← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 112

Sashe 36

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ledar ya ajiye a gefe yana murmushi, Ni na zama dodo kenan! Harɗe hannu yayi haɗe da fita daga ɗakin yana ganin zallar yarintar Nawaz

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Misalin ƙarfe bakwai da rabi ya safiya SARFRAZ ne zaune ya kasa ya tsare akan wai dole sai hassu tayi mishi wanka, bandi yayi yayi akan ya hakura shi zaiyi mishi amma Sam yace shifa na hassu yakeso tunda itace ƙawarshi, wai yana fushi da bandi saboda jiya yaƙi wanke mishi poo da yayi...

Duk wata dabarar duniya hassu da bandi sunyi amma yaƙi yarda, shifa ala dole sai anyi mishi wanka kuma babu wanda zaiyi mishi face hassu...
Da abin yaci tura sai sarfraz kawai ya fara rusa ihu baji ba gani....

Lallashin duniya amma yaƙi yin shiru, shifa a mishi wanka kawai

Da dai bandi yaga abu yaci tura sai kawai yacewa hassu "tashi kuje bayin kiyi mishi ina zuwa.

Chogewa hassu tayi ta tsaya tana kallonshi, tsawa bandi ya daka mata kin wuce kun tafi ko kuwa? Wato ina wasa dake ko?
Ai duk ke kikace kinason a daukoshi a taimake shi don haka duk abinda ya kwaso kanki zai kare....

*Ina yiwa kowa fatan Alkhairi, kuma ina fatan kowa yana lafiya, kwana biyu kunjini shiru, anyi mana rasuwa ne*

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 37*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

Da sauri hassu tayi hanyar shingen da suke hura wuta, tukunya ta samu ta ɗora ruwan bayan ta hura wutar.
Shi dai sarfraz yana biye da ita duk motsin da tayi.

Shi kuma bandi yana gefe sai dariya yakeyi yanaso yaga yanda abun Zai ƙare, koda ruwan yayi zafi sai ta ɗauki babbar robar da sukeyin wanka da ita ta juya ruwan zafin sannan takai bayi.

Gurin bandi ta ƙarasa ta tsaya ɗan nesa dashi tace "banda na dafa ruwan"
Gumtse dariyar dake bakinshi yayi "to ina ruwana, kije kiyi mata mana! Tunda dama abokinkice

Juyawa tayi batare da tace komai ba, Sabulu da soso ta ɗauka a inda suke ajiye ta kama hannun sarfraz bata kuma ko kallon inda bandi yakeba, har cikin bayin inda suka ajiye dutsen da suke zama ta kai sarfraz tasa ya zauna a dutsen, sannan daga bisani ta cire mishi riga da dogon wandonshi sai tabar gajeren ajikin shi.

Ganin ta nufi bayin batace komaiba yasa bandi miƙewa hade da fargabar Allah yasa ba wankan zatayi mishi ba, cikin sanɗa ya karasa gurin bayin ya leƙa .
Har wata ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske ganin irin dabarar da hassu tayi, shi dama wasa yakeyi mata yasone tayita bashi hakuri shi kuma yayi ta ja mata rai...

Lafiyar Allah aka gama wankan suka koma ɗaki, akwatin ƙarfen da bandi yake zuba kayanshi ta buɗe ta zaɓi me kyau sannan ta bashi tace "zan fita kafin na dawo kicire wannan jikakken wandon kisa waɗan nan kayan.

Waje ta fita ko kallon inda bandi yake batayiba Saboda Abinda yayi mata ya ɓata mata rai, shikuma ta gurin bandi ji yayi wata fargaba ta kamashi saboda fushin hassu baida kyau don sai su wuni su kwana bazata kulashi ba.

A hankali ya karaso kusa da ita "hassu sannu da kokari ashe kinzata da gaske nakeyi? Nifa wasa nake Miki so nake inga yanda zakiyi!

"Ai kaga yadda nayin Koh" haka tace batare data kalli inda yake a tsaye ba, sannan ta daɗa murtuke fuskarta...

Fitowa SARFRAZ yayi jikinshi sanye da kayan bandi, abin gwanin ban dariya saboda Sam basuyi mishi ba duk a ɗingile duba da irin girman jikin SARFRAZ ɗin...

Itama shiryawa tayi ta kama hannun sarfraz din suka nufi gidan Malam, ganin yadda hassu ta ɗauki zafi yasa bandi be kulataba illa shima sai yayi sauri ya shirya sannan yabi bayansu....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Tunda tai sallar asbah bata tashi a saman dadduma ba, azkhar taitayi tare da addu'oi tana fatan Allah ya bayyana sarfraz sannan Allah ya kawo mata hanyar da zata koma gida taci gaba da yin rayuwarta kamar da.

Wata irin ƙullewa cikinta yayi kasancewar yunwar da takeji, gashi jiya da dare babu yanda ba'a yi da itaba akan taci wani abuba amma taki.
Kallon su mummy tayi taga sunata barci itada Aseey dayake muhsien a gurin Aayaan ya kwana.

Ledar da Aayaan ya ajiye mata jiya da dare ta janyo sannan ta buɗe ta a hankali....

Kwalalo ido waje tayi ganin tulin chocolate da ice cream duk sun huce ma sun zama ruwa kasancewar ba'a sasu a fridge ba.

Murmushi ne ya kufce mata batare data shirya zuwanshiba. Robar ice cream ɗaya ta dauka ta kafata a bakinta Saida ta shanye sannan ta cire robar..
Chocolate ɗin ta ɗiba da yawa ta zuba a cikin aljihun rigar ta sannan ta maida ledar ta ajiye....

Miƙewa tayi a hankali kasancewar kafarta Tayi tsami saboda daɗewa da tayi a zaune.
A hankali ta buɗe ƙofar ta fita saboda bataso ta tashesu daga barci, shiru faloun babu kowa hakan yasa taji sha'awar ta fita harabar gidan taɗan miƙe kafarta.

Hanyar garden ta nufa tana tafe a hankali kamar batason zuwa har ta isa dai dai wata bishiyar mango babba, a ƙasanta garden chairs ne jere guda biyar, a saman ɗaya daga cikin su ta zauna tana ɗan waige waige daga nan kuma ta faɗa duniyar tunani

Aayann dake bakin window ɗin ɗakin sarfraz tsaye, yana kallon Nawaz tundaga fitowar ta har shigar ta garden ɗin.
Samun kanshi yayi da son bin bayanta ko don yaga kyakkyawar fuskar ta da takeson hanashi saƙat.
Be jira komaiba kawai ya fita daga ɗakin ya nufi garden ɗin, Nawaz dake zaune zuciyarta ta lula can cikin duniyar tunani sam tama manta a inda take sai jin Muryar Aayaan tayi yana cewa "Barka da safiya sister hope dai Lafiya kika fito nan da safen nan"

Bayan kirjinta daya buga Saida jikinta ya dauki rawa kamar mazari, da kyar ta saita kanta sannan ta iya cewa "babu Komai! Ina kwana"

A Kujerar dake gefenta ya zauna sannan yace "lafiya lau ya kika tashi?

A hankali tace "lafiya lau" haɗe da mikewa tsaye

Wai Nawaz meyasa sam bakyaso na raɓe ki? Kuma bakyaso mu zauna a inuwa ɗaya?

Ganin shima ya miƙe yasa kawai Nawaz ta ruga da gudu zuwa cikin faloun.

Dariya Aayaan ya ƙyalƙyale da ita "oh my God wai meke damun Nawaz ne haka? Jiyama daga shiga dakin ta shige bayi.

Shafa fuskarshi yayi yana jinshi cike da nishaɗi sannan shima ya nufi hanyar komawa ɗakin...

Koda Nawaz ta koma faloun bata tsaya ako inaba sai a kitchen...
Tsayawa tayi tai shiru don jin motsin ko Aayaan ya biyota....

Takai minti biyar bata ji motsin kowa ba sai kawai tace bari ta koma daki, har ta kusa fita daga kitchen ɗin sai taga ai Gara da sama musu break fast tunda babu wanda ya tashi a gidan.

Babban freezer ɗin dake cikin kitchen ɗin ta buɗe, tsayawa tayi ta zubawa cikin fridge ɗin ido tana nazarin abubuwan dake ciki.

Kayan dazata buƙata ta ɗiba ta rufe fridge ɗin sannan ta shiga store ta kwaso sauran kayan da zata haɗa, ta yanke shawarar zatayi yam wages da potatoes omelet... Sai kunun gyada.

Hankalinta yayi nisa sosai a aikinta don har tayi fin rabi sai kuma jin Muryar Aayaan tayi Yana cewa "sannu da aiki sister, duk kin cika gidan da kamshi me dadi.
Murmushi tayi amma taɗan daburce, sai dai tayi ƙoƙarin ɓoye hakan.

Kusa da ita ya matsa sosai "yauwa a faɗa min amsar tambayata ta rannan!

Baya tayi ya kuma Binta, haka ta riƙa yin baya har Saida ta haɗu da drawer tukuna ta hakura shima rumfa yayi mata yana cewa "yanzu wa na kama? Ai duk taketaken ki ina sane dake!
Ki faɗa min amsar rannan sannan kuma ki faɗa min meyasa kike min kallon dodo? Har gudu kikeyi idan kika ganni.

Duk ta hargitse ga wani mugun tsoro dayake neman ya buga mata zuciya, har sautin bugun zuciyarta tana jiyowa kamar zata fasa kirjinta ta fito....

"Oh gosh!! Wai duka wannan tsoron na menene? Na taba yi Miki wani abune da Bakya so?

"A'a" Nawaz tace tana goge zufar data tsatstsafo mata a gaban goshi
Haɗa hannunshi yayi guri ɗaya 🙏 pls and please Nawaz kidena jin tsorona, idan muka cigaba a haka za'a fara zargina pls

Gaba daya ya ƙureta domin harta da numfashinsu ya gauraye guri ɗaya, burinta be wuce ya matsa ta wuce ba...

"To zan Dena Amma ka matsa in wuce"

Ɗan matsawa yayi ɗin ta wuce sai kawai yaga ta kwasa a guje da nufin tayi falour, kasancewar shi soja kuma gwanin gudu hakan yasa taku biyu yayi ya chafketa, ai kuwa take ta faɗo saman kirjinshi.

Mutsu mutsu ta fara tana cewa "ni dai ka sakeni Allah idan baka Dena kulaniba Zaku nemeni ku rasa, wallahi zan gudu,

Shi kuma matseta yayi dakyau yana cewa "Ni kuma sai kin faɗi Dalilin da yasa kika maidani dodo!

Ƙara yaji alamun za'a buɗe kofa, ai cikin hanzari yayi sama da ita kamar ya daga jinjiri ya koma kitchen ɗin cikin azama.
Suna shiga ya sauketa amma be saki hannunta ba "nifa gaskiya ka dena yimin irin wannan, fisbilillah ka maida mutum kamar wata yar tsana, binibini ka daukeni!
Gaskiya ka bari banaso, kuma wallhi idan ka matsamin ko Abujan bazaniba!

Daya hannunta ya kamo ya riƙe ya haɗa duka biyun cikin nashi "pls and pls kada kice haka nidai sam banason tsorona da kikejine nafison ki saki jikinki Dani domin Ni yayankine.
"Naji sakin mini hannu to" Nawaz tace tana murguɗa baki
"Ni kike murguɗa wa baki? Idan kika kuma saina cinye bakin!
"Nidai ka sakeni pls" Sakinta yayi yana murmushi don yasan daƙyar idan zata tsaya, ai kuwa da gudu ta ruga shima ya bita yana take mata baya...
Dai dai zata buɗe kofa Aseey ta buɗe ai cikin rawar jiki ta faɗa jikin Aseey tana sauke ajiyar zuciya

"Lafiya kuwa Nawaz? Meya sameki? Menene? Duka Aseey ta jera mata tambayoyin
"Yaya Aayaann ne! Nawaz tace hawaye yana zubowa a idonta, "meya Miki?

"Be min komaiba, ni kawai tsoronshi nakeji banaso yana zuwa gurina amma shi sai yayita zuwa.

Aayann dake tsaye a bayanta yace "kuma bazan denaba har sai randa kika faɗa min meyasa kikejin tsoron nawa ba.
Chapter 36 · 0% Book details