← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 112

Sashe 7

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idon safraz yayi ja, Yana Kallonta amma yakasa magana...

Sakamakon wani takaici daya rufeshi "wai ace Kamar shi mummy bata yarda dashiba.....

Cewa tayi "wato ka maidani mahaukaciya koh?
Inata magana amma kayi banza Dani koh?

Wani siririn Hawayene ya zubomai a ido d'aya, "tunani yake azuciyarshi, Dana bar yarinyarnan a wajensu da Allah ne kadai yasan abinda zai faru da ita.... Wai kuma na taimaketa abin kuma ya juya kaina...

But I know Allah wouldn't allow this to happen cuz i did it with a good intention.....

Mummy ce ta dawo dashi daga tunanin dayakeyi "wato safraz munkai gejin dazan rika yi maka magana kanajina kuma kayi banza Dani koh?

Tunda yaji tace safraz yasan ranta Yayi mugun baci, domin bazai iya tuna last data Kira tsuran sunan shiba......

Ahankali ya iya had'a Kalmar "yi hakuri mummy"
Murmushin takaici mummy tayi "Hmmm hakuri ya rage naka ai,

Yanzu fad'a min a Ina ka daukota? Kuma wacece ita?

dakyar safraz yace "bansan taba kuma bansan ko wacece ita ba......

Hanyar d'akin shi mummy tayi "bari ni naje na tambayeta dakaina kaga saitamin bayani..... Sannan ta shige d'akin .....

Nitsewa safraz yayi a cikin sofa, gaba d'aya zuciyarshi na mishi tukuki, saboda baiyi abinda ake tuhumarshi akaiba.... Kuma mai tuhumarma mummy....

Tarar da ita tayi tana yinkurin tashi, da alamu tanajin jiki....
Taimaka mata mum tayi ta Mike....

A Gefen gadon ta zauna ta Dafata "Sannu kinji "
Ya jikin naki?
A yanayin tsoro nawaz tace "Dan Allah a Ina nake?

Cewa tayi kada ki damu babu abinda zai faru dake kinji?
D'aga Kai nawaz tayi alamun "to"

mummy ce tace zaki iya magana 'yata?

Ahankali nawaz tace "eh zan iya"

please inaso duk abinda zan tambayeki ki fad'a min gaskiya kinji?

nawaz ta d'aga Kai had'e da cewa "to "

Mummy ta gyara zama tace "my dear inasone ki fad'a min abinda ya faru Wanda kika Sani a matsayin abinda zaki iya tunawa na karshe..

Nawaz tace to "Amma Dan Allah sammin ruwa nasha!
Dasauri Ta Mike ta fita falour tayi dispensing din ruwa a dispenser. sannan ta koma ciki da sauri

Mika mata tayi "gashi "
Amsa tayi Tasha rabi sannan ta ajiye ragowan a Gefen bed side drawer...

Abinda zan iya tunawa shine Daren jiya
Na fito daga bayi na shiga d'aki kawai sainaga Maza biyu suna mana dubedube.
nace su waye ?
Sainaga sun nufoni zasu kamani danaga da gaske ni sukeso su kama shine Nayi Waje da gudu..
Haka Suma suka yi ta bina a baya tundaga layinmu har saida mukakai captain street, sannan ne suka kamani....
Dayan ya rike hannuna da karfi yanda bazan iya kwacewaba, shi kuma Dayan ya Fara yagamin Riga...
ganin Dagaske zasu wulakantani yasa na ciji Dayan a hannu, dayaji azaba shine ya sakeni...
na juya da gudu naji nayi Karo da wani abu mai karfi to Daganan bazan iya tuna komaiba .....

mum ce tace "ko zaki iya siffantamin kamannin wadanda suka biyoki..
nawaz tace "Eh nasan d'aya ma domin yana zuwa gurin uwar gidan abbana kuma sunanshi Tasiu, Amma bansan Dayan ba, kuma dukansu daka kallesu zaka gane y'an shaye shaye ne......

shiru mum tayi sannan "tace to ke ina mum dinki lokacin da abin ya faru?

mamana batanan ta tafi maiduguri a ranar. Sai dai umma kuma koda zantayin ihu bazata kula ni ba.....

Mummy ce tace "I'm sorry my dear in a pity face 🤦🏽‍♀.....

Wata damuwa ce Mai karfi ta kama mummy domin tasan a yanayin maganar yarinyar babu safraz a ciki kuma batada masaniya ma akanshi ,
Nayi kuskure Dana dauki mataki banyi kwakwkwaran bincike akaiba!
to yanzu me zancewa safraz? Ko taya zan iya kallon shima?
Tashi tayi tace wa nawaz bari nazo ƴata!
Da sauri nawaz tace, to amma don Allah kafin ki tafi waya kawoni gidannan?
Mummy tace "Dana ne ya kawoki, kuma yana falour, haɗe da fita daga ɗakin.......

Kallon gadon da take Kai tayi "hmm dagani masu kudine wadannan, domin ji gadon ji closet d'in ma, daga carpet harda yanayin curtains d'in daka kalla kasan masu uban tsadane....

hakadai taci gaba da Kalle Kalle tana wasi wasi...

SAFRAZ.....

A inda mum tabarshi anan ta tarar dashi Yayi tagumi, wuceshi tayi domin batasan me zata iya ce mishiba.....

Bayan mummy ta fita ya mike ya shiga ɗakin.
azaune ya tarar da ita a Kan gado tana tunani "tsayawa yayi ya zuba mata ido, domin itama batasan ya shigo ba...
"wow! Gaskiya she's very beautiful and charming ...
Kalli fuskarta so innocent, da nazo ne na koreta saboda zargin da mummy tayi min akanta Amma na tabbata bazan iyaba...
may be Allah just gave me my own crush......

Kusa da ita ya karasa, a gaban gadon ya tsuguna.
Charming queen me kike tunanine haka?
Firgigit tayi ta kalleshi, wani mamakinne ya daɗa kamata...
safraz tagani a gabanta Yana mata murmushi "meya faru?
naga ure some how scared, just be calm nothing will happen to you, coz you're safe here
Muryarshi da taji yasa ta dada tabbatarwa shine, ga kuma kamshin turarenshi dataji "oud Al azhar"
Murmushi tayi mai tace "nagode safraz, wai dama kaine ka kawoni nan?

cewa Yayi Eh nine "and please kinsan nine?
Sai sannan nawaz ta tuna cewa safraz be taba ganin fuskartaba "sai cewa tayi ai kaima ka sanni koh?
A'a wallahi ni bantaba ganinkiba sai dai muryarki is familiar, amma sai dai na kasa tuna inda nasan muryar.....

cewa tayi nasanka kuma ka sanni amma Kace baka sanniba....

shikenan tunda bazaki tunamin a inda nasankiba kawai yanzu ki faɗa min wadanda suke binki su waye?
Bashi labarin duka abinda ta fadama mummy tayi...

shiru safraz yayi "wato dama sun cemin kishiyar mamantace tasasu.

Amma kuwa zan musu rashin mutunci wallahi, dago da idonshi Yayi ya zubawa kirjinta ido....
shan jinin jikinta tayi takai hannunta gurin donjin meye, ji tayi rigar ya matseta sosai...
Sai sannan ta tuna a yanayin da take "dukunkune hannunta tayi a kirjin ta sauke kanta kasa...

karamar wig d'in dake katane ta karasa cirewa , gashin kanta ya baje sakamakon babu kitso a kan..

duk gashin ya rufe mata fuska, Hannu tasa ta kawar da gashin tayi baya dashi, sannan ta haɗa fuska Kamar zatayi kuka "ni Don Allah kadena kallona haka!
Ajiyar zuciya sarfraz yayi ya mike ya fita....
a faloun shi ya zauna a Saman center table Yana tunani "meyasa?
Nashiga in tambayeta sunan ta kuma in tambayeta abubuwa da yawa Amma na kasa, sai wani cikamin fuska datayi....
Hope kada ta daukeni da wata manufa....

Nawaz.......

zaune take a takure tana tuna irin kallon da safraz yayitayi mata "wai dama shi wannan safraz d'in rashin kunyarshi ba iya baki bace?
Ji yanda ya zubamin ido, sannan mamakin yanda be ganetaba take, kuma ya akayi ya fita da dare harya kawota gidansu.....
sannan dole Yayi rashin kunya masu kudine sosai Ashe.....
tana wannan tunanin ya kuma shigowa ya wuceta, closet ya bude
wata sky blue ɗin shadda ya ciro Sai daukar ido takeyi, Zanenta Dara Dara "getzner"
Sai wani milk ɗin Yadi ya kuma cirowa ya haɗa guri ɗaya ya fita dasu a hannunshi....

be Kalli inda takeba sakamakon yanda yaga ta takure guri ɗaya....
sasan daddy ya shiga Yayi wanka ya shirya, sannan ya dauki shaddar da key d'in Motarshi yabar gidan...

A shagon abasu colour yayi parking, cikin shagon ya shiga yana murmushi.....

da sauri abasu colour ya taso "oga sarfraz ya akayi baka kirani nazo da kaina...
murmushi sarfraz yayi "inani Ina kiran oga mai bamu colours gida, ai Sai a kamani kuma a Hana belina.
murmushi abasu colour Yayi "oga sarfraz akwai barkwanci "toya gida ya Al'amura ya makaranta?
Lapia lau abasu, dama dinki na kawo urgent inzan samu?
Haba oga sarfraz ai kasanma zaka samu....
Wane iri za'a yi maka?

murmushi sarfraz yayi "dama daddy ne ya siyomin shaddar nan last week yace amini malinmalin da y'an ciki...
to ni kuma na chanza Shawara, inaso adinkamin yadi biyar sauran yadi biyar d'in kuma a dinkawa Wata kanwata.

Abasu colour yace ai babu damuwa , sai in dinka maka naka ita kuma Sai dini ya dinka mata, hope kazo da gwajinta?
Sarfraz yace Aa banzo dashiba "Amma dai tsahonta Kamar wannan Dana Ke gani a shagon nan kwanaki, Amma saidai gaskiya wannan tafita kirji da kwankwaso.....

abasu colours yace Kodai itace madam ɗin?
Daria SARFRAZ yayi "Aikuwa kasan abu a duhu

cemishi Yayi zai zo ya Amsa da Karfe 3:00pm
kudin ya bashi sannan Yayi mishi sallama ya tafi....

Hafab closet ya tsaya ya nemi takalmin couple box ya siya takalman iri daya komai da komai saidai shape d'aya banbanta na Mace Dana miji..

fruit ya tsaya ya siya, sannan ya wuce gida....

20minutes earlier......

mum naga ta fito daga dakinta rike da gyale ta shiga ɗakin sarfraz, a zaune taganta.
daughter na zo muje parlour kici abinci kisha magani koh?

nawaz tace to mummy, nagode da kulawar da kikayimin Amma inaso naje gida.
to indan wannan ne kada ki damu sarfraz na dawowa Zansa ya kaiki kinji.....

Shiru tayi "to Amma dakin bari zanje dakaina.
dakyar mum Ta shawo kanta ta yarda akan zata bari ya dawo saiya kaita.....

dinning mummy ta jata, sannan ta shiga kitchen ta kwaso warmers d'in abincin da vacuum d'in ruwan zafi....

tea Ta had'a mugs biyu sannan ta zuba mata potatoes wages da fried egg Sai raising bread a gefe ta ajiye a gabanta...
ita kuma nawaz mamakin girman parlourn takeyi da uban kudin da'aka kashe kafin a hadashi......
tanaso Ta Kore kwarkwatar ido gashi kuma tanajin nauyin Matar....

ta yi shiru tana wasa da yatsunta taki taci abincin, mummy tace my dear kici mana!
Ko inzo inyi feeding dinkine?

Dasauri nawaz tace "no thanks zanci yanzu, cup din ta dauka, takai bakinta kenan taji sallamar safraz,
Dasauri Ta ajiye a table tayi shiru.

Kujerar dake kusa data Nawaz ya ja ya zauna "Barka da safia mum, saboda Sam sarfraz baya iya yin fushi da mummy.
Barka safraz, Ina kaje da safennan?
mummy naje gurin tailor ne...
cewa tayi ok, bari nayi serving dinka, zuba mishi tayi shima ta tura mishi gabanshi...
Chapter 7 · 0% Book details