi musu addu'a, Nawaz harda y'ar kwalla, shikuwa SAFyRAZ ya jingina kanshi da Kujera.....

fita sukayi daga gidan, sai sannan mummy taji kwalla na neman cika mata ido, saboda ta saba da SARFRAZ ga kuma naywaz itama akwai shiga rai.......

Haka ta koma parlour ta zauna tayi shiru.......

Shikuwa driver direct yadauki hanya,

tun ba'ayi nisaba SARFRAZ ya Fara barci, itama nawayz dama irin masu barci a mota ne.....

SARFRAZ baifi minti goma da Fara barciba itama ta fara gyangyadi....

ganin sunyi Kusan awa d'aya suna tafiya driver yace....

Yallabai ko akwai abinda zaku siya, domin mun kusa fita daga gari, kunga babu damar tsayawa kenan koh?

shiru driver yaji, hakan yasa ya waigo..

murmushi yayi ganin Nawaz a Saman kirjin SAFRtAZ sai faman sheka barci sukeyi....

ohh nifa har yanzu na kasa sanin meye alakar wannan yarinyar da SARFRAZ domin nidai ance shikenan d'an d'an su hajiya......

Kila ita zai aura kuma.... share zancen yayi yaci gaba da tukinshi.

*misalin 4:23pm suka Isa Kano*

Anan driver ya samu guri Yayi parking domin tayarsu ta sace.....

me Gyara ya nemo, daya Duba ya sanar mishi cewa sai an chanza tube saboda bazai liƙu ba domin ya ɓuɓɓule.....

kudi ya bashi domin yaje ya siyo....

shi kuma ya koma motar Yana tunanin irin wannan barci nasu SAyFRAZ....

Saida aka kwashi kusan rabin awa d'aya sannan Mutumin ya dawo da tube ɗin yake fadawa driver cewa dakyar ya samo.....

nan suka kwance taya suka fara gyara.....

SARFRAZ ne ya bud'e ido, ganin Nawaz yayi kwance a kirjinshi hani'an sai barcinta takeyi.....

murmushi yayi "itama wannan ta kamu da ciwon barcin kenan...

ganinsu yayi su kadai babu driver, glass ya sauke, anan ya hango driver da bakanike, driver ya Kira yace "Lapia meya faru?

Ehm dama tayarce ta samu Matsala shine ake chanza tape yanzu hakama Muna kano unguwa uku..... Cewar driver

SARFRAZ yace "babu komai ku natsu ku gyara dakyau...

wayarshi ya dauko Don kiran mummy nan yaga missed call dinta yafi ishirin, da sauri yayi dialling din number.

kara biyu ta dauka "haba handsome meya faru inata Kira kunki dauka kunsa duk hankalina ya tashi..

kasa Yayi da murya "mummy kiyi hakuri wallahi dukanmu barci mukeyi, yanzuma natashi ni, ita kuwa bata tashiba....

Mum tace to shikenan babu Matsala, toya hanya? Nasan yanzu kunkai jigawa koh.

A'a mummy bamukai jigawaba har yanzu Muna kano motarce ta samu Matsala....

da sauri mummyn tace Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, meya faru?

Mum ki kwantar da hankalinki tube kawai ake chanzawa ba wani abu bane..... Sai sannan Tayi hamdala tace to anjima zan kira inji ko an gama gyaran, sannan ta kashe wayar....

tashi Nawaz tayi a kirjin SARFRAZ "nifa kaga banason iskanci yazaayi don Nayi barci saika wani janyoni kirjinka ka rungume.....

mamakine ya kama SARFRAZ "nine na rungume ki, kecepah kika rungumeni wallahi...

muɗimuɗi tayi da rai, nifa iskancinka ya Fara isata Allah.....

Nawaz nine d'an iska?
Kallonshi tayi dakai meye inba dan iskaba?

yaji zafin maganar amma saiya basar.

driver ne ya zagaya ya shiga motar yace yallabai angama gyaran, nawane cewar sarfraz.
A'a oga Aina biyashi.

Nan suka dauki hanyar jigawa Misalin shida saura......

Haka suke ta tafiya har saida aka Kira magrib lokacin sun Isa gaya anan suka tsaya sallah amma banda Nawaz tunda batayi.

tunda suka tashi a gaya suka tarar da goslow basu suka Isa dutseba sai Misalin takwas da rabi.

anan sukayi sallama da driver yace shi birnin kudu zai wuce.

babu Wanda yakeyiwa Dan uwansa magana tun fad'an da sukayi a Kano....

shiru SAyFRAZ Yayi, ya koma driver seat,
A sahad ya tsaya yashiga ya siyo ice-cream da yoghurt.

nan ya karasa gurin mai nama ya siya musu steam chicken.

cikin dutsen ya shiga yanata dube dube, nan ya hango wani guest inn.

Karasawa yayi, ya fita anan ya Samar musu d'aki aka bashi key.

dawowa Yayi kifito muje, bata kulashinba ta fito, shi kuma ya dauki ledoji yayi gaba tana biye dashi.

a falour Ya zauna yace mata tazo taci abinci,
Cemai tayi to bari nayi wanka sannan ta shiga ciki tasawa kopar key.

sai Bayan minti ishirin ta fito sanye da doguwar Riga ta yafa gyalenta.

Kallonta yayi ya mika mata ledar, tana ci tana cika tana batsewa Sai Kace mecin magani....

dariya yayi a ranshi zanyi maganinki ne yarinya....

tashi Yayi shima ya shiga ciki yayi wankan ya fito dagashi Sai gajeren wando...

Harararshi tayi ta tashi ta shige ciki harda sa key

murmushi SARFRAZ Yayi Wanda shi kadai yasan maanarshi....

Bayan Kamar awa d'aya, goma saura kenan,

sarfraz naga yasa key ya bud'e bedroom d'in, ciki ya shiga ya mayar ya rufe a hankali, hajiya Nawaz na kwance anata faman barci, da wata yar yololuwar Riga.

kan gadon ya karasa ya dauketa ya d'ora a Saman cinyarshi
bakinshi ya had'a da nata Ya fara sumbatarta, baabu shiri ta tashi daga barci,

ihu ta fara amma babu hali saboda ya rufe bakinshi da nata,

Sarfraz kuwa cewa Yayi "nine SARFRAZ d'an iska, nazone na nuna miki iskancin nawa ki ganshi ra'ayil aini...

ihu ta fara don Allah kayi hakuri wallahi wasa nake maka cikin shakakkiyar murya....

cewa Yayi "bansan wannan ba ya dad'a hade bakinsu guri d'aya.....

Toh masu karatu ku biyoni donjin wace waynar SARFRAZ zai toya

*MATAR RASHEED**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*episode 22*

*🤳written by Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji (Oum aeyman)*

*Supreme writers association (SWA)*

*We write with the ink of era, that's era is our ink*

*We satisfy entertain and touches our readers mind*

Cewa Yayi bansan wannan ba, ya dad'a had'a bakinsu wuri d'aya......

Shure shure nawaz taketa faman yi tana kokarin kwace kanta, amma takasa ko kwace hannunta....

Iya ko'kari tayi naganin ta kwaci kanta Amma ta kasa, hakan yasa kawai ta fara zubar hawaye tunda babu ba'kin magana.....

Sunfi minti goma a haka, sannan SAFRAZ ya saketa......

Jikinta Sai rawa yakeyi tana zazzare ido....

D'an guntun murmushi yayi "naga Kamar akwai magana a bakinki?

Cikin sauri tace "Eh wallahi....

Kallonta yayi "to fad'i muji meye,

Cikin hawaye tace "Don girman Allah, Don darajar alqur'ani ka kyaleni kada kayi mini komai Don Allah.....

" Kuma koda nace maka Dan iska wallahi wasa nake maka, ba Haka nake nufiba....

"Domin kaf duniyarnan ban ta'ba ganin mai kyawawa Hali irinkaba.....

"Hmm Idan kika kumafa? Cewar safraz yana Kallonta

"wallahi idan na kuma kayimin abinda yafi wannan,,

d'aga gira yayi "Haka kikace koh, to na yarda....

Sauketa yayi daga jikinshi sannan yace "kwanta kiyi barci domin gobe da wuri zamu dauki hanya......

Jikinta sai rawa yakeyi, gaba d'aya ta rasa natsuwarta ...

Kallonta yayi, sannan ya fita daga d'akin ya koma parlour,,

jallabiya yasa ya dauki duvet ya kwanta a Saman sleeping couch ya rufa,

Sai dariyar zuci yakeyi saboda nawaz ta bashi Daria sosai....

ooh wato nawaz harta yarda cewa zan iya yi mata wani abu kenan?

hmm batasan nima karfin Hali nayiba, Ashe itama muguwar matsoraciyace naketa wahalar da kaina....

Kuma cewa Yayi "ya Allah ka karemu da son zuciya da aikata aikin dana Sani....

Yana wannan sake saken barci Yayi awon gaba dashi.

ita kuma nawaz tana nan inda ya barta ko kwakwkwaran motsi ta kasayi, domin gani take zai dawo.

tafi minti ishirin a haka sannan ta tashi ta bud'e fridge ta dauki ruwa Tasha, kwantawa tayi taja bargo ta rufa.....

har lokacin jikinta rawa yake, tafi awa daya a kwance Amma fir barci ya 'kauracewa idonta.....

Haka dai tayi shiru ta sa'ka wannan ta warware, tana rokon Allah yasa safiya tayi

har gajiya da kwanciyar tayi, amma barcin yaki zuwa, bata ankaraba saijin kiran sallar farko tayi,

Tashi tayi ta shiga bayi tayi wanka ta dauro alwala Ta fito,
Shiryawa tayi sannan ta shimpida praying mat Ta fara sallah.....

Tana cikin sallah SAFyRAZ ya wuceta ya shiga bathroom d'in, wanka yayi Yayi alwala sannan ya fito....

Jin fitowarshi yasa nawaz ta Mike tayi Kamar bata idar da sallar ba domin bataso ko magana ta had'a su....

wucewa yayi ya koma parlour, Bayan ya shirya ya fita zuwa masallaci.....

Tanajin fitarshi Ta cire hijabi ta hau Saman gado Ta zauna...

mudubi ta dauko ta duba bakinta, gani tayi Yayi ja Kamar jini zai fito.....

Tsaki tayi "Mtswess Allah ya isana, kuma bazan yafeba.

mugu kawai

kuma ance Dan iska, kayi abinda zakayi

*(Nidai OUM AEYMAN cewa nayi Aida kinbari Yadawo saiki fad'a a gabanshi)*

Cewa tayi mutum sai karfi Kamar babu jini ajikinshi, nidai Allah ya rabamu lapia tana dada jinjina irin tsaurin iso da rashin kunyar da sarfraz yake nuna mata....

da ace jiya yamini wani abu dana shiga uku na lalace.....

yanzuma lallabashi zanyi mu rabu Lapia.....

Komawa tayi ta kwanta, kasan cewar batayi barciba da dare yasa tana kwantawa yayi gaba da ita....

shi kuma SAFRAZ Bayan an idar da sallah bai fito daga masallaci ba, zama yayi ya dauki alqur'an yana karantawa....
bashi ya fito daga masallacin ba saida gari yayi haske...

reception yaje Yayi musu order d'in breakfast, sannan ya koma d'aki....

Jin shuru shuru yasa ya shiga bedroom d'in, ganinta Yayi tanata faman barci hani'an......
Chapter 18 · 0% Book details