← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 112

Sashe 8

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallon nawaz yayi "mum wannan takici kosaina taimaka na bata?
Kallonshi mum tayi "ga mamakinshi yaji tace "to Kila itama irinkace, taimaka kabata sannan ka kaita gida......
gida kuma? Domin ji yayi Kamar ta buga mishi guduma a kirji...
mummy tace eh sarfraz ita tace zata tafi....
cewa Yayi to taci abincin tukun, shima ya Fara cin nashi hade da tunanin wace hujja zai kawo wadda zatasa mummy ta hanata tafiya yanzu....

gaba d'aya nawaz a takure take domin Saita faki idansu take ci, kuma idan bataciba sarfraz ya taka mata kafa ta kasan dining, idan takalleshi sai Yayi mata alamu da ido akan taci....

kadan taci tace ita ta koshi,
mum tace to my daughter har zaki tafi bansan sunankiba bansan wani cikakken labarinkiba kuma bakibani number wani nakiba balle infada musu cewa su kwantar da hankalinsu kina lafiya....

nawaz ta nuna sarfraz "mummy ai wannan ya sanni.
sarfraz yace mummy ni bansan taba.....

Cewa tayi shikenan,
"mummy sunana Nawaz Muhammad, kuma nice nake musu QUR'AN da fiqhu a HAYATUL ISLAM.......

da sauri safraz ya mike Yana nunata "malama Dama kece?
wallahi banganekiba...
mum tace yazaayi Kace baka gane malamarkaba?

mummy bata daɗe da Fara mana karatuba kuma bata taɓa buɗe fuskartaba kullum da niqab take zuwa..

mummy ce tayi murmushi Kace yar tawa ustaziyya ce........
nan safraz ya kwashe yanda yaga Nawaz da masu binta ya fadawa mummy kuma ya Kara da cewa kuma sunce kishiyar mamantace ta turasu
gaskiya mum bazata koma gida yanzuba tunda kinga babu Kowa a gidan, kuma zata iya kuma turo wasu su illatata

_*Matar Rasheed*_✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 8*

*🤳by oum aeyman*

Supreme writers association......

We write with the ink of era....
That's era is our ink 🖊

Kuma zata iya turo wasu daban suyi mata illa....

Mum tace hakan Yayi sannan kuma gaskiya ka faɗa saboda yanzu tana cikin riskine....

Nawaz ta shiga tunanin cewa kiyayyar umma har takai ta turo ƴan dabaa su illa tata, Tabbas tasan umma bata ƙaunarta amma bata taɓa tunanin ƙiyayyar takai hakaba....

Safraz ne ya dawo da ita Daga tunanin data keyi "kinji mommy tace bazaki koma bako❓

😔naji cewar nawaz, saboda ba Haka tasoba.....

Mummy tace yanzu yaza ayi da kannenki❓
Charaf SAFRAZ yace mum ai batada kanne ita kadai ce Kamar ni,

Murmushi mum tayi "Lallai Ashe dole kacemin kasamu kanwa.

To yanzu dai kaje ɗaki ka huta tunda Sai 1:00pm kakeda lecture koh?

"Eh mummy amma banajin barci yanzu...

nawaz dai kanta na Duke domin a takure take kuma ita da so samune tafison a barta ta tafi gida....

SAFRAZ ne yayi wa mummy signal akan ta Kalli nawaz, Kallonta tayi tace "my daughter meke damunki?

Firgigit nawaz tayi "babu komai mummy, dama dai inaso Nayi wanka ne ... Sannan inaso Nayi waya da ummi na..

Mummy tace haba dear, kibari Sai hankali ya kwanta, kada ki kirata ki tayar mata da hankali, idan ta dawo da kaina zanje gidan nayi mata bayani....

Kuma abinda nakeso dake shine ki saki jikinki Kamar kina gida, idan ma kina bukatar wani abu ga yayanki ko dalibinki sai ya siyomiki kinji?

Ɗaga Kai nawaz tayi... sannan tace "please inane bathroom d'in?
Mummy ce ta rike hannunta,"zo muje na had'a miki ruwan...

Mikewa sukayi mummy ta nufi dakinta da ita,
a Saman bed ta zaunar da ita sannan ta shiga bathroom d'in.

me nawaz zatayi inba kalloba, idanuwa ta baza 👀 tana kallon kayan alatu,

hmm masu kudi na abinda sukaga dama, abinda nawaz tace kenan a zuciyarta, domin ganin irin kudin da aka kashewa d'akin.

Mum ce ta fito, daughter shiga kiyi wankan na had'a miki ruwan.
cewa tayi "nagode mummy "sannan ta Mike ta shiga bayin
A bathtub 🛀 taga ta had'a mata ruwan zafi, gashi Sai uban kamshi yake, a gefe kuma ta ajiyemata liquid soap da towel..
ta dad'e a tsaye kafin ta shiga ta Fara wankan,

♾♾♾♾♾

a falour safraz ne zaune Yana tunanin wannan sabon al'amarin!

domin ji yake shidai bazai iya rabuwa da nawaz ba, kuma yanajin cewa muddin ya bari ta tafi gida to Lallai bashi ba kuma yin barci,

cewa Yayi dama mummy ta roketa akan cewa ta aureni (wayaga Wanda bai Isa aureba kuma yana tunanin ayi mai yanzu)

nidai gaskiya nasan son ta nakeyi koda dai ban ta'ba soyayya ba, amma Ai Ina karanta littattafan soyayya kuma Ina kallon movies ..

Allah nidai mummy zan fadawa cewa ta fadawa daddy Ina sonta,

Mummy ce ta fito ta nufo gurinshi, zama tayi a kujerar dake kallon shi "gyaran murya tayi "safraz Dan Allah kayi hakuri😔 wallahi bada gayya na mareka dazuba...

hanata karasa maganar Yayi "haba mummy yanzu aduniyar nan dama akwai abinda zakiyimin ki bani hakuri a kanshi?

Mum ta kuma cewa "wallahi safraz akwai domin na zalunceka kuma na maka kazafi saboda na zargeka akan abinda bakayiba kuma na..........

Hannunshi ya d'ora a Saman bakinta "mum keep quite pls, i don't want you to say a word again about what have been a past now...

Ni wallahi banji haushi ba, saboda laipinane daban fad'a mikiba kuma abinda kikayi, haka kowace uwa ya dace tayi hardai tanason danta ya zama na gari....

abinda yasa kuma ban fad'a miki da darenba, tsorone kuma banaso dad yasani...

Amma Insha Allah zan kiyaye gaba kuma kiyi hakuri bacin ran Dana saki.....

kukane ya subce wa mum domin irin maganganun da safraz ya fad'a mata sun kara tabbatar mata da irin tsantsar kaunar daya Ke yimata...
amma gashi ita harta zargeshi, kenan yafi sonta?

Mikewa safraz yayi ya rungumeta "Dan Allah mum kidena, banaso...
goge Kwallar tayi sannan Yayi shiru tana Duba irin Hakurin safraz....

Zama Yayi kusa da ita Yana cewa "ko kefa mum?
Dazuma Ina kallo ko abincinma baki wani ci Dayawa ba....

D'iba Yayi a spoon ya nufo bakinta dashi "mum bud'e in Kara miki kadan domin nasan baki koshiba.....
Murmushi tayi ta bud'e bakin....

♾♾♾♾♾♾♾

umma nagani zaune ta doka uban Tagumi domin Tasiu ya kirata ya bata labarin cewa wani ya taimaki nawaz..
sannan ya shaida mata abokin aikin nashi ma 'kashin hannunshi ya goce, Shikuma Yana fama da wani irin azababben ciwon Kai saka makon gusumar da mutumin ya buga Mai...

Waya ta dauka ta Kira fauziyya ta shaida mata cewa Maza Maza tazo akwai Matsala ....

ko mintuna goma ba'a yiba sai ga fauziyya...

nan umma ta zauna ta zayyanemata abinda ya faru.
shiru fauziyya tayi "to umma yanzu yaza ayi?

fauziyya wannan abin bafa karamin abu bane domin idan nawaz ta dawo zasu fadawa y'an sanda.
kuma nawaz zata fad'a cewa akwai Tasiu, kuma kinga idan Tasiu yaji duka zai iya fad'a cewa Nina turasu....

fauziyya tace "umma aini nasone kisa Wanda bata saniba.. Gashi yanzu kinga abinda ya Faru....

umma tace na shiga uku kada asirina ya tonu!
Fauziyya tace "abinda za'a yi yanzu shine ki shirya mu tafi gurin boka mufada mishi abinda ya faru, kinga in akwai abinda zaiyi ya kulle bakinta ta kasa fad'a aikinga mun samu sauki ko?

Umma harda yin wani shu'umin murmushi domin tasamu mafita....

agurguje suka shirya suka dau hanya...

♾♾♾♾♾♾♾

nawaz ta fito daga wanka, tarar da Wata sabuwar doguwar Riga orange colour da veil dinta a gefen gado...
Sannan kuma harda kayan make'up Sababbi..

lotion tadan shafa kadan tasa powder, sannan tasa matte lipstick 💄 tadansa kohl da eye liner..
Rigar ta d'aga zata sa, ga mamakinta saiga bra harda pant Sababbi a kasan rigar..

shiru tayi daga bisani ta dauka tasa, sannan ta d'ora rigan a sama...
wow! What an amazing lady?

dai dai rigar tayi mata, Kamar an gwadata...

Mirror ta karasa ta dauki comb tadan taje kanta sannan ta tufkeshi,
Veil d'in tayi Rollin a kanta sannan ta dauki wani turare hayaa tadan fesa...

rasa yanda zatayi da nata bra da pant din tayi, yanke Shawara tayi ta kaisu bathroom ta wanke tayi hanging....

Parlour ta fito a hankali domin nauyin mummy takeji....
Safraz da fuskarshi take santar kopar mummy, tana fitowa ya zuba mata ido Kamar Dan kauye yazo binni ..

ta lura da irin kallon daya Ke yi mata Amma Saita basar...

bataje dinning ba Saita zauna a couch dake tsakiyan faloun....

tashi Yayi ya koma kusa da ita, "harkin shirya?

Murmushi tayi "Eh safraz nashirya, ina mummy?

mummy tana kitchen zata dora mana lunch, kinsan ita tace batason y'an aiki wai itama yar aikin kantace..
Murmushi nawaz ta kuma yi "ai tanada gaskiya gara tayi abinta da kanta ta samu lada sannan nagama ai bakwada wani yawa.

Safraz yace eh bamada yawa, Daga ni Sai dad da mum da maiba garden ruwa Sai driver, yanzu kuma kinga mun karu koh?

murmushi tayi "nida zan koma gidanmu, ai bandani...
ji yayi Kamar ta zuba mishi ruwan zafi a zuciya...
barin yanda kayan suka Kara mata wani irin kyau kasancewarsu orange ga kuma fuskarta dayaga hartafi da yi mishi kyau....
Cewa Yayi "hmm kinzo kenan dankiji!

yar siririyar dariya tayi "to shikenan bari na je na taya ummi Au mummy girki...
Mikewa Tayi ta nufi inda take zaton nanne kitchen d'in....

bin bayanta Yayi da kallo, Hip dinta na juyawa a hankali Kamar dakanta takeyi, sannan tana tafiya a sanyaye...

cewa Yayi wallahi bazai yuwuba, nasan gidansu akwai Maza.
kenan haka Suma suke Kallonta?

Mikewa Yayi yabi bayanta, tarar da ita yayi Tana cewa "Allah mummy kibari zanyi, mum tace "to shikenan yanzu ni ki dafamin farar shinkafa da beef stew, ku kuma saiku dafa duk abinda kuke so...

safraz ne yace " to mum we will do as you said....

da sauri ya bud'e fridge ya dauko freeze beef da freeze chicken,
Murmushi mummy tayi "to agama Lapia, sannan ta juya Ta tafi.

kunna gas nawaz tayi ta dora tukunyar akan wuta sannan ta zuba naman a ciki Bayan ta wanke....
albasa ta yanka akai ta zuba curry da sauran seasoning da spicies ...
d'aya gas d'in ta kunna sannan ta d'ora sanwar ruwan shinkafar...
Chapter 8 · 0% Book details