← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 112

Sashe 5

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

yanzu abinda za'a yi ka shiga d'aki kayi wanka anjima saikafito amatsayin ka gama kararun..
rungumeta Yayi ya sumbaceta a goshi "I too much love you my love....
sannan ya wuce Yana Daria..... Cewa tayi kayi sauri ka gama abinda zakayi da wuri saboda kasan gobe Monday kuma kacemin kanada test koh

d'aga mata Hannu Yayi "as you command my only queen
kwallace ta fito mata a ido, tayi sauri ta goge, zancen zuci ta Fara "bansan yanda sarfraz zaijiba duk Randa yasan cewa banice asalin mahaifiyarshi ba....

hanyar d'akin daddy tayi tana dada goge idonta....

NAWAZ.......

koda tashiga gida d'aki ta wuce, a falour Ta tarar da ummi tana sallah

dakinta ta shiga ta ajiye parcel d'in a Saman gado...
Sannan ta shimfida praying mat Ta fara sallah, Bayan ta idar ta fita wurin ummi sunata hira,
acikin hirarne ummi tacewa nawaz wai waye yazo gurin kine dazu?
"ummi wani senator ne, abin har tsoro ya bani domin ba anan yake zamaba yana zamane a Liverpool can kasar ENGLAND...
Amma gaskiya bazan amince mishiba domin bazan tafi nabarkiba coz you're my everything my love, my hope, my role model, my World, my desire......

Daria ummi tayi "to shikenan kiyi Ta addu'a Insha Allah nima zan kara a wadda nakemiki kuma idan Allah yayi mijinkine hakanan Zaki tafi ki barni...

Rungumeta tayi to my sweet mum I love you so very much....

(me karatu zaiso yaji meyasa nawaz ta shirgawa ummi karyako?
umma tayiwa karya ba umminta ba, domin tun sanda nawaz ta fito daga d'aki Ta hango umma da fauziyya labe a Gefen window, shiyasa tace haka kodon Ta sosawa umma zuciya.

sai gurin goma suka gama hira, ummi ta shiga dakinta sannan Nawaz ta shiga nata itama...

asaman gado taga parcel d'in sai sannan ta tuna da zuwan sarfraz "wai meyasama na saurari sarfraz ne? (wata zuciyar tace saboda kibatawa umma rai mana)
To Amma yanayin maganar da mukayi ta dace?
Kawar da tunanin tayi ta bude parcel d'in Don ganin Menene aciki

Me karatu ka biyoni donjin me safraz ya bawa malamarshi

Ciwon Kai🤯*🎀🎀 SAFRAZ 🎀🎀*

*Episode 6*

*Written by oummou muhsien* ✍️

Supreme writers association.......

We write with the ink of era....... That's era is our ink 😉

Bude parcel d'in tayi Don ganin Menene aciki...
Ga mamakinta takardu tagani da yawa sannan kuma sai Wata karamar jaka a ciki mai kyalli..

Bude jakar tayi, zoben diamond 💍 ne mai kyau aciki.
A yatsanta na kusa da karami ta gwada cikin Sa'a kuwa yayi mata dai dai.

Yatsan taketa kallo don zoben ya matukar burgeta suka cewa batasan kudin shi ba.
Takardar farko ta dauka ta fara karantawa kamar haka.....

Assalamu alaikum

Malama Don Allah Kiyi hakuri da abin da muka yi miki. Insha Allah bazaki kuma samunmu da makamancin abinda mukayiba......
Zainab kabir

Ta biyu ta dauka itama exactly abinda aka rubuta ana farkon amma saidai sunan ba d'aya bane....
Haka tayita bin takardun har saida takai ta karshe......

Assalamu alaykum...

Malama Ina mai neman afuwarki kuma Ina cike da baƙin ciki da Dana sannin abinda mukayi miki musamman ma ni...
Don Allah malama kiyi mini aikin gafara,
Kuma Don Allah kada ki dena koyarwa a makarantarmu domin idan kika dena zuwa nima nadena zuwa islamiyya har abada.....
Ina Fatan zaki yafemin....... Nagode

Sarfraz Muhammad goni......

Murmushi tayi "Mtswess yafi Kowa neman magana da rashin kunya Amma yafi Kowa zaƙin baki da neman yafiya, saboda in koma sucigaba da garani Kamar kwallo...

Zoben yatsanta ta kalla sannan tace to zobenma meye manufarshi kuma Oho?

nidai na gaskiya zoben 💍 yamini kuma bazan cireba....
Takardun Ta tattara Ta mayar dasu cikin parcel d'in ta ajiye a saman drawer....

addu'o'i tayi sannan taja bargo ta rufa......

Nawaz saimuce safiya ta gari 🌠🏝

MORNING........ 8:30AM

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

SARFRAZ........

zaune yake a dining Yana cin French toast da stir fry noodles, saboda idan zashi school yafison yaɗanci abu me nauyi coz he's not use to abincin Waje.....

mum ce tafito rike da black back pack,.
Turus Ta tsaya "sarfraz wai meke damun Kane? Kacemin 9:00am kakeda lecture kuma test Kace za'a muku amma yanzu har to 9 Amma kaƙi tashi ka tafi.... Shiyasa nafiso ka tafi da dad dinka wallahi.
mum kiyi hakuri wallahi abincine da zafi kuma bake bace kikaki bani kikace naci da kaina......

Hmmm bansan Randa zaka girmaba sarfraz, ruwa ta tsiyaya a tumbler ta mika mishi yi sauri kasha ruwan nan..
Amsa yayi yasha sannan ya amshi back pack ɗin yasa a baya yayi hanyar Waje yana murmushi "bye my love "
Ɗaga mishi hannu itama tayi tana murmushi "bye 👋 sweetheart....

motanshi kirar Honda continue discussion fara yahau....
Reverse yayi gate ya bude Yayi hanyar University dinsu.....

NAWAZ............

EXACTLY that morning, share dakinta tayi sannan ta fito ta share d'akin umminta da falour ta gyarasu duka...
Turaren wuta ta kunna sannan ta fita ta share tsakar gida ta wanke duka bayin gidan....

Ɗaki Ta koma ta shiga kitchen.....
sanwan taliya da wake tayi sannan ta dawo falour Ta zauna tana duba hisnul Muslim dinta.
sallamar Khadija taji (wadda sukayi B.ed a F. C. E tare)

da sauri ta tashi suka rumgume juna..
Khadija tace "nawaz kwana biyu kin gujeni ko wani abu nayi miki?
Murmushi nawaz tayi "habadai niko me zakimin kawaidai ban cikason zuwa gidan matan aure bane kuma kinga nasamu koyarwa a HAYATUL ISLAM.....

"ikon Allah saikace Kema watarana bazakiyi auren ba, kinga muma saimuki zuwa naki gidan. Cewar Khadija tana hararar nawaz...

Dariya nawaz tayi sannan ta tashi ta kawo mata ruwa da d'an abin motsa baki..
sannan suka zauna aka fara hira......
niko nawaz ina ummi?
tana barci Amma nasan takusa tashi tunda goma tayi ....

Abincin ta sauke ta zuba musu suka faraci suna hira jefi jefi...
ummi ce ta fito daga dakinta tana Gyara dankwalin kanta....

"A'a Khadija yau kece a gidannan?
kwana biyu ban ji duriyarkiba....

murmushi Khadija tayi "wallahi ummi kwana biyu banga kawar Tawaba shine nazo Biko.....

dariya ummi tayi tace "aikuwa kin kyauta ya megidan baki fatan duk kuna lafiya?

" Lafiya lau ummi"...
"Masha Allah haka akeso" cewar ummi sannan ta wuce kitchen.....

sai wurin Karfe biyu Khadija ta tafi gida....

Nawaz ta dawo daga rakata suka hadu Da umma a zaure, dagewa umma tayi ta rusa ihu "wayyooooo zata kasheni......

Nawaz ko abin mamaki ya bata ta tsaya tana Kallonta.
Ummi ce ta fito zauren da gudu tana tambayar Lapia?

Ga tsinanniyar datakeson ganin bayana nan ace kamarni zan wuce bazata iya kaucewa ba saidai mu bangaji juna saboda tsabar rashin tarbiyya.....

hakuri ummi ta bata da nufin Insha Allah baza'a kuma ba domin zatayima Nawaz magana....

hannun nawaz ta rike suka shiga d'aki,
"wallahi ummi ban bangajetaba.
ummi tace yi shiru nasan halinki, bazaki taɓa bangaje waniba balle umma.
nidai abinda nakeso dake shine Don Allah ki kara kula sosai, ki rika kiyaye wa.

Kuma dama inaso na fada miki cewa jibi zan tafi maiduguri.......

"da sauri Nawaz tace ummi saboda mene? Amma dai Dani zaki koh?
A'a Nawaz badake zaniba saboda kinga kinada koyarwa dakikeyi kuma idan baki koyarba kinsan bamuda abincin da zamuci, kinfi Kowa sanin halin da muke ciki kuma kinsan dai ko wata daya da tafiyar mahaifinku ba'ayiba ta rufe store wai abinci ya kare..
Yanzu ko kinsan watanshi sha d'aya da tafiya, babu zuwa babu aike kuma ko wayarshi muka Kira bata zuwa shine nakeso naje, idan naje gidanmu sai inje gidansu inji ko lapiya

amma zan cewa umma Kano zani inna batada Lapia saboda idan na fada mata cewa maiduguri zani Saita San yanda zatayi Ta hanani zuwa...

"to ummi Allah yakaiki Lapia ya dawo dake Lapia, jibi kikace zaki tafi koh?
Ummi tace Eh nawaz d'an Allah kiyi hakuri da halin ummanki kinji sati daya kawai zanyi Insha Allah..
Murmushi Nawaz tayi "to ummi Insha Allah babu abinda zai faru, zan kiyaye

3:00pm
A gajiye sarfraz ya shiga falour Yana tafe yana tangadi Kamar Dan Maye,
Mummy ce ta rikeshi da sauri "meyafarune sweetie?
bata rai Yayi "mum I'm exhausted, kuma kinsan cewa lecturer nan banzoba Sai wurin Karfe d'aya, saboda yanaso mu tafi ya bamu carry over.....

cewa tayi Sai ka dada hakuri kaga kana last year ne saida kauda kai koh my boy?

Murmushi yayi "mum me kika dafa mana ne yau?
White rice and chicken stew hope zakaci?

Eh mummy zanci Sosaima saboda yunwa nakeji sosai...

Dining ta jashi sannan ta yi serving dinshi "yi sauri ka ci saikayi wanka kaga lokacin islamiyya yayi.

To yace sannan ya Kara yawan abincin yanaci da sauri...
Saura kadan ya cinye ya mike "mum nakoshi bari Nayi wanka.
OK to kayi sauri kaga saura ƴan mintuna Hudu tayi kada kayi latti..

HAYATUL ISLAM......

Malama Nawaz nagani zaune a teacher's seat, rike da Quran tana budewa

dai dai nan safraz ya shigo rike da hulanshi a hannu, gabanta ya karasa sannan ya ɗan rage tsawon shi malama don Allah ayimin afuwan rashin zuwa na dawuri daga school nake.

Ɗaga mishi hannu tayi "babu komai jeka seat dinka...

tashi Yayi yaje seat dinshi ya zauna.....
abin yaba nawaz mamaki domin gaba ɗaya yau tunda Ta Fara karatu har tagama babu Wanda ya tambayeta, kuma babu alamun rashin kunya a tare dasu...

Adduar tashi tayi ta fita, da sauri sarfraz yabi bayanta,
"malama Dan Allah in kaiki gida mana...

waigowa tayi "A'a sarfraz nagode kabarshi, nema Yayi ya matsa mata, ta wuce ta bashi guri....

Haka Koda ya dauko mota yayi ta binta ita kuwa tayi banza dashi.
har takai gida yana binta.....

Yau Ta kama ranar da ummi zata tafi maiduguri, fitowa tayi ta fada wa umma cewa zataje kano gurin innanta batada Lapia kuma Kila tayi sati daya...
murmishi umma tayi saboda ita kadai tasan abinda take ƙullawa a zuciyarta "Allah ya kiyaye hanya kuma Dan Allah ki gaishemin da ita, kice ina mata Sannu....

Har Tasha Nawaz ta raka ummi, inda ummi keta jaddada mata kada ta sake tayi abinda umma zata ce ta mata rashin kunya,
dakyar Nawaz tabar Tashar Ta koma gida........

tunda Ta shiga gida bata fitoba saida zata islamiyya...
Chapter 5 · 0% Book details