Sashe 57
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan Nawaz ta waiga, ganin kwalaye tayi jibgi amma kuma wai ahaka ne yake cewa ko sunyi kaɗan! "Lallai ya Aayaan " abinda ta raya kenan a zuciyarta.
"Akwai wasuma a boot duk nakine" murmushi ya Kuma yi mata, "Sweet love kinƙi yi Min magana, ko kina fushi da nine?
Murmushin yaƙe tayi "a'a bana fushi dakai, amma kayan ne naga kamar sunyi yawa, Bansan ya zanyi da suba.
"Komai nawa nakine, Wannan kaɗan ne daga cikin abinda zan iya yi Miki. Ayanda nake ƙaunarki wallahi Zan iya mallaka Miki komai nawa...
Mamaki maganar Aayaan taba Nawaz, wai shi meyasa komai yake daukarshi a matsayin wasa ne?
"Ya za'a yi yace zai iya mallaka min komai nashi??
"Nasan wannan shurun da kikayi kina kokwonto ko wasa nakeyi Koh? To wallahi da gaske nakeyi, ko haufi kada kiyi..
"Nagode sosai, ALLAH ya ƙara girma!".
"Ameen dear, amma da cewa kikayi Allah ya bani ke da nafi farinciki...
Murmushi Nawaz tayi batare da tace komai ba...
Bayan sun isa kofar gidan Inna yayi Parking Sannan ya daukar mata kwalin chocolate da na caramel suka shiga cikin gidan, falour ya ajiye sannan ya koma ya rufe ƙofar gidan saboda dare ya riga yayi.
Kafin ya koma harta kunna haske a dakin, sannan ta dauko warmers guda biyu ta ajiye a Saman table..
Murmushi yayi "me aka tanadar min?
"Tuwon alkama ne da miyar riɗi"
"Wow Masha Allah, Gaskiya naji daɗi bari nazo naci, wanko hannu yayi sannan ya sauko da kulolin ƙasan carpet inda ya zauna, budesu yayi Tare dayin Bismillah yana fara ci, sosai ya maida hankali yake cin Tuwon kuma da Alamu yayi mishi daɗi...
Kallonta yayi "gaskiya kin iya abinci sosai, randa na fara cin abincinki Saida nayi overdose, Gashi yanzuma zakisa nayi kuma kinsan darene babu kyau cin Abu ne nauyi da yawa.
"To kabarshi haka sai in Kawo maka zobo ka sha, Nawaz tace Tare Da ɗauke kular daga gabanshi.
Murmushi yayi "shine kika ɗauke baki bari na ƙara kadan ba?
Ita dai gaba tayi ta ajiye kular a gefe sannan ta dauko mishi jug ɗin da zoɓon yake ciki ta dawo gabanshi ta ajiye....
Godiya yayi mata tare da buɗe jug ɗin yana kafa kai, namma Saida ya kusa shanye wa Sannan ya cire jug ɗin daga bakinshi yana cewa "wai sweet heart komai kin iya ne?
Gyara zama yayi ya miƙe kafafunshi dakyau sannan yace "bari abinci ya ɗan saukar mini sai muje mu kwanta.
"Zaro ido Nawaz tayi"mu kwanta fa kace? Wai kana nufin Tare zamu kwana?
Murmushi Aayaan yayi "just trust me for today only, namiki alƙawarin babu abinda zai faru.
"Damuwar data fita daga ciki ce yan mintocin da suka gabata ta dawo mata sabuwa, koma ince tafi tada.
Amma abin mamaki koda ya dauke ta suka kwanta a cikin dakinta tasan dai ya rungumeta a jirgin shi amma ko kaɗan babu abinda yayi yunƙurin yi mata, tanajinshi yayi barci, sai Sannan itama barcin ya dauketa.
Misalin ƙarfe huɗu da rabi ya tashi, kitchen ya shiga ya kunna wuta Sannan ya ɗora ruwan zafi, koda ya tafasa ɗaki ya koma ya dauko Flask a Saman tables ɗin Inna ya juye Ruwan zafin Sannan ya maida wani.
Koda yayi zafi sai ya juye yayi wanka dashi tare da dauro Alwala Sannan ya dawo ya tashi Nawaz don itama tayi alwalar saboda Biyar har ta wuce..
Salin alin ya jasu jam'i, Saida suka daɗe yana addu'oi Sannan ya juyo yana kallonta da murmushi a fuskarshi yace "good morning sweetheart!
Duƙar da Kai Nawaz tayi tare da cewa "ni ya kamata na gaisheki, ina kwana"
"Lafiya Lau dear, fatan kin tashi Lafiya, and kuma meye abin laifi don masoyi ya gaida masoyiyarshi?
Nan ma dai Nawaz shiru tayi batare da tace komai ba .
"Sweetheart Akwai ruwan zafi a Flask kiyi wanka ki shirya inaso mu isa gida da wuri, kuma kinga inaso mu fara zuwa gidan bikin da Inna ta tafi saboda in gaisheta Tare dayi mata godia na gurin fakewa data baki...
Murmushi dai Nawaz tayi batace komai ba.
"Sweetheart naga Yanzu komai saidai kiyi murmushi, kin dena magana, ko kunyata kike ji?
Tashi tayi da sauri tare da shigewa daki batare data kula Shiba, (Mutane zasuyi mamaki saboda nace Aayaan ya hura wutar coal, to amma ba abun mamaki bane saboda soldiers kullum suna daji babu abinda basayi, kumani ina kewaye ne da soldiers iri iri, daga kan navy, army har Air force)
A gurguje Nawaz ta shirya Sannan ta fito ta sameshi yana zaune inda yake, yana ganinta ya miƙe tare da cewa "za'a bani one hug? Ko in hakura?
Ita dai batace komai ba, kuma bata matsa daga inda takeba, hugging ɗinta yayi na two sec sannan yace "to kwaso mukullin kofar mu rufe mata gidan idan munje sai mu bata..
Har sun shiga Mota Nawaz ta hango hadiya tana tawowa, da sauri tace yaya Aayaann pls ga Wadda tayi Min kunshi can, don Allah ka tsaya muyi Sallama.
"You have More Time, lokacina nakine kiyi abinda kike so!
Fita tayi daga motar Tare Da yiwa hadiya murmushi "yau zan koma ki bani Number ki, zamu riƙa yin waya.
Saroro hadiya tayi, aini baki cemin Yau zaki tafiba, to zuwa gidan bikin fa? Nifa na shiryo ne.
"Au to Shikenan ma, shiga muje Kawai daga nan sai muyi Sallama.
Baya ta buɗe ta shiga tare da gaishe da Aayaan, ai Saida ta haɗiyi wani tsinkakken miyau ganin Aayaan da tayi "tab hakan mijin nata yake? Lallai Dole tarika gyara, wannan kyau , hu'um. Abinda hadiya take raya wa kenan a zuciyarta.
Amsawar da Aayaan yayi ne ya katse mata tunaninta,
Ƙara cewa yayi "dama ke kika gyara min amarya ta? To gaskiya kinada babbar kyauta, Nagode
Kusan suma hadiya tayi "wai yau itace wannan mashahurin me kuɗin yake godewa, ai ita ta gama jin daɗin duniya..
Haka dai har suka isa gidan bikin, Aayaan be Bari Nawaz ta fita ba saboda maza daya gani cike da Kofar gidan, hadiya ce taje ta kira innan.
Ai Koda Inna ta fito tsayawa tayi tana kallon motar dasu Nawaz suke ciki, cewa tayi " Lallai wani jinkirin Alkhairi ne, ai bata ƙara tsinkewa ba Saida sukayi ido huɗu da Aayaan.
Tasan photunan Aayaan ɗin a gurin ɗan autanta saboda beda aiki kullum sai cewa Allah yasa ya zama soldier Kamar Aayaan...
Ko banza tasan bata gyara Nawaz a Banza ba, sosai suka gaisa a mutunce tare dayi mata godia sosai, ita kuma ina ta noƙe murya "kada kaga sanda tazo bance ta koma ba, abinda yasa bance ta koma ba shine kar inje tayi wani gurin kaga yarinya ce ba Wani hankali suke da Shiba.
Murmushi Aayaan yayi Tare Da cewa "Babu Komai Inna mun gode, Yanzu sazu tafi chan Maidugurin ne, idan naje zan hadaki da Mummy na sai ku gaisa.
Wrappers ɗin yan ɗari Biyar Guda biyu ya miƙawa hadiya yace taba inna, ita kuma ya bata wrappers ɗin yan ɗari biyu yace nata ne, ai kuwa hadiya sai godiya takeyi, ita kuma inna ta Fara noƙe noƙe "anya ayi haka kuwa?
Tafiya dai Aayaan yayi ya barta tanata shi mishi albarka.....
Saida suka isa flyover Sannan ya kira securities ɗinshi suka dauki Hanyar komawa gida, tuƙin ya basu sannan suka koma baya shida Nawaz
Tun ba'a yi nisa da tafiya ba yaga Nawaz ta fara gyangyadi, Amma ƙarfin hali ya hanata ta kwanta..
Kallonta yayi Tare Da cewa "kirjina yana maraba dake akowane irin lokaci..
Kin kulashi tayi ta kauda kanta gefe Amma tana murmushi ƙasa ƙasa.
Misalin ƙarfe ɗaya saura suka tsaya a Gaya sukayi Sallah Sannan sukaci gaba da tafiya....
Anan Barci yayi awon gaba da Nawaz ba Tare data shiryaba, ai tuni ta faɗa jikinshii, shikuma ya rungumeta tsaff.
Sai gurin ƙarfe Biyar suka isa gida, hamdala yayi wa Ubangiji Tare Da ciccibar Nawaz yana shiga falourn da ita Bayan yacewa securities ɗinshi su shigo da kayayyakin dake cikin motar harda na Boot.
Wata irin ƙara Aseey ta kwala Tare ta nufar Aayaan da gudu tana cewa. "Mummy ki fito yaya Aayaann ya dawo da sister Nawaz!!!
A firgice Nawaz ta farka, sai ganinta tayi a hannun Aayaan, gefe kuma ga Aunty Aseey tana murmushi, ita kuma Mummy tsaye take a bakin kitchen ɗin riƙe da ludayin girki itama murmushin takeyi, shikuwa honourable muhsien harya bude kwalin chocolate ya fara ci, sai Wata data gani a zaune a kan kujera ta ɗora Kafa ɗaya kan ɗaya tana aikin taunar chewing gum, ita Nawaz ma sai taga Kamar hararar ta takeyi.
Cewa tayi "saukeni" a hankali.
Sauketa yayi aikuwa Aseey ta rumgume ta tanata murna, itama Mummy karasowa tayi suka rungumeta juna, babu wanda yayi mata Maganar guduwar da tayi saboda Ashley da take zaune a faloun, basason wani yaji family issues ɗinsu saboda kada su jawa kansu abin Magana...
Mamakin abin da Ashley tayi mummy takeyi, "ke Ashley bakiga matar yayanki bane kike zaune baki tashi kin tarbeta ba?
Yamutsa fuska Ashley tayi "Mummy aini ban san taba" sai kuma ta kalli Nawaz tace "sannunki"
Sam Nawaz neman miyau tayi a bakinta ta rasa saboda Cewa da Mummy tayi ita ɗin matar Aayaan ce!
"Ko kallon Ashley bata yiba, sakamakon jin jiri yana Neman kwasarta, sai sannan Mummy ta lura da abinda tayi ganin Nawaz zata zube musu Anan, Aayaan tayiwa magana da ido akan ya ɗauke ta ya Kaita ɗaki....
Aikuwa suna shiga ta fashe da kuka, Mummy ce ta Kalli Aseey tace "Aseey maza kisan yanda zakiyi ku fita keda Ashley, banason taji wani Abu dazai iya jawo mana ɓaraka.
Aida sauri Aseey taje ta samu Ashley tace tazo ta rakata ShopRite, Ashley mayyar yawo kuwa ta mike tana washe baki, muhsin kuwa ko kallonsu beyiba yaci gaba da cin chocolate ɗinshi har suka fita daga falourn..
Wani Abu Nawaz takeyi Kamar me aljanu, duk idonta sun kaɗa sunyi ja, sannan sai Wani shure shure takeyi.
Addu'a Aayaan ya Fara yi mata Yana tofa mata, ita kuma mummy ta fita don ɗauko ruwan zam'zam.