Sashe 60
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi yayi "da naso na Daga miki kafa amma naga Kunyar nan taki zata hanani rawar gaban hantsi Dole nayi saurin kawar da ita. Kila na samu Nima a fara kula dani kamar Yadda ake kula da sauran magidanta.
NAWAZ kam ji tayi kamar ta nutse a gurin tsabar kunya, duk ta daburcewa gaba ɗaya.
"Yanzuma kin kuma yin shirun ne? Shikenan babu komai Kawai yanzu ki shirya wa dawowata Don a randa na dawo zanyi fatali da wannan Kunyar da take wahalar Dani, Kinga kila ma a Samar Wa Mummy jikoki Yan biyu masu kama dake.
Da sauri Nawaz ta yanke wayar tare da dafe ƙirji domin gani takeyi ma kamar yana gabanta...
Shikam Aayaan yana can yana dariya, don dama yana sane yace Bari ya tsokaneta yaga ya zatayi.
Tana wannan halin saiga Aseey ta shigo niƙi niƙi janye da akwati har guda biyu, saida tazo gaban Nawaz ta ajiye su tare da cewa "Ni nama manta sai yanzu na tuna, tun randa Aayaan zai tafi yace na Kawo miki tsarabar ki daki.
Akwatin Farko ta nuna "kinga wannan tsarabar kice tun wadda ya siyo miki sanda yaje Abuja, shikuma wannan dayan akwatin tsarabar da yayi miki sanda zai je ya tawo dake daga Zariya ne..
Kuɗaɗen hannunta ta miƙa Mata, wadannan kuma kudin daya bakine randa kika gudu, su kuma wannan cewa yayi na baki ranar dazai tafi Eritrea manta wa nayi, kiyi hakuri..
Sakin baki Nawaz tayi ta tsaya tana kallonta, duk wannan tulin kayan ne za'a ce nata ne, sannan ga Wasu kudi har wrappers huɗu wai suma nata ne, to ina zata kaisu?..
"Ni gaskiya Aunty Kayan Nan sunyi mini yawa, Bansan ya zanyi dasuba, kuma kuɗin ki kike nabar miki.
Harara Aseey ta zabga Mata. "wato Ni zakiba kyautar kuɗi koh? To sannu da ƙoƙari, ida konasu zakiyi saidai kiyi amma banso.
Tashi tayi ta fice daga ɗakin ba Tare data ko saurari me Nawaz ɗin zata ƙara cewa ba.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Wani ba gani kamar SARFRAZ ya dire ta window, yana dirawa saiga bandi shima ya diro, ikon Allah!🤔 Hassu ce naga itama ta diro, charaf sarfraz ya rike ta saboda kada ta faɗi.
Sif sif suka wuce harabar gidan, mukulli ya ciro daga aljihunshi ya buɗe motar haidar suka shige ciki, ai kuwa ya figeta da gudu suka shiga cikin gari.
"Bandi zaka gane wadannan Yan iskan turawan da sukayi mana dariya ɗazu sanda Yan sandan nan suka kamamu?
"Eh zan iya gane wasu amma ba dukansu ba.. bandi Yace tare dayin murmushi
"Kada ka damu idan muka kama wasu nasan zasu fito da sauran ne..
Sosai ya miƙa titin da gudu, duk wanda ya hango shi sai dai ya kauce da gudu.
Suna Isa anguwar yaja wani wawan burki saida hankalin kowa ya dawo kansu...
Barkanmu da juma'a, yau Babu yawa amin afuwa.
*MATAR RASHEED✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*54*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Parking ɗin motar yayi ya fito waje, suma su hassu da bandi suka fito, itadai Hassu Tunda taji cewa SARFRAZ yazone ya Nemi wata fitinar taji zuciyarta nata bugawa...
Kusa dashi ta matsa Sannan tace "sarfraz don Allah ka rabu dasu, tunda har Allah yasa ba'a rigada an kaimu chaji office dinba ka kyalesu. Kuma ko yanzu da suka ganmu nasan dole suyi mamakin ya akayi aka sakemu.
"Eh wallahi, Nima a nawa Gara ka kyalesu kawai" cewar Bandi yana dafa kafaɗar SARFRAZ.
Shiru SARFRAZ yayi na ƴan daƙiƙu Sannan yace "to Shikenan tunda kunce haka zan rabu dasu, amma wallahi idan wani shashasha ya kuma kallonmu yayi mana dariya wallahi saina fasa mishi hanci.
Cikin motar suka shiga amma bada nufin komawa gidaba sai don su shiga gari su yawata.
Cikin rashin Sa'a sunzo wucewa ta gefen wani Filin kwallo aikuwa aka samu wani yayi dagon shot sai a kan Hassu, ji kake "Tummm" dayake motar irin me budadden saman nance...
Baya hassu tayi kamar wuyanta ya karye tare da sakin wani irin marayan kuka "wayyo yaya bandi wuyana ya karye, zan mutu....
Wani irin wawan burki SARFRAZ ya taka, cikin hanzarin dabesan yanada shiba ya dira daga gidan gaba tare da zuwa gefen inda hassu take yana Cewa ɗaga kanki mugani, ya kan yakeyi Miki? Zaki iya magana?
Ganin Irin hawayen da yake zuba a idon hassu yasa yasan Cewa ba ƙaramar azaba takejiba.
Juyawa yayi ya nufi cikin filin kwallon tare da ƙarewa waɗanda suke dariya kallo, da sauri Bandi yace "SARFRAZ ka shigo kawai mu tafi gida, kada kace zakayi musu wani abu, nasan bada gangan suka buga mataba.
Ko takanshi SARFRAZ bebiba yayi cikinsu da hanzarin shi, yaron farko ya damƙarwa gashi ya fara wujijjigashi iya ƙarfin shi, Sannan ya fara naushinshi a baki da hanci "ance muku ita ɗin banza ce? Ko ance muku ita din batada galihune? Wato so kukeyi ku kasheta ko? Dama ai ɗazu harda Kai akeyimana dariya...
Memakon sauran su kawo mishi agaji sai kowa yayi ta kanshi, cikin ƙanƙanin Lokaci duk suka watse a filin, da sauri bandi ya fita daga motar yaje Yana riƙe SARFRAZ tare da cewa "sarfraz ka sakeshi kada ka kashe shi, bafa a kasar mu muke ba, don Allah ka bari mana!
Da kyar dai bandi ya iya amshe yaron a hannun SARFRAZ, shikuma yaron yanajin SARFRAZ ya sakeshi ya arta a guje, dayake gurin Kamar park yake babu wasu mutane sosai a gurin.....
Haba SARFRAZ! Dama haka kakeda baƙar zuciya, to daka kamashi kana mishi wannan mugun dukan ce maka akayi ta mutu, ko kuma ce maka akayi zata mutu? Ni a ganina da wannan dukan daka tsaya yi gara mu kaita asibiti.
"Lallai bandi to bari kaji, idan kai baka dauketa da muhimmanci ba nina dauketa, kana kallon sanda banida lafiya ita ta zamemin kamar uwa, duk wani shirme da wahala ta ta ɗaukar wa kanta kuma ba tare data San koni waye ba! Don Haka Nima na bata Babban matsayi a zuciya ta Sannan babu yanda za'a yi inga wani yayi mata wani abu inyi shiru in zuba ido" duk wannan sharhin da Sarfraz yakeyi a zafafe yakeyi kamar zai mazge bandin.
Shikam bandi tsaye yayi baki buɗe yana kallon SARFRAZ har ya gama jawabinsa ya wuce shi ya shiga Mota.
"Zakazo mu kaita asibitin ne ko kuwa in tafi?
Gaba ɗaya bandi ya tsorata da sarfraz, hakan yasa bece komai ba kawai ya shiga motar ya zauna...
Itakam hassu sai wash kawai takeyi ga wuyan harya kumbura kuma yayi jaa..
Asibitin su haidar sukaje, inda aka yiwa SARFRAZ aiki, don haka suna zuwa aka ganesu, basu wani sha wahala ba suka samu docton da zai duba Hassu.
Bayan ya gama duk abinda zaiyi ne, yace kwallon ta bigeta sosai ne shiyasa har jini ya mutu a gurin, dayake ya tambaye su Meye musabbabin ciwon.
Magunguna ya rubuta yace suje pharmacy su siya Sannan idan suka tashi gobe basuga improvement ba su dawo.
SARFRAZ sai Wani lailayeta yakeyi, idan akazo step ma ɗaukar ta yakeyi, shikam bandi bawan Allah sai dai ya bisu da ido yana binsu kamar jela.
Nidai matar Rasheed cewa nayi:- *MUJE ZUWA DAI*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Zaune take bayan ta gama duba kayayyakin da Aseey ta kawo mata, mamaki takeyi "waɗannan kayan aiko lefe akayi dasu a wannan ƙarnin sunyi yawa balle ace wai tsaraba... Itafa lamarin Aayaan ya fara bata tsoro..
Ƙarar turo ƙofar da akayi ne yasa Nawaz ta juya da sauri don ganin ko waye ya shigo, Ashley ce tsaye tana ƙarewa ɗakin kallo Tare Da taɓe laɓɓanta Masu kama da ragadada Sannan tace "waike waɗan nan akwatinan danaga ana ta binki dasu wai iya sune lefen naki?
Da Nawaz taso ta shareta amma sai taga abin Kamar ya koma rainin wayau, saboda ya za'a yi ta biyota har inuwarda take tace zata faɗa mata magana! Nawaz tanada hakuri saidai ta tsani cin mutunci a rayuwarta.
Murmushi tayi tace "tsarabar da Captain ya siyo min ne a hanya sanda zamu dawo!
Cikin harzuka Ashley tace "mtsewwwss aikin banza aikin wofi! Wai ke ance miki Bansan asiri kikayiwa Aayaan ba har kika samu yayo ciki dake?
Murmushi Nawaz tayi cikin kwanciyar hankali tace "Allah sarki Ashe malamina yafi naki iya aiki tunda har aikinshi yasa Aayaan ya tsallake ki ya shiga duniya cikin miliyoyi ya laluboni, aiko ya kamata naje na ƙara mishi kudi.
Cikin hargagi Ashley tace "Wallahi! Allah ya fiki kuma in'sha Allah sai asirinki ya tonu Ni dama nasan ba haka kawai Aayaan yake wannan rawar ƙafar akankiba, Aayaan ɗin da ko kallon Mata bayayi ta ina har zai hango ki? Ai dama nasan sai an haɗa da tsubbu..
Gefe Nawaz tayi da kanta Sannan tace "Meye duka na wani tada jijiyoyin wuya? Naga gurin boka naje, to me zai hana kema kije ki gwada taki sa'ar? Kika sanima kila idan kikayi naki tsubbun shi Aayaan din yace be taɓa ganina ba! Ko be taɓa jin irin sunana ba" Duk wannan maganar da Nawaz ta yaɓawa Ashley cikin ruwan sanyi ta faɗa mata babu hargagi balle daga murya.
Itako Ashley tuni ta koma kamar wata zararriya "To wallahi tunda haka kikace to kuwa mu zuba mu gani, za'a ga wanda zaiyi zarrah! Shegiya munafuka.
😊Murmushi Nawaz tayi Sannan tace "to Allah ya bada Sa'a, fatan alkhairi 🙏, kuma shi munafunci nonon uwane nasan kema kinsha, kuma ai dama shege sai shegiya
Fuu Ashley ya buɗe kofa tayi waje tare da bugo kofar da ƙarfi, ji kaje "baammmm"
Ƙwafa Nawaz tayi tace "kajimin aikin banza, Ni zata nunawa cewa ita shashasha ce? Ko ce mata akayi Ni nasan wani Aayann ne?, in banda hauka ma irin Tata auren ma da ake magana akan shi Nima yaushe nasan dashi?
Tsaki tayi ta tashi zuwa bathroom donyin alwala.
*KAI ASEEY SAI DAI A BARKI, WATO KE KOMAI SAI KINJI*
Tun sanda Ashley ta shiga ɗakin Nawaz ashe Aseey na bakin kofa tana kallonta, labewa tayi a jikin kofa donjin me yakaita shiga ɗakin Nawaz, tunda tasan ko magana ma basu taba yiba.
Ile kuwa duk maganganun da sukayi tanaji, daɗi Kamar ya kashe ta jin amsoshin da Nawaz taba Ashley. Ko Banza yanzu tasan ba kowa Nawaz zata bari yaci mata fuska ba.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°