Sashe 78
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
A saman table ta ajiye Sannan ta fice, shikuwa gabanta ya ƙarasa yana cewa ''Sweetheart anya wannan shirin na Allah da Annabi ne kuwa? Fitata ace har kin gama shiryawa"
Murmushi dai kawai tayi mishi don bata da tacewa kuma baso take zancen nasu yayi tsawo ba.
"Zo ki zaɓi abinda kikeso Anan"
"Ko wanne ma kabani inaso" cewar Nawaz a hankali
"Nop Gaskiya saikin zaɓa! if not kuma na baki da kaina"
Gabanshi ta dawo tare da buɗe duka take away ɗin, farfesun kaza ne a cikin ta farko, ta biyu kuma farfesun naman rago na ƙarshen data buɗe nema taga snacks ne marasa nauyi.
Shi ta riƙe tare da cewa "wannan nakeso"
Murmushi Aayaan yayi domin dama yasan bazai wuce shi zata zaɓa ba "to ai nima shi nakeso"
Miƙa mishi tayi tare da cewa "gashi Ni bari na ɗauki kazan kawai"
"Nop sai dai mu raba gaskiya" ita dai Nawaz shiru tayi tana binshi da ido domin ta gane neman magana kawai yakeyi.
Tana kallo ya ɗauki Flask ɗin Tare Da tsiyaya musu mint tea a cikin cups ɗin sannan ya ajiye mata a gaban ta, take away ɗin ya ajiye a tsakiyarsu tare da cewa "to Bismillah muci"
Batason ta riƙa yawan yi mishi musu domin ta lura kamar hakan yakeso, domin tana farawa sun soma yin jayayyah kenan.
Kallonta yakeyi ta gefen ido yadda take yafitar cake ɗin kamar ana yi mata dole, tea ɗin ma idan tayi sipping Dinshi saita jima bata kuma kaishi baki ba.
Take away ɗin da kazar take ciki ta janyo tare da buɗewa, cinya ɗaya ta ɗauka takai bakinta ta gutsura a hankali, sosai tayi mata daɗi yadda taste ɗin be Wuce ƙa'ida ba saboda sosai kamai yayi normal.
Tama manta da wani Aayann na gurin saida ta cinye cinya guda biyu ta ɗauki ƙirji Sannan ta tuna, basarwa tayi ta ɗan yagi kaɗan sannan a ajiye ragowar tana miƙewa.
Bathroom ta shiga ta wanke hannunta tare da kuskure bakinta Sannan ta ɗauki towel ta goge.
Tana fitowa shima ya shiga, haka dai kowa yayi jugum kamar kurame, wayarshi ya ciro tare da sanar da driver yayi warming ɗin mota gasunan fitowa.
Komawa yayi kusa da Ita ya zauna sannan yace "my beloved Hope Ban ɓata miki rai ba, naga kamar kina fushi dani".
Babu shiri tayi murmushi "Wallahi Babu abinda kayi min, kawai dai Bansan me zance maka bane shiyasa kaga nayi shiru.
"Thank God tunda sarauniyata ba fushi takeyi daniba, amma da harna tsorata "
Dole yasa ta ƙarayin murmushi duba da yadda yayi maganar kamar gaske.
"Let get going, driver is waiting"
Miƙewa Nawaz tayi tare da duƙawa tana zira takalmanta sau ciki, shima Nashi ya zira yana kallonta yana taɓe baki.
Cewa tayi "menene?"
"Kawai dai Naji muna tsami ne, kinsan kayan jiya muka mayar, kuma gaskiya banaso mu shiga jirgi aji muna wari saboda raina mana class za'a yi.
Da sauri ta ƙarasa gabanshi tana shinshina ƙirjinshi "yaya wallahi kamshi kakeyi sosai, kamshin ma me daɗi "
Rau rau Aayaan yayi da ido "Nasan tunda kikace haka Allah tsami nakeyi "
"Wallahi kamshi kakeyi me daɗi sosai"
Kashe mata ido yayi "dagaske" ɗaga kai tayi "eh da gaske"
Be jira Komai ba ya rungumeta a ƙirjinshi tare da kama bakinta yana bata 2minute kiss "gaskiya sweetheart inaga sai munje kasuwa na siyo Miki wayau don sam bakyada wayau ko kaɗan"
Ita dai Nawaz rufe ido tayi Domin tun kiss ɗin da yayi mata kunya ta rufeta.
Ciccibarta yayi suka fita daga ɗakin, betsaya ko rufe kofar ba ya ƙarasa reception ya basu key ɗin Tare Da cewa suje su gyara dakin kuma su rufe.
Duk Abin Nan da akeyi Nawaz na rungume a ƙirjinshi, ko a cikin mota kanainayeta yayi, sanda suka isa airport ɗin ma be bari ta taka da kanta ba, nan ma shi ya ciccibeta, duk abin duniya ya ishe ta, ga wata uwar kunya dake damunta.
Saida yayi clearing ɗin komai Sannan sukayi Sallama da driver akan zaiyi ƙoƙari ya koma Zaria yau saboda a Wuce Maiduguri Tare dashi.
VIP nanma suka sauka, a seat ɗinta ya ɗora ta sannan yasa mata belt, ita kuwa rufe idonta tayi Kamar me barci saboda wata uwar kunya data kulluɓeta.
"Zama ki buɗe ido ne idan kikaji bakina cikin naki"
Ai kam da sauri ta buɗe saboda tasan tsaff ze iya aikata Abinda yayi ikirarin yi, sai dai sam taƙi yarda su haɗa ido dashi.
Gyara belt dinshi yakeyi Amma idonshi na kanta, ya lura akwai tsoro tattare da ita sai dai tayi ƙoƙarin basarwa. "Sweetheart what's wrong?"
Jinjina kai tayi Sannan tace "Nothing kawai dai harna Fara kewar ƙasata ne tun Kafin in barta.
Murmushi Aayaan yayi "you're right dear, Allah dai ya kaimu lafiya kuma ya dawo damu lafiya"
"Ameen" Nawaz tace tana satar kallonshi, ai Kuwa charaf suka hada Ido, take ya sakin mata wani shu'umin murmushi me ɗauke da fassara kala-kala.
Saurin kawar da kanta tayi itama tana murmushi ƙasa-ƙasa.
"Saura ƙiris dai" cewar Aayaan yana kashe mata ido ɗaya
Maida Idonta tayi ta rufe tana sauraron bugun zuciyarta, saboda gaba ɗaya tsoro ne ya kamata amma tana ƙoƙarin dannewa saboda kada Aayaan ya samu abinda zai riƙa tsokanarta nan gaba, sarai Aayaan yasan bata taɓa hawa jirgi ba, ya kyaleta ne don yaga iya ƙarfin jarumtarta.
Haka aka fara sanarwa cewa "All passengers should please fasten their seatbelt"
Su dai dama tuni sunsa nasu belt ɗin kawai Sai sukayi shiru suna sauraron motsin kowa.
Kara rufe ido Nawaz tayi tana addu'a a cikin ranta, duk abinda take yi Aayaann yana kallonta, sosai jarumtarta ta ƙara burgeshi "Lallai kin amsa sunan ki na matar soldier, bari ma mu gama sabawa har harbi zan koya miki saboda koda ta kwana" shi kaɗai yake hira da zuciyarshi
Sosai ya shiga tunani akan rayuwarshi da Nawaz, tunda yake be taɓa kawowa kanshi Aure nan kusa ba, kuma be taɓa tunanin akwai wadda zata chanza mishi ra'ayi cikin sauƙi hakaba, ya ajiye cewa Allah subhanahu wata'ala ne Kawai ya kawo mishi Nawaz a Matsayin mata ba Tare Da wata dabara ko wayau nashiba.
Kuma zai cigaba dayi mishi godiya har ƙarshen rayuwarshi....
Firgigit ya dawo daga nisan tunanin da yayi, hannu yasa ya taɓa kafaɗarta donya ce mata ta buɗe idonta sun dai-dai ta a sama, amma cikin Sa'a sai ya Tarar Ashe tayi barci.
Murmushi yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta sannan cikin zuciyarshi yana jin wani abu mai ƙarfi game da ita, dramar jiya da dare ne ta dawo mishi, sanda Nawaz ta daddage ta zuba mishi ido tana ƙarewa halittar shi tanadi batasan tun tashinta shima ya tashiba, duk Abinda tayi yana jinta kuma shi hakan ma daɗi yayi mishi yadda ya lura halittar shi tayi Mata.
Har yau ya kasa yarda cewa shekarar Nawaz 25, Ganin yarinta yakeyi ƙuru-ƙuru a duka lamuranta, shi a nashi gani yakeyi idan tayi wutar gaske to ƙila ace 20years.
Lumshe ido yayi ba wai don yana jin barci ba kuma ba wai don ya gaji ba, sai don wani irin ɗoki dayaji yana kamashi, haƙiƙa yana son soyayya kuma yanaso ya maida matarshi Tamkar ƙawa a gare shi, yanaso suyi sabon da babu wani abu dai-dai da girman ƙwayar zarrah da zasu iya boyewa junansu.
Kuma ga Dukkan Alamu ya fara Ganin alamun Nasara, saboda ya lura cewa zuciyar Nawaz ɗin wanke take tass babu kowa a ciki, yanzu ɗora hadda ne Kawai ya rage mishi, tunanin mafita ya fara yi.
Ai kuwa beyi nisa ba Allah ya taimake shi ya samu, jinjina kai yayi yana daɗa jajdada wa kanshi cewa tabbas mafitar tayi.
Waya ya ciro a aljihunshi ya fara rubutu a cikin notes yana saving saboda beso ya manta, still kuma yana so ya turawa haidar sako Amma babu dama saboda ya rigada yasa wayar a Flight mode.
Ajiye wayar yayi a saman cinyarshi yasa hannu yana gyara mata kanta, saboda ya ɗan karkace kuma beso yayi mata tsami, haɗa ido yayi da wata baturiya ta sakar mishi murmushi alamun ya birgeta "couple's?" Baturiyar ta tambaya
"Yea" cewar Aayann.
Wani murmushin ta ƙara yi tare da cewa "wish u All The Best"
"Ameen thanks" Aayaan yace yana murmushi, sosai yaji daɗin addu'ar datayi musu koda kasancewarta ba musulma ba.
Attendant ce ta fara zuwa tana tambayar su me za'a kawo musu, wasu suce ruwa wasu su faɗi wani Abu daban, data zo kan Aayaan sai yace mata he's Okay Amma idan Madam Dinshi ta tashi zai nemeta.
Dariya tayi tace "okay I will always be ready"
Jinjina kai yayi alamun ya gamsu...
Duk second ɗaya idonshi na kanta, ya rasa me yasa yakejin kamar ya buɗe cikinshi ya sakata ya huta, wata irin ƙauna yakeyi mata wadda besan sanda ya soma ba, yanajin kamar idan babu ita bazai iya rayuwa ba.
Duk tsawon tafiyar amma sai Aayaann yaga kamar ƙiftawa da Bismillah har an fara sanarwa cewa "kowa ya shirya sun iso kuma jirgi na gaf da sauka, abinda be lura dashiba shine tun Kusan 35minutes baya Nawaz ta tashi Amma kunya da tsoro ya hanata ta nuna idonta biyu.
Bayan jirgi ya dai-dai ta a ƙasa aka buɗe kofa passengers suka fara fita a jere a jere, Aayaann ne ya miƙe da nufin ya ciccibi Nawaz Bayan ya cire mata seat belt ɗin, buɗe idonta tayi da sauri tare da cewa "yaya ka barni zan iya"
Mamaki ne ya kama Aayaan Yadda yaga idon Nawaz tarwai babu alamun barci "kenan rainamin wayau kikayi dama idonki biyu Koh?"
Ciccibarta yayi batare daya kula taba, Ita kuma ta fara wuntsil-wuntsil wai ya sauketa zata iya.