← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 112

Sashe 53

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tagumi Nawaz tayi! "Gaba ɗaya ta rasa abinda keyi mata daɗi, ita yanzu ya zatayi ne, me zatayi a rayuwarta indai akace ciki ne da ita? Ta shiga Uku kenan! To amma idan cikine dole na Aayaan ne.

Wayarta ta ɗauko ta kunna, tana gama booting message ɗin Aayaan ya shigo, ko gama karantawa batayiba ta maida wayar ta kashe....

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 50*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

Ajiye wayar tayi a gefen kujera tana jin haushin kanta, "danasan zanga wannan message ɗin wallahi da bazan ma buɗe wayar ba, shi dama be manta daniba? Yana chan yana jiran indawo saboda yaci gaba daga inda ya tsaya.
Wata zuciyar ce tace "Anya Nawaz bakya ganin yanzu ya kamata ki koma, kinga koda ma Cikin gareki hakanan zai amsa"

"Amma Nawaz kin taɓa jin inda mace tayi ciki dare ɗaya? Kuma da Aayaan ya kwanta dake dole sai kin sani sakamakon babu wanda ya taɓa kwanciya dake" abinda kwakwalwata ta faɗa mata kenan.....

Ajiyar zuciya Nawaz tayi tana kai kallonta kan Nafisa, Sannan tace "wai ina yaran namu ne? Yauma Bangansuba?

"Suna gidan surukaina, kinsan da safe idan zai fita yake kwashe su ya tafi dasu tunda kinga yanzu hutu akeyi.
"Allah sarki, yana ƙoƙari shima wallahi. Nawaz tace tare da miƙe kafafuwanta a saman kujera.

"Yaushe zaki tafi? Ina fatan dai zaki min yini Koh?

"Eh zan jima sai wajen uku za'a zo a daukeni, kinsan a gidan inna talatu na sauka.

Shiru Nafisa tayi alamun tunani Sannan tace "wallahi Nawaz ban gane taba!

"Inna talatu fa ta hayin ojo, wadda muke zuwa gidanta har muyi wainar fulawa.

"Allah Sarki! Cemin zakiyi innarmu, fatan tana lafiya?
"Lafia lau take, tanama gaisheki.

"Ina amsawa wallahi, inkin koma kice nima ina gaisheta dakyau dakyau don walllahi inna Akwai mutunci.

Tashi Nafisa tayi "zakici wainar fulawa in soya mana, Wallahi faɗar sunanta da kikayi sai naji inason ci.
Miƙewa Nawaz tayi itama "muje kitchen ɗin muyi tare. (Nikam cewa nayi mayyar girki)

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Aayaann na kwance yana tunani kamar yadda ya maida kanshi yanzu, kullum tunani gashi ya zama so silent, wayarshi ce tayi kara alamun notification ya shigo.
Kamar kar ya duba sai kuma Wata zuciyar tace duba mana! Ƙila Alkhairi ne.
Janyo wayar yayi a kasalance, ai zumbur ya miƙe ganin message ɗin daya Turawa Nawaz yayi delivering, da sauri yayi dialing ɗin number, Amma switch off.
Jiyayi Kamar yayi wurgi da wayar don takaici, komawa yayi ya zauna yana tunanin mafita, so yake yi ya kama Nawaz a hannu don yaci burin rama abinda tayi mishi, amma ta wata fuska daban.

Wani shu'umin murmushi ya yayi tare da cewa "yarinya wasa kikeyi dani, amma na wuce da yanda kike tunani, Allah ma yayi zakikai haka kina soyamin zuciya ne shiyasa idea ɗin bata zo mini ba.
Wata number yayi dialling, Hello ola! pls ka duba email ɗinka zakaga Wata Number, track The number and send the location details to my email.

Komawa yayi ya kishingiɗa yana murmushin cin nasara, yasan Yanzu damuwar shi ta kusa zuwa ƙarshe, tunda anga sarfraz Yanzu kuma ga Nawaz zata bayyana itama...

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Zaune Nawaz take a Saman dadduma ta idar da sallar zuhur, zuciyarta tayi nisa a tunani "ko me Aayaan yakeyi Yanzu oho, ina mum da mummy, Yanzu a Wane matsayi suke kallona? Ajiyar zuciyar tayi Sannan ta miƙe tana ninke daddumar.

Dayake sai gurin karfe biyu da rabi tayi sallar saboda basu gama wainar da wuriba, ɗan gyara jikinta tayi saboda tasan Mai napep ya kusa zuwa, sosai sukeyin hura ita da Nafisa Anan Nafisa take cewa:- Nawaz don girman Allah ki riƙe mijinki hannun dubu dubu, wallahi samun irinshi a wannan ƙarnin sai an duba, kuma Kinga ga kyau ga ilimi ga kuɗi, to kowannan ya isheki izina, wasu fa zaki gansu zaune gidan mazajen nasu amma walllahi su suke ci da kansu kuma babu Wanda ya sani, balle kuma wadda ta samu ana ci da ita.

Kinga kuwa ke Saidai kice Alhamdulillah! Kuɗin fa da Ni kaina ya bani rannan dana ƙirga dubu Talatin da hudu na gani, Kinga ko iya haka aka tsaya Nima ba yagi arziƙi...

"Tabbas haka ne, to amma Yanzu Meye mafita?" Abinda NAWAZ ta raya a zuciyarta kenan, sai kuma tace to yanzu fa ya kamata kafin nayi aure nasan inda SARFRAZ yake.

Sallama akayi daga kofar gida, ai kuwa nafisa ta tashi ta leka, da sauri ta dawo tana cewa mai ɗaukar kine yazo, "Yanzu rubutamin number ki anan, cewar Nafisa tana mika mata biro da takardar data ɗauka saman fridge.

Bayan ta rubuta ne, Nafisa kece wa "to ƙawata Allah ya raba lafiya, sai na kiraki, a gaishemin da muhsien shida baban shi.

Ita dai NAWAZ batace komai ba Tunda ta lura Nafisa tayi nisa bata jin kira, duk da dai tasan Aayaan ne yaja mata.

Har bakin kofa ta rakata Saida suka tafi sannan itama Nafisa ta koma gida cike da kewar Nawaz ɗin.

Hira mai napep yaketa janta ta ita, ita kuma nawaz taƙi sakin jikinta, daga eh sai a'a, kuma dai taga alamun mutumin Babu ruwan shi, sai dai ta lura mayen surutu ne ...

Har kwar gidan inna ya kaita Sannan sukayi Sallama ya tafi bayan yace idan zata fita ta duba junction zata ganshi, sai tayi mishi magana zai Kaita duk Inda takeso...

Da fara'a Nawaz ta shiga tare da cewa "Inna Barka da gida! Nabarki ke kaɗai Koh? Murmushi inna tayi "a'a Nawaz ai baki ma daɗe sosai ba don hudu fa batayiba har yanzu, ki shiga ki chanza kaya saiki fito kici abinci idan kuma wanka zakiyi to.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

👀👀👀 London na leƙa Don ganin wace wainar ake toyawa, ai kuwa sarfraz na gani kwance cikin wani dakin Glass an rufe ko ina, alamu ma ya nuna ba'a bari a shiga sai dai idan doctors ne, a cewarsu wai ba'a son hayaniya tayiwa mutum yawa, saboda aikin nasu Zai iya dawowa baya,

Hassu na hango sanye da doguwar riga Pink colour ta yafa mayafinta, a yanda hassu ta koma Yanzu da ace banyi dagaske ba Bazan gane taba. Zauna take ta zubawa cikin ɗakin ido, shikuwa bandi Yana tsaye akanta yana cewa "kiyi hakuri hassu in'sha Allah zaiji sauki, ki tashi mu tafi, Kinga tun ɗazu nake miki magana amma kinmin banza... Don Allah kiyi hakuri kinji! In'sha Allah zai warke saurai.

Kunnen Uwar shegu tayi, itafa bazata tashi ba, haka kawai ansaka Mutum cikin daki sannan A ki bari kowa ya gansa, Nifa na faraa gajiya,

Da bandi yaga abin nata da gaske ne, sai kawai ya samu guri a gefe ya zauna, yana jiran duk sanda ta gama sai su tafi, kasancewar gidan Babu nisa shiyasa ma Madam haidar take bari suke zuwa da kansu wani zubin...

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

E-mail ɗin da ola ya Turo mai yake zaune yana dubawa "lallai sweetheart! Ashe tana zaria, hmm Allah ya tona miki asiri, gobe asubanci zanyi na koma Zaria, kuma in'sha Allah bazan dawo ba Saida ke.....
Sakayau yaketa jinshi yau, ga Wani farinciki dayake cinshi a zuciya, harya ƙosa goben tayi yaga Yadda za'a ƙare.

Shiru yayi da bakinshi be faɗawa Mummy ba saboda kada tace zata bishi, ko Aseey yaƙi fadawa saboda tsaro, yafison sai dai su ganshi da Ita Kamar yadda aka tsara na sarfraz.

Bayi ya shiga yayi wanka, kwalliya sosai yayi Saboda farin cikin dayake ciki, tshirt ce fara mai v neck sai wando Blue Black na jeans, sosai kayan suka ƙara fito da kwarjinin shi, ga faffaɗan kirjinshi da damtsenshi (Idan kunsan John Abraham actor ɗin India wanda yayi Film ɗin "Rocky handsome" to sak jikinsu iri ɗaya, saidai Aayaan yafishi kyau a fuska)

Yama manta da zuwan wata Ashley, hankali kwance ya fito falourn yana tafiyar shi mai jan hankali don hannunshi ɗaya yana cikin aljihu while ɗayan kuma yana shafa ƙasumbarsa dashi.

Ji yayi an rungumeshi ta baya, da sauri ya waiga don Ganin ko waye, Aikuwa idonshi ya sauka a fuskar Ashley sai murmushi take yi mai.
Shikam Aayaan saiya ganta kamar dodo, take ya murtuke fuskarshi kamar besan Wani abuba waishi murmushi "ke sakeni!!! Aayaann yace yana tureta Daga jikinshi Sannan ya ƙara da cewa "ke mahaukaciyar Ina ce? Wai so dubu nawa zance kidena taba Min jiki ne?

Mumy da aunty Aseey ne suka fito Jin Muryar Aayaan Yana faɗa, "lafiya kake wannan faɗan haka?" Mummy ta faɗa tana kallon Aayaan ɗin alamun tana jiran ya bata amsa..

"Mummy saboda hauka fa ina tafiya shi ne tazo ta rungumeni ta baya, kuma tun kafin jikin ya zama mallakin Nawaz nake ce Mata banaso, amma ita taki bari salon ta kashe Min aure.

Tsaye Mummy tayi tana kallon Aayaan, ita kuwa Aseey Sai dariya takeyi, Don tasan halin Aayaan Akwai jisgi kuma ya faɗi hakane don ya ɓata ma Ashley rai.

Itakam Ashley kamar ta mutu, duk ta haɗe fuskarta, ta chuno baki da wargajejen laɓɓanta zuciyarta Kamar zatayi bombing.....

Yasan mamakin abinda ya faɗa ne yasa Mummy yin shiru shiyasa shima beyi wata wata ba ya fice daga falourn, can garden ya ƙarasa tare da zama a saman wata kujera da aka haɗa ta da katako, wayarshi ya ciro Sannan ya shiga gallery, photunan Nawaz ya nuno yana ƙare mata kallo Tare Da yin wani shu'umin murmushi...
"Allah yana sona shiyasa ya bani basirar dazan nemoki cikin ruwan sanyi, wallahi nasha wahalar Rashin ki kusa dani amma komai yazo ƙarshe bi'iznillah....

Wani nishaɗi yakeji Kamar itace zaune a gabanshi..... Ya daɗe a haka Sannan ya koma contact, dialling Number Daniel yayi "Daniel inform your colliques to get ready tomorrow morning by 7am we will travel to Zaria.

"Okay sir" abinda Daniel Yace kenan Sannan ya yanke wayar.

Number haidar ya kuma kira don yaji ya jikin sarfraz ɗin, Saida suka ɗanyi waya mai tsaho Sannan ya kashe ya kira Farouk, namma dai sun ɗan tattauna Sannan sukayi Sallama.

Tunanin Abinda Zai Kai mata yakeyi dukda uban tarin kayan daya jido mata daga Abuja, ga kuma sarƙar Gold ɗinta.
Rasa mai Zai siya yayi, sai kawai ya yanke cewa insun fita goben ya duba abin da ya kamata.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Chapter 53 · 0% Book details