Sashe 65
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannun Nawaz ta haɗa da nata guri ɗaya, "Nawaz Nagode! Nagode!! Allah ya saka da Alkhairi, Allah ya shiga lamuranki, kuma ya ƙara mana danƙon ƙauna.
Murmushi Nawaz tayi tace "Ameen Aunty, Nima Nagode "
Yanzu ki ɗauko hijab ɗinki kizo muje in nuna Miki wani abin farin ciki da Aayaan yayi saboda ke. Mikewa Nawaz tayi ta karasa inda ta ajiye hijab ɗin ta ɗauka "to Aunty muje in gani!
Mikewa Aseey itama tayi sannan tace "muje sister"
Koda suka fito faloun babu kowa kasancewar Daddy ya tashi sai Mummy ta nunawa hassu ɗakin baki tace ta shiga shikuma bandi tace yaje ɗakin SARFRAZ,
Sannan su suka tashi suka shiga ciki.
Har cikin harabar gidan Aseey ta rakata Sannan tace "ki tsaya anan zakiga abin dana faɗa Miki, Sannan kuma kome zakiyi kada ki manta akwai haƙƙin auren wani a kanki. Sannan Aseey ta juya ta koma baya, amma bata shiga Cikin ɗakin ba ta laɓe a gefe saboda ganin me zai faru.
Nawaz na tsaye taji an dafata ta baya, cikin sauri ta juya don ganin waye?
Ai Saida numfashinta ya tsaya na wucin gadi sannan ya dawo, baya tayi zata faɗi tsabar ruɗani, ai kuwa da sauri Sarfraz ya tareta ya dawo da ita.
Zaro ido tayi "Sarfraz kaine? Ko dai gizo kakemin? Don Allah kaine?
Murmushi yayi "nine malama, ba gizo nake yimiki ba , buɗe hannunshi yayi alamun tayi hugging Dinshi.
Shiru Nawaz tayi tana tunani "tabbas sarfraz ya cancanci na rungumeshi ko don farincikin ganinshi da dawowarshi da rai da nayi a Yanzu, amma haƙƙin auren dake kaina fa? Tabbas idan na rungume Sarfraz kamar naci amanar Aayaan ne tunda aure dai aure ne koda ta wace hanya aka ɗaura shi.
Basarwa tayi "Wato ka dawo zaka cigaba daga inda ka tsaya ko? Rimi-rimi yayi da ido " haba Sweet heart Yanzu hug kadai kin kasa yi min? Ko bakya farin cikin dawowata ne?
Zaro ido Nawaz tayi cikin mamakin kalamansa "haba sarfraz nasan duk duniya babu Wanda zai fini farincikin dawowarka Idan aka cire iyayenka, Sarfraz Ni nasan irin halin dana shiga bayan bakanan, Nifa har burin mutuwa saida nayi, nayi kukan zuciya nayi na fili har Saida zuciyata ta ƙeƙashe, kuma duk sanda zan tuna dakai kaina nake ba laifi.
Daɗi ne ya ziyarci zuciyar Sarfraz ganin akwai alamun Nasara, to shikenan nabar hug ɗin, amma to ko One kiss ki bani mana! Ina so naji ɗumin jikinki ta yadda zan yarda cewa kece a gabana
Namma dai Nawaz murmushi tayi "hmm ashe dai me hali baya manta halinshi, nidai yanzu ka bani labarin abinda ya faru bayan mun rabu, ta faɗi hakan ne Saboda ta kawar da Maganar kiss ɗin.
Gefen inda aka zagaye Flowers ya samu yace ta zauna sannan shima ya zauna, "Nawaz nashiga tashin hankali da damuwa bayan an tafi dake, cigaba yayi da bata labari har zuwa sanda ya farka ya dawo hankalinshi, kuma ya bata labarin su hassu da bandi da kuma wahalar da sukasha dashi sanda baya cikin hayyacinshi.
Sosai Nawaz taji wani girman Aayaan ya kuma cika mata zuciya jin cewa ta dalilinshi akaga Sarfraz, kuma be tsaya iya nanba ya kaishi har ƙasar waje don neman lafiyar shi, ga tausayinshi ya ƙara kamata , wato shidai babban mutum daban yake, basai dole a shekaru ba. sannan a yanayin Labarin taɗan lurada Sarfraz ya damu da hassu sosai, kuma itama taji ƙaunar hassun ta cika mata zuciya dukda bata ganta ba.
Cewa tayi "masha Allah" tare da goge ƙwallar data ke zubowa daga cikin idonta "sarfraz lallai mun fuskanci jarabawa me girman gaske amma ga Dukkan alamu munyi nasarar cinyeta, kuma naji daɗi da Allah ya kuma haɗa mu cikin inuwa ɗaya, Sannan ina fatan mu kasance a haka har gaban abada.
Daɗi sosai SARFRAZ yake ji don a ganinshi Nawaz tana nufin su kasance tare har abada ne ta Hanyar aure.
Bashi labarin bayan sun rabu tayi saidai Koda wasa bata faɗa mishi cewa Aayaan bane ya taimaka mata kuma bata ce mishi anyi mata aure Ita da Aayaan ba.
Shiru SARFRAZ yayi yana duba wannan lamari, "Lallai Nawaz ta shiga gararin rayuwa, Amma komai yazo ƙarshe tunda gani na dawo".
Hannuwanta ya kama tare da marairaice murya "malama Don Allah zaki aureni? PLS ki taimaka Min mu zama abu ɗaya, Wallahi ina ƙaunarki Fiye da yadda kike tunani, sannan nayi miki alkawarin zaki kasance cikin farin ciki har ƙarshen rayuwarki muddin kika aureni.
Kwace hannuwanta Nawaz tayi Tare da ja baya "Sarfraz wai har yanzu bazaka dena wannan Labarin ƙanzon kuregen naka ba? Wai tayaya ma zan aureka, ya kamata ka gane niba tsarar aurenka bace, shekaruna sunfi naka, kuma Ni banada ra'ayin Auren Wanda na girmeshi.
Da sauri Sarfraz ya ƙara matsawa kusa da ita da niyyar hugging ɗinta sai tayi sauri ta goce tare da nuna mishi yatsa "SARFRAZ wallahi ka kiyayeni kada ka sake ka kuma taɓa min jiki, wai ina wasa dakai ne.
Banza yayi da ita ya nufeta gadan gadan, ganin Idan ta tsaya zai rungumeta da gasken ne yasa tayi Hanyar ɗaki da gudu.
Cikin hanzari SARFRAZ ya riƙe hijabinta yayo baya da ita, ai kuwa take wuyan hijab ɗin ya yage sakamakon yadda ya jashi da ƙarfi, sauka hijab ɗin yayi saman kafadarta.
Sai sannan Sarfraz ya tsaya Yana ƙare mata kallo, gani yayi kamar ba Nawaz ba, ta ƙara kyau kuma kamar tayi ƙiba.
Hannu yasa ya tuge hijabin gaba ɗaya Daga jikinta.
Rufe idonta tayi tana cewa "wai SARFRAZ Meye haka? Bakada hankali ne, meye zaka ciremin hijabi.
Binta yayi da kallo, tabbas Nawaz ta chanza sosai, to ko dai Daddy da gaske yake dayace tayi aure.
Baya takeyi yana binta, "Nawaz wai aure kikayi da gaske?
Cikin tsiwa Nawaz ɗin ta buɗe idonta tace "eh Aure nayi sai me? Saboda abubuwan da yake mata sun fara kaita bango.
Take idanuwan Sarfraz sukayi jajir, finciko ta yayi ya matseta a ƙirjin shi yana cewa "Wallahi be isaba ko waye shi, taya zai kai kanshi gonar daba tashi ba?
Na rantse da Allah dole ma ya sake ki, don ke ɗin mallakina ce kuma don ni aka halicceki, kici kicin kwacewa Nawaz takeyi shikuma ya samu damar haɗe bakinsu guri ɗaya.
Ai da sauri Nawaz ta chafki leɓen shi na ƙasa ta gatsa mishi cizo, da sauri ya saketa saboda azabar data ziyarci kwakwalwar shi.
Ganin ya saketa ita kuma ta arta a guje ba tare data gane ina tabi ba, shima rufa mata baya yayi, don ya kudiri niyyar idan taƙi bashi haɗin kai ya aureta ɗaukarta zaiyi ya gudu sai dai Duk Abinda zai faru ya faru.
Firgici ne ya kama Nawaz ganin ta da tayi a bakin gate, da sauri ta fara Neman yadda zata buɗe gate ɗin, domin ta gwammace ta fita a haka data tsaya Sarfraz yayi Yadda yaga dama da ita, don anata gani takeyi zai iya yin komai duba da Yadda idonshi ya kaɗa yayi jajir.
Dai dai lokacin shikuma Aayaan ya dawo Daga waje saboda bayan Aseey ta shiga kiran Nawaz colonel ya kirashi a waya kuma ya zamana baya jinshi alamun network Babu kyau, shine ya fita waje saboda ya samu service.
A jikinshi ta faɗa tana cewa "yaya Aayaann don Allah kada ka bari ya taɓa Ni, Wallahi bashida kunya.
Shikam Sarfraz saiya tsaya yana ganin ai kaman Nawaz takai kanta gida ne, tunda yasan Aayaan zai ribaceta ta aurenshi.
Daɗi Aseey taji ganin Aayaan ya shigo gidan, don gaba ɗaya mamakin rashin kunyar Sarfraz takeyi, "yana kallon wannan garɓasheshiyar macen yace zai hake mata.
Kuma daɗin dataji na biyu daya kasance Aayaan bega duka abinda ya faru ba, tasan shi namiji ne, dole idan yagani ranshi zai ɓaci.
Maida gate ɗin Aayaan yayi ya rufe "to ki sakeni" yace yana kallon Yadda ta ruƙunƙumeshi
Kasa sakinshi tayi tana cewa "yaya Aayaann don Allah idan na sakeka kada ka barshi ya matso kusa Dani.
Shi abinma dariya yaso bashi don Yadda Nawaz ta dage bilhaƙƙi ita tsoron Sarfraz takeyi.
"Okay to kada ki damu bazai taɓa kiba"
Sakinshi tayi a hankali tana kallon inda SARFRAZ ɗin yake a tsaye, murmushi yaketa yi ya zuba mata ido.
Harara ta balla mishi sannan ta kauda kai daga kallonshi.
"SARFRAZ meya faru haka naganku Kamar masu dambe? Aayaann yace yana kallon sarfraz ɗin.
" Yaya wai kawai don nace ta taimaka ta aureni shine tace ita wallahi bazata aureni ba, wai ta girmeni kuma ita batada ra'ayin Auren Wanda ta girma.
Kallon Nawaz Aayaan yayi sannan yace "wai hakane?
Ɗaga kai Nawaz tayi alamun eh, "to meyasa bazaki auri Wanda kika girma ba? Naga ai sunnah ne? Aayaann ya kuma tambayar ta
Ni kawai bazan iya shirme bane, wai taya ma zan auri wanda shi kanshi be iya control ɗin kanshi ba, to taya kenan Ni zaiyi controlling ɗina? Kuma kaima naji ai sunnah kace ba farillah ba.
Dariya ce taso kwacewa Aayaan ɗin, yadda Nawaz ta dage tana koro jawabai, yau ko kunyarshi da take ji ma babu.
Shanye dariyar yayi Saboda kada su maida abin wasa, "to yanzu ya kukeso ayi?
SARFRAZ ne yayi saurin cewa hakanan zata haƙura ta aureni, aiba shekaru zata duba ba ƙaunar danake yi mata zata duba, kuma naga ai aure ibada ne sann......
Ai Nawaz bata bari ya gama faɗar abinda zai faɗa ba tace "nifa ban yarda ba Wallahi, kai bari kaji ma nifa da in aureka gara na mutu single.
Sosai dramar take ba Aayaan dariya amma yana ƙoƙarin saita kanshi, it means yanada rabon zama da Nawaz kenan? Tunda gashi ita bilhaƙƙi taƙi yarda da batun Sarfraz.
"To yanzu abinda za'ayi muje kowa ya samu ya kwanta tunda kunga dare yayi sosai, da safe saimu ƙarasa maganar Koh?
Sarfraz beso Hakan ba, amma dayake yanada hope a gurin Aayann saiyace to Allah ya kaimu.
Itama Nawaz sai tace "to", koda suna tafiya zasu koma cikin ɗakin bata bari SARFRAZ ya matso kusa da ita ba, tana gefen Aayaan.
A falour suka tarar da Aseey zaune a kujera tana danna waya.