Sashe 61
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aayaan kam ya ƙagu daya koma gurin Nawaz ɗinshi, Sannan gaba ɗaya duk wanda yasan shi yasan ya chanza, saboda duk fadan nan babu Sannan yana zaune shi kaɗai yayi ta murmushi..
Allah yasa ma aikin nasu ba wani me wahala bane, dama ana zargin Yan leƙen asiri sun shigo ƙasar ne shine akace Suzo suyi sumame, idan gaskene su gurfanar dasu a babbar kotun duniya.
Tsaff ya gama haɗa kayan shi da iya gejinsu back pack ɗinshi, sosai yake murmushi Domin so yakeyi direct Yanzu ya sauka a London Idan ya kwana gobe sai su ɗauki hanya zuwa gida Nigeria.
Sallama yayi da sauran colliques ɗinshi Sannan ya nufi masaukin colonel, sara mishi yayi Sannan ya ƙame,
Murmushi colonel yayi "Aayaan dole Akwai abinda kake ɓoye min, Ni nasan ba hakanan kawai ka chanza ba, ko ka Fara Soyayya ne?
Zaro ido Aayaan yayi " sir nina isa?
"Aayann kenan, duk wanda ya ganka Yanzu yasan akwai abinda yake special a gurinka, kuma shi namiji babu abinda ke saurin chanza shi kamar mace, ko dai daughter Nawaz Taci nasarar sace zuciyar namijin zakina ne?
Sosa ƙeya Aayaan yayi tare dayin murmushi donya gane colonel kallonshi kawai yakeyi, tunda dama ance duk wanda ya rigaka kwana dole Ya rigaka tashi.
Maganganun da zasuyi sukayi, inda Colonel yace ya ƙara mishi hutun wata biyu akan sauran wata dayan daya rage mishi tunda a banza suka ƙare be samu ya hutaba..
Jin haka da Aayaan yayi kamar ya ciccibi colonel yayi ta rawa da shi, sosai yayi mishi godiya daga bisani colonel Yacewa pilot ɗin private jet dinsu ya kai Aayaan London ɗin...
Namma sosai Aayaan yaji daɗi, sallama sukayi Aayaan ya Wuce gurin jirgin suka daga zuwa kasar England.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Parking ɗin motar SARFRAZ yayi a inda suka dauketa, sannan ya ciccibi Hassu a hannu har zuwa bakin window ɗin da suka diro sanda zasu fita, mikawa bandi ita yayi "Bandi riketa, idan na kama nahaura zan leƙo saika miƙo min ita.
Amsarta bandi yayi sannan sarfraz ya haura ya dira, sai Wajen cicciba hassu ɗinne aka samu matsala domin bandi be kai sarfraz karfi ba, saida kyar da sudin ludayi ya iya cicciba ta sanna SARFRAZ ya janye ta sai shima bandi ya haura, suna isa falour suka fara sanɗa, aikuwa ganin babu kowa yasa kowa ya arta dakinshi da gudu.
Sosai Hassu take dariya, ita wannan kwallon da aka buga mata daɗi taji tunda har tagane SARFRAZ ya dauketa da muhimmanci, kuma ya nuna zai iya yin komai akanta.
Shima sarfraz yaji daɗi sosai ganin har suka fita suka dawo haidar be sani ba tunda shi ya ajiye cewa haidar ɗin ya cika s ido ne.
Ai su SARFRAZ basuyi minti goma da shiga gidanba aka fara buga gidan da Wani irin mugun ƙarfi kamar za'a jijjige kofar a ajiyeta gefe guda.
Jin hakan da sukayi sai kowa yaja bargo Tare Da rufe ido harda munshari irin su sun daɗe dayin barci.
Haidar bawan Allah, kwance yake shida Madam Dinshi yana barcin huce gajiya Kasancewar duty ɗin dare yayi jiya, a firgice ya tashi jin irin bugun kofar da akeyi.
Sa sauri ta ɗauki riga ya ɗora a saman singlet Dinshi Tare da Cewa madam Dinshi ta tsaya ya dawo tunda takamaimai besan dalilin bugun kofar ba.
Koda ya dauki mukullin kofar gidan be fita ba Saida ya leka dakunansu SARFRAZ don ya tabbatar basu suka sashi a wata matsalar ba. Ai kuwa tarar dasu yayi duka suna barci, sosai yaji daɗi don yasan wani abun ne daban ba matsalar su SARFRAZ bace.
Yana buɗe ƙofar ya tarar da Wani ɗan saurayi tsaye gaba daya bakinshi da hancinshi sun kumbura sunyi sumtum, dayake farar fata ne duk sun haɗe sunyi jajir.
Gefen shi kuma wani Babban mutum ne tsaye shima, amma ga dukkan alamu babban yaron ne, sai kuma kauya tsaye a gefe rungume da file.
Haidar ka Banu tunda Aayaan ya aɗaka da Sarfraz, don ma Allah yasa yana hanya. Koya zaku ƙare dasu oho.
*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*55*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Gaishesu haidar yayi cikin sakin fuska don a tunanin shi patient aka kawo mishi,
Kicin kicin da rai baban yaron yayi tare da cewa "niba gaisuwa ta kawoniba, gurin baƙinka nazo.
Cike da mamaki haidar yace "me baƙi na zasuyi maka?
"Nazo ne su faɗa min abinda yasa suka kamamin ɗana sukayi mishi wannan ɗanyen dukan Kamar sun kama ɓarawo.
Murtuke fuska haidar yayi don yaga alamun rainin wayau a lamarin, shidai yasan sarfraz be taɓa dukan waniba, a dai abarshi da tsokanar fada da shiga sharo babu shanu, idan kuma tayi ƙamari shine ya haurawa Mutane cikin garden yayi barnar fruit Yadda yaga dama.
A yaushe su baƙin nawa sukayi mishi wannan dukan? Haidar ya tambaya don tabbatar da zargin su da yake yi nason shiryawa SARFRAZ sharri.
"Ko cikakkiyar minti talatin ba'a yiba, don yana zuwa gida ya faɗa min mukayo nan.
Wata dariyar rainin hankali haidar yayi "sannu da ƙokari, to ku sani ƙaryarku bata samu shiga ba Saboda Ni Na dawo dasu cikin gidan nan da hannuna kuma tunda suka shiga ɗakunan su basu fitoba domin Yanzu haka barci ma sukeyi, kuma koda ma ba barcin sukeyiba babu Yadda za'ayi su fita waje saboda na rufe ƙofa da mukulli..
Cikin Muryar kuka yaron yace "Wallahi shi ya bigeni.
Shidai haidar cewa yayi "na gama magana, domin Babu Yadda za'ayi yara basuyi abuba ace sunyi, dayaga Kamar basu yarda ba sai ya shiga ciki ya taso SARFRAZ ya tawo dashi.
Koda SARFRAZ yagansu saida zuciyarshi ta buga, amma dayake cikakken ɗan basaja ne sai ya maze beko nuna alamar rashin Gaskiya ba.
"Sarfraz inaso ka kalli wannan yaron dakyau, shin ka taɓa ganinshi?
"Gaskiya ban taɓa ganinshiba! Wani abunne ya faru? Cewar sarfraz cikin dakiya.
Girgiza Kai haidar yayi "you see ni dama nasan basu bane, kawai Idan zaku tafi ku tafi ni zan shiga gida inada abin yi, rantse rantse yaron ya Fara yi tare da cewa "baba na rantse da Allah shine ya bigeni, Allah ba karya nakeyi ba. Shi dai baban yaron ganin abinda ya faru sai ya yarda Cewa ba SARFRAZ bane, dakawa yaron tasawa yayi tare da cewa "Wuce muje! Nasan kila Wasu ka tsokana sukayi maka haka, shine Ni zaka zo kamin karya donka haɗani da makwabcina.
Shikam sarfraz Har ya ƙosa yaje daki don yaba bandi labarin cewa yaudai haidar ya shigammusu faɗa.
Shi kuma haidar mayar da kofar yayi ya rufe tare da wucewa nashi ɗakin...
Aikam SARFRAZ na shiga daki ko zama beyiba ya fara ba bandi labarin abinda ya faru, harda kwatanta wa bandi yadda yaron yake rantsewa, shi ko bandi babu abinda yakeyi inbanda dariya...
Hassu kumi tuni barcin gaske ya tafi da ita saboda cikin magungunan da aka bata a asibiti akwai na Barci....
Saukar C.A kenan a British airport, dayake dama Anan suke ajiye jet ɗin idan aiki ya kawosu England ɗin, wayarshi ya ciro yayi dialling ɗin number haidar Amma Abin haushi switch off, cab ya tara yace takaishi St Leo's Street.
Cikin minti 15 suka iso ƙofar gidan haidar, sallamar me cab ɗin Aayaan yayi sannan shi ya nufi cikin harabar gidan, murmushi sosai ne a Fuskarshi na farincikin yau zasu samu lokaci mai tsawo Tare Da ɗan uwanshi su tattauna, kuma yasan yanzu in'sha Allah bazasu kumayin nisa da juna ba.
Ya buga kofar yafi sau goma amma babu alamun an tawo buɗewa, tsaki Aayaan yayi don wani zubin be cika son jiraba barin idan Akwai abinda ya ƙagu ya samu, "Nasan sunanan tunda ga motar haidar ɗin a compound"
Ɗan ƙara bugawa yayi saboda yayi tunanin ko basa kusa, dadai yaga alamun baza'a buɗeba sai ya samu wata kujera a cikin varendar ya zauna.
Sai tsaki yakeyi gashi ya ƙara kiran haidar ɗin still numbershi a kashe.
Ta cikin gidan kuwa haidar yanajin bugun, koma ince duka suna ji, amma gani sukeyi ko wannan mutumin ne ya dawo shiyasa suka ƙi zuwa su buɗe.
A ƙalla Saida Aayaan ya kwashi Kusan minti 40 zaune a gurin amma babu su babu alamar su, duk haushi ya cika muyshi ciki, Gashi ya kira Number Aseey switch off, ta Nawaz kuma bata daukaba.
Kuma miƙewa yayi da nufin ya ƙara bugawa idan basu buɗeba sai ya tafi asibiti ƙilan suna chan.
Bugu uku yaji alamun an tawo buɗewa, aikuwa take yayi kicin kicin da rai "wato dama sunanan shine suka shanyani a titi.
SARFRAZ ne ya buɗe ƙofar, ai kuwa yanayin ido biyu da Aayaan ya daka tsalle ya rungume shi, "Naji daɗin dawowarka yayana🥰, gaskiya yinin yau Ni mai Sa'a ne.
Haidar dake tsaye gefen dining ne yaga sarfraz yaƙi dawowa, ai da sauri ya nufi kofar don kada yaje Mutanen dazu ne suka dawo.
Yana isa yaga SARFRAZ ya ruƙunƙume Aayaan kamar zai koma cikin shi, ai kam da sauri shima ya washe baki don yasan wahalarshi akan SARFRAZ tazo ƙarshe.
"Yoo! yaushe ka iso? Ai ya kamata ka sanar damu kafin ka tawo ko don mu haɗa maka wata kwaryakwaryar walima.
Balla mishi harara Aayaan yayi "Gaskiya haidar wayarka batada amfani, ace kana Matsayin babban likita amma ka kashe waya hakanan, wato kai kazo gida ka kwanta baka tunanin al'ummar da suke jiranka.
Kyalkyalewa da dariya haidar yayi "Auwo ashe kaima kaji yanda naji sanda naita kiranka inaso na faɗa maka SARFRAZ ya tashi amma taki shiga, Nima yau Ranar hutu nace don haka dole na kashe waya kada a dameni.
Murmushin takaici kawai Aayaan yayi, tare da riƙe hannun SARFRAZ wanda sai yanzu ya sakeshi suka nufi cikin falourn.
Babu kowa amma Akwai alamun ana kitchen ne, tunda ga kamshin abinci nan ya cika faloun.
Ɗaya daga cikin sofa ɗin da suka zagaye falourn Aayaan ya samu ya zauna tare da cewa SARFRAZ "Bro kawomin ruwa!
Hassu ce ta fito daga corner da dakinta yake sanye da hijabi, (tasa hijab ɗinne saboda kada haidar ko matar shi suga kumburin da wuyanta yayi.