← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 112

Sashe 107

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Goggo ce tace "wai Ni kam gidan nan sai naga yana komawa kamar ba gidan zaman makoki ba"

"Eh goggo ai kinsan idan mutum ya daɗe yana jinya mutuwarshi bata cika damun Mutane ba kamar wanda ana tare da an rabu ace wane ya mutu" cewar kanwar marigayiyar

"Ai kuwa dai ai Aunty tasha jinya wallahi, Allah dai ya jikanta yasa kankarar zunubai ne" cewar yayar Colonel tana miƙewa

°°°°°

Sosai Nawaz tayi barci domin sai bayan la'asar ta tashi, samun kanta tayi rungume cikin jikin Aayaan shima yana barcin shi peacefully.
Motsin data yine ya tashi Aayaan, da sauri ya tashi ya zauna tare da cewa "sweetheart kin tashi? Ya jikin naki? Fatan babu inda yake miki ciwo Koh?"

Ɗaga mishi kai tayi kawai domin bata sanma tambayar da zata amsa mishi ba,
Ɗaukar ta yayi ya kaita bathroom ya wanke mata baki shima ya wanke nashi sannan ya dawo da ita ya zaunar da ita a saman bed.
Duka abubuwan daya siyo mata ya buɗe mata tare da cewa "Ranki ya daɗe Bismillah!.

Sosai take cin kazar kamar ɗan gudun hijrar daga fi sati be ga abinci ba, tana gama ci zata sha madara sai amai ya kwace mata, tashi tayi da gudu da nufin ta shiga bayi amma Aayaan yayi saurin riƙe ta tare da rungumeta "dear kiyi anan kawai..
Tun kafin ya ƙarasa tuni aman ya tunkuɗo waje, duk jikin Aayaan ɗin ya ɓaci har wajejen wuyanshi, sam shi ba wannan bane ma ya dameshi illa yunƙurin da yaga tana ƙara yi, sai faman jera mata sannu yakeyi kamar wadda za'a shiga da ita ɗakin haihuwa..

*MASU KARATU KO A IYA NAN AI MUNGA ILLAR SON ZUCIYA, JUST KU KWATANTA JAMILA DA WAHALAR DA TASHA, NAN KUMA GA NAWAZ DA YADDA AAYAAN KE KULA DA ITA*

MATAR RASHEED ✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*90*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Duk ya rude sai sannu yakeyi mata, saida ya samu ta gama duka aman sannan ya kwantar da kanta a ɗaya gefen kafadar shi inda be ɓaci ba, bayanta ya riƙa shafawa a hankali soboda tayi saurin samun relief.

"I'm sorry sweetheart, wallahi na kasa riƙe aman ne Kum......

"Shiii🤫 keep quiet, meye zaki bani haƙuri bayan Nine nayi cikin! Kuma after that aini zaki haifawa yaro and kuma ma aike kika sha wahala baniba, so Kinga ai Ni ya kamata na baki hakuri!! I'm sorry dear duk Nasan nine naja miki duka wahalar nan, da ace banyi cikin ba da yanzu kina sabgarki cike da lafiya"

Mamaki ne yasa Nawaz tayi shiru tana sauraron shi batare data ce komai ba har ya gama maganar shi, "wai wane irin miji Allah ya haɗa Ni dashi ne? Wasu mazan fa sun san su sukayi cikin amma kyamar ka suke komawa suna yi, wasu har ma su riƙa kyarar ka suna daka maka tsawa idan kayi wani abun, Lallai Allah ya zaɓe ta a cikin dubu" zancen da Nawaz ta gama ayyana wa kenan a cikin zuciyarta.

"Sweetheart bakice komai ba! Hope ba fushi kike dani ba!"

Duk maganar da Aayaan zaiyi sai taga kamar ƙara kwance mata notikan mamaki yake ƙara yi,
"No dear, ni baka yimin komai ba, kuma ai dama burin kowace mace ta zama uwa. So kaga babu wani laifi daka yimin"

Ɗaukar ta yayi ya shiga bathroom inda ya gyara mata jiki sannan yayi mata wanna shima yayi suka fito.
Zaman ɗakin duk sai ya ishi Nawaz duk motsi saiya ce menene? Me yake damunta? Ko akwai abinda take bukata?

Tafiya ma ya hanata yi sai dai komai ya ɗauke ta, hatta bayi idan zata shiga saiya rakata.
"Sweetheart pls kabarni mana! Meyasa zaka riƙa wahalar da kanka haka ne?"

Dariya Aayaan yayi "lallai har yanzu akwai sauran shakkun dakikeyi akaina game da soyayyar ki kenan Koh?"

"A'a sweetheart"

"Hmmm to meyasa kike cewa na rabu dake"

"To shikenan kaci gaba! Nagode" cewar Nawaz tana kwantawa a saman jikinshi

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Kafin wani lokaci Inna talatu da ummi sun gyara ko ina tass kamar ba inda aka haihu ba, ko ƙarni babu illah kamshi da ko ina keyi, gefe ɗaya kuma Fauziyya ce kwance ana ƙara mata ruwa.
Likitan ce tace "a buɗe jikin Jamila ta gani saboda tasan me zata dauko wanda zatayi amfani dashi wajen yin ɗinkin, koda ta duba sai ta girgiza kai kawai ta fita.

Inna talatu ce ta kalli ummi tace "Rahma ko na kira Khalifa na basu yaron nan suje su birne shi? Kinga har yanzu Abban Nawaz be fito ba kuma ga yamma ta fara yi"

"Ki tambayi umma kiji" abinda ummin Nawaz tace kenan saboda bataso ace ta cika zaƙewa a abun.

Kafin ma Inna talatu ta tambayeta Umma tayi saurin cewa "duk abinda ya dace kuyi, aini babu abinda zance muku domin kun nuna min ku ƴan halal ne, kuma ai Jamila ƴar kuce"

Waya ta ɗaga ta kirashi tare da cewa yazo bakin junction ya sameta.
Ba'a fi minti goma ba ya kira yace ya karaso saboda dama yana kusa da gurin.

Nannaɗe jinjirin tayi cikin fallen zani ta tallabeshi a cikin hijab dinta ta fita, a tsaye ta sameshi bakin wata kwata, "yauwa Khalifa don Allah so nake ka samu abokan ka ku ɗan binne Yaron nan, wata yarinyar kawata ce tayi ɓari, kuma ba'a nan garin suke ba sunzo ne"

"Haba inna ai babu komai kin wuce nan, amsar shi yayi ya wuce ya tafi tare da ciro wayarshi a cikin aljihu don kiran sauran abokanshi saboda asamu wanda zai siyo likkafani da sauri.

Koda inna ta koma ta tarar likitan ta dawo harta yiwa jamilan allurar kashe zugi data barci, likitar yare ce shiyasa basu damuba domin sunsan maganar bazata fita waje ba tunda ba sanin su tayi ba.
Shiyasa ma sanda inna talatu taje Asibitin don samun likitar da zata biyota gida tace a bata yare, tunda su ba kasafai suka cika magana ba. Kuma basaso su fito da jamila kada asan halin da suke ciki.

A natse take aikinta, tsaff tayi ɗinkin ta gama sannan ta ƙara yi mata wasu allurorin sannan ta rubuta wasu magunguna tace a siyo mata ta shasu na tsawon sati Daya.

Duk wani kudin da ake buƙata ummin Nawaz ce ta biya.

Saida taga komai ya kankama sannan ta tashi ta nufi ɗakin da Abban Nawaz ya shiga domin ayita ta ƙare
Koda ta shiga a kwance ta ganshi yayi nisa cikin tunani, zama tayi gefen shi tare da taɓa shi kaɗan.
Firgigit ya dawo hayyacinsa tare dayi mata murmushi, itama murmushin ta mayar mishi tare da cewa "Akwai abinda kake bukata ne? Inaso zamuyi magana Don Allah"

"Bana buƙatar komai tauraruwata, sai dai ina fatan sun fita sun bar min gidana "

Ƙasa da murya ummin Nawaz tayi tana tausar zuciyarshi akan yayi hakuri don Allah, ita bazata so ace ya rabu da umma ba Saboda tayi mata wani Abu ba, ai ko babu komai itace Uwar gidansa

Hutsancewa Abban Nawaz yayi akan ta rabu dashi, domin shi abinda yayi shine dai dai kuma bazai taba nadamar yin hakan ba.

Saida aka kai ruwa rana tukuna ya Yadda da cewa umma ta zauna tayi idda a cikin gidan,idan ta gama saita tafi.

Ita kuma ummin Nawaz tayi hakan ne saboda ta samu isasshen lokacin da zata kira baffansa ta faɗa mishi Abinda ke faruwa.

*Kamar yadda iska ke kadawa haka lokaci ke gudu yana wucewa dakiƙa bayan dakiƙa, Sa'a bayan Sa'a, kwana bayan kwana, sosai komai ke chanzawa wani ya canza mana da Alkhairi wani akasin haka, wani ya bamu abinda muke so wani ya karbe mana.*

Yau su Mummy ke shirye-shiryen komawa gida domin har anyi Bakwai ɗin matar colonel, kuma duk iya zaman da sukayi Mummy taƙi ba colonel wata dama samm.

Ita kuma Nawaz abu ya isheta domin sam bata komai sai barci, hatta da abinci Aayaan baya bari taci da kanta sai ya bata. Ga mummy da Aunty Aseey a gefe, suma su Naufal da fudail ba'a barsu a baya ba saboda ko fita sukayi sukaga mai kayan marmari sai sun siyo mata.

Ganin fa da gaske tafiya zasuyi yasa colonel ya kira Aayaan gefe "son nidai bazan gajiya ba, don Allah akan dai maganar nan ce da mummyn ku bata so, nayi iya kokarina amma taƙi bani wata dama, Wallahi Ni harna fara karaya domin dama cewa takeyi bazata Aure niba saboda kawarta, to yanzu saboda meye bazata Aure niba? Ko dai nine bata so"

"I'm sorry sir, pls kada kace haka, yanzu Abinda nake tunani guda ɗaya ne kawai, idan mun koma gida zanje na samu baffa (kakan Aayaan, wato baban mahaifinsa) na faɗa mishi Abinda ke faruwa, to nasan hardai naje gurinshi to ka ajiye anyi Auren ka da Mummy an gama in'sha Allah,"

Godiya sosai colonel ya rinƙa yiwa Aayaan Kamar zaiyi kuka, har Saida Aayaan yaji duk kunya ta kamashi me karfi, wato shi yau colonel yakewa godiya kamar zai mishi sujada.

Namfa ake yinta domin Fudail da Naufal kame wa sukayi kan cewa sufa sai dai a tafi dasu, babu musu colonel yace "umma ta gaida Aysha" shima dama nemar hanyar dazaije maidugurin yakeyi da wuri, to kuwa idan su Naufal suna chan Babu maiyi mishi shamaki da zuwa, kenan Abin zai zo mishi a saukake.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Ta ɓangaren ummin Nawaz kuwa ta samu lokaci ta kira baffa inda tayi mishi bayanin Muhammad ya dawo sannan ga abubuwan da suka faru, sosai yaji daɗin dawowar ɗan nasa sannan yayi Allah wadai da halayen Umma, amma ganin yadda ummin Nawaz ta damu akan don Allah ya sa Abban Nawaz ya maida umma sai yaji jikinshi yayi sanyi.
Cewa yayi ta kaiwa Abban Nawaz ɗin wayar, tana zuwa ba tare data faɗa mishi waye ba ta kara mishi wayar a kunne, sallama yayi yana cigaba da sauraro.

"Ina so gobe ku tawo maiduguri kaida duka iyalinka" Abinda yaji Muryar mahaifinsa tace kenan.

Kallon ummin Nawaz kawai yakeyi "wai meyasa a komai saita yi mishi shigar sauri ne?"
Chapter 107 · 0% Book details