← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 112

Sashe 2

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Risinawa tayi "Barka da yammah umma!
Kamar abin arzi'ki umma tace Barka dai nawaz, har kin dawo daga gantalin?
Itadai nawaz batace komaiba ta wuce d'aki, a zaune ta tarar da umminta a Kujera rike da hijab da alamu tana shirin yin sallah ne....
"Barka da yammah Ummi "
"yauwa Nawaz Kin dawo? Ya makarantar?
"Lapia ummi Amma gaskiya nidai dakyar in zancigaba da zuwa......
haba Nawaz bansanki da raki ba, ace yau d'aya daga fara zuwa harkin karaya?
"ummi wallahi dalibanne Marasa kunya ga tambayar bala'i sannan kuma wai Kowa surarshi daban,....
haba Nawaz ace duk yanda nasanki da hakuri?
ummi wallahi da Matsala.....

Ummi tace "to yau adakinma bazaki cire Dan gadonba (niqab)
Ace mutum shi kullum baza'a ga fuskarshi ba Kamar aljani....
cewa tayi "zan cire ummi, kwance igiyar niqab din yayi......
Wow godia ta tabbata ga Allah subhanahu Wata'ala daya yi wannan halittar 🤩
nikaina saida nashiga shakku Anya kuwa itace sanye da niqab?

farace irin milky white dinnan Kamar (tamanna bathia) ga face dinta very well shaped
Hancinta irin siririnnan ne kuma tsawonshi har kusa da cute lips d'in ta wanda suma light pink ne kuma da alamu batasa lipstick 💄 ba.
idonta madaidaici me dauke da zarazaran eye lashes..
kwayar idonta bakace sosai, kasancewarta Fara Sai hakan ya Kara mata wani sirrin kyau....
tanada siririyar gira wadda ta kusa hadewa.......

Mikewa tayi "ummi bari naje nayi alwala!
"to " kawai ummi tace...
tsakar gida ta fita, a inda tabar umma anan ta tarar da ita bata tashiba.

fampoo Ta karasa ta Kunna Ta tara butar dake hannunta....
Harara umma tabita dashi "shegiya Sai kyau Kamar aljana Amma babu mashinshini...
ace Mace har ta Kai shekara 25 Amma batada saurayine saboda tsabar ba'kin jini.....
Itadai Nawaz batace komaiba domin inda sabo ta saba da maganganun umma.
Amma abinda ya bani mamaki shine jin danayi umma tace shekarun nawaz 25 ...
Anya kuwa gaskene? Saboda ayanda naga nawaz bazata wuce shekara 17 ba......

alwalarta ta gama Ta wuce zata shiga d'aki, "abbanku na dawowa Zansa Yayi Shela a masallaci inda me sonki saiya badake sadaka, cewar umma tana dada doka mata Wata uwar Harara....
d'aki ta shige donyin sallarta domin yanzu maganganun umma sun dena bata haushi saima Daria da suke bata........

tayi ruku'u a raka'a ta biyu kenan wani yaron makwaftansu ya d'aga labule,
ummi yagani rike da chasbaha alamun tana azkar.....
"ummi wai aunty Nawaz tazo inji wani mutum a Waje......
mamakine ya rufe ummi lokaci d'aya had'e da farin ciki, domin rabonda ashigo gidan nan ace ana sallama da nawaz shekara ta uku kenan.....
cewa yaron tayi to yasir je Kace gatanan zuwa, fita yasir Yayi....

Nawaz na idar da sallah ta waigo fuskarnan Kamar ta zabga ihu "haba ummi Daga ance ana sallama Dani saikice ace ganinan, kumafa bakisan ko wayeba......

daka mata Tsawa ummi tayi "nace d'in, in kinada hukuncin daza kiyi min saikiyi koh!

Baza ki tashi ki fitaba saina bata miki rai?
niqab ta dauka a hannun Kujera a fakaice domin idan ummi tagani bazata barta ta fita dashiba.....

still a tsakar gida ta tarar da umma Harara tabita dashi zuciyar ta na tukukin ba'kin ciki, wato duk abinda tayi ya karye kenan koh...
Itadai Nawaz zaure Ta karasa ta saka niqab dinta.....
Mutum ta gani tsaye ya juya baya a Gefen boglary d'in gidan...
Karasawa tayi "Assalamu alayku........
kasa karasa sallamar tayi ganin Wanda bata ta'ba zatoba ko a mafarki.........

bata rai tayi "meya kawoka gidanmu?

MASU KARATU KUNSAN WA NAGANI👀❓

safraz na gani tsaye yana mata murmushi "malama wankan da kika koyaminne Sai Bayan naje gida kuma na manta.....

aranta tace da alamu dai wannan yanada Tabin hankali.
"to kuma ya akayi kasan gidan mu?
Cewa Yayi "malama google na Duba "
Mamaki abin tabata "Ta tabbata Tabbas wannan kwarkwar ne.....
dad'a maimaitamai tayi sannan tace kayi sauri kaje kayi kasan salloli ne akanka da yawa.......
Hannu yasa a aljihu ya ciro wata wayar daban "malama ga wannan ki rike a hannunki saboda koda naje gida idan na manta sai in kiraki ki tunanin......
Duba wayar tayi "iPhone" tace aranta.
cewa Yayi malama don Allah ki Amsa...
Amsa tayi tace to, yanzu kayi sauri kaje gida, kaga dare yayi.
harta juya yace malama Don Allah babu Wata addu'a daxaki bani Don indena irin wannan mafarkin........
murmushi tayi "I guess aure kawai zakayi domin shine mafita..........
juyawa tayi, daidai nan umma dake labe a zaure tana lekensu ta shiga gida da gudu....
a tsakar gida ta tarar da umma, "Ashe yau kwarton naki be biyaki a hotel d'in dakike zuwa bane shine ya biyoki gida ya kawo miki...... Cewar umma da ranta keta tafarfasa saboda taso taji me suke cewa Amma batajiba kuma gashi taga ya bata wani abu kuma shima batasan meyeba.....

'Daki Nawaz ta shiga,
bataga umminta a falour ba saidai ta shiga cikin d'aki,

"Ummi ashema d'an ajinane, wai tambaya yazo yi,,,
kinga harda bani wayarshi wai idan yaje gida koda ya manta zai kuma kirana ya tambayeni.....

ummi tace abinda nake fad'a miki kenan Ke kuma kina biyewa rudin shedan...
ki daure kici gaba da koyarwar Sai kiga Allah yayiwa abin Albarka.
nawaz tace to umma......

atsakar gida naga umma ta kasa kunne a jikin kopar shiga nawaz tanaso taji mai suke cewa, amma kasan cewar suna ciki batajiba.....
d'aki ta koma ta Kira fauziyya ('yarta)
"hello fauziyya Dan Allah kizo gobe domin aikinmu ya karye..
d'aga chan bangaren fauziyya tace meya faru?
umma tace nidai saikinzo sannan ta yanke wayar......

To masu karatu wai Ina safraz ne?
Motarshi dayayi parking a wani lungu yashiga ya tuka zuwa gida Yana tafe yana murmushi domin yasan burinshi ya kusa cika na korarta.....

Azuci yake magana "wai ita koda darema da niqab take yawo?
kuma naso naga fuskarta......

Wani bangajejen mansion naga ya nufi gate d'in, babu Wanda yazo budemai Amma sai naga gate d'in Yana zugewa da kanshi....
gidan yakai plot bakwai domin a gefe swimming pool ne harda foot ball field, dasu flowers iri iri chan wajen karshen gidan na hango gymnasium da garden a gefe....

Ko parking mai kyau beyiba ya fito daga motar, wani Babban apartment ya nufa da sauri,
yana Isa gurin kopar ya zuge yashiga ciki.
Wata hamshakiyar hajiya na gani zaune taci uban Ado Kamar wadda zata gasar kyawawa ...
Shekarun ta bazasuwuce irin arbain ba zuwa da d'aya...
jikinta safraz ya fad'a "mummy wallahi yau nagaji "

Murmushi tayi "sweetheart ai kaine idan nace kabari driver yakaika saikace kai kafi karfi....
kawar da maganar yayi dacewa "bari Nayi wanka nazo...
"to sweet ♥ afito Lapia.

Wani balcony yabi ya tura kofar ya shiga.
d'akin babbane sosai kuma yasha sofa milk colour 's da carpet shima milk, kayayyaki dai Kamar d'akin mai mata, su dispenser, fridge, dasu frames iri iri...
bandada tsinkewaba saida ya shiga bedroom, wani makadeden gadone yasha light blue d'in bed spread..
cire kayan jikinshi Yayi ya rage dagashi sai boxer,
sannan ya bude bathroom yashiga...
Kusan twenty minute Yayi sannan ya fito sanye da bathrobe da small towel Yana tsane kanshi....
wayarshi ya kalla a Saman bed side drawer sai sannan ya tuna da malama Nawaz...
dauka yayi ya Fara dialling d'in number wayar daya bata,
saida ya Kira Kusan so hudu sannan ta d'aga "Assalamu alaykum " me wayar baya nanne, tace cikin siririyar muryarta....
"malama ainine" cewar safraz.
To safraz ya akayi?

Kanne idonshi yayi sannan yace malama gani a bayi na cire kaya kuma ga ruwa a gabana, to ki fad'a min yadda zanyi...

jin muryarta yayi tace "nashiga uku, wai wannan wane irin mutumne ❓❓
Sai kuma ta d'aga murya...
kayi niyyah ka wanke hannu sannan ka yi tsarki saika wanke jikinta, d'in d'in yaji karar yanke waya...
dariya yayitayi wallahi nakusa da alamu bazansha wahalar korar wannan ba....
farar armless yasa da wandon track suit da kadan ya wuce gwuiwa....
fita yayi zuwa falour, abinda malama nawaz tayine ya dawo mai
Falour Ya shiga yana kyalkyale dariya harda rike ciki...
sakin baki mummy tayi"sweetheart meke damunka.
ai tambayar datayi saiyaji Kamar dad'a zugashi tayi.... sai dad'a kyalkyala dariyar yake...
Assalamu alaykum,
Muryar daddy Ta gauraye falour, da gudu safraz ya karasa ya rumgume dad oyoyo daddy kwana daya kawai kayi Amma Nayi mugun kewarka,,,
mummy ta taso Ta amshi jakar hannun shi tayi mai Sannu da zuwa..
yauwa madam azo ayi feeding d'ina domin I really missed your delicious food...
da sauri safraz yace "daddy yau nizan baka,
dad yace to muje dining din saboda yunwa nakeji sosai..
warmer ya bude Yayi serving din fried rice ya zuba coleslaw a gefe.
fara ba dad yayi Amma idan yabashi cokali daya Sai an kusa five minutes bai kara bashiba saboda tsabar surutu..
daddy ne ya gaji da haramiyar da safraz yake mishi
"safraz tashi kaje dakina a drawer akwai wasu takardu ka dauko min..
Mikewa Yayi to daddy...
Yana tafiya dad yaja plate d'in gabanshi ya cika spoon Sai baka....
dariya mummy taketayimai, Kallonta yayi "hajiya ainayi kokari ace bada abincine idan aka baka cokali d'aya sai anyi minti biyar, kidubafa kigani mintinmu ishirin Amma duka suka cokali Hudu yabani gashi inajin yunwa kuma abincin naki Yayi dadi...
kuma cika spoon yayi yakai baki yanata kada Kai...
tuni naga plate d'in babu komai...
ruwa yasha sannan Yayi hamdala
safraz ne ya fito rikeda wasu takardu.......

kubiyoni donjin wacece umma..
kuma ya safraz zai kare da Malama Nawaz
OUM AEYMAN CE 💖🎀🎀SAFRAZ 🎀🎀

Episode 3

Written by oum aeyman

Safraz ne ya fito rikeda wasu takardu,
Daddy ya naga ka tashi a dining d'in?
"nakoshine shiyasa, Amma anjima saikazo ka kuma bani koh?
Bata fuska safraz yayi, gaskiya dad baka koshiba, duka duka spoon nawa kaci?
Dad yace "Allah nakoshi ,anjima zan kara ai.......
Chapter 2 · 0% Book details