Sashe 66
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon Nawaz tayi tace "kinga surprise Koh?
Kauda kai Nawaz tayi ta shige ɗaki Don yanzu gaba ɗaya ma haushin sarfraz takeji, tama rasa murna takeyi ko akasin ta.
Ɗakin SARFRAZ su Aayaann suka wuce, anan suka tarar da bandi har yayi barci, "tashi kayo alwala muyi sallah" Aayaan ya cewa SARFRAZ shima ya miƙe ya ƙarasa bayin donyin alwalar. Sallah sosai sukayi Aayaan yana addu'ar Allah ya zaɓa musu abinda yafi Alkhairi, shikuma Sarfraz gani yakeyi ai babu Alkhairin daya wuce ya samu Nawaz a matsayin mata.
°°°
Koda Nawaz ta shiga ɗaki sai Aseey ta miƙe ta shiga ɗakin baƙi ta tawo da hassu suka shiga dakinsu don kwanciya.
Sakalo hassu tayi tana kallon Nawaz, tasan tafita komai bazata iya ma haɗa kanta da itaba, amma kuma cikin ikon Allah ko kaɗan bataji tanajin haushin Nawaz ba, sai jima da tayi tana ƙaunarta.
Itama ta ɓangaren Nawaz ɗin sai taji tanajin tausayin hassu ɗin, gata ƙarama kuma a haka tayita jigila da sarfraz.
Sosai Aseey ta ƙara ganin hankalin Nawaz, Yadda Sam taƙi yarda farin cikin ganin SARFRAZ ya rufe mata ido tayi abinda bashi bane.
Ko hirar ma basu samu sunyi ba kowa yayi barci kasancewar dare yayi sosai kuma duka a gajiye suke.
Haka da safe ma a makare suka tashi, lokacin ma Mummy ce tazo tace Musu su fito Daddy yace yanada zama da za'ayi a main falour, shine ta tashe su.
A gurguje suka shirya Sannan suka tafi zuwa mai falour ɗin, Anan suka tarar da kowa zaune saboda dama su kadai ake jira.
Addu'a daddy yayi Sannan yace "haƙiƙa sarfraz kabani mamaki, ban taɓa tunanin zakayi haka ba, Yanzu abinda kayi shine godiyar da zaka yiwa Aayaan na duka Alkhairin daya yi maka?
Ɗago kai Sarfraz yayi yana kallon dady da alamun tambaya a Fuskarshi.
Sosai dady ya karanci hakan a fuskar SARFRAZ ɗin.
"Nawaz dai ba kowa bane mijinta illah Aayaan, kuma a gabanshi kake duka rashin Mutuncin da kakeyi, kuma ka ƙara da cewa koshi waye saiya saketa.
Yanzu gashinan saiya saketa ka aureta.
Zumbur sarfraz ya miƙe yana zare ido tare da nuna Aayaan bakinshi na motsi alamun yanaso yayi magana amma ya kasa.
Nagode da addu'oin ku, Allah ya saka da Alkhairi kuma yabar ƙauna.
*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*58*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Chigaba da nuna Aayaann ɗin yakeyi still bakinshi na motsi, kowa na falourn binshi yake da ido yana tunanin me zai yi.
Juyawa yayi ya ruga da gudu zuwa dakinshi ya faɗa akan gado, sai Sannan ya samu damar fitar da abinda yakeso ya fitar tun ɗazu "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Lahaula wala quwwata illah billah, wai meyasa tun farko ban tambayi waye mijin nataba?
Yanzu haka nasan Nagama ɓata kaina a gurin yayana, meyasa idona ya rufe haka? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un yanzu ya yake kallona? Fashewa yayi da kuka yana girgiza kai.
"Na barta! Wallahi nabar Nawaz har abada koda ita kadai ce macen data rage a duniya.
Alkhairin yaya Aayaann a gurina ya Wuce wai in tsaya ina wani shirme akan mace.
A chan falour kuma bayan Sarfraz ya ruga da gudu shima Aayaan saiya tashi da sauri zai bishi, Daddy ne ya dakatar dashi "Muhammad kull, kada ka sake ka bishi! Kyaleshi.
Abin duniya duk ya ishi Nawaz, gani takeyi Kamar kowa zai tsaneta Tunda kusan duk don Ita hakan ta faru.
Mamaki ne Ya kama kowa ganin SARFRAZ ya fito yana tafe yana tangaɗi idanuwanshi duk sun kaɗa sunyi ja, a gaban Aayaan ya tsaya Tare Da zubewa kan gwuiwowinshi Sannan ya duƙar da Kai "yayana Don darajar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ka taimaka ka yafemin, Wallahi Ni butulu ne kuma na cika mai son kans.......
Dakatar dashi Aayaann yayi "yi shiru, kada ka kuma neman yafiyata, ni baka yimin komai ba.
Daddyne yace "kyaleshi ya fitar da duk abinda ke zuciyarshi tanan ne zan gane idan da gaske yake ko kuma so yake yayi wasa da hankalinmu domin naga ya chanza daga Sarfraz ɗin dana sani.
Wani irin ihu sarfraz ya saki "Daddy wallahi ban chanza ba, don Allah kuyi hakuri! Wallahi na haƙura da Nawaz har abada kuma wallahi dad tun sanda kace matar yaya Aayaann ce Naji duk wani abu danakeji game da ita ya goge, wallahi Ayanzu kome zai faru bazan taɓa iya aurentaba, girman yayana ya shafeta, Ayanzu Ita ɗin Aunty nace.
Mamakine ya kama kowa dake falourn "Ashe Sarfraz akwai sauran hankali a tare dashi, kenan shima ya fara shiga shekarun Dattaku, shikam Aayaan sai Sarfraz ɗin ya bashi tausayi yanda ya nuna yana matuƙar ganin girmanshi.
Ita ma Nawaz ji tayi kamar sarfraz ɗin ya tsamotane daga cikin ruwan ƙanƙara yasaka ana ɗumi.
Mummyn Aayaan kam tafi kowa murna, Domin bataso ta rasa Nawaz a Matsayin suruka sannan a lokaci ɗaya kuma bataso Sarfraz ya shiga ƙunci na rasa abinda yakeso saboda nata kwanciyar hankalin.
Daddy ne yace "zo ɗan albarka! Ni dama nasan mummynka ta baka tarbiyya me kyau, ayau kuma nayi alfahari da ita da Kai gabaki ɗaya, zo ka zauna kusa Dani.
A hankali SARFRAZ ya karasa kusa da Daddy ya zauna, rungumeshi Daddy yayi yana cewa Allah yayiwa rayuwarka Albarka kaida ɗan uwanka, Naji daɗin yanda ka nuna cewa kasan halalci.
Fashewa SARFRAZ yayi da kuka, Daddy idan banyiwa yaya Aayaann halallciba babu wanda zan taɓa yiwa halalci a rayuwata, shiya zamemin garkuwa a rayuwata sanda na rasa Komai da kowa, kuma shiya nunamin me kalmar ɗan uwa take nufi, ya sadaukar da dukiyarsa a kaina mara adadi duk dan in samu lafiya.
Kuma shidin yayanane saboda abinda yayi mahaifiyarsa shi yayi tawa, zan iya cewa ma abu ɗaya ne amma Allah ya maidasu biyu, ina kaunar su sosai, kuma ina ƙaunar Mummyna ma Domin ita ɗin uwa ce tagari bata taɓa yimin abinda zanji cewa ba ita ta haifeni ba, fashewa yayi da kuka "abu ɗaya ne zaitamin zafi a zuciyata shine sanadina mahaifitata ta bar duniya"
Toshe mishi baki daddy yayi tare da cewa "kul! Kada kace haka SARFRAZ, kowa akwai tashi kaddarar a rayuwa"
Kusan a Tare suma su mum sukace "safraz kada kayi saɓo mana, Allah ya fimu sontane shiyasa ya amshi abinshi, kuma abinda zaka dage dashi ayanzu shine yi mata addu'a.
Aayaann kam har yanzu ya kasa magana domin be taɓa tunanin sarfraz yanada hankali haka ba, itama dai Nawaz sai sharar ƙwalla takeyi ta rufe fuskarta da hijabi, gashi duka nauyin Mutanen faloun takeji musamman Daddy da mummyn Aayaan dashi kanshi Aayaan ɗin.
Ita kam Aseey rai ƙwal tunda sarfraz yace ya haƙura da Nawaz.
A hankali Nawaz ta mike da niyyar komawa ɗaki donta gani ko hassu ta tashi, dady ne yace "Amarya Nawwarah dawo ki zauna muyi maganar tarewarku keda Muhammad Ayatullah..
Kasa motsi Nawaz tayi a inda take, Aseey ta mike ta zaunar da ita tana cewa "zauna mana Amarya" Daddy ne yayi murmushinsu na manya tare da cewa amma fa SARFRAZ ya kamata ace Ranar da yayanka zai tare kaima a ɗaura maka Aure sai ayi shagalin tare.
"Daddy Ni banida wadda nakeso fa"
"Ina Yar fulaninka take? Ko itama baka sonta" Daddy yace yana kallon SARFRAZ.
"Daddy nifa da.....
Aseey ce ta hanashi karasa Maganar dayayi niyyah "wallahi daddy ka kawo shawara mekyau, domin yadda yarinyar nan tasha wahala dashi idan be auretaba be yi mata halalci ba.
Girgiza kai kawai SARFRAZ yake yana murmushi "to ina take?" Sarfraz ɗin ya tambaya
Da sauri Nawaz ta Miƙe "bari na kira ta"
Bata jira amsar kowaba ta tafi da sauri saurinta Don bata son a tsaida ita domin zaman faloun ya isheta.
Tana shiga ɗakin ta tarar da hassu zaune ta zabga uban tagumi.
Ƙarasawa kusa da ita tayi "hassu lafiya naganki haka? Meyafaru?
Ƙwal ƙwal hassu tayi da ido kaman zatayi kuka "Aunty dana tashi naga babu kowa duk sai tsoro ya kamani na zata kuntafi kun barnine"
Murmushi Nawaz tayi "Lallai hassu ta dace da sarfraz halinsu kusan daya, "to yanzu kiyi hakuri, babu inda zamu tafi mu barki, muna babban falourne an haɗu ana magana, Yanzu hakama ke ake kira.
"Muje in nuna Miki hanya" Nawaz tace Tare da kama kafaɗar hassu tana mikar da ita.
Fita sukayi daga dakin, Nawaz ta nuna mata inda zatabi sannan ita kuma ta koma ɗaki.
Hassu na zuwa falourn saita daburce ganin idon kowa akanta, rasa Wanda zata gaisar tayi sai kawai tace "barkanku da safiya".
Gabanta sarfraz ya ƙarasa Tare da cewa "ikraam kina so na? Zaki aureni?
Abinka da yarinta sai kawai hassu tahau murmushi Tare Da daga kai alamun eh sannan kuma ta furta da baki "Eh ina sonka, Wallahi zan aureka!" Batare data ji kunyar su Mummy da dady Dake zaune a falourn ba.
Daddyn ne yace "yauwa Hafsatu, zo nan mu tattauna.
Kunya rufe Mummy tayi, ai kuwa ta mike da sauri tayi hanyar dakinsu, itakam aseey sai murmushi take yi, tasan akwai sauran hassu, yarinta na cinta a ciki.
Mummyn AAYAAN ma taji daɗin yadda SARFRAZ ya samu me sonshi bilhaƙƙi, har Saida tayiwa Aayaann addu'a a zuciyarta akan Allah yasa Nawaz tasoshi kamar haka.
Aayaann duk ya ƙagu dayaga Nawaz Gashi yanajin Kunyar ya tashi daga faloun.
Message ya turawa haidar "haidar don Allah ɗan kirani yanzu"
Aiko cikin mintuna biyu wayar Aayaann ta hau ƙara, koda ya kalli screen ɗin sai yaga sunan haidar ɓaro ɓaro.
Mummy ya kalla da dad "bari na amsa waya, colonel ne ya kirani.
"Okay to jeka mana" Daddy yace tare da maida hankalinshi kan hassu yadda taketa murmushi, shi kanshi daddyn yasan hassu batasan meye aureba shiyasa taketa wannan fara'ar.
Aayaann na fita daga faloun ya kashe wayar Tare da sakata a cikin aljihu.
Direct ɗakin da Nawaz take ciki ya nufa, a zaune yaganta a Saman gado tana danna waya kuma ga dukkan alamu hankalinta yayi nisa da danna wayar, maida kofar yayi ya rufe ya samata key tare da takawa zuwa cikin ɗakin.
Sai sannan Nawaz ta dago da kanta don ganin waye, Zaro Ido tayi ganin Aayaan yana smirking.
Ruɗewa tayi ta rasa inda zatabi, shikuma ya fara murmushi gashi ya kafeta da ido "wa na kama? Ai duk gujegujen naki yaudai gani gaki"