Sashe 27
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba daya fadar ta kaure da surutu, sai daga baya komai ya dawo dai dai, amma daka kallesu zaka gane suna cikin matukar farin ciki...
Mummyn Aayaan ce tayi gyaran murya sannan tace "baba da mama da mahaifiyar Nawaz da kuma duk wanda yake da hakƙi akan Nawaz don Allah ina Neman alfarma akan a ara mana Nawaz mu tafi da ita zuwa gidanmu.
Saboda dalilin abinda ya faru Governor da sauran ministoci harda yan majalisu suna so suga Nawaz, saboda dalilinta anyi nasarar kama ƴan ta'adda, da kuma ceto rayukan mutane masu yawa....
"Haba ke kuwa" cewar baffa yana kallon mummyn Aayaan, Ai Nawwarah ki dauketa kamar yadda kika dauki Ayatullah, itama ƴar kice..
Amma ma haka tace, kowa ya nuna babu wata matsala hatta ummin Nawaz, dubada yadda suka nuna suna kaunar Nawaz ɗin....
Baffa ne yayi gyaran murya Sannan yace "amma dai bayau zaku tafiba, saboda dare yayi idan Allah ya kaimu gobe sai kuyi sammako....
Dubada yadda baffa ya nunawa Mummy halarci, ga kuma abinda baffan ya faɗa akan Aayaan game da Nawaz yasa taji bazata iya yi mishi musu ba,
"To Allah ya kaimu"
Shima Aayaan sai murna yakeyi saboda lokaci ɗaya yaji dattijon ya shiga ranshi, ko babu komai zasu kwana suna hira, kuma zai kara sanin cikakken tarihinshi...
Nura baffa yasa ya gyara ɗakin baƙi, saboda anan su mummy zasu kwana ...
Koda dare yayi mummy sunata hira da amma ita kuma Nawaz alokacin ta samu damar keɓewa da umminta har ta bata labarin sarfraz tun daga farko.
Fashewa ummi tayi da kuka "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, yanzu kina nufin ba'a ga sarfraz ba? Kuma ta dalillinki hakan ta faru?
Shiru Mummy tayi tana tunanin yadda zata warware wannan al'amari.
Cewa Nawaz tayi kinsan halin baffa idan yaji Maganar nan nashiga uku, yanzu abinda zakiyi shine kiyi ta addu'a, nima zanyi sosai, idan kika dawo daga tafiyar da zakiyi sai mu shirya muje gidansu SARFRAZ ɗin tare da Nura da Amma.
Aayann yana can ya buɗe baki da hanci yana sauraron baffa, shiko baffan sai bashi labarin lokacin da kakanshi yayi aure har zuwa sanda aka haifi Muhammad wato baban Aayaan..
Sukuwa guards ɗin Aayaan a cikin mota suka kwana bayan an aika musu da abinci.....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Koda gari ya waye da wuri suka shirya don tafiya, baffa ne ya ƙara kallon mummy yace "ƴata ina fatan zaki bani haɗin kai a ƙudirin dana dauka?
Murmushi mummy tayi "Insha Allah baba, nama riga na baka, komai kayi Ni ƴar kace Aayaan kuma jikanka ne..
Aayann ne ya kalli mummy "Mummy wai me kuke magana akai ne nifa ban ganeba?
Baffa ne yace "jikana akan ka muke magana akwai abinda zanyi ne, kuma sai kafi kowa amfana da farin ciki da abun...
Girgiza kai Aayaan yayi badon ya ganeba....
Har mota suka rakasu suna ta Daɗa yiwa mummy da Aayaan godiya..
Bayan sun tafi haka suka koma gida cike da kewa musamman baffa daya kwana hira da Aayaan, kuma ya lura yarone me hankali da girmama nagaba dashi..
Ko minti goma kwarara basuyi da fara tafiya ba mummy tace wa Aayaan ya Dena driving,
Daya daga cikin guards ɗin ta kira tace yayi driving ɗin duba da Aayaan baiyi barciba da dare.
Cewa tayi ya koma baya dayake dama ita a gaba ta zauna Nawaz ce kawai a baya...
Bayan ya koma ya zauna, itadai Nawaz bata kalleshi ba sai dai gabanta nata dukan uku uku, sannan kamshin turarenshi ya cika mata hanci...
Ɗago da kanta tayi aukuwa cikin kuskure suka haɗa Ido, murmushi yayi mata haɗe da ɗaga mata gira ɗaya, da sauri Nawaz ta kau da kai domin itafa abin Aayaan ya Fara bata tsoro, mutum kamar wani kwarto, shi bazaiyi maka maganaba sai dai ya riƙa ɗaga maka gira..
Suna nan zaune Nawaz taga Aayaan yayi barci, ajiyar zuciya ta sauke, domin itama barcin takeji amma bataso tayi saboda shi, ɗan kishingiɗa tayi itama don taɗan rage gajiya aikuwa nan barci yayi gaba da ita.
Ashe dama idon Aayaan biyu yana kallon duk abinda takeyi...
Zubawa fuskarta ido yayi yana kallonta, gashin idonta wanda ya kwanta luff a fuskarta yabashi sha'awa sai madaidaicin cute lips dinta me shape ɗin heart....
Hannu yasa zai taɓa fuskarta kome ya tuna oho sai kuma ya fasa,
Shima dai barci ne yayi gaba dashi dukda shiba gwanin barci a mota bane amma kasancewar kusan kwana uku baiyi barciba yasa barcin ya daukeshi be shiryaba....
"Aayann tunda muka shiga week ɗin nan idan na kira Aseey a waya bana jinta sam, tun ban damuwa wallahi har na damu.... Cewar mummy
Shiru taji Bai Bata amsaba, waigowa baya tayi aikuwa nan taga Aayaan kishigiɗe Nawaz kuma tayi pillow da damtsen shi na dama sunata sharar barci abin su...
Murmushi mummy tayi ganin yanda sukayi kyau kamar couples, ita dai batada addu'ar daya wuce Allah yasa Aayaan yace yanason Nawaz, yarinyar ta shiga ranta sosai...
Ahaka aka isa gida amma basu tashi ba, fita mummy tayi ta shiga ciki sannan tayiwa guards ɗin kashedi akan kada a tashesu a bari su tashi da kansu.....
Ashe Aayaan ya daɗe da tashi kunyar mum ce ta kamashi ganin yanda Nawaz tayi nashe nashe ajikin shi, shiyasa ya nuna kamar be tashiba
Yana nan zaune yana tunanin yanda zai kwantar da ita ya fita daga motar, ji yayi ta motsa sai yayi saurin maida idonshi ya rufe.
Aikuwa da sauri Nawaz ta tashi daga kirjin shi tana salati " Allah yasoni Ni na riga tashi da bansan irin kunyar da zansha ba.
A hankali ta buɗe ƙofar zata fita sai jin shu'umar Muryar Aayaan tayi yace "tun tuni na tashi nadai bari ki tashi ne duba da yanda naga kirjin nawa yayi miki daɗi...
Ai Nawaz bata iya rufe ƙofar ba ta kwasa a guje tayi cikin falourn..
Murmushi yayi shima yabi bayanta, koda ya shiga falourn babu kowa sai kawai ya wuce dakinshi domin wani irin azababben barci yakeji.
Watsa ruwa yayi sannan ya kwanta, ba'a ɗauki lokaci me tsawo ba barci me nauyi ya dauke shi..
Ita kuwa Nawaz Koda tashiga falour itama bataga kowa ba sai kawai tashiga ɗakin da mummy ta nuna mata a Matsayin nata, wanka tayi ta shirya amma kuma ta kasa fita falour saboda bataso koda wasa su haɗu da Aayaan...
Hakanan tayi shahada ta fita, cikin ikon Allah kuwa mummy ta gani zata shiga kitchen.
"Daughter Ashe kin tashi?
"Murmushi tayi "eh Amma na tashi harma nayi wanka..
Okay to ki zauna a falour ki huta zan dafa mana abinci saboda kukun mu taje ganin gida....
Cewa tayi a'a Amma kibari zanyi,
"A'a Nawaz kije ki huta"
"Don Allah Amma ki bari inyi wallahi ban gajiba" cewar Nawaz tana marairaice fuska..
"To shikenan tunda kin matsa bari na shiga ciki idan kin gama kizo ki min magana.
"To Nawaz tace sannan ta shiga kitchen ɗin....
Bayan awa biyu.......
Nawaz ce ta wanke hannu tana goge wa a duster...
Falour ta fito ta nufi fridge ta dauki ruwa, kai ruwan bakinta keda wuya taji an bude ƙofar falon an shigo.
Wata matashiyar mata ta gani wadda a shekaru bazata gaza talatin ba rike da hannun wani kyakkyawan yaro wanda shima bazai wuce shekara biyar zuwa shida ba...
Yaron ne ya kwace a hannun maman nashi yayi gurin Nawaz da gudu yana cewa "Aunty Aunty......
Mamaki abin yaba Nawaz saboda itadai bata san matar ba balle yaron, amma sai kawai itama ta buɗe wa yaron hannu ya faɗa kirjinta, take taji wata irin kaunar yaron ta shiga zuciyar ta......
Wallahi na gaji
Kuma idan ba'a yi min comments yanda ya dace ba bazanyi update gobe ba.
*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ🎀🎀*
*Episode 30*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji✍️*
Cikin falourn matar ta ƙaraso tana murmushi "sannu sister, ina Mummy take?
Mamaki ne Ya cika Nawaz, itadai tasan bata san suba amma su kuma sun nuna mata sanayya "tana ɗaki" Nawaz tace tana ci gaba da mamakin wannan lamari
Hanyar ɗakin mum bakuwar ta nufa ta shiga ɗakin...
"Da alamu waɗan nan ƴan uwa ne na jiki...
Mikewa Nawaz tayi rungume da yaron ta shiga kitchen, buɗe warmer tayi ta dibar mishi fried rice din da tayi da yam balls
Falour ta fito ta buɗe fridge ta daukar mishi fresh milk sannan ta nufi dakinta dashi...
Zama tayi ta riƙa bashi abincin a baki cikin nutsuwa har saida ya nuna mata ya ƙoshi sannan ta bashi fresh milk din yanasha da kanshi.
Bayi ta shiga ta haɗa ruwan wanka a jacuzzi Sannan ta fito ta dauki yaron, kaya ta cire ƙoshi sannan tayi cikin bayin dashi.
A ciki ta saka shi ta fara yi mishi wanka, ai nan ya fara fachal fachal da ruwan yana watsa mata..
Dariya ta fara yi itama tana watsa mishi, nan wanka ya tsaya aka fara wasan watsa ruwa...
Sai farinciki takeji dama gata mayyar yara kuma batada kannai.
Da kyar ta lallabashi ya tsaya akayi wankan sannan ta nannaɗoshi a cikin towel ta fito dashi.
Cire kayanta tayi saboda gaba ɗaya sun jiƙe sannan ta koma cikin bayin itama tayi wankan.
Fitowa tayi daga bathroom ɗin sanye da pink ɗin bathrobe gashinta a barbaje sai ɗigar ruwa yakeyi alamun ta wanke shi, ganin yaron tayi a kwance har yayi barci, itama kawai sai ta samu gefenshi ta kwanta saboda dama tanajin barcin sosai.
°
Mummy na zaune taji an turo ƙofa, bata damu da ta waiga ba saboda tasan bazai wuce Aayaan ba, ji tayi an rungumeta ta baya.
Ai da sauri ta waigo, wani irin farin ciki ne ya mamaye fuskar mummy ganin first born ɗinta tana yi mata murmushi.
"Aseey saukar yaushe? Gaskiya kin tayar min da hankali sosai yau kusan kwana shida kenan ina kiranki baya zuwa, gaskiya kada ki ƙara yimin irin haka.
"Mum kiyi hakuri ki bari mu gaisa tukuna, wallahi nayi kewarki har gani nayi jirginmu kamar baya tafiya.
"To Aseey na bari amma ai abin ne akwai farbaga, dama ace kina kusa ne sai in shirya inzo amma abu ba'a nan ƙasar ba gari i London kinga ai zuwa sai an shirya.