← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 112

Sashe 103

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fita yayi daga ɗakin ya dudduba waje ko zai ganta a wani guri, duk inda ya duba be ganta ba sai kawai ya koma ɗaki domin yasan bazata wuce ɗakin su Mummy ba.

Ita kuwa Hajiya Nawaz tana chan bayan gida inda aka hura wuta jiya, wuta ta hura Sannan ta ɗora babbar tukunya inda ta ɗauki bokiti ta riƙa debo ruwa a fampo tana zubawa har saida ta kintaci dai dai wanda tasan zai isa dama kunun Sannan ta barshi haka, murfi tasa ta rufe tukunyar, inda taga mummy ta debo waken da akayi kosai jiya ta shiga ta auno tiya Uku, a hankali a hankali ta riƙa zubawa a turmin tana surfawa har saida ta gama Sannan ta kaishi bakin fampo ta ajiye, cikin store ɗin ta koma ta buɗe babban bawon da gasara ke ciki ta kwashe ruwan saman sannan ta ɗibi bokiti ɗaya da rabi ta rabashi gida Uku ta ajiyesu a bakin tukunyar inda Ruwan keta tafasa, cikin store ɗin ta koma ta dauko wani madaidaicin bokiti wanda zata rika dibar Ruwan zafin tana zubawa a cikin gasarar.

Cikin mintunan da basufi Goma ba ta gama dama kunun tsaff, murfi tasa ta rufe bokitan Sannan ta kuma ɗebo ruwa ta zuba rabin tukunyar ta rufe.
Bakin fampo ta koma domin ta wanke wake, a daidai nan mummy ta fito domin ta hura wuta ganin garin ya fara haske.

Mamaki ne ya kamata ganin manyan bokitai har uku cike da kunu, ga kuma wani ruwan a cikin tukunya shima yana shirin tafasa.

Ƙarar Ruwan dataji a lungun da fampo yake yasa ta ƙarasa da sauri, Nawaz ta gani a duƙe tana wanke atarugu da tattasai tana zubawa a cikin waken data gama wankewa...

"Lahaula wala quwwata illah billah! fisbilillah daughter dama kece kiketa faman wannan aikin? Kin manta kedin ba wata cikakkiyar lafiya ce dake ba! Maza bar aikin nan ki koma ɗaki ki kwanta ki huta Nagode sosai sosai, Allah ya saka da Alkhairi kinyi kokari sosai.."

"Allah mummy naji sauƙi, kuma Ni kwanciyar ce bana so, don Allah ki barni saiki cigaba Ni kuma ina tayaki "

Bayanda mummy ta iya ganin Nawaz ɗin ta nace saitayi, sai kawai ta kyaleta bata kuma yunkurin hana taba "daughter bari to naje na kira su Fudail suzo sukai nikan waken"

"To mummy saikin dawo" cewar Nawaz tana ɗaukar bawo a bakin fampo tare da yin haryar store, shinkafa ta auno tiya biyar ta wanke ta zuba kafin Mummy ta dawo.

Koda Mummy ta dawo faɗa tahauta dashi, "haba daughter! Yaza'ayi ki riƙa daukar abuu mai nauyi haka bayan kinsan cikin condition ɗin da kike!"
Riri rimi Nawaz tayi da ido tare da cewa "Mummy shinkafar kawai fa zan dafa ke kuma sai kiyi miyar"

Jinjina kai kawai mummy tayi tana mamakin ƙarfin halin Nawaz.

Cikin awa daya har tayi perboil ɗin shinkafar ta maida ita ta tirara, lokacin ma har Nawaz tayi nisa da suyar kosai da tayi kane kane ta hana mummy yi, ganin haka sai Mummyn ta hura mata wata wutar saboda idan akace sai an jira shinkafar ta dahu kafin a fara suyar to za'a bata lokaci sosai gashi gari ya fara wayewa.
Itama mummy gasara tasawa kunun Sannan ta zuba sugar yadda kowa sai dai kawai ya dibi yadda zai mai, itama Nawaz a cikin warmer take zuba kosan data soya.

Duk mutane sun fara cika gurin saboda sai fitowa suke suna diba domin su karya,
Itama Nawaz ta gama soya kaskon ƙarshe tana tunanin yadda zata sauke man da tayi suyar dash Naufal ya fito yana dariya "Aunty yau ashe better kikace muci! Wannan irin Natural delicacies haka" hakanan Allah ya ɗora musu son Nawaz da ganin girmanta tun lokacin da sukaje Zaria.

Murmushi mai kamar dariya Nawaz tayi tare da cewa "Nidai bar wannan tsokanar taka ka taimaka ka daukemin man nan ka kaishi store ka adana Saboda da zafi Sosai kada wani ya ƙone"

Sara mata yayi Irin na wasa Tare Da cewa "an gama ranki ya dade matar Captain"

Girgiza kai kawai tayi tana mamakin yadda suke mu'amulantar ta kamar dama sun santa tun tuni..

Towel yasa ya ɗauke kaskon a saman wutar yayi hanyar store ɗin tare da cewa mutane "a kauce mai ne me zafi"

Ƙoƙarin tashi Nawaz tayi saboda tanaso ta samu ta watsa ruwa saita ɗan kwanta kafin akira Sallar azahar, mikewarta keda wuya wani irin jiri ya rufe ta cikin ƴan dakiƙu duhu ya baibaye idonta baya tayi zata faɗi Allah ya taimaka daidai lokacin Naufal ya dawo daga kai man, shi yayi sauri ya tareta cikin hanzari.

Cikin sauri da karsashin da mummy batasan tana dashi ba ta karaso gurin cikin tashin hankali "Naufal meya sameta?"

"Mummy wallahi nima kawai gani nayi zata faɗi shine na rike ta" cewar Naufal Muryar shi na nuna alhini akan abinda ya faru, kuma still dai yana rungume da Nawaz a jikinshi..

Kafin wani lokaci Mutane duk sun iso gurin suna ta yi mata Allah ya kyauta da sannu, amsarta mummy tayi ta jinginata da jikinta sannan ta nufi ɗaki da ita donta samu ta kwanta, tasan aikin data cikawa kanta ne yasa hakan ya faru.
Mamakin Son barci da son jiki irin na Aseey Mummy take tafe tana yi "wato har Yanzu barci takeyi shiyasa bata fito ba kenan, ita dai Aseey sai kace bata girma ba, fisbilillah Nawaz kwara nawa take da har tasan ta tashi ta ɗora Abinda mutane zasu karya dashi?"

A cikin corridor Mummy tayi kaciɓis da Aayaan, tsaye yayi yana karewa Nawaz ɗin kallo tare da mamakin
Me ya faru mummy ke rungume da ita sannan daga bisani, yace "mummy me ya faru naga dear wani iri?"

"Mikewa tayi bayan ta gama soya kosai kawai sai gani mukayi tayi baya zata faɗi, to Allah ya taimaka Naufal na kusa ya rike ta"

Tsoro ne ƙarara ya bayyana a fuskar Aayann "Mummy faduwa fa! Innalillahi wa'inna alaihi raji'un, yanzu meyasa hakan ta faru?"

"Wallahi nima dai ban sani ba, amma dai ya kamata kuje asibiti a duba ta.

"To mummy In'sha Allah"
Ɗakin Aayaan mummy ta kaita saboda zatafi sakewa tunda babu kowa a cikin ɗakin balle a dameta da hayaniya.

Mummy na fita Aayaan ya ƙarasa ya dago Nawaz ɗin zuwa jikinshi "dear idan nace ki bar Abu please ki taimakeni ki riƙa bari, yanzu da wani Abu ya sameki fa? Kuma kinsan ba cikakkiyar lafiya ce dake ba"

Ciki murya dishi dishi Nawaz tace "I'm sorry sweetheart, wallahi bawai banajin Maganar ka bane, kawai dai banaso Mummy ta wahala ne saboda idan banyi ba Nasan dole ita ce zatayi."

"Hmmm shikenan!! Thanks for the love and care... Amma dai ya kamata ki dena pls"

Bata kuma cewa komai ba har zuwa sanda ga sunkuceta yayi bayi da ita don yayi mata wanka.

Cikin ƙasa da mintuna Talatin ya shirya su, ɗaukar Nawaz ɗin yayi ya ratso ta tsakar gidan be damu da Yadda mutane ke Binshi da ido ba, shi yanzu ta lafiyar matarshi yakeyi bata Kowa ba.

Bayan sun yi sallama da Mummy ne ya buɗe ɗaya daga cikin motocin dake Parke a parking space ya saka Nawaz a seat ɗin me zaman banza Bayan ya ɗan kwantar mata da seat ɗin, shiga driver side yayi ya figi motar zuwa wani babban private hospital wanda yake mallakin abokinshi ne wanda sukayi karatu tare.

Yan mintoci ne ya ƙarasa dasu dayake babu nisa daga gidan colonel ɗin.
Direct office ɗin Dr Uthman ya karasa, bayan ƴan gaishe gaishe da ya Bayan rabuwa Aayaan ke sanar da shi Abinda Ya samu Nawaz, sannan ya ƙara da cewa "friend mata nakeso su duba ta ba maza ba, "bakada matsala abokina" cewar doctor uthman yana ɗaukar wayarshi dake ajiye a saman desk
Nurses biyu Dr uthman ya kira suka tafi da Nawaz bayan ya faɗa musu Abinda zasuyi haɗe da basu wata takarda da ya danyi rubuce rubuce a jiki.

Aayaan na zaune a office ɗin Dr uthman ne amma zuciyarshi is out there, damuwa da fargaba ne ke Nuƙurƙusar shi, tsoro yakeyi kada ace wani abu gagarumi ne ke damun Nawaz.
Duk hirar da uthman keyi mishi babu Abinda yake ganewa aciki, illah dai yasan bakinshi na bada amsa.

Saida ya sauke wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya sanda yaji sallamar daya daga cikin nurses ɗin da suka fita da Nawaz, ɗan rusinawa tayi bayan ta shigo sannan tace "sir Doctor dejert ce tace nazo na faɗa maka wai tanaga sai anyi mata ultra sound"

"No problem! Ayi duk Abinda Ya dace, nidai burina a gane meke damunta" Aayaan yaba nurse ɗin amsa Kafin Dr uthman ya bata.

Murmushi Dr Uthman yayi sannan yace "kinji Abinda mijinta yace, so ya gama magana, U can go."

Bayan kamar minti 35 Nawaz ta shigo office ɗin tare da taimakon wata nurse guda ɗaya, da sauri Aayaan ya mike yana gyara kujerar da Nawaz zata zauna akai.

Murmushi nurse ɗin tayi tare da risina tana mikawa Dr Uthman wata takarda sannan ta juya ta fita.

Bayan ya gama karantawa ne ya mika wa Aayaan takardar Fuskarshi ɗauke da matsanancin murmushi...

Aayaan be jira ya gama karanta takardarba ya fadi ƙasa yayi wa Allah subhanahu wata'ala sujuda ba Tare daya damu da Kasancewar a inda yake ba.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Ummin Nawaz itama tunda gari ya waye Abban Nawaz keta tattalin ta, komai ya hanata yi, data yunkura zatayi abuu sai ya hanata, ko kuma shi yayi sauri yayi.
Duk sanda suka haɗa ido kuma saiya sakar mata wani irin sassanyar murmushi, mamakin yadda komai nata baya tsufa yakeyi, domin kuwa kamar yadda yace Amarci zaisha to kuwa haka yasha Amarcin Domin kuwa Ummin Nawaz bata yi sanya ba a daren bayan ta haɗa mishi ruwan wanka ya shiga bayi itama ta samu ta ɗan yi gamje gamjen mu na mata ta haɗa kanta Emergency, tunda dama bata yarda ta zauna batare da kayan gyaran jiki a ɗakin taba, balle wannan karon bata daɗe da dawowa daga Maiduguri ba.

Bayan sunyi wanka sun shirya ne Abban Nawaz yacewa Ummin Nawaz tazo suje ɗakin Umma akwai maganar da yake so suyi.
Chapter 103 · 0% Book details