Sashe 92
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Toshikenan in'sha Allah bazan baka kunya ba..."
"Subhanallah! Na manta da magungunan dana siyo Miki a Mota, sai kuma Babbar kyautar ki ta shayar dani Ni'imtacciyar madara natsuwa da kikayi."
Duƙar da kai Nawaz tayi "Nidai don Allah ka dena bani kunya"
"Wai wannan kunyar yaushe zata barni na huta ne?" Cewar Aayaan yana ɗaukarta
Fita sukayi daga ɗakin inda ya rufe kofar suka shiga cikin lifter, be sauke taba har saida ya saka ta a cikin mota sannan shima ya zagaya ya shiga gefen driver.
Drawer ɗin cikin motar ya buɗe ya ciro wata polythene bag madaidaiciya, wani madaidaicin akwati ya ciro a cikin jakar ya buɗe, wata Irin sarƙa ce a ciki sai walwali takeyi Saboda fararen duwatsun da aka ƙawata ta dashi, haɗe take da Abin hannun da ɗan kunne sai zobe.
Kusa da ita ya matsa sosai sannan ya zame mayafin kanta, sarkar ya fara sa mata sannan ɗan kunnen sai Abin hannu da zoben.
Sosai sarkar ta birge Nawaz sai kallon zoben takeyi tana murmushi, yana gama sa mata tace "Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi ya ƙara budi ya rufa asiri, ya tsare kullum sannan yasa kafi haka"
Toshe mata baki Aayaan yayi tare da cewa "ke kika fara min kyauta shiyasa nima nayi Miki, kinga kenan ba gode min zakiyi ba, and kuma tun tuni nace miki komai nawa nakine! No need ki riƙa min godiya" Amma sosai yaji daɗin addu'ar datayi mishi har cikin zuciyarshi...
"Hmm yaya kenan! Ai ko ajiya na baka idan na amsa dole na gode maka, balle bansan dashiba ka bani"
Magungunan ya cirar mata sannan a ɗauki ruwa a beverage pack ɗin dake cikin motar ya buɗe mata, a baki ya kafa mata ruwan Sannan ya cire ya zuba mata maganin ya kuma maida mata da ruwan bakinta.
Saida ya tabbatar tasha ruwan da yawa yadda maganin zai fara aiki da wuri Sannan ya ajiye robar ya maida hankalinshi gurin kunna motar, tuƙi yakeyi a hankali dayya hannunshi yana rike dana Nawaz wanda ke gefenshi.
Ita dai tana zaune ne kamar gunki, takarda ta gani a cikin ledar da Aayaan ya ciro dan akwatin sarkar daya sa mata, ɗaya hannun da Aayaan be riƙe ba tasa ta ciro takardar tana dubawa.
Receipt ne na sarkar daya siyan mata, kallon takardar Nawaz take tana kallon Aayaan, duk hankalinta ya tashi ta zaro ido waje "yaya naga ansa 2.5million a jikin receipt ɗin nan"
"Menene"
"Wai kana nufin haka ka siyo sarƙar nan?"
"Eh what happen?"
Ɗaya hannun dake cikin nashi ta kwace tare da cewa "yaya million biyu da rabi fa"
"Yea! Da kyar ma na samu wannan ɗin shiyasa kikaga na daɗe ban dawo ba inata yawo inason wadda tafita tsada amma ban samu ba."
"Amma yaya million biyu da rabi fa! Marayu nawa za'a farantawa rai da wannan kuɗin? Shine ka siyo min Abin wuya kawai inyi ado dashi?"
Haƙiƙa Nawaz tana birgeshi sosai, tausayinta da sanin ya kamata ɗin ta yana birgeshi "okay to yanzu kada ki damu, zan samu lokaci saiki lissafa min marayun da kikeso a farantawa rai, but wannan nakine saboda faranta nawa ran da kikayi, diamond ne da pearl aka haɗa su guri ɗaya, kece farkon Wadda ta fara sa irinta a wuyanta, Royal design ce"
Shiru Kawai Nawaz tayi tana duba wannan lamari, "to waishi Aayaan wane irin mutum ne? Haƙƙin shine fa ya amsa, amma sai wani gode mata yakeyi yana mata hidima"
Shima ganin Nawaz ɗin tayi shiru, sai yaci gaba da tuƙinshi yana Nazarin yanayin ta, sam bata ɗauki duniya da zafi ba, yasha ganin abokanshi sun siyo wa matansu abu amma memakon suyi godiya sai su kushe abun suce beyi musu ba ko suce tsohon yayi ne ko kuma ba irinshi suke so ba.
Amma ita Nawaz ko me ya bata saita nuna mishi farincikin ta a fili da ɓoye, ta riƙa godiya kenan tana mishi addu'oi.
Sun ɗauki lokaci me tsawo a haka inda Aayaan ya kamo hannunta ya matsa a hankali, ɗago kanta tayi suka haɗa ido, da sauri ta kauda kai domin kunyarshi take matuƙar ji.
"Sweetheart tunanin me kike yi?"
"Rayuwata nake duba yadda ta koma sanadin SARFRAZ"
"Inaso in samu lokaci na musamman ki ƙara bani full labarinki, inaso naji usulin wacece MADINATUL MUNAWWARAH wato my beloved wife"
"Kada ka damu anytime ka shirya just let me know, zan faɗa maka komai In'sha Allah"
Murmushi yayi ya jinjina kai Alamun ya gamsu da maganar ta, wani gurine babba iya ganinka, a kewaye yake da fencing wire dai Babban gate shima na wire, ciki Aayaan ya shiga da motar yaci gaba da tafiya, Saida yayi tafiya mai nisa a cikin gurin Sannan yayi Parking dai dai wata kasan bishiya.
Shiru gurin babu alamun kowa illa allon koyar harbi me suffar mutum wandanda da suke jere a jikin wani gini. "Dear kinga inda zan koya miki Harbin, hope zaki bani haɗin kai, kuma pls ki cire tsoro"
Murmushi Nawaz tayi, ita dai tunda yace mata zai koya mata harbi taji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, amma tanata danne wa saboda kada ta ɓata mishi rai.
Bayan sun fito ne ya zagaya baya ya buɗe ya buɗe Boot tare da ciro wani akwati baƙi me faɗi, bindigogi ne kala kala acikin da bullet harda su salansa, zare ido Nawaz tayi tare da cewa "yaya duka wadannan naka ne?"
"Yea nawane! Ko kema kinaso in baki?"
"Eh" Nawaz tace tanata murna, shikam Aayaan ganin Irin farin cikin da Nawaz keyi yasa yake jinshi cikin annashuwa, sai murmushi yakeyi.
Komai ya haɗa na bindigar inda daga bisani ya janyo Nawaz cikin ƙirjinshi Tare Da ɗora hannuwanta saman bindigar sannan ya ɗora nashi daman nata, sosai yake nuna mata Yadda zatayi, sunfi ƙarfin awa ɗaya suna abu ɗaya.
Sakinta yayi ya miƙa mata bindigar Tare Da cewa harba mugani, Rufe ido Nawaz tayi zata harba, da sauri ya dakatar da Ita tare da cewa "sweetheart buɗe idonki! Idan kika rufe idonki bakisan inda zaki harba bullet ɗinba, buɗe ido Nawaz tayi a hankali Sannan ta saita bindigar tare da harba kunamar, a daidai 80degree bullet ɗin ya faɗa, wani irin tafi Aayaan ya sakin mata tare da fitoo yana cewa well-done, gwajin Farko, gaskiya naji daɗi sosai, nasan ko sati baza muyiba zaki fini iyawa.
Sosai Nawaz taji wani kwarin gwuiwa ya shigeta, take ta nemi tsoron datakeji ta rasa saboda yadda taga Aayaan yaji daɗi sosai.
Maida komai yayi cikin akwatin Sannan ya maida Boot ɗin, beverage pack ɗin dake ajiye a cikin motar ya ciro waje tare da ɗaukar carbonated drink yanasha, Hannu Nawaz takai zata dauka itama, ai da sauri Aayaan ya ɗauke kwandon, miƙo mata milk drink yayi tare da cewa "Ai daga yau babu ke babu kuma shan carbonated drink har saina gama observing ɗin danake yi a kanki," Amsa tayi bata ce mishi komai ba.
Ƙaramin carpet ɗin dake cikin motar ya ciro ya shimfiɗa ya zauna a kai, janyo Nawaz yayi saman cinyarshi Sannan ya ciro wayarshi dake aljihun wandonshi.
Number Aseey yayi dialling, ringing ɗin farko ta daga da jaraba "Malam meye na kirana, aini na yafe ka tunda baka damu daniba, ko ka nemeni, na rasa Yadda zanyi da raina duk sanda zan kiraka switch off kuma kai kaki kirana, idan na kira Mummy itama ta rufe ni da faɗa wai ina so na dameku, fisbilillah yanzu fa kusan kwananku arba'in amma ko ka nemi wani, wai dama haka honey moon ɗin yake? Baka tunanin ka shiga haƙƙin Sis Nawaz ɗin kummm.......
"Calm down! Calm down, yanzu bansan wane laifi zan amsa ba, don Allah kiyi haƙuri, Nasan nayi laifi amma gani nayi nima babu wanda ya kira yaji ya muka sauka shiyasa nima ban kira kowa ba"
Sanyi jikin Aseey yayi, tabbas Aayaan be taɓa yin hakaba, kuma su kansu be kamata ace ya tawo da ƴar mutane amma babu Wanda ya kira yaji ya suka sauka, "bro to amma dakaga ba'a kiraba kai ai saika kira?"
"Nifa gani nayi kamar an gaji dani ana neman kai danine"
"Kai sweetbro! Wane irin an gaji dakai? Yanzu fa wani irin muhimmanci ka kara a idon kowa, kazama magidanci, where is my sis?"
"Gatanan bama tajin daɗi "
Daɗi ne ya kama Aseey tana tunanin ko ƙaramin laulayi Nawaz ta fara " bata wayar"
A kunne ya kanga wa Nawaz wayar Tare da cewa "yi sallama"
"Assalamu alaikum, barka da Rana Aunty"
"My dear nayi kewarki sosai, fatan kina lafiya? Ya ƙarfin jikin naki?
"Nima haka Aunty, nayi kewarki sosai da Muhsin, yana ina?
"Be dawo daga school ba"
"Don Allah Aunty yaushe zakizo"
"Idan kun gayyaceni, kuma nace miki ya jiki baki bani amsa ba"
"Aunty ba wani ciwo bane, zazzaɓi ne fa kawai kuma naji sauki!"
"Okay to Allah ya ƙara sauƙi, and kuma yayi maza ya kaiki Asibiti kada ayi sake"
Haka dai suka ɗanyi hira inda Aseey ta daɗa jaddadawa Aayaan cewa ya tabbatar ya kira Mummy da Ummin Nawaz don jineya suke!"
Yana kashewa ya kira wayar mummy akashe, kiran wayar Ummin Nawaz yayi, koda ta ɗaga da sallama kasa amsawa yayi sai ya miƙawa Nawaz wayar tare da cewa "Ummu ce"
Fashewa da kuka Nawaz tayi tare da cewa "ummina nayi kewarki sosai"
"Jimin shirme! Yanzu Madina kuka zaki kirani kina Min"
Mummyn Aayaan dake gefenta ne ta amshi wayar tare da cewa "my dear meya faru? Ko wani abun yayan naki yayi Miki?"
"Ina wuni Mummy "
"Lafiya Lau my daughter, ya kike?"
"Lafiya Lau Mummy "
"To faɗa min meyayi Miki"
"Mummy wallahi bemin komai ba, Kawai dai nayi kewar kune"
"To stop crying! Zansa ya kawoki konji"
"To mumy Nagode "
Miƙawa Ummin Nawaz wayar tayi, namma dai nasiha tayi mata suka ɗan tattauna Sannan akayi sallama suka kashe wayar.
"Kuka kuma dear?
"Kayi haƙuri, Wallahi inajin muryarta naji kukan yazomin.
"Okay to stop cryingy, ɗauki madararki ki shanye"
Cigaba dashan madarar tayi tana ɗan tunani ahankali. Saida ya tabbatar ta shanye sannan ya goge mata baki da tissue ya bata Ruwa.
A gurguje suka biya Asibitin haidar ɗin inda Aayaan ya faɗa mishi Irin magungunan da yakeso aba Nawaz.