← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 112

Sashe 77

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya aini ya kamata na haɗa maka ruwan wanka bakai ka haɗa min ba"
"Kefa Sarauniya ce a cikin faɗar zuciya ta, babu abinda bazan iya yi miki ba muddin befi ƙarfina ba, hope banyi laifi ba dana haɗa ba Tare Da na tambayi mai girma Sarauniya ba?
Ware idanunta tayi "yaya bazakayi min laifi ba, Nagode sosai! Bari na shiga nayi" da sauri ta miƙe Tare Da bin Hanyar dataga ya fito.

Zama Aayaan yayi a dai-dai saitin inda Nawaz ta tashi, ɗumin jikinta be bar sofa ɗin ba sanda ya zauna "me yake Yawan sa sweetheart tunani ne? Ina Fatan bani nake takura mata ba! Inajin tsoron addu'ar da mummy tayi na cewa Idan na Cutar da ita bazata yafe min ba, but bari ta fito in tambayeta meke damun ta"

Shiru shiru kusan awa ɗaya Nawaz taki fitowa Daga bayin, shi kanshi yanaso ya watsa Ruwan kafin ya kwanta, gashi harya fara gyangyadi saboda gaba ɗaya a gajiye yake tuɓus.

Bakin bayin ya ƙarasa ya fara kiran sunanta, amma shiru babu amsa, ƙara ƙarfin kiran yayi namma shiru bata amsa ba, wata irin fargaba ce ta kamashi Lokaci guda ya tura bayin da ƙarfi.

A cikin bath ya ganta ɗaure da ɗan ƙaramin towel ta ɗuƙunƙune jikin ta guri ɗaya tanata sharar barci, kasaƙe yayi yana kallon yadda take barci kamar Wadda take akan gado, dariya sosai abin ya bashi don yasan kunyace ta hanata fitowa.

Duƙawa yayi ya ɗauketa dukanta tare da fita daga bayin zuwa cikin bedroom, a Saman King size bed ɗin ya kwantar da ita sannan yasa duvet ya rufeta.

Bathroom ɗin ya koma tare da haɗawa kanshi nashi Ruwan wankan, kamar mace haka ya zauna yana ƙalƙale-ƙalƙale, ko ina saiya wankeshi daban kuma a tsanaki.

Koda ya gama wankan shima be wani tsaya saka kaya ko shafa Mai ba, towel kawai ya ɗaura a ƙugunshi Sannan ya haye saman gadon tare da janyo Nawaz Zuwa ƙirjinshi yana rungumeta sosai sannan yaja duvet ɗin ya rufesu.

Dayake barcin ya gama kama mishi ido sosai, ko minti biyar ba'a yi ba sai jin saukar numfashi nayi yana sauka peacefully.

Sai wajen ƙarfe Uku Nawaz ta farka, jinta tayi cikin Wani faffaɗa, yalwatacce kuma Ni'imtaccen ƙirji, to bata tsaya wani dogon tunaniba tasan Aayaan ne, sosai yanayin ɗumin jikinshi ya kayatar da ita saboda duk uban sanyin da ake yi sam ita bataji, har wani damshi-damshin zufa ne ma yake a tsakanin kirjinsu daya haɗu guri ɗaya, a hankali ta buɗe idonta kamar Me jin tsoron buɗewa.
A saman fuskar Aayaan ta sauke idonta, Zuba mishi idanunta tayi tana ƙare mishi kallon da bata taɓa yi mishi Irin Shiba, sosai taga kyawunshi wanda bata taɓa ganin irinshiba dayake dakin gauraye yake da wadataccen haske.

Zarazaran gashin idonshi taketa kallo kamar wanda yasa fake lashes, Saida ta kalla ta gaji Sannan ta dawo kan hancinshi, Gaza haƙuri tayi Saida tasa hannu ta taɓa hancin, tunda take bata taɓa ganin hancin da yayiwa meshi kyauba Kamar nashi, sosai ya zauna a tsakiyar fuskarsa gashi dogo and well pointed.
Babu abinda ma ya tafi da imaninta kamar laɓɓansa yadda suke pink-pink maroon-maroon brown-brown kamar wanda ya shafa wani jan baki na musamman, sosai ta shagala wajen kallonsu, shape ɗin su kanshi abin kallo ne ga wani kwantaccen gashi me santsi a saman top lip ɗin.

Yatsanta manuniya tasa ta taɓa leɓen, hakanan taji jikinta yayi mata wani iri, taushi sosai taji saman laɓɓan nasa, murmushi ne ya suɓuce mata sannan afili tace "taɓ wannan mutumin da Mace ce Bansan Irin goslow ɗin Da za'a riƙa yi a kofar gidan suba, jifa kyau kamar danshi aka halicci Kowane abu mekyau"

"Ai ban kaiki kyau ba my Queen👸"

Koda wasa Nawaz bata taɓa zaton idonshi biyu ba, ruɗewa tayi gaba ɗaya kunya ta rufeta, ji tayi dama ƙasa ta buɗe ta rufta da ita kawai ta huta da wannan abin kunyar data tafka, ita mema ya Kaita yin wannan ɓaranɓaramar?

"To kici gaba, yanzu saura gira ki duba kiga itama tayi Miki ko akwai gyara, and daga gira sai gashin kaina da kunne, idan kika kainan kin gama da kai sai kuma a koma kirji.
Sai hannu da yatsu, infact har manhood ɗina ma saikin duba kinga ko ya miki! "Yanajin yadda bugun zuciyarta ya ƙaru, dariya yakeso yayi amma bayaso ta fahimci wasa yake mata, to sweetheart kici gaba mana!

Tuni Nawaz ta ɗauke numfashinta, kunya nauyi da tsoro ne suka saukar mata lokaci guda jin cewa wai har length Dinshi saita duba. Bata taɓa zaton wasa yakeyiba saboda yadda taji muryarshi a dake.

"Shikenan tunda ke bazaki yabi ɗan mummunan mijin naki ba, Ni bari na faɗa miki abinda yaja ra'ayi na akanki my beautiful wife"

"Kinga da fari babu abinda ya fara ɗaukar hankalina akanki kamar jarumtar da kikayi a daren da kika gudo daga Wajen ƴan ta'addan nan.
Na biyu kuma yadda kika damu da wanda kuka tawo tare dashi (SARFRAZ) kinga hakan yana nuna kinada riƙon Alkawari kenan.
Na uku yadda ƙaddara tasa kika zauna tare damu Batare da kin shirya ba, naga ko dai-dai da rana ɗaya baki taɓa nuna kin damu ba duk da baki sammu ba, kin yarda kin zauna damu koda a cikin ranki bakya so, hakan ne ya nunamin kinada amsar kaddara, kuma koda Mutum ya aureki wani abu ya faru daga Baya nasan bazaki guje mishi ba.
Na huɗu shine yadda kika ɗauki mummy kamar Wadda ta haifeki, kullum cikin girmama ta kike da mutuntata, sannan Aunty Aseey ma kin ɗauketa kamar yayarki babu raini ko nuna damuwa tsananin ku, Sannan muhsien ma kin daukeshi kamar ɗan da ke kika haifa, sam Bakya gajiya da shirmenshi.
Kinga ko iya nan na tsaya nasan na haɗa qualities ɗin da akeso mace tagari ta samu, balle Akwai saura babu adadi

Kuma Kinga duk sanda zan taɓaki sai kince min babu kyau, to wallahi Allah ne kadai yasan irin daɗin da nakeji a cikin zuciyata. Sannan abu kaɗan zaki kawo aya ko hadisi.
Idan nace zan iya lissafa miki abubuwan da suka jani zuwa gareki wallahi nayi ƙarya.
Kinga kinada kunya, kuma duk inda kikaga kunya to akwai imani a gurin Domin tagwayen junane ɗaya baya tafiya saida ɗaya.
Ga hakuri ga kawaici da yakana, hmm nifa na dace, Allah ya zaɓeni cikin miliyoyi kuma babu abinda zan iya yi mishi sai godiya gareshi a kullum.
Yanzu abar fannin halayyah a dawo dabi'a.
A yadda na lura da dabi'un ki shine Bakya wasa da Sallah, kinada son addinin ki sosai, nasha Kamaki kina karatun Alqur'ani mai girma, kuma gaskiya zaki fadeta koda ke bazata yi miki daɗi ba.
Nanma zan barshi haka.

Ƙirar jiki kuwa Bansan me zance ba gaskiya, Domin kedin full package ce, sama da ƙasa dass, komai yaji babu makusa daga body structure har kyawun fuska.
Donma dai har yanzu ni ɗin an ɗaukeni a Matsayin dodo kinki bani damar dazan gama mallaka miki kaina gaba ɗaya.
Zuwa wannan lokacin babu abinda jikin Nawaz Keyi in banda rawa, haƙiƙa idan tace bataji daɗin yabon da Aayaan yayi mata ba tayi karya, amma kalmomin da yayi Amfani dasu ne sunyi mata Nauyi.

Sosai Aayaann yakejin dama su dauwama a yanayin da suke ciki har abada, ya gama karantar cewa Nawaz ta afka cikin soyayyar shi batare da itama ta sani ba, Yanzu abu ɗaya ne ya rage mishi da zai yi yaƙi dashi shine kunyarshi da take matuƙar ji, ya lura kunyar cema take kawo tsoron.

Daɗa rungumeta yayi sosai a ƙirjinshi tare da sumbatar goshinta yana cewa "my fear fear wife"

A haka har barci ya ɗaukesu gaba ɗaya, koda asbah ma ya rigata tashi, shiga bathroom yayi yai wanka Sannan ya haɗa mata nata ruwan Sannan ya fito ya tasheta a hankali "sweetheart kije kiyi wanka kizo muyi Sallah sai mu shirya, kinsan 6:30am jirginmu zai tashi Koh?

Harta yunkura zata tashi saita tuna da abinda ya Faru jiya da dare, sosai ta koma ta lafe tare da cewa "to ka tafi Zan tashi"

Murmushi yayi donya gane abinda ta tuna " as you say my Queen" matsawa yayi gefe sannan ya juya bayanshi yadda koda ma taganshi bazataji kunya ba.

Salalau jiki a mace haka ta miƙe ta shiga bayin kamar wadda babu laka ajikin ta tare da turo ƙofar tana murmushi.

Ko Bayan ta shiga shima Aayaan murmushi yayi Domin childish behavior ɗinta na matukar burgeshi.

Ta daɗe da gama wankan amma ta kasa fitowa, duk towel ɗin dake cikin bayin ƴan ƙananu ne sosai, gashi kuma ita gaskiya bazata iya fitowa gaban Aayann a haka ba.

Aayaann na tsaye harya fara gajiya, sanin cewa ba fitowar zatayiba yasa shi tura kofar bayin tare da ciccibarta yana fitowa.
Jikinta taketa karewa wai ita a dole kunyarshi takeji, shammatarta yayi ya fige towel ɗin daga jikinta gaba ɗaya, aiko babu shiri takai mishi wata wawiyar runguma tare da fashewa da kuka tana cewa "don Allah yaya ka bari, kayi hakuri".
"Ni bakiyimin laifi ba mai nakeso na shafa miki saina shirya ki saboda kinsa mun kusa makara.

*Fatan alkhairi ga kowa*

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*67*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Kuka sosai Nawaz ta fashe mishi dashi akan don Allah ya kyaleta kada ya shafa mata zata shafa da kanta.

Sosai abin yake ƙayatar da Aayaan domin dama Allah ya halicce shi dason mace mai tsoro da kuma ƙarfin hali a wani fannin, kuma Nawaz duk tana dasu.
Duƙawa yayi ya ɗauki towel ɗin a inda ya faɗi sannan ya rufa mata a bayanta, ajiyeta yayi a saman gado tare da cewa "bari nayi mana order ɗin abinda zamuyi break fast kafin mu tafi, and kuma ki tabbatar kinyi sauri kin shirya kafin in dawo, don inba haka ba saina shirya ki da kaina.

Yana fita ta miƙe da sauri ta ɗauki doguwar rigarta ta zira, ko bra ɗin ma saita ƙasa tasata, mai taɗan mutstsika agaggauce sannan ta maida hijab ɗinta, ai kuwa tana gamawa saiga shi ya shigo riƙe da take away guda uku, wata budurwa na biye dashi da flask da disposable cups a hannun ta.
Chapter 77 · 0% Book details