Sashe 24
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani ward aka nuna mata, tas ta zagaye gurin bataga sarfraz ba, zuciyarta ce ta tsinke innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, shikenan sarfraz ya mutu kome?
Ai ihu ta fara rafkawa take idon kowa ya dawo kanta, ganin ta sanye da kaya sojoji kuma tana tafka uban ihu, colonel ne yace menene?
"Banga yayana ba shikenan ya mutu, don Allah ku kaini mutuary inga gawarshi.
Colonel ne yasa aka rakashi mutuary ɗin amma abin mamaki nanma babu sarfraz baby alamun shi .
Damuwace ta kama Nawaz ne ƙarfi "ina sarfraz yake, me ya sameshi?
Tafe suke hawaye ya na zuba a fuskarta,
Bakin asibitin suka fito, motocine guda biyu sukayi parking a gabansu, colonel ne ya shiga daya yana musu sallama "saimun haɗu a Abuja , and please take good care of your self and my daughter...
Ayaann ne ya shiga daya motar itama tabi bayan shi ta shiga...
Duk wani iri takejinta, kewar gida ta kamata ga damuwar ina sarfraz yake,,,
Tana ta tunani ta saƙa wanna ta warware ta saƙa wancan shima ta warware,. A haka barci yayi awon gaba da ita (mayyar bacci mota)
Ji tayi ana yi mata tafi a fuska, firgigit ta buɗe ido "ki fito mun gida"
A hankali ta sauko tana bin gidan da kallo "Allah mai halitta, lallai duniya dama ance a Fika ne kaima kafin wani, duk irin kyan da take gani na gidansu SARFRAZ sai taga wannan ya damashi ya shanye...
Babu abinda babu a cikin gidan dangin su swimming pool, garden, gym, football field hand Ball field, parking space, meeting point, sai can wani guri data hango runfunan bunu masu kyau ga dawisu sai yawo suke a gurin can gefe kuma harda su jimina....
Bin bayan shi tayi ganin yabi wata hanya, a bakin wata haɗaddiyar kofa taga ya tsaya, a cikin wani sensor ya saka yatsanshi babba.
Take kofar tayi sliding, yana shiga itama tabi baya shi da gudu ta shiga, ai kusan suma tayi ganin cikin ɗakin.
Gaba daya komai design ɗin Larabawa ne zaka iya rantse wa ba'a Nigeria kake ba, tsayawa ma siffanta falourn kamar rage mishi kyau ne,
Duk ta tsargu sai take ganin anya batayi azarɓaɓi ba, dama bata shigo ba.
Ɗan gefe taja ta tsaya tana rarraba Idanuwa, wata mata ce haɗaddiya mai cike da haiba da kwarjini a shekaru bazata fi hamsin zuwa hamsin da biyu ba ta fito daga wata kofa, ai da gudu ta tawo shima Aayaan ganinta yasa ya nufeta da gudu, yana zuwa ya ɗagata sama "my world nayi kewar ki sosai" sannan ya sauketa ya rungume ta,
Nan ya fara yi mata shagwaɓa kamar ƙaramin yaro, ita kuma tana biye mishi
Ɗagowar da zatayi kawai tayi ido huɗu da Nawaz wadda ta saki baki da hanci tana kallon yanda Aayaan yake abu kamar ƙaramin yaro, kamar ba soja ba..
Murmushi tayi "wacece wannan" tace cikin Yaren Larabci...
Nan Aayaan ya kwashe komai ya faɗa mata shima da harshen larabci...
Nawaz na gefe tanajin duk abinda suke faɗa,
Hancinshi taja "har Nasha ko nayi suruka ne, naganta kyakkyawar gaske,
Gaban Nawaz ne ya bada dumm, shima ɓangaren Aayaan hakane ta faru sai ya dago ya kalleta a hankali....
Gun Nawaz amma ta ƙarasa ta rungume ta haka kawai ita taji yarinyar ta birgeta kuma ta natsu da ita sosai, tunda amma tayi maganar cewa Nawaz ko surukar tace kirjin Aayann keta bugawa da karfi ....
_*~MATAR RASHEED~*_✍️*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀🎀*
*Episode 27*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️
Yanda ya fita ya bar su haka ya dawo ya samesu a inda suke, baffa ya kalla "baffa babu inda ba'a kaini ba, tun daga kan dakin majinyatan har dakin waɗanda aka kwaso har mutuary babu Nawaz sam..
Fashewa da kuka baffa yayi "shikenan abinda nake fargaban ji Saida naji shi, yanzu shikenan ba'a ga nawwaraba?
Nura ne yace "baffa kayi hakuri insha Allah za'a ganta tunda ai bata cikin gawarwakin.
Amma ce tace "Nura kayi shiru kawai, kaifa yanzu da bakinka kake faɗa mana har asibitin kunje amma bata, to a ina za'a ganta kenan?
Ummin Nawaz tace "baffa da amma kuyi hakuri kawai mu dauki kaddara haka Allah ya tsara, amma mu zauna muna daɗa ɓata wa kanmu rai bashida wani alfanu...
Ni nayi imani da Allah kuma nasan komai ya faru haka Allah ya tsara tun farko...
"Yanzu ke da zamuba hakuri mu kike ba? Allah yayi Miki albarka kuma insha Allah sai hakan ya zame mana Alkhairi dukan mu..
Nura dake gefe yace "Amin" yana goge hawaye..
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Mota mummy zata shiga dadyn sarfraz Yace a'a bazaki iya driving ba, Nima da nake na miji bazan iyaba, yanzu abinda za'a yi shine Ni zan tuka motar muje tasha
Achan saimu samu driver ya kaimu ya dawo damu inyaso sai ya fadi nawa zamu bashi,
Haka kuwa akayi suka samu driver akan shi zai kaisu ya dawo dasu amma a motar su, sannan suka dauki hanya...
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
A hankali ta saki Nawaz daga rungumar da tayi mata "ƴata ya sunanki? Amma ta faɗa cikin Hausar ta mara fita..
"Sunana Nawaz" cewar Nawaz a hankali...
"Wow sunanki is special, kada na dameki zo muje in rakaki ɗakin ki ki samu kiyi wanka kici abinci kiyi barci ki huta idan kika tashi sai muje gidanku mu kaiki ko?
"To" Nawaz tace tana mamakin wai takaini ɗaki na, to a ina ya zama nawa?
Bakin wata ƙofa ta tsaya tayi danne danne sannan ta kama hannu Nawaz tasa a cikin sensor ɗin dake jikin kofar take kofar ta buɗe,
Sakin baki Nawaz tayi, murmushi Amma tayi mata "it is your room, kije ki shirya, hannunta taja ta saka a cikin ɗakin sannan ta rufe mata kofar ta koma gurin Aayaan...
Ganinshi tayi ya cika yayi famm, dama tasan za'a rina Domin Aayaan akwai baƙin kishi..
Ƙarasawa kusa dashi tayi "sweet heart Yana ganka haka?
Ko kanajin zazzaɓi ne? Pls kaje kasha magani kayi wanka kaci abinci saika kwanta kafin a kira sallah ko?
Shagwaɓe fuska yayi "mummy wallahi kinsan abinda ke damuna shine kika chanza magana!
Oh oh oh! Aayaaaann Wai har yanzu baza'a Dena kishin nan ba? Yanzu fa ka girma.
Mikewa yayi "shikenan ai dama na lura kina ganinta kika manta dani, Saida kika gama shirya ta sannan kika dawo gurina.
Kawai don Allah yayi ni namiji ke kuma mace kikeso shine za'a riƙa nunamin wariya..
Da sauri ta rufe mishi baki "I'm sorry, ba haka bane, she is our guest, ya kamata muyi comforting ɗin ta, amma daka shigo saika kyaleta a tsaye bakace ta zauna ba baka bata ruwa ba, and kasan wannan ba halin musulmi na kwarai bane...
Kuma Ni na kula tane saboda na wanke laifin da kayi
Murmushi yay "to mum Amma kada ki kuma kyaleni kinji?
"To" kawai tace tana mamakin halin Aayaan da bazai chanzaba...
Dtaga hannu Aayaan yayi sai sannan amma taga bandejin dake hannunshi
Hankalin tane ya tashi ta rike hannun "Aayaan me ya sameka a hannu?
Murmushi Aayaan yayi "mum kada ki damu pls na bigene shine na ɗan ji ciwo.
Kallon shi mum tayi "haba Aayaan nasanka sarai ba bigewa kayiba ka fadamin gaskiya
Murmushin ya dada yi "mum gaskiya na faɗa Miki, please ki bar maganar..
Addu'oi tayi mishi tana Dada sa mishi Albarka,
Shima ɗakin dake gefen wanda Nawaz ta shiga yasa hannu a sensor ɗin ya bude sannan ya shiga.
Direct bathroom ya shiga yayi freshing up sannan ya fito, ko mai be shafa ba yasa farar armless ɗin riga da three quarter din wandon sojoji....
Ya mike da niyyar fita dining ya ci abinci, sai kuma ya koma ya zauna.
Laptop ya dauka yayi danne danne saiga Nawaz ta cikin Laptop din zauna akan gado ta tafka uban tagumi tanata zubda hawaye...
Tsaki yayi "shit wai kukan na meye ne?
Tashi yayi ya fita falour gurin mummy, zama yayi a kasa ya dora kanshi a cinyarta ..
"Mummy Nawaz Bata fitoba kije ki duba ta saiki zo muci abinci...
"Okay dear bari nayi checking dinta i am coming ..
Tana mikewa ya fito da wayarshi a aljihu yayi dialling ɗin number colonel.
Mamakine ya kama mummy ganin nawaz zaune tana shirga uban kuka, da sauri ta karasa gurinta ta dafa kafaɗarta "daughter meya faru? Ko Bakya son gidanmu ne?
Girgiza kai Nawaz tayi,
"To menene"
Cikin Muryar kuka Nawaz tace "ba'a ga sarfraz ba kuma inaso naga mummy da ummi na..
"Okay calm down my dear, kije kiyi wanka, akwai kaya acikin closet saiki zaɓi wanda yayi Miki ki shirya kizo falour muci abinci saimu tafi..
Goge hawayen Nawaz tayi "to amma Nagode" sannan ta mike sai kuma ta waigo "amma bansan bathroom ɗin ba, wata kofa ta nuna mata Sannan tace kisa babban tumb dinki zata buɗe saikiyi Wankan..
Komawa falour tayi dai dai lokacin da Aayaan ya gama waya da colonel
Cewa yayi "amma colonel yace wai governor yace yanaso yaga Nawaz and yan majalisa da yawa ma suna so suyi mata kyauta, wai ashe Akwai yan uwansu da yawa daga ciki harda babban yaron ministan kudi, da matar ministan ilimi.
Murmushin mum tayi "ai shiyasa nace maka yarinyar tawa ta musamman ce mijinta ma sai nayi mishi screening tukuna, idan yaci sai a daura auren.
Kallon ta yayi "mum wai yaushe ta zama ƴar takine? Kuma Ni basai kinyi min haka ba zansan kin Dena kauna ta ba.
"Oh oh oh Aayaan wai yaushe zaka dena wannan kishin naka ne, kaifa ba yaro bane yanzu?
"Kuma inada tabbacin yanda Nawaz take da kirki nasan iyayenta ma haka suke, zasu bani ita .
"To mum Allah ya taimaka Ni nayi nan, hanyar dining yabi.
Serving din kanshi yayi sanan ya fara ci beko kuma kallon inda mum take ba.
Mamaki abin yaba mum "wai meyasa Aayaan bazaisan ya girma bane?
Itama kyaleshi tayi bata kuma cemishi komai ba..