← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 112

Sashe 6

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana fita umma tadauki waya "hello Eh ina Tasiu,? To Kai mishi wayar Kace mishi maman su Fa'iziyya ce tanaso zasuyi magana ne.....
Wata muryace irin da ƴan sigari tace "hello hajiya "
" Tasiu yagida?

Lapia lau hajiya, ya aiki?

Lapia lau Tasiu, wani aiki nakeso kayimin Dan Allah ...
to hajiya inaji

Ina nawaz yarinyar kishiyata?
Eh hajiya Na ganeta, meya faru?
ba kwanaki kacemin kana sontaba...
Eh hajiya anyi haka.

to dama ce ta samu, kaga idan baka auretaba saika cire kishirwa ko kuwa?

"Hajiya banganeba?

"Ehm Ina nufin mamantace tayi tafiya yau, shine nace kozakazo da dare zan barmaka kofa a bude kaga saika shiga ɗakin kayi Sha'anin ka, kuma kaga ita kadaice babu mai taimakonta......

hahahahahahahahaha hajia kenan gaskiya nagode da wannan damar da kika bani zan kuwa Kore ƙishi sosai, faɗa mishi yanda za'a yi tayi sannan sukayi Sallama ta yanke wayar (Ya Allah kasa mu dace ace wai ƴar mijinka zakasa ayiwa fyade saboda baƙin kishi)

NAWAZ....

Koda taje makaranta haka take sukuku , ko Daliban ta saida suka lura tana cikin damuwa,,
Sarfraz ne yace "malama don Allah meke damunki, dukda bama ganin fuskarki Amman yanayin move ɗinki ya nuna kina cikin damuwa...

cewa tayi "safraz babu komai mamanace tayi tafiya shine nakejin kewarta ..

Kowa addu'a Yayi mata cewa Allah takaita ya kuma dawo da ita Lapia, nan danan nawaz ta saki suka cigaba da karatu cikin raha....

zainab tace " malama Dan Allah yaushe zaki nuna mana fuskarki?
dariya tayi tace gobe (tace hakanne Don abar maganar)
nan duka y'an Ajin suka dau kuwwa Kowa yana murna zaiga fuskar malama nawaz...
cewa tayi ya Isa ya Isa yanzu mucigaba da karatu.....
yauma Kamar jiya koda aka tashi sarfraz ne biye da nawaz yana rokonta akan ya kaita gida, ƴan aji Kowa mamakin chanzawar sarfraz suke domin ya dena yi mata rashin kunya kuma yaƙi basu dama su tambayeshi dalili saboda da antashi shima zai tafi gida ba kamar da dayake tsayawa yi musu lecture ba.

still har gida ya bita, saida ta shiga gida shima ya tafi...
Bayan tashiga gida tayi sallah tayi karatu sannan tayi sallar isha taci gaba da Duba littattafan ta.

wurin Karfe goma taji cikinta ya murɗa...
cewa tayi A'a niko me naci cikina zai lalace da tsakar Daren nan, gashi banason fita wallahi....

hakanan ta bude Kopa ta fita, tanashiga bayi su Tasiu suka shigo gidan.
Bayan Kamar minti biyar ta fito, ajiye butar tayi a bakin fampoo sannan ta shiga d'aki tana d'aga labule Ta hango mutum da torch 🔦 Yana haska dakunan faloun..

cewa tayi waye?
nufota yayi gadan gadan, baya ta farayi Yana dad'a biyota.
wani ta gani shima ya fito daga dakinta cewa yayi "shegiya itace riƙeta...

da gudu tayi Waje, suma suka rufa mata baya, tsakiyar titi tabi da gudu iya karfinta tana mamakin me waɗannan yan daban zasu yi mata a tsakar daren nan.

SAFRAZ.....

AROUND 10:00PM
bude dakinshi Yayi ya fito falour, kitchen ya shiga ya bud'e freezer, murfin freezer ya buga "damn it yanzu ace duka gidannan babu lamun tsami ko guda daya?

mtsews yanzu yazanyi?
Falour yaje ya zauna yayi shiru ya hada Kai da kafa...
mum ce ta fito daga d'akin daddy rike da mug da alamu coffee zata had'a mishi ..

sarfraz ta gani zaune Saman couch yayi uban Tagumi....

sweetheart meya faru naganka zaune anan bakayi barciba?

"mumy wallahi kitchen naje kuma babu apple 🍎 babu pear 🍐 babu berries babu wani abu dazan iya ci, kuma na kasa barci....

sweetheart matsalata dakai kenan, Haka kake Kamar mai ciki idan Kace kanason abu to baka ta'ba samun kwanciyar hankali saika samu abin..
yanzu yakakeso ayi?

mum kawai kibari inje fresh vitamins nasan zan samu yanzu tunda kinga su Sai twelve suke tashi...

kanka d'aya sweet heart?

yaza ayi inbarka kafita yanzu Bayan goma ta wuce?
"mum yanzufa zanje na dawo wallahi idan banci apple dinnan ba bazan iya barciba, please mum ki tausayamin....
okay naji amma dai gaskiya kayi sauri kuma kada ka bari daddy yasani saboda zaiyi fad'a....
Dasauri ya mike Yana murmushi "thank you so very much my dear, I love u

fita yayi zuwa parking lot Yana hamdala da Allah yasa mummy ta barshi domin yasan idan bai samu lemun tsamin yasha ba babu shi babu barci ayanda yake jin feelings na tasomai, yadai cewa mummy apple ne saboda yanajin kunya.

Tada motar yayi sannan ya fita ya dauki hanya,
yazo shan corner ya hango Kamar mutane sun wuce da gudu,,
mamakine ya Kamashi "su waye Ke gudu da wannan tsohon Daren.....
ya juya zai cigaba da tuki yaji muryar Mace tana ihu "wayyo Allah na Mena muku, Dan Allah ku kyaleni.....

juya motar yayi yabi Bayan su, Maza biyu yagani sun rike wata yarinya, ɗaya ya rike hannun ta na hadu, ɗaya kuma ya bankare hannun dama .....

parking yayi nesa dasu, sannan ya fito Yana tunanin mezai dauka Wanda zai taimakamai wajen kwace yarinyar...

Hammer 🔨 ya hango a cikin mota, da sauri ya dauka yabi bayansu, kafin ya karasa yarinyar ta kwace kanta ta ruga da gudu....
yanayin firgicin datake ciki yasa bata lura da poll wire d'in dake gaban taba..

jikake kummm taci Karo da ita, aikuwa take ta zube kasa a sume kasancewar poll wire ta karfe ce....

dariya suka kyalkyale da ita "duk gudunki gashi Mun kamaki a sadaka....
kinga azaba ta farfad'o dake koh????

dai dai nan safraz ya karasa kusa dashi, d'aga kasan hammer din Yayi daidai handle ya zabga mishi a tsakiyar kai...

faduwa Yayi yana shure shure kasan cewar Wata sabuwar azaba dayaji Ta ziyarci kwakwalwarshi....
Dasauri Dayan ya ciro wuka a kugunshi ya nufi safraz da ita....
d'aga hammer ɗin safraz ya kuma yi ya buga mishi a hannu take Wukar ta fad'i, shi kuma ya dafe hannun yana ihu, dad'a buga mishi yayi a gwuiwa
shima ya fad'i.
Daidai nan na farkon ya mike ya ruga da gudu, ganin idan ya bishi dayanma na iya guduwa yasa ya tsaya..
kafarshi ya d'ora mishi a kirji ya taka da karfi, ku wasu irin Marasa imanine, ace Mace kukebi zaku ciwa mutunci, irin Kune Marasa kishin Addini ko...

a wuyanshi ya d'ora kafar "me yarinyarnan tamuku kuke binta haka?

kakari ya Fara 'Aa a a a zan fa...d... 'aaa,
d'aga mishi wuyan yayi yace faɗa inajinka,
kishiyar maman Yarinyarce ta Kira ogana tace muzo muyi mata fyaɗe....
shine
mukaje gidan tagudo Waje mu kuma muka biyota...
"Hmmm Allah ya shirya ku". Kyaleshi Yayi ya karasa kusada yarinyar..
Kallonta yayi helplessly dakyar take iya numfashi...
amma gata very beautiful and charming, tashi ɗaya yaji ta burgeshi....
da sauri ya suƙa ya dauketa yasata a mota ya koma gida bemabi takan siyo lemun tsamin ba....

Sai Bayan ya shiga gida yafara tsoron taya zai tinkari mummy dazancennan..
brinta yayi a mota ya shiga falour a zaune ya samu mummy tana jiranshI, Dasauri ta Mike yauwa kasamo kuwa?
A'a
mum ya tashi da wuri yau, cewa tayi Ayyah kasha wahala sweet heart pls kayi hakuri zan Duba maka d'akin dadunka, jeka kwanta..

Ɗaki Ya shiga ya tsaya a bakin Kopa, saida ya tabbatar mum ta shiga ɗaki sannan ya fita ya ɗaukota yakaita dakinshi,

kayanta yagani duk sun baci da kwata kuma duk sun yage....

shiru yayi Yana kallon innocent face dinta, "yanzu ace wannan akebi za'ayiwa fyad'e mtsews God forbid da mugun halin wasu....

rigar ya zare kadan Dayake doguwace, kirjinta yaga ya bayyana, da sauri yace auzubillah,
towel ya dauko ya ɗora a saman kirjinta sannan ya zare rigar ta kasa...
santala santalan kafafuwanta ne suka bayyana, harya tsaya Yana kallo ya kuma cewa A'uzubillah sannan ya kauda kanshi daga kallonta bathroom ya shiga..
kaya ya cire ya sakinwa kansa showa Yana tunanin rashin imanin wasu...

mum ce ta turo kofar, rike da pear guda daya, sarfraz ansamu ɗaya ko manage kayi kafin safiya ko...
gani tayi Kamar bashibane kwance...
Karasawa tayi, ga mamakinta saitaga Mace ce, ɗaga towel ɗin tayi ganin kyakkyawar budurwa tayi kwance daga ita Sai bra da pant 👙, towel d'in ta gyara ta fita a hankali,
koda ta koma ɗaki kasa rintsawa tayi, maiyasa sarfraz zaiyi mana Haka? duk gatan da muka nunamishi ya rasa da abinda zai saka mana saida zina, kuma a cikin gida ma, har yanamin kariyar zaije siyo fruit ashe ita zaije daukowa?....

haka tayita wasiwasi, duk yanda barci ya kware wajen iya sata amma hakanan ya hakura ya kyale idon mummy...

koda sarfraz ya fito daga wanka doguwan rigarshi ya dauko a closet ya rufe idonshi ya sa mata, sannan ya Kalli Gefen inda ta bugu da poll wire, be kumburaba Amman Yayi ja sosai kuma kanta yayi zafi.....

yanda mummy batayi barciba Haka safraz shima

sarfraz kwana yayi gadin yarinyar gashi ko ƙwaƙwaran motsi batayi..

saida asuba ya fita sallah afalour ya hadu da mum yaga idonta Kamar a kumbure " kusa da ita ya karasa mum meya sameki a ido?

be wani samu good response daga garetaba hakanan ya kyaleta ya fita zuwa masallaci Bayan Yayi sallar ya koma ɗaki,
bathroom ya shiga ya dibo ruwan zafi a basin yasa karamin towel yana danna mata goshinta inda ta bugu a hankali..

numfashinta yaji ya fara fita da sauri da sauri...
yana
zaune har gurin takwas ya zuba mata ido....

tari yaji tayi tana motsi, da gudu Yayi hanyar falour Don kawo mata ruwa, Karo sukayi da mummy zata shiga d'akin, cewa Yayi mum dama............

bata bari ya gama faɗan abinda zai faɗa ba ta zabga mishi Mari, yana mamaki takuma zabga mishi wani "Hawayene suka zubo daga idonta "safraz duk gatan da muka yimaka Amma ka rasa abinda zaka dawoka saka mana dashi Sai zina, kuma zinar ma a cikin gidan mahaifinka?

tunda mukaji matsalar ka mukace zamu yi maka aure amma kakyi yarda..

shine yanzu zaka koma biyebiyen mata.

idon safraz yayi ja Yana Kallonta Amma yakasa yin magana jin zargin da mummyn shi keyi mishi

Masu karatu kunji abinda ya faru da sarfraz... Shin mummy zata fahimci abinda ya faru kuwa

_*MATAR RASHEED*_✍️🎀🎀 SAFRAZ🎀🎀

Episode 7

Written by oum aeyman 💝

Supreme writers association....
We write with the ink of era......
Chapter 6 · 0% Book details