Sashe 34
Safraz Complete Hausa Novel · about 7 min read
Koda Nawaz ta idar da Sallah samun guri tayi a daddumar ta jingina da jikin gado tanata azkhar saboda an kusa kiran magriba domin basuyi sallar da wiriba saboda zaman da sukayi .
Duk abinda take yi Aseey na lura da ita, duk sai takejin babu daɗi sam... Kowa yasan ƙaddara ce, kuma dole dama hakan saiya faru tunda Allah ya riga ya tsara Hakan tun tuni .
Tashi tayi ta fita zuwa falour, dakin sarfraz ta shiga Domin tanaso suyi magana ita da Aayaan..
Cikin Sa'a kuwa ta tarar dashi a zaune a saman gado yana kallon photo album ɗin sarfraz...
Zama tayi suka kalla tare, abin gwanin ban tausayi domin Saboda sarfraz kaman zaiyi magana...
Tabbas kuma sun tabbatar sarfraz ɗan uwan sune, domin babu waybda zai kalli hoton sarfraz kuma ya kalli Aayaan be rantse cewa kaninshi bane harta da hancinsu iri dayane da yanayin gyaran gashinsu da saje, saidai sarfraz yafi Aayaan fari Kasancewar shi farin mahaifiyar shi ya dauko sukuma su Aayaann Golden skin Ɗin babansu suka dauko.
Gyara photon Aayaan yayi ya maidasu inda suke "sis Wallahi inaso naga SARFRAZ, kuma Insha Allah saiya zama soja har dai yana raye.
Nine kullum dama cikin yin korafin Ni Banda kani to ashe Allah ya bani ban saniba...
Murmushi Aseey tayi "Allah dai ya Bayyana mana shi, Nima wallahi ina son naganshi....
"Hmmm sis ƴan uwa daɗi garesu, yau kawai da mukaji gaskiyar lamarin yar uwar mummy duk mun samu salama a ruhinmu. Kuma yanzu mun ƙara yawa ko babu komai zamu bigi kirji mu nuna daddy muce dan uwan mummyn mune, wanda ada bazamu iya ba.
Murmushi Aseey tayi "Maganar ka gaskiya ce, Allah ya kara datar damu.
"Ameen " Aayaan yace yana mikewa
"Koma ka Zauna inaso muyi Magana....
"Komawa yayi ya zauna yana Maida hankalinsa zuwa gareta...
""Aayann inason muyi Magana ne akan Nawaz.
Ɗago kai Aayaan yayi ya kalleta.
"Ko kaine a matsayin da Nawaz take yanzu dole saika rikayin abinda take yi , saboda she is feeling guilty of her self, Gani take itace sila, so yanzu ina sone mu hada kanmu Wajen Bata farinciki...
Bazai yiwu mu rabota Daga Wajen iyayenta ba mu kuma ta riƙa chutuwa ta sanadin muba.
"To sis yanzu me kikeso ayi?
"Yauwa my bro, inasone anjima bayan anyi sallar isha'i ku fita tare kaɗan kaita guraren maybe taɗanji sauki, amma fa ba wai ƙiri ƙiri zaka nuna mata ita zaka kaiba, zakacene muhsien zaka kai amma kai baka san guraren ba tazo ta raka ka.
Murmushi Aayaan yayi, domin yaji daɗin wannan al'amarin "to sis Insha Allah.....
Hirar sanda suna makaranta suka farayi har zuwa sanda aka kira magrib Sannan Aseey ta koma daki, shi kuma Aayaan ya shiga bathroom don ɗauro Alwala, sai murmushi yakeyi shi kadai.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
"Baffa meya faru da ita? Bandi yace tare da maida duka hankalinsu gurin baffa
"Eto na lura da wani abuu kamar wannan saurayin ya kamu da ciwon mantau ne fah!
Sarkewa Muryar bandi tayi har Saida ya ɗan yi tari tukuna yace "baffa kana nufin ciwon mantau ne ya kamashi?
"Eh gaskiya abinda nake tunani kenan amma bari mugani.
Gyara zama baffa yayi ya kallon sarfraz sannan yace "ɗan samari yaya sunan ka?
Gab dashi sarfraz ya matso sai murmushi yakeyi "sunana sarfraz,
"Yauwa to shekarar ka nawa?
Shiru yayi yasa yatsanshi a baki alamun tunani sai daga baya kuma yace "bansaniba, na manta Amma idan naje gida zan tambayi mummy gobe saina faɗa muku...
"Shikenan Wallahi ta tabbata, Sai dai nashi akwai sauki saboda bata ɗin din din bane, ana sa ran idan yaga wanda ya sani zai tuna komai Insha Allah... Kuma yanzu zai iya gyaruwa ma saboda kwakwalwar shi tazama kamar ta yara duk abinda kuka nuna mishi shi zaiyi kuma idan kukace ya dena zai dena...
Hassu dake gefe tun ɗazu tana jin jawabi sai yanzu ta sako baki "baffa kana nufin wai yanzu mu kaɗai ya sani?
"Tabbas a Yanzu kafin ya koma dai dai babu wanda ya sani irinku... Don haka nake rokon ku akan gobe ku kawo minshi satu mu kaishi asibiti aduba ko za'a iya yimishi wani abu, sannan wannan ciwon nashi a wankeshi a bashi magani dukda naga kayi kokari sosai ciwon yayi kyau be kwaɓe ba....
Sallama sukayi da malam suka shiga ciki suka gaida adda balki sannan suka fito sukayi hanyar gida .....
Garin yai duhu saboda magriba tayi hakan yasa sarfraz sai wani shigemusu yakeyi alamar tsoro, gashi duk yayi biyinsu a girman jiki,
Aikuwa da hassu da bandi sun gane me yake nufi Kawai sai suka mamaye shi suka kwasa a guje ....
Ganin suna gudu shima ya kwasa ya bisu a guje yana ihu " wayyo Allah na wayyooo kujirani tsoro nakeji..... Irin dai yanda yara sukeyi a duhu.....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Kowa na zaune a falour amma banda Nawaz domin har yanzu ta kasa sakin jikinta, koda tayi sallar isha'i sai kawai tayi wanka ta nemi guri ta zauna tayi jugum, babu abinda keyi mata yawo a zuciya face fuskar SARFRAZ sanda yake yi mata shakiyancinsa....
Sanda zasu fita falour Mummy tayi tayi da Ita akan ta fito amma sai tace suje tana zuwa...
Achan falourn Aayann ne ya fito sanye da kuftan farare ɗinkin ya amshi jikinshi tsaf Gashi ya ɗora hula baƙi da ratsin fara, sai yayi wani sharr dashi Kamar ka saceshi ka gudu....
Zama yayi yana tunanin yanda zai kira Nawaz ganin babu ita a falourn..
Aikuwa be gama gyara zamanba muhsien yayo kanshi da gudu yana cewa "Uncle please muje ka kaini wajen shan ice cream...
Wani irin daɗi Aayaan yaji ganin abin yazo mishi cikin sauki..
Amma sai yace wa muhsien ɗin sorry ka bari sai gobe sai muje Koh?
Ai nan fa ake yinta muhsien dagewa yayi ya fara ihu yana cewa "Wallahi kuma babu ruwana dakai, kuma mun ɓata kada ka kumamin magana...
Nan hankalin kowa ya dawo kansu, Mummyn sarfraz ce tace "bazai yiwu ba maza ka tashi ka kaishi inba hakaba duk mu ɓata dakai, yazaayi ka ɓatawa mijin mu rai...
"Mummy ai bansan gurinba kin manta mu baki ne?
Duk Neman baasin da kakeyi don karkaje saika ce, Aseey jeki kira Nawaz kice ta tawo da mayafinta, ita saita raka ka ...
Shi dai Aayaan sai murmushi yakeyi be taɓa tunanin abin zaizo minshi da sauki hakaba...
Koda Nawaz ta fito jikinta duk babu kwari , fuskarta tayi fayau da ita alamun tana cikin damuwa.
Mummy ce tace mata "my daughter don Allah ki taimaka ki raka su muhsien Apple white ko chicken republic, oh koma dai inane wai zesha ice cream ne..
Gaban Nawaz ne ya yanke ya fadi jin tare da Aayaan zasu fita, tana kallonshi tunda ta fito yake kallonta ga turarenshi dake damunta duk ya cika mata hanci...
Mikewa Aayaan yayi yai waje domin yaga alamar idan ya zauna Nawaz zata iya rusa minshi lissafi.
Kamar ta rusa ihu haka tayi musu sallama ta fita...
A cikin mota ta tatar dasu suna labari, bata kulasuba illah dai ta samu gefen me zaman banza ta zauna..
Shima be kula taba Kawai ya ja motar yayi hanyar fita, saboda dama tun sanda ya fito yayi magana da securities dinshi aka kada su biyo shi ..
Saida ya fita bakin titi tukuna ya kalli Nawaz "ranki ya daɗe ina zamubi?
Nuna mishi tayi da hannu batare data kalleshi ba, sanin halin datake ciki yasa Aayaan be matsa mataba ba sam...
Sunzo wucewa ta PZ muhsien ya hango hotunan waya nanma wata rigimar ya dauka "Uncle pls ka siyan mini ipad kaga Mummy ta bata tawo min da nawa ba, pls uncle .
Cewa yayi "to zan siyan maka bari muyi Parking, bayan yasamu guri yayi Parking ne ya Kalli Nawaz kema zo muje!
Batace komaiba ta buɗe kofa ta fita, suma suka fita ta ɗaya kofar.
A tare suka shiga cikin store ɗin..
Namfa me store ɗin ya fara turo musu wayoyi kala kala yana cewa "Alhaji asiyanma maman boy mekyau Wadda idan ta shiga cikin kawaye za'a gane kanaji da Ita....
Dummmm gaban Nawaz ya buga da ƙarfi, atare suka kalli juna sai Kuma tayi saurin kauda kai...
Murmushi Aayaan yayi "Kamar kuwa kasan dama inaji da ita sosai, yanzu zaɓar mini wadda tafi ko wacce tsada a shagon nan saika sa mata sim card da memory sai kuma ka samomin babbar ipad itama me kyau....
Kirjin Nawaz ne ya fara dukan uku uku daya saba yi mata, duk saitaji tsayuwar ma ta isheta....
Wani matashi ne yazo shiga cikin store ɗin saiya kalli su Aayaann da muhsien sai kuma ya kalli Nawaz, murmushi yayi yace gaskiya Madam yaronki yanada kyau sosai, ko don saboda dake yayi kama ne?
Kai kuma Alh, baka lura Madam bata da lafia bane shine ka fito da ita,
Ƙasa ƙasa yayi da murya sai kuma yace "ko an samar wa da boy Kani ne ko kanwa?
Ai fuuu Nawaz ta fita daga store ɗin tayi hanyar mota, tanajinsu sunayi mata dariya
*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ🎀🎀*
*Episode 36*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️
Koda ta shiga motar ta zauna abin bai fita a ranta ba, inbanda hauka daga ganin mace da namiji sai akace dole su zama mata da miji, babu tunanin yaya da ƙanwa.