← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 112

Sashe 46

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Nawaz tayi kirjinta kuma na bugun tara-tara, hakanan taji Maganar batayi mata ba ga Wani tsoro daya dirar Mata a zuciya lokaci guda ta zaro ido "Aunty Don girman Allah ki sanar dani koma menene"
Murmushi Aseey tayi "ooh! Sisto meye na tada hankalin ki haka? Sekace nace miki gobe zaki mutu! To gaskiya Ni banason wannan tsoron inasone ki zama jaruma.

Nawaz Kamar zata zunduma ihu tace "Aunty ba wannan ba don Allah Ni kiyimin bayani ne yadda zan gane me kike nufi" itakam Aseey abinma dariya ya koma bata domin duk Nawaz ta fita daga hankalinta harda ƴar zufarta...

Murmushi tayi tace "my sister nothing bad, bafa Wani abu bane kawai dai naji kamar Mummyna tana cewa zataje ta roƙi baffa akan a barmata ke kici gaba da zama tare damu, wai tanajin daɗin zama dake....

Saida Nawaz ta sauke Wata sassanyar ajiyar zuciya Sannan tace "indan wannan ne babu Matsala Insha'Allah lokaci zuwa lokaci zan rika zuwa ina yi mata kwana biyu.

Rashin wayon Nawaz Aseey ta gani Saboda Yadda ta yarda da maganar Lokaci guda batare data tuna abinda Aseey ta fara ce mata ba .

Bata fuska Nawaz tayi 😞 a gaskiya banji daɗin Abinda yaya Aayaann yayi mini ba, ace a gaban su Mummy ya fito rungume dani Amma shi ko a jikinshi, kuma hmmm bari Kawai nayi shiru tunda babu wani amfanin faɗa domin aikin gama ya riga da ya gama.

°
Yau kusan kwana huɗu da dawowar Aayaan Amma Nawaz ta kasa samun damar guduwa, saboda duk sanda ta tashi da asbah sai dai taga Aseey zaune, abin har mamaki yake bata saboda da ita take tashinta amma yanzu sai taga ta rigata tashi, har Saida Nawaz ta Fara tantamar anya ko dai Aseey taji sanda tace zata gudu ne!

Ta ɓangaren Aayaann kuma yaune za'a yi passing out a N.M.S barrack ɗin dake sabon Gari a Zaria, inda achan zai haɗu da Mutane kala kala harda waɗan da a ƙalla ya Kai 5years rabon da su haɗu....
Shiryawa yayi sosai a cikin complete New uniform waɗanfa suka bi ingarman jikinshi suka zauna kamar Anan Allah ya halicce su, sosai yayi kyau Sannan ya ɗauko Beret ɗin soldiers ya kafa a kanshi ya ɗan karkata ta gefe abin dai gwanin ban sha'awa sai wanda ya gani...

Bai ɗauki komaiba ba illah side pack wadda ya ɗan Zuba abubuwan da zai iya buƙata Tare Da ƙaramar bindiga koda wani abin zai iya faruwa.

Duk Cikin kwanaki huɗun sam bai kuma ganin Nawaz ba, abin har Saida ya ɗan taɓa shi Amma ya shanye tunda komene ne ma ai shi yaja.

Falour ya fito inda be tarar da kowa ba sai motsi da yaji a kitchen alamun akwai Mutun a ciki..
Kitchen ɗin ya ƙarasa ya leƙa Don ganin ko waye a ciki, ai kuwa Aseey ce ta kuƙe sai yanka cabbage takeyi da carrots.

Murmushi yayi "Aunty sannu da aiki! Murmushi itama tayi "yauwa bro harka shirya?

"Eh sis" Aayaann yace yana rungumeta, sannan ya ƙara cewa "sis kiyi mini addu'a, Sannan inasu Mummy suma inyi musu sallama?

"Suna back yard! Tun ɗazu naga sun fita suda MUHSIEN kasan sai bankwana sukeyi Tunda sukaji cewa gobe zamu koma, Wallahi bakaga ɗazu ba har Saida suka bani tausayi duk sun damu Kamar suyi kuka...

Yar dariya Aayaan yayi "nifa amintar Nan tasu har dariya take bani, Ni nakancema ko soyayyar biyunin Mummy ce ta koma kan ɗaya Mummyn? Ita ma Aseey dariya tayi Sannan tace "kila hakane, and Kafin ka tafi ka shiga kuyi sallama da sweety ɗinka Don Nasan Kayi kewarta da yawa.
"Ooh Aunty kin Zama Yar sa ido 👀 amma zaku haɗu Ni babu ruwana ...

Sakinta yayi yace "to mudai sai Allah ya dawo damu, sannan ya fita daga kitchen ɗin zuwa dakin su Aseey.

Yauma dai a kwance ya tarar da ita tana barcinta hani'an, sanye take da pink ɗin girly sleeping dress 👗 half gown ce wadda ta tsaya mata iya cinya, sai hular kanta Wadda itama Pink ce wadda akayita da net amma ta zame zuwa baya inda ta bayyanar da kyakkyawan baƙin gashinta mai santsi, abin gwanin ban sha'awa..

Murmushi yayi yace "sleeping beauty" sannan ya ciro waya ya dauketa photo, mayar da wayar yayi amma ya kasa fita, yanaso ko yayane yau dai yaji duminta tunda Allah ya haɗa su..

Side pack ɗinshi ya ajiye a gefe sannan ya zauna a saman gadon tare da ɗaukar ta kacokan ya ɗora ta a Saman cinyarshi, Cikin Barci Nawaz taji kamar an dauketa Sannan kuma sai turaren Aayaan da yayi Mata sallama a kwakwalwar ta, a hankali ta fara buɗe ido don ganin gaskene ko mafarki, aikuwa bata kai ga budewaba taji yasa hannu ya matsar mata da gashin daya sauko mata a goshinta.

Aayaan dake kallon fuskarta sai yaga fatar idonta nayin rawa alamun ta tashi daga barcin, murmushi yayi sannan yace "Sweetheart kin tashi?

Saukar muryarshi data jiyone ya ƙara tabbatar mata da cewa lallai ba mafarki takeyiba.
Aikuwa da sauri ta buɗe ido tana kallonshi a razane "wai yayaa Aayaan meyasa bazaka rabu dani bane? Mai yasa kake son taɓa min jikine? Nifa gaskiya na gaji Wallahi....

Duk wannan masifar da takeyi Aayaan beji komai ba illa laɓɓanta daya ƙurawa ido sunaa juyawa kamar da gangan take musu hakan.

Kanta ya kama ya haɗa bakinsu guri ɗaya ya fara sucking ɗin lips ɗinta, aikuwa Nawaz sumane Kawai batayiba, tashin hankali shock da komaima haka suka sauka a cikin kwakwalwar ta a Tare.....

Sosai Aayaann yayi kissing ɗinta Sannan ya saketa yana maida numfashi da sauri da sauri, gaba daya mood ɗinshi ya chanza.
Side pack ɗinshi ya buɗe ya ciro wrappers ɗin yan dubu ɗaya guda biyu ya ajiye mata a Saman cinyarta Sannan cikin kasalantarciyar murya mai kama data Mai jin Barci yace "Ni zan tafi Please kiyi mini addu'a, wancan karan haka na tafi bamuyi Sallama ba wallahi har zazzaɓi Saida nayi, hope zakiyita yimin addu'a, kuma Kinga dana dawo bamu samu isasshen lokaci nayi miki bayanin Abinda ya faru a Abuja ba, Sannan kuma sun baki kyaututtuka da yawa, sai tsarabar ki amma duk suna mota saboda naga gobe zamu tafi gida kuma kayan da yawa shiyasa na barsu acan kawai..

ita dai Nawaz tana zaune Kamar Wadda aka dasa, murmushi yayi sannan ya sunkuceta ya ɗaga ta sama yana juyi da ita, ƙasa yayo da ita Sannan ya saita bakinsu ya Kuma bata Wani passionate kiss ɗin...
Hugging ɗinta yayi sosai Kamar zai maida Ita Cikin jikinshi Sannan ya ɗora kanshi a Saman kafaɗarta.. Magana Ya fara "i really love you Nawaz, with All my heart, I want to have u as a sister, daughter, mother, Best friend and wife...
Don Allah ki soni kema 😭 Wallahi a yanda nakeji sonki Zai iya haukatar dani.....

Aseey ce ta buɗe ƙofar tare da cewa "Aayaan Daga cewa zakuyi Sallama shine ka kwashi Tsawon awa ɗaya baka fit........ Maganar ce ta tsaya mata a wuya Ganin Irin rungumar daya yiwa Nawaz.

Aayaann ka saketa mana! Kada fa ka ballata, ajiyar zuciya ya sauke Sannan ya saketa tare da ɗaukar side pack ɗinshi Yana fita daga Dakin...

Nawaz dai ko motsi ta kasa, haka zalika kwakwalwarta ta Dena aiki har saida taji fitar motar su sannan wata wawiyar ajiyar zuciya ta kufce mata....

Aseey kuwa dama tuni tabi bayan shi ta rakashi gurinsu mummy sukayi Sallama Kafin ya shiga Mota sannan suka tafi.

Nawaz dai jikinta take kallo da yololuwar rigar jikinta, Lallai Aayaan ya gama da ita, yanzu haka ya gama ƙare Mata kallo? Sannan be barta Anan ba ya kuma yin kissing ɗinta...

Aiko SARFRAZ da yake muna Mata tsaurin ido idan zaiyi mata Abu a ɗari ɗari yakeyi, kuma baya wuce gona da iri, amma ta lura Aayaan hankalinshi kwance yakeyin komai kuma Sam babu ko ƴar kunya...

Tana zaune Aseey ta shigo "sis kina zaune har Yanzu, bari na shiga bayi na watsa ruwa sai in fito in kira su mum a garden sai muci abinci.
Ci kanki" Nawaz batace ba, ko kallonta ma bata yiba.

Aseey na shiga bayi Nawaz ta miƙe ta cire rigar jikinta tasa doguwar riga Sannan ta ɗora hijabi, wayarta ta ɗauka sai dubu biyu data Zara a Cikin kuɗin da Aayaan ya bata tayi hanyar waje cikin sauri.
Cikin iKon Allah har ta fita Daga gidan Babu wanda ya ganta, mai keke napep ne yazo wucewa ai kuwa ta tsayar dashi jikinta na rawa ta shiga tare da cewa "malam kaini dogarawa.

Har saida taga sun fita daga layin tukuna ta sauke ajiyar zuciya tana lulawa duniyar tunani "naga Idan na zauna mutumin Nan zai iya hakemin inyaso daga baya sai yace ruɗin shedan ne, nikuwa dana zauna wani ya keta Min haddi Gara na gudu wallhi koma menene ya faru na yarda.

Sosai ta faɗa Duniyar tunani, tana tunanin taya zata koma gida? Gashi Babu Wani kuɗi a hannunta illa dubi biyun data ɗibo,

Tunani ta fara yi akan ina zata inda zaifi safe Yadda ko umminta Kada a faɗa wa, Domin tasan Idan ummi taji to baffa yaji, kuma kenan dole ta koma....

Tsaki tayi ganin Kamar fitowar Tata ma ba nasara....

Danguntun murmushi ne ya kwace mata data tuna da Wata aminiyar Mummy wadda take a hayin ojo commercial.

"Driver pls kaini ojo kawai, Abar zancen dogarawar nan,. "to Hajiya" drivern yace tare daci gaba da tukin shi.

°
Aayaann kam yana zaune a Mota amma zuciyar shi tana gurin Nawaz, ya rasa meyasa yake yiwa Nawaz Irin Wannan son, sosai yake sonta, kuma zai iya bada komai saboda ya mallaketa...

Abubuwan da suka faru yake tunawa yana murmushi "to Yanzu idan Nawaz tasan Ni mijinta ne koya za'a yi, hmm Nasan dai dole asha rigima,

Dai dai nan suka isa barrack, koda Aayaan ya fito saiya murtuke fuskarshi Kamar wanda besan ma meye dariyaba, soldiers ne sahu sahu Sai salute sukeyi mishi.

Shi kam yana wani ciccijewa, nace Ooh Aayaan a waje ZAKI a gurin Nawaz kuma jinjiri🤣🤣🤣..
Chapter 46 · 0% Book details