← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 112

Sashe 4

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Nan kuma saimu shirya walimar da za'a yi ta cin nasarar mu

Cheers 👏🏼👏🏼👏🏼👏👏👏 sannan Yayi hanyar Waje sauran y'an Ajin suka rufa mishi baya.......

Motarshi ya shiga zuwa gida Amma abin mamaki shine ko Sahun malama nawaz be ganiba, Sai kuma yaji beji dad'in hakanba.....

Koda ya Isa gida sai yajishi duk acikin damuwa komai ma a sanyaye yakeyinsa "Anya kuwa na kyauta abinda nayi, Anya ban zalunci kaina da itaba?
Ai kodon darajar Qur'an din da take karantawa yaci na rabu da ita, to koma dai damuwace ta sata koyarwar?

Tun abin be nunaba har Saida mummy ta gane "sweet heart meke damunka?

"Mummy babu komai, kawai dai banjin dadine"

"Fab don Allah in wani abunema ke damunka please kada ka boye min, idan baka fada min ba wa zaka fadawa?

Duk duniya bamuda Wanda yafi junanmu, idan Kanada damu ka fada min saimu naimi mafita.

Kuma dama inaso na Maka magana gameda auren da dad Dinka yakeso kayi "gaskiya hakurin shi ya soma karewa, kuma naga auren ma is for your own good, please ka duba maganar

"To mummy insha Allah kada ki damu zan duba" ya Fadi Hakan ne kawai don ya Yankee maganar bayaso tayi tsawo

NAWAZ...........
A kufule ta shiga gida ko umma Dake zaune a tsakar gida Bata kalla ba balle tayi mata Sannu da gida.
A falour Ta tarar da ummi tana ninke kaya
"Sannu da aiki ummi" abinda ta iya cewa kenan Ta wuce dakinta...
Jefar da jakar tayi a Kan gado ta tuge niqab da hijab d'in a tare.....
Kan gadon ta fada "wai wadannan wasu irin yarane Allah ya had'a ni dasu?

Ace mutum beda kunya beda Ta ido, Kowa duk maganar datazo bakinshi haka zaike fad'a min ita!

Amma zanyi maganinsu, wani tunani ya Fado mata "Anya bada gayya sukemin wannan iskancinba?

Idan kuwa hakane zasu gane shayi ruwane, don bazan bar makarantar ba saina koya musu hankali.
Mikewa tayi ta fita falour, a kofa ta hadu Da ummi zata shigo "nawaz wai Meyafaru naga kin shigo ranki a bace???

Ummi wallahi y'an ajinane, na gaji da rashin kunyarsu na gaji da wulakancinsu basa da kunya ko kadan........

nawaz koda yaushe Ina yawan umartarki da yin hakuri duk fa Wanda kikaga yayi nasara a rayuwa sai yayi hakuri tukuna, Dan Allah kiyi hakuri kici gaba da zuwa aikin Nan da kika samu rufin asirine a gurin mu...
wallahi mutane basason aikinnan dakika samu kuma idan har kika bari to kinga burinsu ya cika kenan son haka nake umartarki da ki jure kuma ki toshe kunnuwan ki akan duk wani abu da zasuyi ko auce, illa ke dai kiyi abinda ya kaiki ki dawo gida.....

To ummi zanyi duk yanda kikace indai zakiyi farin ciki, amma inaso ki kara yawan Adduar dakikemin akullum domin ita zata karamin samun nasara a rayuwa.....

to nawaz Insha Allah zan 'kara akan wadda nakeyi, yanzu Maza ki tashi kije kiyiwa umma Barka da gida domin inajinki sanda kika dawo baki gaishetaba...
to ummi " Mikewa tayi ta fita.
A kofar d'akin umma taita sallama Amma ba'a amsaba, Saita yanke shawarar ta shiga cikin d'akin......
Tashiga ta nufi hanyar bedroom d'in umma, Amma ga mamakinta abinda taji shine : "Tunda Rahma Ta yarda Ta auri mijina wallahi ita da kwanciyar hankali har abada, kuma yarinyar data haifa ita Zansa ta zame mata bala'i da annoba a rayuwar ta saitayi burin mutuwa akan rayuwa, na tsani Rahma na tsaneta wallahi don kawai bazan iya kasheta bane Amma da tuni na kashe shegiya.
Amma dukda haka saina dasa mata tabo a rayuwarta
Domin nawaz bazata ta'ba yin aureba har abada kuma badai Alhaji ya tafiba to kuwa shida ya dawo Sai ruwan daza su Kai bakinsu ya gagaresu....
Muryar fauziyya taji tace umma kidena damun kanki da wani zancenau domin bokan yacemin duk abinda kike Bukata zaiyi miki hardai akwai kudi......

umma tace " fauziyya wai jiya saiga yaro ya shigo gidannan wai ana sallama da nawaz.......
Idan kinji yanda zuciyata ta kusa fashewa saikin tausayamin tsabar bakin ciki da damuwa Saida na Dena ganin gabana, kuma Baki saniba wai Dana leka mutumin harda mota alamun Mai kudine sosai duk da a duhu ne Amma bakiga yadda shaddarshi ke kyalliba.....
Daria fauziyya tayi " nace ki kwantar da hankalinki kuma ki kaddara cewa wannan kiran da aka yi mata jiya shine kiranta na karshe son wallahi yadda ban auri me kudi ba Bata Isa ta aura ba, ai wahalace ta dace da ita ba niba....
"umma tace nifa Dan bokannnan yace bazatabi duniya bane Amma wallahi ni a yanda natsaneta naso ace ta zama karuwane tana haifar shegu uwarta na mata raino da goyasu, yanda ba'kin cikintane zai kashe uwarta har lahira........

Amma dukda haka babu komai "tashi mu koma falour zan duba inga abinda ya dace muyi ni matsalata kudin da bokan ya bukata sunyi yawa

"Hmm umma biyan bukata yafi dogon buri kawai ki bashi ayi komai a gama" cewar fauziyya tana duban umman......
da sauri nawaz ta fita tana mamakin maganganun umma "dukda bayau ta Fara jinsuba amma nayau sun d'aga mata hankali matuka,. To wai ita meye laifinta? Ba ita ta zabarwa kanta uba ba .....
ruwa ta d'iba a buta donyin alwala ,
Tana cikin wanke fuska wani yaro ya shigo "wai wani mutumi a waje yace aunty nawaz tazo!
ha'ki'ka nawaz taji dad'in kiranta da akayi kodon ta kuntatawa umma zata fita kuma koma waye zata tsaya Ta saurareshi tunda Taga abin na umma dada yin gaba yakeyi.
Da sauri tacewa yaron "je Kace tana sallah Amma yanzu zata fito ...
to yaron yace sannan ya fita
a gur guje ta karasa alwalar ta shiga d'aki donyin sallar,

sai sannan umma da fauziyya da suke labe Bayan labule suka fita Don ganin waye yazo gun nawaz din... "ga mamakinsu kyakykyawan matashi Mai karfi a jika suka gani jingine da mota da waya a hannunshi Yana dannawa kumA da alamu kudi sun zauna Mai sosai duba da irin sututar Dake jikinshi, da irin Motarshi da kuma yanayin shigarshi...
Kwafa umma tayi "fauziyya Bana jiya banefa gaskiya ya kamata ayi wani abu domin wallahi ciwo zai iya kamani muddin aka cigaba da Haka kada fa yarinyar Nan ta auri Mai kudi....

cikin gidan suka koma suna tafe suna kulla makirci (Allah kasa Mufi karfin zuciyarmu, wai uwa da yane suke wannan Al'amari)

Bana Jin Dadin jikina kuyi manage da wannan

_*YAR CHIKAJI*_✍️✍️*🎀🎀 SAFRAZ 🎀🎀*

*Episode 5*

Written by oum aeyman

Supreme writers association......

We write with the ink of era......

Cikin gidan suka koma suna tafe suna kulla makirci.......

Nawaz ta fito sanye da niqab, ta fita Waje

A Gefe ta hangoshi jingine da mota..
Karasawa kusa dashi tayi "Assalamu alaykum"
"wa'alaykis salaam" yace yana murmushi.....
"meya kuma kawo ka gidanmu?
What did you come for?
Dariya safraz yayi "am sorry aunty nawaz I'm really sorry please,
"it's okay, now tell me what are you up to?

Truly I'm not up to anything malama
Dariya nawaz tayi "really?
Wallahi Dagaske nake ba komi, dama daddy nane ya aikeni shine nace bari na biyo mu gaisa....

OK nagode sosai safraz, kasamu ladan ziyara, I will be getting inside now...
No malama pls don't go,...
Dariya abin yaba nawaz yanayin yanda Yayi magana Kamar karamin yaro, dakewa tayi "why"?

"Saboda akwai maganar danakeso muyi"....

"Okay inajinka Menene?

"Ehm dama cewa nayi ni kadai mummy na ta haifa banada kanwa ko yaya....

To what's wrong with that? Nima ni kadai ummina ta haifa....

"Yauwa kinga faduwa tazo dai dai da zama kenan koh, yanzu Sai mu zama y'an uwan juna koh?
Bata fuska nawaz tayi "as how?
Dariya safraz yayi saboda ya gane me take nufi "as in inzama yayan ki Ke kuma kanwata, kinga that will be I have a sister and you have a brother, right?

Murmushi nawaz tayi "Sannu Dason girma har kawani zabarwa kanka yaya to gaskiya bazan yardaba I will be the senior sister ....

OK Kowa ya fad'i shekarunshi, kinga duk Wanda shekarunshi sukafi yawa shi zai zama yaya...

"it's okay I'm 25yrs how about you?

"Lallai malama dama Haka kikeda son girma ? Ina laifin ma kice 20yrs

" bawannan ba Kai nawanaka?

I'm 24yrs old,,,
hmm Sannu "wai kai gudun shekarun kake?
"No malama I'm serious....

"Okay nima I'm serious me zan samu idan nayi Maka karya?

"A'a malama duk maganar batakai namba, naji zan zama 'kani saiki zama yaya.

" Don't worry nabar maka girman, Allah yasa ka iyayin abinda yaya yakewa kanwa .....

"amen sister, Allah yasa, kuma nagode da kika amsheni a matsayin yaya....

to zan shiga gida kaga an Fara kiran isha'i, zanje nayi sallah..

malama please Dan tsaya,...
bata rai tayi "naga na saurareka, an then what next?

ba komai malama dama cewa nayi ki tsaya ki amshi present Daga yayanki..

wani karamin parcel ya ciro d'aga cikin mota ya mika mata gashi sisyna, and please meyasa har da dare bakya cire niqab, aiya kamata ki cire kodon kiji iska

no, i can't take anything from you! And kuma niqab raayi nane
why sis? Pls consider this from your brother not from your student....and zancen niqab kuma kiyi hakuri banyi Don na bata miki raiba
Amsa tayi tace thank you, good night...
harta juya ta waigo "yauwa safraz tsaya in dauko maka wayanka,
No malama kibarshi i will take it when i am ready ....
"to"tace sannan ta yi hanyar gida....

Dasauri umma da fauziyya suka shiga gida har suna gware saboda kada nawaz ta gansu,,

safraz be tafiba har saida ta shiga gida sannan ya shiga mota,
A masallacin dake kusa dasu yayi sallah sannan ya shiga gida...

A falour Ya tarar da mummy tana safa da marwa....
tana ganinshi ta rungumeshi hade da ajiyar zuciya "haba sweetheart Daga cewa bari kazo yanzu zaka dawo shine har kafi one hour?
Wallahi duk hankalina ya tashi,
Dariya safraz yayi "kada ki damu mum gashi na dawo, ina dad?

🤫🤫tun dazu ya dawo, yace Ina Kake shine nace mai kana daki kana kararu saboda nasan zaiyi fad'a idan yasan nabarka ka kuma fita Bayan ka dawo daga islamiyya...
Chapter 4 · 0% Book details