Sashe 93
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya haidar yayi tare da cewa "dama wannan lodin da kayi na shekaru idan ba'a samu ribaeda wuri ba ai anyi asara"
"Dalla malam kabani Abinda nace kabani, banson munafurci!
"Iyyeh! Dayake na gama nawa amfanin Koh? To ai Shikenan "
Koda suka fito zasu tafi yana kallon Yadda Nawaz ta zubawa motar haidar ido al'amurra bata sha'awa, daga karshe ma saida ta taɓa seat ɗin, dayake Irin me budadden saman nance.
Sallama sukayi da haidar suka kama hanya, "Madam motar haidar ta baki sha'awa!"
"Ya akayi ka sani "
"Nasan duk abinda kike so ai" murmushi Nawaz tayi tare da cewa wallahi ta burgeni ne sosai kuma dama ko a cikin film naganta ji nakeyi kamar na shiga cikin TVn na ɗauko.
"Don't worry, kisa a cikin ranki kema nan da 30mins kinada irinta!"
Zaro ido Nawaz tayi "me kake nufi"
"Just keep quiet and see"
Ita dai Nawaz shiru tayi tana tunanin me Aayaan zaiyi.
Be tsaya a ko ina ba sai wani Babban gurin da ake siyarda motoci, magana sukayi da baturen ta Yan mintoci, sai suka bi wata hanya, dayake ita Nawaz an bata kujera ta zauna.
Ko minti Bakwai ba'a yi ba, saiga su a cikin irin motar haidar komai da Komai.
Da sauri Nawaz ta Miƙe tana yiwa Aayaan kallo me cike da tambayoyi.
*BAYAN SATI SHIDA.....*
Abubuwa da yawa sun faru, wanda daga ciki zargin Aayaan na tunanin Nawaz ta samu ciki tun a Daren su na farko ya tabbata, don yanzu haka ɗauke take da ciki na sati shida amma ita bata saniba, ga wani irin mugun barci da takeyi kamar kasa, kuma sam batada abinci sai nama da Madara, ko hatsi bata yarda taci sai Aayaann yayi da gaske tukuna.
Makarantar ma ta jingine ko maganarta bata yi, su maman sudeis sunyi bikon har sun gaji..
Sun ziyarci Aseey, sannan Aayaan yayiwa maman sudeis kyautar mota KIA kerato ita da Fatima.
Koda wasa Nawaz bata taɓa kawo cewa ciki garetaba, sosai wata irin shaƙuwa ta kamasu ita da Aayaan, bata iya rintsawa idan ba a cikin ƙirjinshi ta jita ba, kowane motsi so takeyi tajita a kusa dashi, sosai takeson kamshin jikinshi.
Misalin Bakwai da rabi na safe Nawaz ta farka da wani Irin mugun mafarki, tunda ta tashi Aayaan ya lura tana cikin damuwa, sosai yake tambayarta meya faru amma sai dai tace mishi Babu komai, kuma data kalleshi sai idonta ya cika da hawaye .
Kuyi haƙuri da typing errors yauma banyi Editing ba🥱
*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*78*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Yayi yayi ta faɗa mishi menene amma sai tace babu komai, daya matsa mata sai ta fashe mishi da kuka tana cewa "yaya don Allah kada ka rabu Dani, Wallahi na dena yi maka musu, kuma duk abinda kakeso zanyi maka"
Lallashinta ya fara yana cewa "dear Nothing will happen In'sha Allah, we will live together, ko a cikin aljannah ke nake fata ki zamo min mata, babu abinda zaisa na rabu dake in'sha Allah "
"Promise bazaka barni ba"
"I promise to be together in'sha Allah, tare zamu raini cikinmu, kuma tare zamu haihu don bazan bari wani ya gan mini Naƙudar mata ta ba"
Shiru Nawaz tayi domin maganar da Aayaan yayi ta karshe ta bigeta, kenan ciki gareta shiyasa komai nata ya canza?
Farin ciki taji a maimakon taji fargaba, "yaya da gaske ciki gareni?"
Mamaki ne ya kama Aayaan ganin Nawaz tanata farinciki, be taɓa tunanin haka Abin zai zo mishi da sauƙi ba, ai da tuni zai faɗa mata, ya zaci zata shiga damuwa ne idan taji,
"Kinaso ne?"Aayaan ya tambayeta
"Eh ina so, amma me kama dakai kuma sunanka nakeso asawa jinjirin"
Rungumeta yayi yanajin wata irin ƙaunarta har cikin ruhin shi, sosai take bashi tausayi saboda cikin data samu cikin gaggawa, sam bata huta ba, danma Allah yasa laulayin na kwadayi ne bana ciwo ba.
"Kinsan wani abu kuwa?
"A'a" Cewar Nawaz tana daɗa shigewa cikin jikinshi
"Nifa kunya nakeji a ganki da ciki, nasan kowa cewa zaiyi ɗan ƙaniya, yayi aika aika"
"Hmmm balle ni kuma, don Allah kada ka faɗawa su mummy da Aunty Aseey"
"Kai! Ni dana ke jin kunya ta ina zan iya faɗa? Sai dai ko ke"
"Rufamin asiri Nima Wallahi bazan iyaba.
Ahaka suka wuni suna hira, sai dai har zuwa lokacin zuciyar Nawaz cike take da fargaba, tsoro takeyi kada abin data gani a mafarki ya zama gaske, idan haka ta faru ta shiga ukunta, bata san inda rayuwa zata kuma jefata ba.
"Dear yanzu ace na mutu zaki iya Auren Sarfraz?" Tambayar da Aayaan ya jefowa Nawaz kenan
Idonta ne ya cika da ƙwalla "kaga ka dena min maganar mutuwa a gurin nan, meye na zancen wani Sarfraz? To bari kaji wanima bazan iya aureba balle Sarfraz, banda ra'ayin kowa face kai."
Sanyi Aayaan yaji har cikin ranshi jin cewa matarshi na sonshi "to misali na mutu kafin ki haihu, idan kika haihu zaki iya ba mummy ɗan da kika haifa ko zaki riƙe ne?
Fashewa da kuka Nawaz tayi tana tuna mafarkinta, cikinta ta shafa tare da kama hannun Aayann tana ɗorawa a saman cikin "kayi alkawarin cewa tare zamu raini ya'yan mu, mu basu tarbiyya me kyau "
"Nayi miki alkawarin hakan, hatta rainon cikin bi'iznillah tare zamuyi shi"
"To yaya don Allah ka dena maganar mutuwa duk da nasan tana kan kowa, amma kada ka manta yanzu fa kaine bango na kuma majingina ta, idan ka mutu ya kakeso nayi, to aini kaina yanzu Yar gidan mummy ce balle Abinda na haifa."
"Nevermind we will die desame day in'sha Allah, hope U Are happy now"
Murmushi Nawaz ɗin tayi tare da cewa "yea i am Happy "
Rufe bakinta keda wuya wayar Aayaann ta fara ƙara, koda ya duba sunan "colonel ya gani "
Da sauri ya ɗaga yana mamaki saboda ɗazu suka gama waya dashi "hello Sir"
"Aayaan kiran ujila ne daga sama, gobe da yamma ake buƙatar mu isa ƙasar Ukraine, muna daga cikin special soldiers guda ɗari biyar da aka zaba cikin ƙasashen duniya wadanda zasu kai musu agaji."
"Okay sir I will be getting ready in'sha Allah "
Kashe wayar colonel yayi bayan ya daɗa jaddadawa Aayaan ya tabbatar gobe sun haɗu a inda akace su haɗu.
Sosai fuskar Aayaan ta nuna damuwa bayan ya gama wayar, "dear kinji wai kiran ujila akayi mana daga sama, wai zamuje mu kaiwa kasar Ukraine agaji"
Zumbir Nawaz ta Miƙe tana tuna mafarkinta, kada fa gaskene Aayaan mutuwa zaiyi ya barta, domin mafarki tayi wai yaje yaƙi Wata ƙasa sai gawarsa aka Kawo ya mutu.
Tashi tayi ta daka tsalle "wallahi bazai yiwu ba, nidai gaskiya baza kaje ba, gaskiya ka nemi uzuri Ni zuciyata bata kwanta min da tafiyar nan ba, tana kaiwa nan ta fashe da kuka tana yarfa hannuwanta.
Da sauri Aayaan ya miƙe shima tare da riko ta yana cewa "sorry ki natsu pls, ji yadda kike tsalle, ko kinaso kiyi ɓarin me kama ko ince takwaran Aayaan dinki ne? Tafiya Ukraine bashi ke nuna miki zan mutu ba, addu'a Kawai zakiyi Allah ya dawo miki dani lafiya"
"Wallahi ni banson kaje, pls ka taimakeni kada ka rabu Dani?"
"Dear don't worry I promise zan dawo gareki cikin koshin lafiya muci gaba da rainon cikinmu Koh?
"Nifa zuciya ta tsinkewa takeyi tun ɗazu"
"Babu Yadda zanyi ne amma dana fasa zuwa, but nayi rantsuwa akan zan kare rayukan al'umma iya ƙarfina, so Please kimin addu'a kawai"
Babu yadda Nawaz zata yi ne amma tunanin Yadda zata bar Aayaan ya tafi wata ƙasa yaƙi takeyi bayan tayi mafarkin ya mutu yana yaƙi, fashewa tayi da kuka wiwi, don yadda takeji a jikinta tasan ba Lallai su kuma haɗuwa da juna ba idan ya tafi.
Babu yadda Aayaan beyiba amma taƙi yin shiru, yayi yayi amma babu improvement, sai Kawai ya kira mummy ya miƙa mata wayar.
"Daughter lafiya kike kuka"
"Mummy yaya Aayaann ne wai zai tafi yaƙi ya barni"
"Iyye to be isa ba, babu yadda za'a ayi ya tafi ya barki a ƙasar da ba taki ba, bashi wayar"
"Hello mum ina yini?"
"Banson gaisuwarka, maza yanzu kayi booking flight, Kafin ƙarfe huɗu na yamma ka tabbatar ka kawo min ita gida, idan yaso sai ka tafi duk inda kake so!"
Ba haka Nawaz taso ba, taso ace mum tace mishi kada yaje ne amma ba wai ya maida ita gida ba.
Koda ya kashe wayar sai yayi shiru, duk jikinshi yayi sanyi yana tunanin yadda zai iya barci ba tare da Nawaz na cikin jikinshi ba, saboda yadda yayi sabo da hakan.
Haɗa Duk wani abu da yasan zata buƙata yayi a cikin luggages ɗinsu, sosai yake cikin damuwa kuma ya rasa dalilin shiga damuwar tashi.
Gidansu maman sudeis da fatima ya kaita sukayi sallama Sannan ya wuce dasu gidan haidar.
Misalin shabiyu na rana suka isa airport ɗin, ita dai Nawaz kallon komai takeyi kamar a mafarki, tana yiwa ƙasar kallon ƙarshe ne, gashi Aayaan yabar komai a apartment ɗinsu yace inya dawo zaizo ya ɗauketa su komo, harta motar ta tana chan gida.
Tana zaune a seat ɗinta ne amma ruhinta is nowhere, wani Irin abu takeji ya tokare mata ƙirji, shikuma Aayaan duk saiya ƙara shiga cikin damuwa ganin yadda Nawaz ɗin ke cikin ƙunci.
Tanajin sanda ake sanar da cewa jirgin zai tashi sai kawai ta rufe ido kamar tana barci. Ganin hakan da tayi yasa Aayaan ya rabu da ita, saboda shima bawai daɗin jikinshi yakeji ba kuma ya lura itama kamar batason damu.
*Bayan kyawawan awanni huɗu da rabi....*
Nawaz ce riƙe da Aayaan tana zunduma ihu akan ita wallahi bazai tafiba, ko kuma ya tafi da ita,
Mummy ta rasa yadda zatayi, daga karshema Mummy ce tace "Ni Wallahi danasan Abinda zai faru kenan da banyi gigin cewa ku sauka a nan Maidugurin ba, da cewa nayi ku sauka a chan zariya nima nai zamana achan, Nasha wahalar zaman mota ne amma da Yanzu zamu koma chan ɗin"