← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 112

Sashe 29

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sarfraz ne ya bani"
Sakin mata hannu yayi saboda wani irin zafi da yaji kirjin shi nayi, "right wai waye sarfraz ɗin nan ne? Nifa da mukaje gidanku babu wanda yayi maganar wani sarfraz, ke kaɗai kawai akace kin tawo ba tare da wani ba.
Kuma Ni sam na manta ban tambayesuba, amma bari na kira wayar baffa in tambayeshi yanzu..

"No don Allah kada ka kirashi" Nawaz tace jikinta naci gaba da rawa.

"So tell me who is he idan bakya so na kirashi.
"Dalibinane" tace a takaice

Wani abu Aayaan yaji ya tokare mishi wuya ga idonshi har wani yaji yaji yake mishi, shi kanshi ya rasa meyasa hakan.
Da kyar ya Iya daurewa yace "look Nawaz ba wasa mukeyi ba please be serious waye shi?
"Allah dalibinane"
"Idan shi dalibinki ne ya akayi ya baki zobe kuma kikasa a yatsanki? Sannan kuma ya akayi kuke tare dashi sanda zakizo garinnan?

Hawayene ya zubo mata a fuska "bazaka ganeba Wallahi ɗalibinane kuma zoben da kanshi ya bani sannan sanda zan tawo shima kakanninshi anan suke zai zo gaishe dasu shine muka taso tare.

Zubar hawayen Nawaz yana dai dai da kamar an zubawa Aayaan garwashi a cikin zuciyarshi.

"Look bance kiyi min kukaba, daga na tambayeki? So i am sorry kawai dai ina so na sanine saboda zoben yanada dogon tarihi a rayuwar mummy na.

"Mummy kuma? Nidai sarfraz ne ya bani Wallahi ba na mumy na dauka ba, bana daukar abin mutane .

"A'a calm down mana meyasa kike da saurin rudewane? I don't mean na mummy kika dauka, dama ai zoben guda biyu ne, amma ki bari yanzu zan kira mummy sai tayi Miki bayani...

Tafin hannunshi ta kalla ganin ya cire bandage ɗin sai ciwon yayi wani irin pink, wani zafi taji a zuciyarta ganin yanda yakeshan wannan azabar a dalilinta.
"I am very sorry naga ciwonka is still new, sannu yana maka zafi koh?

"No never mind, Kim manta ni soldier ne? Ai wannan ba wani abu bane aguri na, Wallahi mantawa ma nakeyi dashi...

Kallonshi yakai kan muhsien wanda ya miƙe ƙafa a kasan tile's sai cin chips ɗin shi yake yi hankali kwance...
Tsugunawa yayi dai dai shi "Superman babu magana ne?
Chuno baki yayi "bakai bane kaketa yiwa Aunty faɗa, kumani ina sonta saboda Nima tana sona.
"Oh no ba faɗa nayi mata ba, kawai dai na tambaye tane.

"Ba har tears naga suna rolling a cheeks ɗinta ba, kuma babu ruwana dakai tunda kasa Aunty na tayi kuka....

Janyo shi yayi zuwa kirjinshi "i am sorry bazan kuma ɓatawa Aunty ranta ba.
"To ka bata hakuri" muhsien yace yana ci gaba da cin chips ɗin shi hankali kwance.

Juyawa Aayaan yayi daidai Nawaz ya haɗa hannunshi guri ɗaya "Aunty Don Allah kiyi hakuri bazan kuma ba...

Da sauri Nawaz tace "please ka bari yaya Aayaann "
Ji yayi kamar babu wanda ya kaita iya pronouncing ɗin sunanshi.
Murmushi muhsien yayi "yauwa to yanzu Nima na hakuri, ɗauke Ni muje falour to.

Sunkutar shi Aayaan yayi suka nufi falour, sai sannan Nawaz taji ta fara samun nutsuwa.
Ta rasa meyasa idan Aayaan yana kusa da ita take neman natsuwarta ta rasa ga wani uban tsoronshi da takeji sannan zuciyarta tayita bugawa.

A hankali take tafiya ta fito daga kitchen ɗin rikeda ragowar chips ɗin muhsien.

Aunty kinga uncle ya cinye min chips ɗina Koh? Muhsien yace yana kwaɓa fuska kamar zaiyi kuka...

Ganin Aayaan zaune kusa da Aseey yasa ta gane yar uwar shice saboda sunyi kama sosai.
A ɗan ɗarare tace ''kayi hakuri ga ragowar na ɗauko maka"
Ɗan gaban Aseey ta ƙarasa ta risina "ina yini Aunty! Ɗazu bamu gaisaba....

Cikin fara'a Aseey ta amsa da lafiya sister ya hidima da muhsien?

"Haba dai Aunty wace hidima kuma, wallahi Ni sabgar yara sam bata damuna...

Aseey kuma jin wani irin kaunar Nawaz tace tana bin jikinta.... Murmushi tayi ai muhsien ɗin ne akwai rigima me iya mishi sai Allah...

Hamma tayi alamun tana jin yunwa "ohh gaskiya yunwa nakeji wai ina kuku ne?

Aayann wanda tun dazu bece komai ba amma yanajin abinda sukeyi sai sannan yace "ta tafi ganin gida.

"Yanzu don Allah shine tunda nazo baka faɗa minba? Aida tuni nayi mana girki....

"Wallahi Aunty Nima fa yunwar nan nakeji babu yanda sanyi ne, kuma mummy bata tashiba nasan da tuni ta girka mana wani abuu.

Kallonshi Nawaz tayi "nayi girki fa tun dazu, yana dining Nasha ma ai kunci!

Ai da gudu Aayaan da Aseey suka nufi Hanyar dining ɗin har suna bangaje muhsien...

Aayann ya riga zuwa, beyi wata wata ba ya bude warmer ɗin ai take wani aroma mai daɗi ya bigi hancin shi.
Daya warmer ɗin ya buɗe itama yamballs din suma sai kamshi sukeyi.

Plate yaja ya zuba fried rice din da yawa sannan ya dora yamballs uku a gefe...

Dinner bowl ya buɗe don ganin meye a ciki, ai kuwa coleslaw yagani yaji uban mayonnaise da ketchup....
Ƙara ɗiba yayi ya zuba sannan yaja kujera ya zauna, diba yayi ya kai bakinshi...

Wow wani irin daɗi ne ya ziyarci kwakwalwar shi har saida yaji kamar kunnenshi na motsi....
Aseey sai korafi takeyi "shine ka zuba iya naka baka zubamin nawa ba..

"Sorry kawai ya iya ce mata yaci gaba da tura abincin.

Itama dai ta gurin Aseey abinda ya faru kenan, amma ita ta kasa boyewa
"Nawaz zo"

A hankali Nawaz ta ƙaraso dinning area ɗin "gani Aunty"

Wata lomar Aseey ta daɗa kaiwa baki, Saida ta cinye tace "sister da gaske ke kikayi girkin nan?

Murmushi tayi "eh Aunty Ni nayi"

" Masha Allah shin a taba faɗa Miki in iya girki me daɗi? Hmm wallahi abincin nan yayi mini daɗi fiye da yanda kike tunani..

Itadai Nawaz sai murmushi takeyi, goga Aayaan be kula suba sai faman aikawa tumbin shi yake yi.

Cikin falourn Nawaz ta koma ta barsu suna cin abincin...

Aayann haka yabar abincin badan ya ƙoshi ba sai don ya gama cika tumbin shi fam....

Nawaz na kitchen tana kokarin haɗawa muhsien smoothie taji kamar anyi mata rumfa, ile kuwa Aayaan ne tsaye a bayanta yana murmushi.
Da ƙarfi kirjinta ya buga, sai kuma jikinta ya dauki rawa....
Duk abinda take yi Aayaan na kallonta, matsowa ya daɗa yi yazo gaf da ita sosai, har yanajin numfashinta na sauka a wuyanshi

Ita kuwa Nawaz ji take kamar zata shiɗe saboda fargaba ga kuma kamshin turarenshi daya gama cika mata hanci.

Cikin soft husky voice dinshi yace "meyasa kikejin tsoro na? Koni dodo ne?

Wani miyau nte gishiri Nawaz ta haɗiye amma ta kasa cewa komai...

Ƙasa yayi da kanshi dai dai kunnenta yace "ki faɗa min Ni dodo ne? Ko zan cinye kine?

Tsigar jikintane taji duka sun buɗe ai da sauri tace "a'a wallahi kai ba dodo bane don Allah kayi hakuri ...

"Meyasa zaki bani hakuri? Kinyimin laifi ne?

Cikin rawar murya kamar zatayi kuka tace "Ni dai don Allah kayi hakuri kuma ka matsa kusa dani...

Murmushi yayi ya Kara matsawa kusa da ita saura ƙiris jikinsu ya haɗu...
Ihu Nawaz ta saka da karfi haɗe da rufe idonta, domin ji tayi numfashinta na sama na ƙasa...

Aseey dake falour a zaune ta taso da gudu ta shigo kitchen ɗin "meya far......

Makalewa maganar tayi a maƙogoranta ganin Aayaan tsaye gaban Nawaz, ita sam batasan sanda ya shiga kitchen dinba, tasha ma Nawaz ɗin ta ƙone ne.

Malam matsa ka bani guri, kazo kana tsorata yar mutane, hannun Nawaz ɗin ta kamo "zo muje sister rabu dashi kinji...

Falourn suka koma dai dai mummy ta fito "daughter meya sameta naga kamar jikinta na rawa, mummy tace tana nufosu

"Wallahi Mummy Aayaan ne yaje ya firgita ta"

"Ayyah sorry my dear, ki barni dashi zan saɓa mishi sosai.....

Fitowa Aayaan yayi daga kitchen ɗin rike da smoothie ɗin da Nawaz ta haɗawa muhsien yana sipping.

"Zo nan mara kunya! Me kayi mata? Mum tace tana zabga mishi harara

Murmushi yayi "mummy ni banyi mata komai ba, kawai dayake banyi sallama bane shine ta firgita.

Kallonshi Nawaz tayi cikin mamaki "kashe mata ido yayi hade da ɗaga mata gira yana yi mata wani shu'umin murmushi...

"To wallahi kada ka kuma, kaji na faɗa maka, Kafi kowa sanin nawaz amana ce a gurina.

"Wallahi Mummy Aayaan mugune, kada ki yarda, Nima don yayar shice shiyasa babu yanda ya iya dani....

"Ke yayar shice" cewar Nawaz da ita kanta batasan sanda maganar ta kufce daga bakinta ta fito ba ..

Dariya Aseey tayi "Wallahi Ni yayar shice, kada ki ganshi gabjeje haka shekara uku na bashi.... Kinga shekarata 36 shi kuma 33....

Murmushi Nawaz tayi "tabɗijan wai da gaske kike? Ita tama manta da abinda ya faru gulma na cinta aciki.....

Aayann ne yace nifa banason raini, aiko makaho ya shafa zai gane gaskiya....

Jin Muryar Aayaan da Nawaz tayi ne ta dawo hayyacinta, ai da gudu tayi hanyar dakinta

Sukuwa suka kwashe mata da dariya.....

Guri mum ta samu tana ci gaba da murmushi, domin abinda Nawaz tayi ya bata dariya...

Shiko Aayaan gefen mummy ya zauna yana cewa mun i have a Great news for u, amma saikin biya.

" Zan biya ko nawa kayi demanding!

"Mum na samo Miki biyuninki" cewar Aayaan yana kallon mummy

Da sauri mummy ta mike "Aayaan put joke apart, don Allah da gaske kake?

"Mum wallahi dagaske nakeyi?

Itama Aseey mikewa tayi "bro kasan mummy bata wasa da wannan maganar don Allah da gaske ne? Kada fa ka bata mata rai ...

Hannun mummy ya kama yace "zo muje mummy ki gani da idon ki...

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 32*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️

Hanyar dakin Nawaz yabi da mummy, suna zuwa ya buɗe security yana riƙe da hannun mummy suka shiga dakin...

A zabure Nawaz ta miƙe ganinsu duka, gani takeyi kamar tayi musu laifine ..

Direct gaban Nawaz ya ƙarasa, ya zuwa ya kamo hannunta yana nunawa Mummy "kin ganshi mummy, Wallahi shine domin bazan taɓa mantawa da zoben nan ba, saboda kullum saikinyi magana akansa.
Chapter 29 · 0% Book details