← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 112

Sashe 33

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin bukkar shi suka taddashi zaune ya rungume allo yana rubutun ajami ajiki.
Yana ganinsu ya fara murmushi ya ajiye Allon a gefe, "maraba da Aliyu da hafsatou...
Suma murmushin sukeyi sannan suka samu guri suka zauna,
Gaisheshi sukayi cike da mutuntawa, shima a sake ya amsa musu yana murmushi...
"Yau kuma ziyara akan kawo mana?
"Eh baffa" cewar bandi Yana Dada gyara zama..
Kallon sarfraz baba jauro yayi sannan yacewa bandi "baƙo mukayi ne?
Eh baffa a hanya muka tsinceta rannan, nan dai bandi ya faɗawa baffan duka Abinda Ya faru tun randa suka tsinci Sarfraz har zuwa yau daya farka da kuma abinda yayi bayan ya farka....

To dayake baffan yayi zaman Maraya sosai, ya zauna a Kano, ya zauna a Abuja har a Lagos ma ya zauna, to hakan saiyasa ya fita daban cikin rugar saboda yanada wayewa sosai sama dasu....

Ashsha! Allah dai yasa ba Abinda nake hasashe bane ya faru.... Cewar baffa yana miƙewa.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Gyara zama mummy tayi tace SARFRAZ dai da kika sani.

"A'a To naji anacewa Ammah ce mamanshi, to kefa? Nawaz tace tana daɗa maida hankalinta gaba ɗaya gurin mummy.
Murmushin ƙarfin hali mummy tayi " ai dama tun usuli banice haƙiƙanin Wadda ta haifi sarfraz ba, amma koshi kanshi besan da hakaba...

Mummyn Aayaan ce tayi gyaran murya sannan tace "Don Allah inaso hankalin kowa ya dawo gareni..

Farko dai Ni sunana mehtab mu yan biyune nida ƴar uwata mumtaz....
Ayanda mariƙai na suka bani labari shine ance wai a tsincemune a Kofar babban masallacin juma'a dake Faisalabad a ƙasar Pakistan...
To shine aka kaimu gidan marayu, anan muka girma nida Yar uwata mumtaz komai tare mukeyi gashi Allah ya ɗora mana wata irin ƙaunar junammu, banaso wani Abu ya samu dayanmu koda wasa....

A haka mukayita girma har mukakai kusan shekara goma,
Wata rana wasu mutane mazauna Pakistan amma asalin su yan Sudan ne aikine ya kawosu Pakistan..
Suka zo gidan marayinmu suka cike Form akan zasuyi adopting dina, to duk cikinmu babu wanda baisan irin kaunar da mukewa junanmu ba..
Haka akace wa mumtaz tabi yayinmu zasu kasuwa, Ni kuma bayan sun tafi waɗan nan mutane suka tafi dani.

Na daɗe ina ciwo, nayi kuka nayi kuka har na gaji, sai dai kawai su bani hakuri, daga bayane suka bani wannan zoben sukace in ajiye shi a hannuna idan na girma zasu kaini gurinta, wai itama sun bada irin wannan zoben a bata....

To haka dai na hakura inata rayuwa amma sai dai zoben nan ya zame mini kamar mumtaz haka zàn Zauna Ni kadai inyita magana da zoben ina murmushi..

Kuma kullum fatana baya wuce Allah ya kawo Ranar da zamu haɗu da yar uwata...
To dayake garin da muke anayiwa yara aure da wuri to saiya zamana banfi shekara sha uku ba maza sukayi ta tururuwa akan suna sunason aurena...
Babana yaƙi yarda sam saboda yasan bazasu rikeni Yadda ya kamata ba.
To anan ne daga baya Allah ya haɗamu da babansu Aayaan wani lokaci da akayi rikici a Sudan , to yana daga cikin waɗanda suka zo bada tallafin gaggawa a jirgin sama, da kuma tallafawa ga wadanda iftila'in ya faru dasu.....

Kwarai mariƙa na sunyi amanna dashi suka bashi izinin ya rika zuwa lokaci bayan lokaci..
To sanda nakai Shekara Goma sha biyar sai aka daura mana aure akayi abubuwan da aka saba na al'ada....
Mun shaku sosai da mijina, saboda baya boyemin komai kuma yana matukar kyautata mun yana kaunata sosai..

Anan Sudan ɗin muka zauna na tsawon lokaci saboda hatta Aayaan Saida yakai shekara 15 tukuna mijina ya Nemi transfer akan zai koma ƙasar iyayenshi.
Munyi kuka sosai sosai nida marikana, haka muka dawo Nigeria, to dayake mijina yasan da mumtaz tun kafin muyi aure.
Bamu Dade a Nigeria ba yayi mana visa zuwa Pakistan don ya cika min burina naganin yar uwata.

To Abin baƙin ciki shine koda mukaje sai akace tayi aure wai tabi wanda ta aura ma Nigeria amma zasu dawo, to saina ce abani address Dinsu na Nigeria saboda muje, amma sai sukace basuda shi, haka na ajiye musu numberta akan idan sun dawo a bata ace mata nazo amma bamu haduba.

To tundaga wannan lokacin Allah bai kuma nunamin yar uwa ta ba, kullum da ita nake kwana nake tashi, duk sujadar da zanyi sainace Allah ya nunamin yar uwa ta..

To cikin ikon Allah kuma sai ya Turo mana da Nawaz a lokacin da bamuyi tsammaniba.

Kuma hakan yasa .....

Gashi dai ba don halinkuba, amma gobe idan adadin liking ɗin bekai yadda nake soba zakuji wayan ne,👀👀

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 35*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️

Kuma hakan yanada nasaba daga zoben dana gani a hannunta, to bayan nayi mata bayanin zoben shine tace min itama ba nata bane wai Sarfraz ne ya bata,
To yanzu mudai munzone a dubemu da idon rahma akan zoben nan don girman Allah idan kunsan wani abu akan shi ku faɗa min.

Daddy wanda tunda ta fara magana yake tuna yadda mumtaz take nuna mishi muhimmancin zoben sanda tana raye, har randa zata mutu Saida ta bashi zoben a matsayin amana idan SARFRAZ ya girma ya bashi.
Ashe shi SARFRAZ ɗin ma yaje yayi kyauta dashi, mummy kuwa harda kwalla domin tasan labarin zoben kuma tasan idan mehtab taji mumtaz ta mutu akwai damuwa duba da yadda ra kwallafa ranta akan ita Yar uwar Tata.

Gyaran murya daddy yayi haɗe da gyara zamanshi sannan yace "tabbas babu ko tababa duk Wanda ya ganki yaga ƴar uwarki mumtaz, kamar takuma har ta ɓaci domin Ni dana gankima sam na manta cewa tace ku Yan biyune, nayi zaton ko fatalwace...
Sai daga baya na tuna, yanzu abinda nakeso dake shine kinsan komai na duniya Allah ne ya halicce shi, kuma sanda zai halicce shi beyi shawara da kowa ba, kuma babu wanda ya tayashi yin halitta.
Kinga kuwa duk abinda yayi dai-dai ne, sannan kuma babu wanda ya isa yace yafi Allah son halittar shi.

Rayuwa da mutuwa kuma duk suna gurin Allah, babu wanda yasan Sanda zai mutu, zai kai gobe balle jibi.

Kuma Allah yanason masu hakuri, kuma yanason waɗanda idan kaddara ta samesu ko wace iri ce su amsheta hannu biyu .

Mummyn Aayaan ce ta katse shi dacewa "komenene kafaɗa min kada kaji komai, Ni dama tuni zuciya ta ta hakura da koma me zanji, amma ina so nasani tabar wani abu dazan riga ganinta dashi?

Kowa na ɗakin idonshi cike yake da hawaye, shikuwa daddy mamakin irin ƙarfin imanin mehtab yakeyi.
Ayanda ta nuna ƙaunar ƴar uwarta be tava tunanin zata amshi ƙaddara haka da wuri ba.

Daddy ne ya fara magana a nutse " nine mijin mumtaz, mun haɗu a University of pesherwar Dake Pakistan , daga baya mukayi aure.......
Nan dai Daddy ya gama bata labarin har zuwa inda bayan ta haihu Allah ya amshi ranta,

Mummyn Aayaan tayi kuka sosai sai dai na zuci, domin idan ka kalleta hawayene Kawai ke zuba a fuskarta baya ko tsayawa....

Babu wanda beyi kukanba, sannan kuma kima da darajar mummy ta Karu a idon kowa dake falon saboda sunji yadda ta rike sarfraz babu kyara babu tsana bare tsangwama...

Haka dai akayita jajanta wa juna, haɗe da alhinin abubuwa da yawa da suka faru...

Nawaz na gefe babu abinda ke fita daga idonta sai ruwan hawaye, tayi iya kokarinta akan ta tsaida shi Amma ta kasa ..

Mamakin halin Mummy takeyi, irin yanda take nunawa SARFRAZ ƙauna babu wanda bazai dafa Kur'ani yace itace mamar shiba...

Lallai ashe har Yanzu Akwai masu yin soyayya don Allah...

Duk motsinta idon Aayaan na kanta dukda shima yana cikin damuwa amma ganinta da yayi a hakan saiya kasa sukuni, bini bini idonshi na kanta....

Rarrafowa Nawaz tayi zuwa tsakiyar falourn sannan ta tsuguna ta haɗa hannayenta guri guda tana rusa ihu, muryarta har rawa take yi tsabar damuwar da take ciki ga idonta ya kumbura yayi jajir.
"Don Allah ku yafemin, wallahi ba'a son raina muka rabu da sarfraz ba, babu yanda na iya ne shiyasa...
Amma nayi muku alkawarin hardai yana raye saina nemo muku shi, dukda Nasan bazaku Dena kallona a matsayin wadda na jawo muku bakin ciki da cikas a rayuwaba amma ina rikon alfarma akan kuyafemin idan zaku iya ..

Mamakine ya kama kowa a falour, domin sam basu lura cewa Nawaz kuka taketayi ba Saida ta fito tsakiyar faloun.
A Tare mummy da mummyn Aayaan suka mike suka kamata "haba ke kuwa Nawaz? Meye haka? Ji yanda kike kuka,
So kike ciwo ya kamaki, to gaskiya idon kinason zaman lafiya ki cire komai a ranki kiyi sabgarki kamar yadda kikaga muma munayi..

Sannan kuma ki Dena tunanin cewa muna kallonki da wani abu, Wallahi sam ko ɗaya illah ma Barka mukeyi da duka baku halaka ba.
Kuma gashi ta dalillinki ma an kuma haɗa zumunci da bakinshi ya wargaje....

Shima daddy cewa yayi "Nawaz Yar albarka, yanzu idan sarfraz ya dawo Kinga saimu fada mishi mahaifiyar shi ta rasu saboda ya rika yi mata addu'a, kuma duk kece sanadi, saboda da na kasa fada mishi ne saboda bansan suwa zan nuna mishi a Matsayin yan uwanshiba.
To Kinga yanzu kin kawo mini su har gida...

Ɗago kai Nawaz tayi "Daddy dagaske sarfraz zai dawo?

Daga mata kai yayi yana murmushi "zai dawo insha Allah, kidena damun kanki kinji, addu'a kawai ya kamata kirika yi akan Allah ya bayyana shi....

Hakanan Aayaan yaji zuciyarshi nayi mishi suya, dukda yanzun nan yasan Cewa sarfraz kaninshine amma idan yaga Nawaz tana nuna damuwa akan shi saiyaji kamar zuciyarshi zata fashe...

Ya kasa fahimtar wannan wane irin al'amari ne me rikitarwa, meyasa zai damu? Inaruwanshi ma?

Haka dai ya daure zuciyarshi yaci gaba da kallonsu.

Tashi kowa yayi donyin Sallah inda mummy ta nunawa Aayaan ɗakin SARFRAZ tace ya shiga chan, su kuma suka tafi dakinta tare...

Duk Nawaz ta kasa sakin jikinta, kome zatayi a ɗarare takeyi domin jinta kawai takeyi kamar mujiya a cikin tsuntsaye...

Duk su Mummy sun lura da hakan, barinma aseey wadda sai janta takeyi da hira saboda Ta saki jikinta...
Chapter 33 · 0% Book details