← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 112

Sashe 83

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa sukayi Nawaz na rumgume da sudeis suka fita daga cikin hall ɗin zuwa harabar Makarantar suna ɗan tattakawa, maman sudeis tana ta dan nuna mata gurare.

Wata ce ta zundumo da gudu itama daga ganinta kaga bahaushiya duba da riga da skirt ɗin atamfar dake jikinta, tana karasowa gurin ta rungumesu "ashe Akwai Hausawa a makarantar nan, wallahi jiya na fara zuwa ga ajinmu chan, babu bahaushe ko ɗaya, na rasa Yadda zanyi.
"Ayyah dayake jiya banzo ba" cewar Maman sudeis

Nan dai itama ta gabatar musu da kanta, tace sunanta Fatima itama ƴar Zariya ce cikin Tudunwada *Magume* itama bata ɗade dayin aureba suka tawo nan England tare da mijinta.

Cikin ƴan ƙalilan ɗin mintocin da suka rage a tashi, sosai Nawaz da maman sudeis da Fatima suka saba da juna sosai, kamar sunfi shekara da sanin juna.
Duk sun faɗa mata address ɗin su amma dayake ita bawai tasaba da garin bane bata san inda suke nufi ba.

Lokaci na cika saiga motar Aayaan ta sawo kai ta shigo cikin harabar Makarantar, daɗi sosai Aayaann yaji ganin Nawaz riƙe da jinjiri ta sake cikin wasu mata guda biyu da be sansu ba suna hira harda dariya.

Kusa dasu ya karaso suka gaisa Sannan yacewa Nawaz "To Madam time yayi fa, idan kuma baku gama hirar ba sai in ƙara miki koda 30mins ne.

Da sauri Fatima tace "A'a gaskiya baza'a yi haka ba, ai muma gida zamu tafi, kawai ku tafi.

Aayaan ne yace "za'a zo a ɗauke kune ko da kanku zaku tafi?
"Da kanmu zamu tafi" cewar Maman sudeis

"A wace unguwa kuke? Aayaan yace yana miƙa hannu yana amsar sudeis a hannun Nawaz

Faɗa mishi sukayi, ashema duk suna kusa da juna, sai an wuce gidajensu ma tukuna zasu ƙarasa hotel ɗin da suka sauka.

Cewa yayi su shiga motar kawai duka ya rage musu hanya, Aikuwa cikin jin daɗi suka shiga suna mishi godiya.

Nawaz tace ya bata sudeis saboda yaji daɗin tuƙin amma fir Aayaan yace tabar mishi shi, sai wasa yakeyi mishi, hakan yasa tuƙin nasu a hankali akeyi.
Koda aka karaso Kofar Gidan Fatima sai ta sauka tana ce musu sai sun haɗu gobe a makaranta.

Tafiya kaɗan aka yi aka ƙaraso gidansu Maman sudeis itama, dakyar Aayaan ya bata sudeis suka shiga gida.

Ko a hanya ma sai hirarshi yake ta yiwa Nawaz ɗin, sosai Nawaz tai mamakin yadda farat ɗaya sudeis ya shiga zuciyar Aayaann.

Abin Allah sati daya da haɗuwarsu amma wata iriyar shakuwa ta shiga tsakaninsu, har Allah Allah Nawaz takeyi gari ya waye ta tafi makaranta don su haɗu da juna, Maman sudeis Akwai mutunci sosai ga bayar da shawarwari masu amfani, itama fatima akwai saurin sabo, ga mutunci itama kuma akwai yawan ɗebe kewa don tanada faran faran ga wasa da dariya.

Tunda suka haɗu Aayaan shike maidasu gida, kuma kullum sudeis yana hannunshi, haka duk sanda Nawaz zata tawo saiya bada su chocolate da abubuwan wasa wai a kawowa sudeis, duk da Nawaz na cewa be iya cin abinci ba amma saiya bayar kullum, fatima ma da maman sudeis ɗin suma Duk ya sai musu wasu dogayen rigunan masu kyau.
Aayaan yana mutunta duk wanda yakeson Nawaz shiyasa cikin Lokaci ƙalilan suma su fatima suke mamakin wace iriyar ƙauna Aayaan yake yiwa Nawaz.

Yau dama su maman sudeis da Fatima suka yi zasuje gidan Nawaz idan an tashi daga makaranta,
Koda aka tashi Aayaan ne ya kwashesu ya kaisu shi kuma ya ɗauki sudeis suka yi waje, sosai ɗakin Nawaz ya burgeshi sai santi sukeyi.
Sunsha hira sosai inda sai wajen ƙarfe shida sukace zasu tafi, anan ne fa Nawaz ta rasa me zata basu, tunawa tayi da magungunan ta, samun polythene bag tayi ta zuba musu da yawa, godiya sosai sukayi mata har Maman sudeis tana tsokanar Nawaz da cewa "Ashe Yau kince mai gida ya ɗan ji chanji kenan" ita dai kunya na hana Nawaz yin magana.
Rakasu gurin Aayaan tayi suka amshi sudeis don tafiya gida.

Cab Aayaan ya Samar musu suka yi sallama suka shiga sukayi hanyar gida, inda shikuma ya ciccibi Nawaz suka koma ɗaki.

Cikin yan kwanakin wata irin shakuwa ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin Aayaan da Nawaz, ga wani irin body contact Daya kamasu, ɗaya baya zama kusa da ɗaya face saiya taɓa jikin daya. Haka zasuyi ta rige rige wajen ayyuka, har dambe sukeyi wajen cin abinci.

Yau ta kama asabar, Aayaan yana zaune yana gyarawa Nawaz ƙumba (Akaifa) bayan ta gama gyara mishi nashi.

Knocking ɗin kofar su aka farayi a hankali, da sauri Aayaan ya mike tare da buɗe ƙofar, maman sudeis da Fatima ya gani tsaye suna murmushi, duk sai suka daburce ganin Aayaan sanye da kayan shan iska.
Guri ya basu suka shiga ciki inda shi kuma ya ɗauko jallabiya yasa ya bar musu daƙin.

Yana fita fatima tace "Madinah bakiyi mamakin dawowar mu yauba bayan shekaranjiya mukazo"

" Haba mamaki? Ni farin ciki nakeyi wallahi"

"Nifa zuwa nayi idan akwai sauran maganin Nan da kika bamu ki ƙara sam mini" cewar Maman sudeis tana ɗora sudeis akan kujera.

"Wallahi Nima haka" Cewar Fatima.

"Dariya Nawaz tayi, akwaiku da abin ban dariya Allah"

" Hmm wane abin dariya, jiya fa ogana har Cewa yayi zamu koma Umrah, ita kuwa maman sudeis Kinga sabuwar wayar da babban sudeis ya canza mata a jiya da safe" Cewar Fatima cikin muryar da take nuna gaskiya take faɗa daga cikin zuciyarta.

Ita kuwa maman sudeis cewa tayi"ashe ba banza ba, dole oganki ya riƙa zargadila akanki yasan abinda yake kwasa"

"Nifa amaryace har yanzu" cewar Nawaz tana sunne kai.

"Au wani yace kin tsufa? Maman sudeis tace tana ɗaukar Ruwan dake saman table.

"Look nifa ba haka nake nufi ba, Ni babu abinda ya taɓa shiga tsakaninmu da ogana, soyayyar da yake min daga Allah ce, amma ba don wani abu bane" Nawaz ta faɗa freely

Saida maman sudeis ta ƙware da Ruwan da take sha Sannan ta miƙe da sauri.

Kusan a Tare sukace "kai Madinah, don Allah bada gaske kike ba Koh?

Miƙewa Nawaz tayi tabi Hanyar dining don Kawo musu abin tabawa, Sannan tace "Allah da gaske"

"To mijin nakine beda lafiya ko kuma ke kikee hanashi?"

"Hakanan, kalau yake"

Tana shiga kitchen Fatima ta Kalli Maman sudeis tace mata ya kamata muyi wani abu fa, inba hakaba Madinah zata kashe ɗan mutane, ace wannan lafiyayen mutumin fanko yake zaune?

Nawaz na dawowa tagansu tsaye, cewa tayi " ku zauna mana"

"Bazamu zauna ba, kuma daga Yau kada ki sake ki kuma nuna kin sanmu, Ashe dama bakida hankali, ashe muma jahilai ne muna tare da ƴar jahannama bamu sani ba.
"To daga yau sai yau babu mu babu ke"

Zaro Ido Nawaz tayi tana mamakin ita kuwa metayi haka da zafi?

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*71*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Ummul Kulsum Muhammad ko ince *Nuwairah* ko kuma *chu-chu* duk Wanda dai kika zaɓa Acikin sunayen yayi, Wannan shafin nakine *100%* amma idan zaki dara ayi kaɗan kada ayi ciwon ciki.

Sosai idon Nawaz yayo waje domin maganganun su sun ratsa ta, "Yanzu fa muke magana! To me nayi da zafi da har zasuce min Yar jahannama? Ko dai wani Abu mara kyau suka gani a cikin Ɗakin?"

Kama hannun Fatima tayi "don Allah sis ki faɗa min me nayi? Ko wani abu kuka gani?"

"Lallai Madinah! Ashe bakida imani kuma baki tsoron Allah, gaskiya da Nasan haka kike ko da wasa bazan taɓa zuwa kusa dake ba balle har mu ƙulla ƙawance ba, irin kune kuke jawa waɗanda basuji ba basu gani ba wahala, fushin da Allah yake yi daku ya shafi sauran bayin Allah" Cewar maman sudeis tana ƙoƙarin maida sudeis ta goya.

Riƙe sudeis ɗin Nawaz tayi da ƙarfi tare da cewa "Don Allah Don darajar ma'aiki ku taimaka ku faɗa min Abinda nayi Kafin ku tafi, Wallahi zan gyara har dai wanda za'a iya gyarawa ne.

Fatima ce tace "kinyi Alkawari?"

"Wallahi nayi! Amma Don Allah ku koma ku zauna"

"Kaini bedroom ɗin da kuke kwana" Abinda maman sudeis tace kenan ta maida bakinta ta tsuke

Jikin Nawaz har rawa yake yi tsabar sauri tayi hanyar bedroom ɗinsu tare da cewa "kuzo muje"

Suna shiga babu a inda Maman sudeis ta tsaya sai gaban drawer, buɗe drowoyin tafara yi tana duba cikinsu Alamun tana neman wani abu.

Wasu robobine kusan guda Biyar iri ɗaya ta cirosu a cikin drawer karshe, kallon jikinsu tayi sosai tana Nazarin rubutun dake jiki.

"Uuhhmmm aini na sani, dole ba haka kawai ba! Wallahi Nawaz Kiyi saurin tuba zuwa ga Allah inba haka ba kuwa kinshiga Uku, ke wallahi idan kika mutu a yanzu ma hmmmm.

Ita dai Nawaz dama a tsure take, ganin kuma maman sudeis ta ciro robobin nan tana wasu maganganu saita ƙara tsurewa.

Ita dai tasan wadannan robobin na magungunan Aayaan ne da yake sha kullum, bazata manta sanda ta rakashi ya taɓa siyowaba lokacin da yazo gidan inna ya sameta sanda ta gudu Zariya, kullum yanashan biyu da safe biyu da yammah amma dai ita batasan maganin me yake yiba.

"Kinga waɗannan robobin? Kuma kinsan wane magani ne acikinsu?"

Girgiza kai Nawaz tayi Alamun bata saniba.

"To ƙwayoyin kashe sha'awa ne! Mijinki yana sonki kuma yana ƙaunarki, babu Abinda ya rage ki dashi amma ki rasa dame zaki biyashi sai da Wannan Madinah?, Kinsan kuwa irin halin dayake shiga na Rashin samun haɗin kanki? Ni nasan dolece tasa ya nemi maganinnan bawai don son raibane"

Fatima ce itama taci gaba da Magana "gaskiya Madinah kin bani mamaki, Ashe wayonki na Banza ne, kinata mutuntamu Ashe mijinki da baƙin cikinki yake kwana yake tashi, kekam da kinsan irin zunuban dake kanki nasan ke kanki ƙyamar kanki zaki riƙa yi, amma it's not late, zaki iya tuba kuma ki gyara.

Duk jikin Nawaz yayi sanyi ƙalau, damuwa ta rufeta, tabbas tasan Aayaan yana tausayinta sosai shiyasa ya kyaleta har zuwa yanzu beyi mata komai ba' amma ita batasan yana chutuwa haka da yawa ba da har zai Nemi ya halakar da kanshi saboda ita ba"
Chapter 83 · 0% Book details