← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 112

Sashe 32

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

NAWAZ tayi mamakin yadda taga Aayaan yana Sallah cike da kwarewa, domin ya bata hakkin ta, daga farillanta har sunnoninta...
Hakan yasa takeson taji cikakken tarihin wannan ahalin.

Mummy ke ce mata "Nawaz kika gujemu, maimakon ki zauna muyi hira shine kika gudu donma Aayaan yaƙi yayi tukin wai zai tayaki zama.

Murmushi Nawaz tayi "Mummy babu komai banaso nasa ku matsu ne .
"To shikenan Nawaz babu komai.

Nan suka zauna sukaci snacks ɗin da nawaz ta hada musu sukayi toping da yoghurt ɗin da Aayaan ya siyo musu.
Ɓangaren Nawaz kuma kasa ci tayi sai ice cream ɗin tasha
Duk yadda mummy ta matsa mata akan taci cewa tayi ta ƙoshi.

Haka suka koma cikin motar kamar yadda suke da, shiru Nawaz tayi bugun zuciyarta na ƙara gudu, duk fargaba ta kamata..

Tsaff Aayaan ya lura da halin da take ciki amma besan yanda zaiyi mata ta saki jikinta ba..
Wata dabara ce ta faɗo mishi ya ɗago daga kishingidar da yayi ya gyara zama sannan yace "sister Saudiyya nakeso inje, zaki biya min?

Duk da tashin hankalin da Nawaz take ciki hakan be hanata yin guntun murmushi ba "nikam yaya Aayaann ina naga kuɗin dazan kaika makkah?

Daɗi Aayaan yaji ganin murmushi shimfiɗe a fuskar Nawaz, ya rasa meye alaƙar shi da ita da yasa sam bayaso ya ganta cikin damuwa...

Murmusawa shima yayi "kefa yanzu billionaire ce, kinsan fa president da kanshi yake neman ki, ga Governor da Minister's, kefa yanzu shugaba ce take Miki baya Yakamata nariƙayi..

Murmushi kawai takeyi tama kasa cewa komai,
Chan kuma ta numfasa tace " Ni awa? pls ka rufa min asiri babu ruwana, kuma naga kai har harbinka akayi a hannu amma kaƙi faɗawa kowa.... Kuma duk ta sanadi na, sannan Ni babu abinda nake bukata agurinsu duka don banaso a baza fuskata a duniya,

"Meyasa" Aayaan yace a takaice
"Saboda tsaro mana, kuma babban reason Dina ma shine kada fuskata ta zama unvaluable kowa ya Sanni, gaskiya hakan zaimini ciwo idan akace duk kafar sadarwa da jaridu akwai photona...

Saida Aayaan ya tafa mata, saboda yadda ta nuna kishin kanta ƙarara, kuma yaji daɗin yanda tasan ciwon kanta....

A haka yaketa janta da hira, sosai yayi ƙoƙari ya cire mata damuwar da take ciki.
A cikin hirar da sukeyi ma ya ɗan tsinci abu masu yawa daga cikin rayuwar ta, hakan kuma yasa ta ƙara shiga ranshi sosai,

Ganin anzo kwangila fly over yasa Nawaz tace idan drivern ya sauka ƙasa zamu bar babban titi mubi cikin gari...

Magana Aayaan yayi wa drivern, cikin girmamawa ya amsa yanayin ƙasan gadar a hankali .

Ta cikin G.R.A sukabi sannan suka fito tacikin anguwarsu wato gaskiya layout, Aayaan kanshi daya saba da ganin gidajen alfarma amma Saida unguwar ta burgeshi saboda anyi gine-ginen ne cikin kwarewa da tsari, gasu madaidaita.

Dai dai Kofar gate ɗin su SARFRAZ Nawaz tace "Anan za'a tsaya.

Parking ɗin motocin duka sukayi sannan kowa ya fito.
Tsaye Nawaz take ta kasa shiga gidan, zuciyarta sai bugun tara tara takeyi...

Mummy ce ta matsa kusa da ita tace "my daughter be strong, we are with u, all will be fine Insha Allah.
Aseey ta kalla taga ta ɗaga mata kai alamun eh, shima Aayaan ɗaga mata kan yayi haɗe da yimata murmushi...

Tana nufar gate ɗin ya zuge da kanshi, a tare suka shiga cikin amma banda securities ɗin Aayaan..

Saida suka ɗanyi tafiya sannan suka ƙarasa ƙofar main falour ɗin
Alarm Nawaz ta dannan ba'a daɗe ba saiga mummy ta bude kofar, wata irin ƙara ta saki haɗe da rungume Nawaz tana janta Cikin faloun " Alhaji dama na faɗa maka SARFRAZ ɗina be mutu ba, kaga Nawaz!!!
Tausayin mum ne duka ya kamasu, cikin sanyin jiki suka bi bayan mumy zuwa cikin faloun...

Nan kuma shima daddyn sarfraz ne yaketa nuna mummyn Aayaan jikinshi na rawa...
Kowa tsayawa yayi yai turus yana kallon ikon Allah
Zubewa daddy yayi a kasa warwas.

Cikin tashin hankali duka sukayi kanshi aguje...
Nawaz ce tayi karfin halin ƙarasa wa kitchen ta ɗebo ruwa..

Da sauri Aayaan ya amshi ruwan ya fara yayyafawa Daddy yana Tofa mishi addu'oi..
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan ya fara buɗe idon shi a hankali, da sauri ya maida idon ya rufe Sakamakon fuskar mummyn Aayaan daya gani.

Gyara mishi zama Aayaan yayi Amma zuciyarshi cike take fam da tambayoyi da damuwa kala kala..

Mummyn sarfraz ma haka domin sam bata fahimci Abinda ke faruwa ba...

Sai bayan Kowa ya natsu Mummyn Aayaan ta gaishe da mummyn sarfraz tare da gabatar da kansu a matsayin yan uwan Nawaz, da kuma yiwa Mummyn sarfraz ɗin Allah ya kyauta akan abinda ya faru,
Anan ta sanar mata suma babu yanda basuyiba akan neman sarfraz ɗin Amma basu ganshiba.....

Murmushin da yafi kuka ciwo mummyn sarfraz tayi "Ni inaji a jikina sarfraz yana raye kuma Insha Allah, Allah zai bayyana mana shi.

Tare duka sukace "Allah yasa hakane Ameen. Allah ya bayyana shi.

Kuma Gaskiya tunda Allah ya nunamin Nawaz naji Kashi 40 daga cikin damuwata ta ragu...

Daddy yana nan zaune inda yake bece ƙala Ba, kuma be buɗe Ido ba.

Aayann ne yacewa Mummyn sarfraz "mummy don Allah kiyi wa Daddy magana akan ya taimaka ya bude idonshi ya kallemu, bamusan me mukayiba, muna rokon afuwa...

Gabanshi ta karasa tana yi mishi Magana ƙasa ƙasa, da kyar Daddy ya iya buɗe baki yace "kareemah waccan matar da kike gani itace maman sarfraz pah...

Jin maganar da Daddy ya faɗa yasa kallon kowa ya dawo kan mummyn Aayaan, itama kanta take kallo, sannan Daga bisani tace "A'a wallahi banida Wani ɗa daban, yarana uku kuma daya ya rasu sannan Shima ba sunanshi sarfraz ba...

Itakam Nawaz miƙewa tayi"wai wane sarfraz ake magana ne?

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

SARFRAZ bawan Allah anacan ana rikici a kanshi shiko yana nan baima san a wace duniyar yakeba, marabarshi da gawa numfashi da yakeyi....

Yauma kamar kullum hassu ce gefenshi ta zauna tayi jugum tanata kallon yatsun hannunshi, wanda daga bisani takai hannunta ta riƙe, addu'a taketayi idonta na zubda hawaye,
Bandi beje kawoba yau saboda yanaso yaje can kauyen gabansu dan ya nemowa sarfraz maganin dazai wanke mishi ciki kila su samu yayi bayan gida...

Hassu ce ta fito da gudu daga cikin bukkar still tana nuna mishi cikin bukkar tana ihu..

A rude bandi yace "hassu menene yasameta?

Ta... Taa...

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 34*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu*✍️

"Ta motsa hannun ta kuma ta ƙifta ido" abinda hassu ta iya faɗa kenan Sannan ta kama hannun bandi tana janshi.

Binta ya riƙa yi kamar igiya har cikin bukkar,
Mamakine sosai ya kama bandi ganin SARFRAZ yana yunƙurin tashi daga kwancen dayake, kasawa yayi saboda ciwon dake kirjinshi ga kuma tsami da jikinshi yayi Saboda daɗewa da yayi a kwance na ƴan kwanaki ...

Da sauri bandi ya rikoshi yana gyara mishi zama, itako hassu sai faman tallan MacLean takeyi.

"Sannu kinji" bandi yace yana zama kusa dashi
Yatsina fuska SARFRAZ yayi Yana yiwa bandi kallon rashin sani.
Ki kwantar da hankalinki zamu faɗa miki ya akayi kikazo nan.

Yatsina fuska SARFRAZ ya kumayi "i want to poo"
Kasan cewar bandi yadanyi karatu yasa ya gane i want Yana nufin ina son,, da sauri yacewa sarfraz ɗin "mekiso" domin shi sam baisan me poo yake nufiba..

Miƙewa yayi ya fara mammatse ƙafafuwan shi Yana Daɗa cewa i want to poo.

Hassu ce tace "bandi kasan fa ta daɗe batayi bayan gidaba koshi take nufin zatayi?

Ai da sauri bandi ya riƙe shi muje, ƴar guntuwar bukkar da suke zagayawa ya kai sarfraz yace to shiga kiyi anan..

Kwalalo ido sarfraz yayi waje "Wallahi Ni ban iya Anan ba, shiru bandi yayi Yana tunanin ta ina zai fara..

"Kiyi hakuri kiyi bayan gidan anan bansan inda zan kaiki kiyi ba,
Tsalle sarfraz ya fara yana cewa wayyo mummy ya matseni!
Duk bandi ya ruɗe "ki shiga kiyi don Allah akwai maganar da nakeso muyi.

Zuwa gaban bandi yayi yace " to cire min wandon.
Zip ɗin babban wandon ya zage mishi sannan ya cire mishi ya barshi da karamin boxers ɗin, shidai bandi mamakine ya kasheshi yanaso yayi tunanin meyasa sarfraz yakeyi abuu irin na ƙananan yara amma kwakwalwar sa ta kasa saboda cunkushewar da tayi da mamaki.

Yana kallo sarfraz ya shiga Cikin bayin da kyar yana gunguni, guri ya samu a gefe ya zauna yana jimamin Wannan al'amari...

Ba'a fi minti Shida da shigar sarfraz bayin ba ya fara cewa "Nagama"
Kasaƙe bandi yayi yana mamakin wannan wane irin abuu ne, ko dama su haka yan Birnin sukene, komai sai anyi musu...

Ruwa bandi ya ɗebo a ƙaramar gora ya mika mishi "gashi ka wanke"
Ihu sarfraz yasa akan cewa shi sai dai bandi ya wanke mishi, nanma ansha fama kafin SARFRAZ ya yarda ya wanke da kanshi sannan ya fito daga bayin yana hararar bandi "Babu ruwana dakai, kuma bazan sammaka biscuit dinaba idan daddy ya siyomin"

Mutuwar tsaye bandi yayi yana kallon sarfraz.

"Anya meye wannan takeyi hakane?
Bin sarfraz yayi a baya.
Shikam sarfraz na karasawa ya tarar da hassu zaune tayi tagumi, ƙarasawa gurinta yayi "aike zan san miki biscuits ɗina amma bazamu ba wancan ba ko? Yana nuna bandi...

Murmushi hassu tayi tace "to" dukda cewa ita bawai ta gane me yake nufi bane ...

Wuce su bandi yayi Ya shiga ɗaki, be ko kallesuba Saboda shi kadai yasan me yakeji, a zahiri idan ka kalli bandi zaka iya cewa su yan biyune shida hassu kasancewar yanada ƙaramin jiki, amma a baɗini shekararshi goma sha takwas, koda yake basaina zauna yi muku bayaniba kunsan dai yadda jikin Ƴan Fulani yake.

Fitowa yayi rike da mayafin hassu "amshi kasa hassu, zamuje gidan baba jauro ne yanzu...
Aikan dai shima SARFRAZ saiya fara kici-kicin maida wandonshi yana cewa Nima zani "irin dai yanda yara suke yi..

Amsar wandon bandi yayi yasa mishi sannan suka nausa cikin daji...
Duk Abinda sarfraz ya gani a hanya saiyace meye wannan, idan na taɓawa ne ya taba..
A haka dai a lalace suka karasa gidan baba jauro ɗin, duk sun gaji kasancewar Akwai tazara sosai tsakanin su...
Chapter 32 · 0% Book details