Sashe 80
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gashin kanshi me kama dana ƴan India (koda yake ai shima jinin Pakistan ne) ta fara kamawa tana rabashi sala-sala tana dubawa, sosai gashin ya bata sha'awa musamman fatar kasan gashin, wato fatar kanshi, fara ce sol har wani yellow yellow takeyi domin tafi ko ina a jikinshi fari.
Saida tabi duka kan ta duba amma babu abinda ta gani, lura tayi yayi barci sai kawai ta lallaɓa ta sauke kanshi daga cinyarta ta miƙe zuwa bakin dressing mirror, comb ta ɗauka da man gyara gashi sannan ta dawo ta maida kan nashi saman gwuiwarta yanda yake ada.
Kwokwonto takeyi Anya barci yakeyi ko kuma yauma likimo yayi mata? "Yaya! Yaya!! Yaya!!! Sau uku a jere ta kira sunanshi, jin be amsa ba yasa ta kama hannunshi ta ɗaga, yararaf ya faɗi Alamun barcin da yakeyi ma yayi nisa.
Ƙyalƙyalewa tayi da dariya " Hmmm Nidai Ina ganin ta kaina a garin nan, daga zuwanmu amma nayi ciwon kai yafi sau huɗu, dama haka auren yake ayita kalle maka jiki, nifa kawai don inajin tsoronshi ne amma wallahi da bai isaba, hmm gaskiya yaya Aayaann ƙarshe ne sam baya jin kunyata, yanzu don Allah ji yadda ya saki jiki yana barci bayama tsoron naje na gudu, au to idan na gudu ma wa na sani? sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya.
Duk abinda take yi yana jinta, so yake ya ƙarar da yarintarta a yau, maganganun data gama sunso su sashi dariya amma ya kanne da ƙyar.
Man ta dage ta riƙa shafa mishi akan sannan ta ɗauki comb ɗin idan ta taje saita yi style dashi sai kuma ta ɓata ta kuma yin wani style ɗin, daga ƙarshe dai itama taji barci me nauyi ya kamata, saman ƙirjinshi ta faɗa ba don ta shirya Ba itama ta fara barcin.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Tuni hassu an ware an maida jiki sam babu abinda yake damunta yanzu illa ƙosawa da tayi a cire mata zaren ɗinkin, kuma gashi Lokaci beyiba, abinda yasa yayi saurin haɗe wa ma saboda yawan shiga Ruwan dumi da takeyi ne da kuma abinci mekyau da take ci, ga kula ta musamman da Inna zuwairah take bata ..
A jiya da dare ma saida Mummyn Aayaan da Mummyn sarfraz suka saci hanya sukazo suka duba ta, ba ƙaramin daɗi sukajiba ganin yadda ta warware tana sabgoginta.
Allah ya taimakesu har suka koma babu wanda ya lura basanan.
Kowa ya shirya don yau ake saran duka baƙin zasu koma gidagensu, alokacin kuma Ummin Nawaz taji tana son zuwa gidan inna talatu sannan daganan ta ɗan leƙa umma taga wace waina take toyawa, ko babu komai ai Zaria ta zama gari a gareta, kuma Inna talatu mutum ce Sannan tanaso su ƙarasa Maganar Auren Nawaz da suka fara ta waya.
And kuma tasan idan taje gida bazata rasa abinda zata ɗauka ba wanda zaiyi mata amfaniba, tunda dai har zuwa yanzu Abban Nawaz yayi ɓatan dabo, babu shi babu labarin shi.
Ammanta ta roƙa akan cewa ko awa ɗaya aɗan bata taje gidan inna talatu, dama a nata idan har Allah yasa an bata to saisu leƙa gidan umman tare da talatu ɗin.
Da kyar Amma ta yarda, kasancewar su Uku za'a maida a tasu motar, dayake group group aka raba tafiyar Kasancewar kowa da inda ya nufa.
Mummyn Aayaan ce tasa baki akan su ɗaga tasu tafiyar zuwa gobe idan Allah yaso saisu tafi tare da ita, hakan nema yasa Amma ta yarda Ummin Nawaz ɗin ta tafi gidan inna talatu ɗin.
Aikam koda ta isa ba ƙaramin girgiza tayiba jin cewa wai Nawaz ta taɓa gudowa gurinta harta ƙaraci zamanta ta koma amma bata saniba.
Sosai take mamakin ita kuwa inna talatu wace iriyar Aminiyar ƙwarai ce? Ace ki riƙe ƴa har ki gyarata amma babu wanda yaji! Itakam dame zata iya biyan ta ne?" Bayan sundan sha hirar yaushe gamo ne ummin Nawaz ta roƙi Inna talatilun akan ta taimaka ta rakata gidansu, tanaso taje taga ya dakinta yake.
Babu musu inna talatu ta yarda, shiryawa sukayi suka ɗauki hanya......
*ENGLAND..........*
A ƙalla saida suka kwashi lafiyayyun awa uku suna barci, koda suka tashi Alwala sukayi Aayaan ya jasu jam'i, suna zaune babu wanda yake cewa ɗan uwanshi ƙala, illa dai Aayaan yakan kalli Nawaz akai akai yayi mata murmushi.
Knocking ɗin ƙofar ɗakin akayi, Nawaz ta tashi zata buɗe yace ta koma shi zaije.
Babban kwali ya shigo dashi ga uban nauyi, cewa yayi sako ne mummy tace a tawo miki dashi ta jirgin kaya buɗe kiga menene da menene?
Koda suka farke gum ɗin babu abinda Nawaz tagani illah kayan magungunan da suka tawo dasu daga sudan, gefe guda kuma aya ce mai uban yawa, wasu abun ma bata gane musu ba, bayan turaruka da humrar da suka tawo dasu daga Sudan Saida taga wasu sababbin da bata sanma dasu ba, ga uwar gumba nan him da dai sauran su, ɗan yatsina fuska tayi ta maida kwalin ta rufe.
"Malama ya za'a yi kisani a duhu, fisbilillah kin buɗe abu kin duba kumani kinsan ban san meye ba sannan kin maida kin rufe"
"Kayayyaki ne fa kawai"
"Ko menene kawai kiyi min bayanin nima zanga ko zai amfani"
Zaro ido Nawaz tayi tana neman yanda zata kufcewa wannan Abu da Aayaan yake neman tattago mata.
*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*69*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Sosai fa Aayaan ya dage akan shifa saita yi mishi bayani, ita kam Nawaz ko mai zeyi mata bazata iya yi mishi bayanin wannan Abin kunyar ba.
Miƙewa tayi tace "bari naje bathroom na dawo"
"Okay to muje na raka ki"
"No pls kabarshi zani da kaina"
"Okay to kiyi sauri kizo kimin bayanin"
"To" Nawaz tace tare da yin Hanyar bedroom ɗin, tana tafiya shikuma yajanyo kwalin zuwa gabanshi, bubbuɗewa yakeyi yana cirosu yana ajiyewa a gefe, ko wanne ya ciro saiya karanta jikin kwalinashi ko robarshi, yawanci rubutun da Larabci ne sai English, hakan yasa duka ya fihimci magungunan na Meye!
Murmushi yayi yace "WOW WOW WOW! Gaskiya ina ƙaunarki Mummy na, yanzu dama duka wannan Abin duk danni akayi shi, gaskiya dagewa zanyi ta riƙa shansu yadda ya kamata...
Hajiya Nawaz kam tana shiga bedroom ɗin ba bayi ta shigaba don dama babu abinda takeji saman gado ta haye abinta taja duvet ta rufe jikinta, aikam bata ɗauki wani lokaci mai tsawo ba barci yayi gaba da ita.
Shi kuwa goga Aayaan yana nan ya dage sai ciro kayan yakeyi yana daɗa bin kowane label yana dubawa, waɗanda basuda rubutu a jikinsu kuma sai dai ya kalla ya jujjuya ya ajiye.
Saida ya gama fito dasu duka Sannan yaga wata envelope a ƙasan kwalin, aikam beyi wata wata ba ya ɗauketa ya buɗe.
*_Assalamu alaikum_*
_Daugter ina fatan kun sauka lafiya, Allah ya albarkaci zamanku ya dauwamar da farin ciki mai ɗorewa a tsakaninku_
_Inason don Allah Don darajar Annabi daughter kitaimakeni kirika shan magungunan nan domin zasu taimaka miki matuka, and idanma Akwai wani abun daya shige miki duhu pls ki kira Aseey zatayi miki bayani, so nakeyi ki yakice tsoron nan da kika jibgawa zuciyarki_
_And kuma Ni burina duk sanda zaku dawo ya zamana an tawo mana da tsarabar ƴar England ko ɗan England_
Haka dai Aayaan yabi duka rubutun yana karantawa sinka sinka har zuwa inda mummy tace
_A gaida Min da Aayaan ɗin kuma kice nace kullum ya riƙa tunawa da Alƙawarin daya ɗaukar min, na barku Lafiya, Allah ya haɗa kanku_
Murmushi yayi ya maida takardar ya ninke yadda take Sannan ya Maida ta Cikin envelope ɗin ya sakata a cikin kwalin sannan ya Maida kayayyakin ciki.
Ganin shiru Nawaz ɗin bata dawo ba yasa shi miƙewa ya nufi bedroom ɗin, murmushi yayi ganinta tana barci lakadan "hmmm sweet heart manya, Allah dai ya barmu tare"
Cikin bargon shima ya shiga tare da janyota ƙirjinshi yana rungumeta tsam, "ita batada wuyar barci ne? Naga fa bamu daɗe da tashiba amma harta kuma komawa, ko batajin daɗi ne? Jikinta ya taba ko zaiji tracing ɗin zazzaɓi amma bejiba, girgiza kai kawai yayi ya cigaba da kallon fuskarta.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Kasancewar ummin Nawaz nada sanyi da karayar zuciya tana ganin umma ta fashe da kuka, kuka takeyi bilhaƙƙi tana tambayarta meyafaru har ƙafarta tayi haka?
Itama umman kuka ta hau yi tana duba irin zaman cusguna musu data riƙa yi amma ace har yanzu ita bata riƙe ta da wani abu ba, wato har kuka takeyi saboda wani Abu mara kyau ya sameta, nadama da dana sani ne suka ƙara rufeta da tsanar kanta.
Itakam ummin Nawaz cewa tayi bazata koma Maiduguri ba tunda umma batada lafiya, zata zauna ta kula da ita har zuwa sanda Allah zai yanke jinyar ta samu lafiya, idan da rabo ma sai Abban Nawaz ya dawo.
Inna talatu kam wani ƙululun baƙin ciki ne ya cika mata zuciya, "wai yanzu duk cutarwar da umma tayi musu ita da Nawaz tana nufin ta manta kenan? Gaskiya sanyin zuciyar Rahma yayi yawa...., Tana ganin idan itace ma saidai tace Allah ya sauwaƙe ta ɗauki Abinda zata ɗauka tayi gaba, amma babu yadda za'ayi ta zauna jinyar umma.
Kafin wani lokaci ummin Nawaz ta zage ta gyara falourn da umma take zaune, ta fitar da komai tasa omo da hypo da IZAL ta wanke shi tass sannan ta shiga dakinta ta ɗauko katifar Nawaz da zanin gadonta ta sawa umma sannan suka ciccibeta a hankali suka ɗora ta akai, harta poo ɗin da umma take bayan gida a ciki Saida ummin Nawaz tayi mishi wanki na musamman Sannan ta kwashi sauran Kayan data cire a shinfidar umma ta da ta wanke su tass.
Inna talatu ce duk take tayata amma cike da mamakin irin sanyin halinta da rashin riƙon ta.
Ba Ita ta samu ta huta ba sai da yamma tayi liss, wayarta ta ciro ta kira layin Amma take sanar da ita halin data je ta tarar da Umma, itama Amma ɗin bataji daɗi ba, sosai ta nuna alhininta Sannan tayi mata addu'oi da fatan samun lafiya, bata ce dole saita bisu sun koma Maidugurin tare ba saboda ai ciwon abokiyar zamanka kamar naka ne, tunda kaima wata Rana zaka iya yin ciwon kuma itace zata taimaka maka.