Sashe 30
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa Nawaz jin abinda Aayaan yake faɗa take fargaba da tsoro suka kamata, durkushewa tayi a gurin tana sakin kuka, "mummy wallahi billahilazeem ban ɗaukar Miki zoben kiba, Wallahi sarfraz ne ya bani.
Ɗagota mummy tayi "yi shiru mu daughter baki daukar min komaiba na sani, shima Aayaan ɗin ne be iya bayani ba.
" I'm sorry" Abinda Aayaan yace kenan yana kallon Nawaz....
Hannunta mummy ta rike ta kaita saman sofa ta zaunar da ita.... "My daughter ki zauna anan bari naje na ɗauko Miki nawa zoben yanda Zaki fi samun nutsuwa"
Fita mummy tayi ba'a fi minti biyar ba ta dawo rike da zobe a hannunta, suko Aseey da Aayaan zaune suke babu wanda
yake iya magana burinsu nawaz ta basu labarin abinda ta sani game da zoben.
Daughter kinganshi! Sunyi kama koh?
Ciro naki mu gani ko akwai banbanci...
Da sauri Nawaz ta zare zoben a hannunta ta mikawa mummy, duddubawa mummy tayi sosai zoben irinsu daya har takai mummy bazata iya gane wannene nataba a ciki..
Hannu mummy ta haɗa guri ɗaya sannan ta durkusa "my daughter don daraja da girman Allah ki taimaka ki faɗa min gaskiyar labarin zoben nan, wallahi tun tsawon rayuwata banida addu.....
Da sauri Nawaz ta riƙe mummy tana ɗago da ita, "haba mummy meyasa zaki duƙa mini?
Kuka Mummy ta fashe dashi "don Allah ki taimaka min wallahi kullum addu'a ta bata wuce inga zoben nan da kuma wanda zoben yake a hannunshi.....
"Mummy don Allah kidena kuka, zan kaiki har gidansu SARFRAZ ɗin inyaso saimuji ko iyayensu sun san labarin zoben, amma wallahi Ni bansan komai gameda zoben ba, har gida yazo ya kawomin sanda sukayi min laifi a makaranta saboda nace bazan kuma zuwaba....
Aseey da Aayaan babu wanda ya motsa domin sun san mummy zata iyayin fiye da haka ma saboda ba'a yini guda batayi maganar zoben ba, har ce musu takeyi su riƙa lura da hannun mutane koda zasuga me irin zoben......
Sai dai duk da haka hawayene yake zuba a fuskarsu, ganin halinda mummyn ta shiga lokaci guda...
Tasowa Aayaan yayi Ya rungume Mummy "we are sorry mum, Insha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe tunda har Allah ya aiko Miki da zoben har gida...
Yanzu duk mu shirya zuwa gobe Insha Allah zamuje chan Zaria ɗin sai muji ko su iyayen sarfraz ɗin sunsan wani lamarin daya shafi zoben....
Sai lokacin itama Aseey tasa baki "mum ayi yanda Aayaan ɗin yace, mu shirya goben sai sister Nawaz ɗin ta rakamu...
"To shikenan Allah ya kaimu" cewar mummy tana goge hawayen fuskarta....
Ɗan matsawa Nawaz tayi Saboda yanda turaren Aayaan ya cika mata hanci....
As usual kallonta yayi ya ɗage duka girarsa biyu alamun tambaya..
Itakam batabi ta kansaba illa kanta data kauda gefe domin ita a yanzu ta riga da ta saba da wannan ɗabi'ar tashi....
Aseey ce ta riƙe hannun mummy "mum zo muje kici abincin da Nawaz ta dafa wallahi bakiji dadinsa ba..
Murmushi mum Tayi "to muje kinji girkin ƴar tawa ya yayi" a tare suka fita falourn harda Aayaan.
Ajiyar zuciya Nawaz ta sauke "menene alaƙar mummy da zoben nan? Hmm yanzu da ace ma na wani mugun abu ne dana Banu, daga bani abu nasa a hannu ban san kona meye ba..
Tuna a abubuwan da suka faru tsakanin ta da SARFRAZ tun daga lokacin da suka hadu har zuwa rabuwar su tayi, wata irin sabuwar damuwa ce ta ziyarci kwakwalwar kanta, a zahirin gaskiya ita dai tasan batason SARFRAZ duba data girmeshi sannan kuma tana matukar jin tausayinshi da mutunta shi, saboda daba don shiba da yanzu ita kadai tasan halinda take ciki....
Tafi minti talatin anan kwance tana tafka tana warwara, turo ƙofar da akayi ne ya dawo da ita Daga duniyar tunanin data faɗa, da sauri tasa hannu ta goge hawayen da suka gangara ta gefen fuskarta...
Ɗagowa tayi don ganin ko waye ya shigo, Aayaan tagani riƙe da waya ya nufo inda take, miƙa mata wayar yayi yana murmushi "dadynkine colonel yace yanaso kuyi magana..
A ɗarare ta amshi wayar ta kara a kunne sannan ta furta kalmar "Assalamu alaikum" cikin nutsuwa
Ta can ɓangaren colonel yace "wa'alaikis salaam daughter na, fatan kina lafia?
Murmushi tayi "lafiya lau Alhamdulillah ya aiki, yasu mama?
"Lafiya lau daughter, dama munyi magana da Aayaan ne akan nanda kwana uku zaku tawo Abujan, saboda ayi komai a gama.
"To shikenan babu komai Nagode.
"Yauwa daughter babu wata matsala koh?
"Eh babu"nawaz tace tana daɗa yin murmushi
"Okay to ba Aayaan wayar, miƙa mishi tayi sannan ta nufi hanyar bathroom, da sauri Aayaan ya riƙe mata hannu
Aikuwa don dole ta tsaya, dama ita babu abinda zatayi a bayin kawai zata shiga ne don gudun Aayaan ɗin.
Sallama sukayi da colonel ɗin Sannan yasa wayar a cikin aljihu...
"Wai meyasa kike guduna? Nawaz ta tsinci Muryar Aayaan a Cikin dodon kunnenta.
"Ko nayi kama da dodo ne?
Ita dai Nawaz har jikinta ya fara rawa as usual, kuma still ta kasa cewa komai...
"Juyo ki kalleni, ina tambayarki shine kikamin shiru?
Rau rau tayi da idonta zata fara kuka "don Allah hakuri...
"Oh gosh wai ke meyasa in cika ba mutum hakurine"
" Cewa nayi fa kawai ki juyo ki kalleni, amma sai ya zama abin kuka?
" Juyo ki kalleni! If not I will do som.......
Cikin sauri Nawaz ta juyo ta fuskanceshi amma bata kalli fuskar shi ba......
"Good girl! Tunda kin juyo to ɗago kanki ki kalleni"
Gum Nawaz tayi, ita bata ɗago ta kalle Shiba sannan kuma bata bashi amsaba.
Murmushi yayi yana ƙara matsowa sannan yace "okay then, i will do.......
Nawaz bata jira ya karasa ba ta ɗaga kanta sama ta kalleshi, Domin tasan Duk Abinda zai faɗa ma ba Mai daɗin ji bane, cikin Sa'a kuwa suka haɗa Ido
Sosai Aayaann yake kallon ƙwayar idonta wanda dama ita yakeson gani, Saboda tunda suka hadu bata bari su hada ido, illah dai ta kalli fuskar shi.
Saurin kau da idonta tayi ganin cikin ƙwayar idon Aayaan ɗin cike take da abubuwan da bata gane musu ba, sannan colour din iris ɗin shi grey ne saɓanin tata da take baka.....
Wani shu'umin murmushi Aayaan yayi, yau ya dauke duk wani abu da yakeji kuma yaga abinda yakeso ya gani, duk sanda yaga Nawaz sai yaga idonta kamar cike yake da hawaye har yake tunanin ita me yake sakata kuka koda yaushe, but yanzu ya gane ba hawayebane ashe tanada bold and oil lense ne, shine yake sawa yaga kamar hawayene a idonta.
Still kuma ganin Black iris ɗinta ya burgeshi, saboda babansu Black iris gareshi amma basuyi irin nashi ba sai sukayi irin na mummy....
Gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke sannan yace yace "i don't know why, but har dai ina tare dake nakan jini cikin nishaɗi sannan nakan manta komai,
So yanzu ki samo min amsar wannan, zuwa gobe kafin mutafi zan tambayeki.
Wani shu'umin murmushin ya daɗa sakin mata sannan yayi hanyar fita yana cewa "You are so special and different..
Nawaz sumar tsaye tayi saboda maganganun sunyi mata nauyi sannan ga wani abu daya kuma sata, wai ta nemo mishi meyasa yakejin nishaɗi duk sanda suke tare.
Lallai wannan kakan sarfraz ne a Rashin ta ido, wato shine yake jin abu amma ita zata nemo mishi amsa, Tabb wallahi wannan ɗan rainin sense ne....
Komawa tayi ta zauna a gefen gado, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, ita wallahi zaman gidan nan ya isheta, ga kuma wani uban tsoron maza da yake ƙara ɗarsuwa a Cikin zuciyarta...
Tsaki tayi sannan ta shige bayi....
°
Aayann kuma koda ya koma ɗaki kasa yin komai yayi "ya faɗa duniyar tunani, shidai tun first time da yaga Nawaz yaji ta burgeshi yanda tayi jarumtar guduwa daga hannun ƴan ta'addan nan, yanaso yaga mace self difendent balle yanzu daya zauna da ita ya ƙara sanin halayanta.
Ya lura bata son magana, kuma ta cika tsoro da jin kunya, tanada son yara bugu da ƙari kuma akwai kyautatawa duk wanda ya raɓeta...
Murmushi yayi yana tuna tsoro irin na Nawaz, dramar da suka gamayi yanzu ne taketa dawo mishi.
Sai kuma ya ɓata fuska "but zanyi missing ɗinta idan ta koma gida"
Take yaji wata irin fargaba ta dirar mishi a zuciya, ga wani bugawa da kirjinshi yakeyi da sauri da sauri, mamaki abin ya bashi domin be taɓa tsintar kanshi a irin wannan halin ba.
°
Koda Nawaz ta fito daga wanka guri ta samu ta zauna bata wani yi kwalliya ba illa dai ta tashi ta samu yar doguwar riga mara nauyi ta saka,
Sannan ta ɗora hijab akai tayi sallah, falour ta fita ta shiga kitchen ta ɗebo abinda zatasa a bakinta saboda bata ci abinci ba tun wanda suka ci a gidansu baffa kafin su tawo..
A tsakiyar falour sukayi kiciɓis da Aseey itama zataje kitchen ɗin "A'a sister har kin tashi daga barcin?
Murmushi tayi bata Bata amsaba sai tace ina muhsien?
"Ai tun ɗazu dayayi barci be tashiba, yana can shida Mummy..
Murmushi Nawaz ta kumayi "Allah sarki ai Gara ya huta, barin gobema zamu kuma ɗaukar wata tafiyar mai tsawo..
Nawaz nakai aya Aayaan yana fitowa daga ɗaki, da sauri ta nufi hanyar dakinta har tana hardewa...
Sakin baki Aseey tayi , meke faruwa tsakanin waɗan nan kuma, kamar tsoronshi takeji fa?
Shiko Aayaan sanin saboda shi ta nufi hanyar ɗaki yasa da sauri yace "sister please kada ki shiga ɗakin nan, don Allah zoki haɗa min smoothie ɗin da kika haɗa wa muhsien ɗazu...
Ja tayi ta tsaya sai kuma a hankali ta juyo ta nufi hanyar kitchen ɗin, ajiye abincin tayi a saman center table ɗin dake tsakiyar ɗakin tayi zata shiga kitchen ɗin...
Dakatar da ita Aseey tayi "zauna kici abincin kafin kiyi koma meya saki, ɗazu bashi ya shanye na muhsien ɗin ba ....
Da sauri Aayaan yace ayya bansan abinci zata ciba, kawai ma ta barshi haɗe da karasowa cikin tsakiyar faloun yana zama a two sitters couch ɗin dake kallon center Nawaz....
Nawaz dai cewa Aseey tayi auntie bari na haɗa mishi ai babu wahala, kinga sai in tafi ɗakin gaba daya inaso na kwanta....