← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 112

Sashe 111

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin mamaki su Naufal ne suka fara shigowa, fudail ne yayi sauri ya sunkuci akoke, shikuma Naufal ya ɗauki Mumtaz tare da cewa "ai sai kayi! duka dai mata ne balle kace"
Duk halin da Nawaz take ciki saida murmushi ya kufce mata, wato dai su ƴan biyu sai dai a barsu, ko sun girma sai sunyi wannan fadan nasu na gado.

Mum da dad ne suka biyo baya, "Au daga Zuwan yara duniya zaku fara wajiga su ko? To duka ku ajiyesu" cewar dad yana nufar inda Nawaz take
" Sannu daughter na, yanzu za'a kawo miki farfesun kajin danasa ayi Miki, fatan zakici?"
Rufe ido Nawaz tayi don kunya, ita kuma mummy ajiye flask ɗin Ruwan zafin dasu Naufal suka tawo dasu tayi tare da basket ɗin da suka zubo kayan tea, a gurguje ta haɗa wa Nawaz ɗin tea me kauri Sannan ta mika wa Aayaan tace ya bata tasha,

A Hakan ma su Naufal sai musu sukeyi wai kowa sai dai yace tashi tafi kyau, mummy ko tanaso ta gansu amma kunya ta hanata amsa, Daddy ne ya lura da hakan "kai ku kawo yaran nan muma mu gansu,
Amsar ta hannun Naufal mummy tayi shima Daddy ya amshi ta hannu Fudail.
Sanda Mummy tayi arba da fuskar yaran saida gabanta ya fadi, Domin sak kama sukayi mata da Aayaan sanda yana jinjiri sai dai waɗan nan sunfi Aayaan fari duba da farin Nawaz suka kwaso.

Shi dai Aayaan tunda ya lura yaran kalau suke saiya Maida hankalinshi duka akan Nawaz....

Basu suka koma gida ba sai bayan magrib, achan gidan har wasu sunzo waɗan da basuda nisa musamman Yan uwan dad da suke Abuja.
Basu daɗe da komawa ba saiga tawagar mummyn Sarfraz da Sarfraz ɗin harda Hajiya hassu😉 dasu bandi, da mamanta., Aseey kuwa ta kira yafi sau Goma,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta iso acikin daren.

Cikin yan kwanaki gaba ɗaya gidan ya cika da mutane ta ɓangare daban daban, yara kuwa daga nan sai chan danma su Naufal sun kasa sun tsare akan kada a wahalar musu da mata, shima Aayaan Saida Mummy ta wanke shi fess sannan ya samawa Nawaz lafiya, amma da yana nakiƙe da ita duk Yan Barka ma anan suke tarar da shi.

Sosai mummyn Sarfraz take kula da Nawaz, abinci take tasa mata agaba saita cinye, sannan ga tea, ga farfesun naman rago da Daddy colonel yasa akeyi mata kullum, suma su Naufal kullum da babbar ledarsu ta Kayan marmari idan suka fita yawo tare dasu Sarfraz da bandi,wai duk na toshiyar baki.

Ana gobe suna kuwa gidan babu masaka tsinke, kowa ya hallara harda su inna talatu dasu jamila da Fauziyya, sosai suka Yadda da kalmar *hassada gamai rabo taki ce* ganin Irin gidan da Nawaz ɗin take Aure, sanda kuwa sukaga yadda Aayaan yake nan nan da Nawaz Saida sukaji kamar ƙasa ta tsage su shige.

Akwati biyar Mummy tayiwa Nawaz da yaran na fitar suna, ita kuma Aseey uku sai Daddy colonel shima biyar, kuma shi ya ɗauki nauyin yanka, kowa rago da tunkiya ga kuma manyan shanu guda biyu.

Mai gayyah kuwa wato Aayaan, Aishi akwatin ishirin yayi, Nawaz goma yaran kowa biyar biyar, sannan ya gwangwaje su duka da sarkokin zinare da abun hannu da zobuna.

Kowa sai baza ido yake yana kallon arziƙi a inda yake.

Ranar suna kuwa Nawaz haka ta zama kamar wata tauraruwa, duk inda tayi ido na Binta, wasu najin daɗi wasu na cewa dama sune wasu kuwa haushi sukeji don babu halin nunawa ne.

Sai shiga take tana fita cikin manya manyan leshina saƙar ƙasar swiss da Australia waɗanda daka kallesu zasu bayyanar maka da kudinsu a fili, taro yayi taro babu wanda be halarta ba sai wadanda ba'a rasa ba, kamar ummin Nawaz, ita dinma anyi anyi tazo tace bazata iyaba ita kunya takeji, wai bayan suna zata je taga kishiyoyinta, sai umma wadda jikinta ne yasa batajeba itama.

An raba kyaututtuka kamar ba'a san zafin kuɗi ba, inda wasu daga ciki sarfraz ne ya ɗauki nauyinsu jin ansa sunan mahaifiyarsa, sai Mummyn Sarfraz da Aseey.

Mutane kowa sai san barka, kowa da Atampopinshi da jakunkuna da bokitai iri iri, Mumtaz da Rahma (anyiwa Nawaz kara akasa sunan mamanta) sunyi goshi sosai inda ake ta turo musu da kyautar kuɗaɗe da kayayyaki har daga wajen Nigeria.

Taro ya watse Lafiya inda washe gari kowa yayi haramar komawa gida, a hankali gidan ya dawo dai dai sai na jiki sosai suka rage, irinsu Aseey dasu Sarfraz da Mummyn Sarfraz, su Jamila da Fauziyya ma suna nan Saboda mummy tace su tsaya sai su koma tare dasu Sarfraz.

Kuka Sosai Nawaz ta riƙa yi sanda Aayaan ya bata takardun kamfanin abaya ɗin shi dake Dubai yace ya mallaka mata halak malak tukuicin twins data bashi, suma duka saida ya Mallaka musu nasu ɗai ɗai.

"Wannan wane Irin abu ne yaya, Company pa kacokan fa!"

"Hhhhhh sweetheart nifa dariya kike bani, wai kin manta abubuwan dake kika mallaka min ne? Ko akwai injin dake haɗa yara ne? Kuma akwai inda kike tunanin zan samu natsuwa ne bayan gurinki, nifa ke nake kauna kuma ke nake so, ke nake sha'awa kuma ke kike birgeni, bani da wani burin daya wuce na ganki cikin farin ciki da walwala...."

Rungumeshi tayi tanata jero mishi addu'oi da godiya.

Haka Nawaz taci gaba da jegon ta cike da
kulawa tako wane ɓangare, abinci me cike da lafiya da gina jiki ake bata, shiyasa tayi fess abinta yan biyu ma sam babu me cewa guda biyu ne domin sunyi kuɓul kuɓul abinsu.

Gaba daya babu abinda takeyi saboda Daddy colonel ya ɗauko kanwarshi ita keyi wa Nawaz ɗin wanka da yaran, kuma da'an shiryasu su Naufal zasu ɗaukesu sai dai in anzo basu nono.

Bayan suna da kwana biyar Mummy ta turawa Aunty khatoume kuɗi tace ta tawo tazo tayiwa Nawaz gyara har tayi arba'in.

Nawaz mamakin irin kaunar da mummy takeyi mata take, Saboda wasu iyayen mijin sam babu ruwansu da matar ɗa, kuma ko labari sukaji kan cewa tana shan magungunan gyaran jiki faɗa akeyi dasu, saboda cewa sukeyi zata mallake musu ɗa, Amma ita Mummy da kanta take sawa ayi mata.

Bayan zuwan Aunty khatoume da kwana uku ne aka nemi su Aayaan tare da colonel.

Ansha fama Kafin ya tafi, mummy ma daɗin tafiyarsu taji saboda tasan Aayaan hanasu sakat zaiyi, kuma itama zata dan samu damar da zata ƙara gyara kanta wa Colonel, domin bajintar da yayi a sunan Nawaz ko ɗan daya haifa a cikinshi yayiwa haka sai an yaba mishi balle kuma.

Shima colonel saida mummy tayita fama Sannan suka tafi.
Koda suka tafi basu saniba ashe an haɗa musu walimar ƙarin girma ne, inda shima Aayaan an cire sunanshi daga cikin masu zuwa yaki sai dai yanzu ya riƙa yin training ɗin wasu.

Saida sukayi sati Uku tukuna suka dawo, shima da kyar domin Dukansu ji sukeyi kamar suyi tsuntsuwa su tawo gurin matansu.

Ranar da suka dawo saura kwana uku Nawaz tayi arba'in, gaba ɗaya Aayaan rudewa yayi da yaga yanda Nawaz ta koma, ga ƴan biyu sunyi manya-manyan abinsu kamar sunyi wata uku, kana musu wasa zasu hau yi maka dariya.

Yadda Aayaan ke rawar ƙafa a kan Nawaz yasa Mummy tasa aka kulleta tasan sarai saiya maida musu da aiki baya kuma saura kwana uku a gama.

Aayaan kuwa kamar yayi hauka haka ya koma, babu yadda beyiba akan Mummy tayi hakuri amma sam taki kallonshi.

Kuma a ranar data cika arba'in ɗin suka daga zuwa maiduguri Saboda Nawaz ɗin tayi yawon arba'in, saida Nawaz ɗin tayi sati tana yawo gidajen ƴan uwa kama daga dangin daddyn Aayaan danata kakannin, haƙurin Aayaan karewa yayi yai tafiyar shi basusanma inda yake ba.

Daga nan ne kuma suka koma Zaria, Ummin Nawaz taji daɗi Sosai ganin yarta ta koma Babbar mace Sosai, kuma kowa ya kalleta yasan tana cikin kwanciyar hankali.
Shima Abban ta haka yaketa nan nan da ita, kuma ƴan biyu kullum suna gurinshi.

Kwananta biyu a gida saiga Aayaan yazo, domin yayi yayi amma ya kasa daurewa daga nisantarta da yayi.

Ganin hakan nema yasa Abban Nawaz ɗin yace su shirya su koma, saida suka biya gidan mummyn Sarfraz itama sukayi mata kwana ɗaya, hassu da Sarfraz sai santin Yan biyu sukeyi, barinma Sarfraz yaji labari.

Suna dira a Abuja Aayaan yace shifa Allah ya kasheshi sai an bashi matarshi sun koma england domin yama rigada ya sayi ticket kuma gobe da safe jirgin zai tashi.

Mummy ce tace bazata koma ba sai Yan biyu sunyi Kwari, misali koda wata huɗu ne suyi.

Ganin abinfa na Mummy da gaske take yasa Colonel yace wa Aayaan ya ɗauki matarshi su koma, domin yasan Aayaan ɗin yayi ƙoƙari.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ENGLAND.......*

Koda suka sauka a England ɗin sai Aayaan yayi banza da ita, wai shi ala dole fushi yakeyi da ita, ita kuma Nawaz da taga haka sai itama ta shareshi domin yanzu tsoronshi takeji kada ta kuma samun wani cikin (niko matar Rasheed nace dama ya lafiyar kura balle tayi hauka?)

Dafa yaga taƙi bi takanshi sai shi ya sauka, tana kitchen tana haɗa lunch saboda dama suna sauka a ƙasar ya samo musu wata baturiya me raino ya bata ɗaya sasan su, idan ba kuka suka yi ba bazata kawo suba.

Kama kwankwasonta yayi ya ɗora kanshi a saman kafadar ta, "dear yanzu sam baki damu dani ba ko?"
Kafin tace komai wannan mayen kamshin nata ya cika mishi hanci, take yaji abinda yakeji akanta ya ninku.

"Bakai bane kahau yin fushi daniba kuma bayan Ni ban san me nayi maka ba"

"Cikin muryarshi wadda ta fara chanza yanayi yace okay to na dena kuma kiyi haƙuri"

"Okay Babu komai, ya wuce?"

Kama hannunta yayi"zo muje kiga wasu files"

"Yaya ka bari na gama girkin kaji"

Be jira komai ba yasa hannu ya kashe gas ɗin Sannan ya ciccibeta yayi waje.

Koda suka je ɗakin babu wasu files daya nuna Mata illah susuce mata da yayi, cikin ɗan tsoro tsoro Nawaz tace "yaya pls fa! Kaga su mamaa two months suke fa?"
Ganin bazata yarda ba yasa yayi mata kwance kwance ya kashe mata jiki yadda kome zaiyi bazata musa mishi ba,
Chapter 111 · 0% Book details